Sashe 18
Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Basma ta sa yatsa a Baki,Arham yace ke tun yanzu ba abinda zan miki wannan romantic sign ne bazan taba komai ba cire yatsanki,Spark kansa ya Dora a kafadar Naila Yana dariya,Basma ta turo baki tace to ai ni tunda nazo ban fita gari ba ban San me ake yi a garinku ba,ana gudu ba ayi ana Waka ba ayi ni Ina zan sani tunda a gida nake,Arham yace shagwaba zaki min ke Yar nan baki tafasa ba zaki Kone,Allah ya kiyaye na Maka shagwaba ni Ina na iya shagwaba,ni sirrina ma baza a sani ba Allah ya kiyaye kayi kadan kadan kasan sirri na,Arham yace ke Nan har sirri ne dake? rufa min asiri na San sirrinki yanzu ni Ina a'a ba haka nake ba ni sanin sirrin ya mace ai sai an shiga daga ciki,Basma bata gane ba tace to ni bazan shiga ciki da Kai ba,Arham yace nima haka Hallareta tana cikin rufin asirinta ba gardiyar da zata ganta,Basma Ashe tana Jin yaren tasan Hallare da fillanci,tsalle tayi tana dariya wlh yasan sunanta idan ba wannan Dan iska bane Allah ya Kona ni Dan iska ne,kana birni kasan Sunan abarku,yeeee Dan iska za a aura min ta tafi da gudu tayi cikin daki tana neman Mima zata fada mata,Bata ga Mima ba ta fito ta fice,Arham ya ja tsaki yace ta zaci tsoron magana nake agaban Mima Hallare Dan na fada mene ko Naila tana ganin ta Spark,Spark yace uhm uhm wlh kasan halina zan sa a kulleka a guard room wlh,kowa yasan tana gani mene sai ka fada tana ganin abarta ai an sani,Shaheed Yana zaune a gefe Yana ta dariya yace au abarta ce to a yanke a bata mu gani,Mufee basa wajen sun tashi tuni tare da Naila,basu San me Arham suke ba.
Mufee ce ta Kalli Naila tace Aunty Naila wai ni wannan da akace Dan gidan Sudan ne ya sunansa ne? Naila tace Haidar? Ae Dan Uwan Ikhram din Rafeeq fa,shine dai Haidar din,tace gaskiya ba karya mashaallah,ko dai kina ciki ne Mufee? Naila ta tambaya,Mufee tace uhm ni Ina zan so namiji Bai ce yana so na ba Allah ya kiyaye,Naila tace in yazo fa? In yazo ai Kinga mutum bazai ki mutum ba,dariya Naila tayi tace kyaji da shi.
Basma ce ta shiga part din Papa a nutse tace Mima kizo,Baki nayi? A'a nice nake nemanki zo ki gani,Mima ta taso ta zaci wani muhimmin Abu ne,suka taho tiryan tiryan har parlo ta nuna Arham tace Mima ki yiwa danki fada Dan iska ne dazu Sunan abarsu ya fada da wani yaren Yana bahaushe har ya Kai ya San sunanta da wani yare,Mima tace me? Abarsu ta fitsari mana ya Fadi sunanta kiri kiri da wani yaren Fulani Kuma Bai San na sani ba Ina Jin yaren ,ai sai Dan iska ko? Spark Yana jinsu yace Mima kizo in ganki tafiya zanyi ni,Basma tace Kuma ma Yaya Spark yaji sanda ya fada duk suna dakin nan babu Wanda ya Masa fada cewar Basma,Mima tace dole ayi Masa fada gaskiya,Arham Yana zaune ko a jikinsa,Spark Mima yayiwa magana na yan mintuna a gefe ya fice ya tafi,Mima ta juya zata tafi Arham ya Kalli Basma yace Enduu,hannaye ta Dora a Kai tace ya Kuma iskanci ya kuma iskanci wlh ya Fadi Sunan nono Mima,Mima baki ta bige mata,Basma tace ba nonon saniya ya fada ba na mutum ya fada,tsaki Mima ta ja ta harari Arham ta fice tace ki bari Basma zanyi maganinsa,tace to ta juya ta shige bedroom tana cewa wlh Dan iskan Miji ne nawa ni wayyo ni Kam na boni.
Jibson ne ya shugo dauke da ledar nama biyu ya fara mikawa uwarsa mahaifiya nata sannan ya shiga da nasu ciki,Hanan wacce tayi kiba ta Kara kyau ta Masa sannu da zuwa ta mika hannu zata karbi ledar yace a'a ba sai kin karba ba zan ma bude mana muci,Hanan tace uhm sabo da nama ne,bana son Zalama kullum Naman nan sai kin ci fa daga dawowa sai kice ledar ma sai kin karba ai abin zai miki yawa ga sannu da zuwa kin yi min Kuma ace Leda ma sai kin karba kina Amarya kyale na ajiye na karasa sauran aikin kin San Ina kaunarki,Hanan tasan duk kawo nama haka yake yi amma Kuma a banza kullum sai anci,sai Hanan tayi zuciya ya bude Naman kaza gasashiya yace to taho,Hanan tace na koshi,murmushi yayi ya kalleta yace Allah? Tace bana ci,yace na gode miki Allah ya saka da Alkhairi,yaci gaba da dumurmusar namansa,Hanan ta tuna da Mohsin shi me hankali da shi ba irin Jibson ba,takaici ya kamata ta auri shashashan miji...tashi tayi ta zauna ta fara cin kazar taga ba ruwansa shi.
Abba kwance yake a Saman katifarsa a shago wani yazo siyan wake,Ya mike ya zauna yace yawwa da Allah jawo min daron waken can,me siyan kaya yace Kai sai kace mace marar lafiya,kullum sai kana zaune ko a kwance yanzu kwanon waken ma sai na jawo maka,Abba ya mike yace duk abinda za a sa mutum ya tashi sai an nemo shi,ya auna Masa ya tafi abinsa,Abinci aka Aiko Zarah ta kawo Masa,yace har an gama girkin ranar? tace ae" to kice nace Allah ya mata albarka da take gama girki da wuri,Zarah tace to ta tafi,tana zuwa tace Umma yace Allah ya miki Albarka da kike gama girki da wuri,Yar Inna tace Ameen,bude Abincin yayi yaga shinkafa da Miya harda nama ga couslow an hada a mazubi dabam,yace bari naci sai na tafi Sallah da karfi na,ya zuba a plate ya fara ci yaji yace Kai kayan miyar nan anyi dacen su,ko dai Yar Inna ce ko kayan miyar akwai sa hannun Daya a ciki wajen bada wannan dandano.
Wayarsa ya jawo ya kira Yar Inna ta daga tace wani abin za a kawo Maka? Yace a'a girkin ne yayi dadi shine nace bari naji kayan a miyar ne ko kuwa a kece ko Naman Dabbar ne taji kiwo haka? Yar Inna tayi murmushi tace a nice,tsohon hannu wasa ne,Abba yace na yarda yau ni zan tsefe miki kitson nan sabo da kin gama dani da girkinki,tace idan yara sun tafi makaranta ba,yace ae ai suna tafiya zanzo na warware miki kitson tace to,yace Kuma saloon zamu je,Kubra tayi dariya tace tunda akwai kudi ai sai muje,yace ni da nake da Naila da Mohsin ga Hidaya itama ta taka Leda kina gani dai Yar tatsitsiya Hidaya har ta rikita mijinta Dan banza kullum sai ya kirani kullum a waya wai gaisuwa ai nasan Bata Allah bace Yar Hidaya ta aka samu ana ta kwalbe ta,dariya Kubra tayi tace Kai dai komai sai ka fada baza ka barshi a ranka ba,yace wlh bazan barshi a raina ya kashe ni ba,Yar Hidaya ta ce ya samu bagas,kullum Abba Ina Kwana Abba ina yini sai kace na gari bayan Yana Nan kullum sai yaga tsirara,ni ba mutuncinsa nake gani ba tunda nasan me yake yiwa 'yata,Umma tace Yar taka ai itama kasan me take yi ne,irin su Hidaya hmmm,shi ya koya mata cewar Abba fitsararre.
Yara suna tafiya makaranta Abba ya dawo ya zauna ya hau Warwarewa Yar Inna kitso da cumb harda rufe gidan kar ayi musu zuwan titse,Yana gamawa yace mu tafi wajen Chinaza ta wanke miki,Yar Inna ta shirya ta sa mayafi Abba yace kinyi local da yawa kamar ba kece uwar Naila da Mohsin ba saka Abaya,Kubra tayi dariya ta canja Abaya baka da mayafi yace yanzu kika fito a matar manya,baza a zaci nine mijinki ba fa an ganni Dan firit sai Kuma aga nine, dole mutane suce na cuce su,na yiwa masu kudi bakin ciki gaskiya,dole masu mota su dinga Jin haushi na a layin nan,Kuma a banza aka bani ke sadaki dubu daya,gashi a iya jikinki na Mori billions ai ni naci riba,Yar Inna tace muje Dan Allah ni ga Baby dauke ta,Abba ya dauki yarsu karama suka fito,Gidan suka kulle.
Beauty ce tayi parking da sabuwar motarta da babanta ya canja mata,ta fito da katon cikinta,Abba yace ya kamata ki daina fita yanzu,Beauty tace na gaji da Zama Abba,Ina zaku je ne? Abba yace Saloon zan kaita,Beauty ta boye dariyarta ita Kam birgeta suke yi,tace to gashi nazo Kuma,yace to akan kinzo sai mu fasa zuwa Inda muka yi niyya ga key ki jira mu,Umma tace ba Nisa Beauty kinji yanzu zamu dawo,tace to na kaiku a mota mana Nima daga Nan sai a wanke min gashin,Abba yace a'a mu a kafa zamu tafi muna hirar mu,Kuma baza a kwaiwaye mu ba,kije wani wajen ayi miki naki kalar,Ina wajen za ayiwa Yar Inna ni zan tsaya kallon na suruka ta ne,Beauty tayi dariya kamar me tace Abba in aka mata sai ku fita ku shiga mota idan aka yi min sai mu taho gida,Abba yace to mijinki ya sani ne? Tace ba matsala zai yafe ma,Yace haka ake so kinyi kokari gwara ki dinga juya shi,motar suka shiga,Yar Inna ta shiga gaba Abba yace sai dai ki dawo baya sai a barni a bayan mota kamar birin turawa.