← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 68

Sashe 10

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Spark ya dafa kafadarta yace ban gane gidanki ba? ta Ina? dariya suka yi ya rike mata jakar har mota chewgum ya sa mata a baki guda Daya Shima Yana cin nasa,driver ne yake tuka su suna bayan mota abinsu,Naila tace Baby" ya amsa na'am Baby,wayarta me tsada iphone ta nuna Masa tace kaga wasu takalma latest a siya min ta nuna Masa,ya gama kalla yace sabo da ga me rijiyar kudi ko,har yaushe aka siya wasu har yanzu na lefe Baki gama saka wasu ba kika ce a siya miki wasu ban damu ba na siya miki yanzu wannan me za ayi da su,bazan siya ba sabo da samun waje Kinga mutane da yawa akwai Wanda suka kwana da yunwa wlh bazan siya ba gwara naje nayi sadaka da kudin,yanzu ma na ware wasu kudi a iya Yan uwa da abokan arziki sai sun kare a taimako, Naila ta Harare shi ta dauke Kai tace zaka zo ne,yace Inzo din"yana dariya,buga kudi nake yi,in ana aiki ba a baki Hallare ba kin dinga korafi kenan ke an daina sonki.

Naila tace to tunda baza ka siya ba sai ka kyaleni Kuma ai,tace ga Data can in zaki ci a siya miki na Naira dari dai ya isheki ko dabino ma kin gani fresh one,Naila ta Masa banza yace Nidai bazan siya ba Kuma sai anyi fara'a dole ya girgiza mata kafada ba shiri tayi dariya,yace ko kefa wayarsa ya zaro ya nuna mata motoci masu kyau Yan 8m zuwa 10m,yace mota zan siya sabuwa zabar min,Naila baki ta tabe tace ai ku son kai ya muku yawa idan kanku ne yanzu za aji Kuna kashe kudi banda matan ku,yace naji nidai zabar min,ta nuna wata baka Yar 10m tace wannan tayi duk tafi birgeni,yace okay,Gidansu suka je suka samu Mima da Mummy suna kallo har yau Mummy taki komawa gidanta,Spark ya nufi wajen Mummy ya gaishe ta ya zauna kusa da ita,ya kalleta yace Uwa ta,tace na'am nice nan gani,Naila Mima ta gaisar sannan Mummy ta zauna tana cewa Ina su Arham? Mima tace suna nan zaki gansu yanzu kuwa.

Spark Mima ya gaisar yace wai kina nema na? Mima tace dama gidan Badia nake so kuje Dan Allah ai dai Kwa dan Kai matan naku,na fadawa Misam da Rafeeq ma,Spark yace ba damuwa, da gidan Anam da Khalil,Spark yace ba matsala za muje Inshaallah.
Arham ne ya shugo palon da cup a hannunsa sanye cikin 3qtr da Yar t-shirt dinsa ga uwar suma,Mufee ce ta fito da gudu tace wlh Mima kice Yaya Arham ya bani abina,Arham yace me? Mima tace kaga bata abinta komai mene,cup din ya mika mata yace gashi kina Sha yau sai kin kwana kina zawo munafuka.

Spark ya mikawa Hannu yace Ina me dakin taka,ya juyo ya Kalli Naila yace Me daki,Naila tace kayi kudi ka guje mu,yace zanzo ne ai kwana zanyi,Spark yace a Ina? Kana da gidan Uba wai ni na haife ku ne? Kun takura min fa,Arham yace wlh sai na zo tunda kayi gida da dakuna ai da baka son mutane sai kayi 2room and parlo,in Kun gaji dani ayi min aure,babu me sake aure a gidan nan sai Nan da 4yrs mun gaji,Arham yace za kuwa kuji bikina kwana nan,Mummy tace wannan Kai banda sakin aure me zaka iya,wa zai Maka aure yanzu me ka sani a duniyar 26yrs in banda ma kayi saurin girma yaushe amma gaka Nan Kai da Rafeeq kanku daya,Shima Shaheed din haka,Arham yace abin ne ya matso ya za ayi dani,Junior ne kawai ba ruwansa,Me balagar zuci cewar Arham ai ya Dade da balaga a zuciyarsa,Spark yace Arham zo na aikeka,Ni bani da zuwa a karami ba kowa ya taso da aikensa sai dai yace Arham,an haifo ni a karami Mima me yasa ba ayi kwazo ba a kaina,Mima ta mike tace Kai ni wai sa'arka ce,wai ni wannan yaro kuwa shine kuwa a mahaifata sanda Ina da ciki ba canji aka min ba,Mummy tayi dariya tace ato in kin San babu addua aka yi dai kiyi magana tun wuri,Mima ce ta harari Mummy tace Allah ya sawwake miki a gaban danki,Spark yace a'a'a'a tayi maganarta me za a boye min nasan white and black,Naila tuni ita tabi Arham sun tafi wajen Papa.

Suna zuwa a bedroom suka same shi,Arham yace Papa gata na kawo Maka samfur ka gani irinta zaka samo min,Papa baiyi niyyar dariya ba sai da ya Dara yace to Arham ni da aka bani zabi sai an kawo min samfur,gwara da samfur ku yanzu idonku yayi dishi dishi kar a dakko min wata Choco milo ace ana so nayi biyayya wlh bazan yi ba,Papa yace to dama Bada zuciya daya kace ba ko,nidai irin wannan Papa irinta Inda hali har Sunan so nake na nunawa Yaya Spark Nima fa yes ae,sannan Papa ka bani jari na kirki kaga dai mu a gabanka muka taso Dan Allah kar a barmu da talauci,Papa a dube mu a bamu jari,Papa yace to Arham za a duba ka dinga tuna min yace to Allah ya Kara arziki,Naila tana dariya kasa kasa tana durkushe ta gaisar da Papa ya amsa da fara'a,yace bakya zuwa kwana biyu ki dinga zuwa kinji,Naila tace to,shi Papa ba ruwansa dan tashi kullum azo gidan,Arham yace Papa Dan Allah ka yiwa Yaya Spark fada ya barta tayi karatu,ko bata yi aiki ba ai karatu Yana da dadi tunda dai zamani yazo a barta tayi ko part-time sai ta gama degree dinta a saukake Friday,Saturday Sunday ai yayi,Kuma ma yanzu ga private da yawa ba wahala an gama karatu in da kudi,gaskiya ka fada Masa ya barta,duk su Ikhram tayi degree ita,Chika ta kusa gamawa ga Misam naji yace zai maidata ta karasa ita sabo da mayata ya hanata,Papa yace bai kyauta ba zan Masa magana.
Naila taji dadin maganar Arham ya taimaketa sosai yau ya birgeta,suna fitowa tace Inama Zarah kanwata ta girma da na baka ita wlh,Arham yace Bada ni ba baza ku Kara mallake ni ba Kun mallake Spark Nima a shanye ni,a wajen ku zamu kare,wani Jinin zan dakko daban can dangin wasu zan samo tawa,Zarah a auren kauye ta Isa mana amma Bata da kudi,kudin kirjinta basu girma ba wannan ana tabawa zata fara kuka wayyo ka fama min,ka fama min,Naila ta dinga sheka dariya tace Allah ya shiryeka Arham ta juya zata tafi suka ci karo da Spark,yace me kuke cewa haka sai faman dariya kuke Allah yasa ba batsa yake koya miki ba,Arham yace na koya mata ko ta koya min,wurin Papa ya wuce,bayan sun gaisa Papa yace me yasa baza ka bar Naila ta koma makaranta ba ne? Spark yace ni bana so wani Boko,Papa yace a'a ka barta tayi makaranta part-time ma ta Isa a hankali sai ta gama tunda zamani ne ba sai anyi aiki ba, shi Ilimi dadi gare shi,Ya dinga lallaba Spark da kyar ya yarda yace shike nan tunda kace zan sata amma in ana so a bata tsaro, a bani sojoji nata daban su kaita su dakkota,idan Ina free na dakkota na kaita,in sun kaita Kuma su jira a tashi a dakkota,Papa yace wai matarka kai tafi ta kowa ne? ni tafi ta kowa a wajena,karya kake bata fi tawa ba,Spark yace to ka sa Mima na sa Naila aga wa zai cinye zabe,tashi kaje karka dameni Kai kullum bakinka baya rasa magana,ka tabbatar ka sata a school,Spark yace to ya fito Yana Harare Harare ance ya sa Naila a school,yayi niyya su yini amma ya fasa yace taso mu tafi gida ke,ana so a hanani Kwalbewa ko wanne time shike nan kullum na dawo gida matar tana makaranta mene amfanin haka.

Naila tana jinsa tayi mukus,yace kinyi shuru,tace ban San akan me kake magana ba,karya ne kin sani kunje Kun hada min makarkashiya wajen Papa,Naila tace ta me? Ni ba ruwana gaskiya,suna komawa gida taga motar da ta zaba dazu a waya,tace wai har an kawo motar, Suna fitowa me gadi yazo ya bashi key din sabuwar motar,budewa yayi ya shiga ya kunna motar yaji zam zam,Naila ta zaga ta shiga gaba tana murna tace munyi mota gaskiya tayi kyau,key din ya cire ya riko hannunta ya sa mata key din a tafin hannunta yace gashi taki ce halak Malak na siya miki,Naila tace na'am? Yace ae taki ce,Naila rasa me zata ce tayi,tace ni Tantiriya yau nice da mota ta fada Jikin Spark.

Tace Innalillahi.... Tantiriya tayi mota,Naila da mota,Jamilu Terror wayyo Abba,Yaya Mohsin kuzo,Umma Yarki tayi car sulluwa,Abba Yarka tayi sulluwa,Spark Yana Jin dadi ya gama birge Naila yau,jikinsa ta fada ta kankame shi tana murna,tace babbar yarinya a Abuja za a gatabara kowa ya Adana yaronsa ba ruwana horn da gadara in na sha kwana duk Wanda bai matsa ba babu ruwana,ni da nake da Ashraf Spark,Spark yace ni daina wannan sambatun muje ki bani Bado shine kawai nasan kinji dadin kyautar, Naila tace Kutmar....kai...muje ciki,Spark yayi dariya sai ya tuna sanda take prison yanda tayi maganar sak yanda take yi a prison,tace muje yau har fish style sai munyi,Spark yace a Ina kika taba ganin na kifi? Naila tace na gano ni yau zaka gani,muje yau bado idan zai koma ragadada ba ruwana,Nima yau bani da hankali kawai.

Maman Wahida ce ta kira Mero tace zo da Allah ki min wanki,Mero ta kalle ta tace wanki? tace ae ke ba yar aiki bace a gidan Yar uwata,a cikin salary din data biyaki zaki min,Mero tace wannan marar mutuncin Yar uwar taki yo ai ko a iya zagina da tayi ta cinye salary dinta,ke Gyatumar Wahida wlh ko Bata zagina bazan miki aiki ba,bari kiji ko kudi zaki biya ni nafi karfin na miki aiki yanzu,wuuu ni rufa min asiri Ina matar Hanif a nan gidan wa ya isa Dani,ke nifa tun yanzu kallon banza nake wa gandrobobi ma bare ke, kin San da wa kike magana? Kina magana da millionaire Khadija,kina magana da me arziki,Maman Wahida tayi murmushi tace a Hakan? Mero tace da ke zan fara na gane fuskarki duk sanda na tashi maganin mutane Dake zan fara,kin san zan iya kulleki na jefar da key din a kasar nan?
Chapter 10 · 0% Book details