← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 68

Sashe 64

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Spark tashi yayi suka tafi da Naila yayi yayi akan Goggo ta fahimta amma Goggo taki yarda,fita yayi Dan yaji haushi,Naila tace Kinga yaji haushi in haka ne mene amfanin yace bazan zauna a wajen Mima ba,wlh ba wani Abu zai min ba,kin sani kema ba halin yin komai,sabo da haka yasa aka taho dake,kullum muna tare dake da jaririn ace bazan kwana a can ba,Goggo tace wlh bari na kira uwarki na fada mata tunda baki da kunya tafiya zanyi,Naila ta kwanta a gadon ta ajiye Baby a gefenta,Spark shi kadai ya kwana ya hakura Kuma da safe ma bai ce komai ba bai nuna fushi ba ko a fuska har wasa suka yi da Goggo,washe gari haka Goggo tayi komai na gidan ta gyara ko Ina ta kula da Naila da Baby,girki me aiki tayi,haka Naila ta sake kwana da Baby da Goggo har kwana uku,kwana na ukun ta kira Abba a boye ta fada Masa,Abba yace kyaleta bari na kira ta mu zata zowa da kauyenci garin Abuja,Abba ya kira Goggo ta daga waya,yace wanne dalilin zaki je ki Hana su sakewa daga ganin sarkin fawa sai Miya tayi zaki,birni ba haka ake yi ba yanzu,ki kyale yarinya,Goggo tace so take ayi mata wani cikin da wuri,ayi mata mana ke Ina ruwanki a jikinki yake,ana ta murna a kira Goggo sai kizo ki watsawa mijinta, kisa musu Ido ki kyaleta,iya aikinki kiyi Dan Allah.
Goggo tace shike nan tunda ku birni Kun lalace babu kunya taje ta kwana,idan yaro Yana kuka ai tayi sintiri a hanya zuwa dakina, yace ba komai tayi sintirin ai Matashiya ce da Kwarin ta kafafun basu fara ciwo ba ya kashe wayarsa.
Naila tana shugowa Goggo tace munafuka har da fadawa ubanki kije kiyi ta kwana ai mayyar miji,dariya Naila tayi tace naji.

Yau da dare bayan Yan barka sun tafi tayi wankanta ta saka riga da wando blue na bacci ta Sha kyau ta dauki Danta ta yiwa Goggo sai da safe,Goggo ta tabe baki,ta shiga bedroom din Spark,baiyi tunanin kwana zata yi ba,yace Goggo ta ishe ni da nasan haka ne bazan kawo ta ba wlh,Naila ta fara hada gadon Baby a gefen nasu hadadden bed fari tas da shi,Spark yace ta yarda ne ki kwana? Naila tace tun yaushe na fadawa Abba ya kira ta a waya kuwa yace ba ruwanta da mu,Spark yaji dadi yace yawwa tsohuwa ta ishe ni haba,Naila tayi dariya ya dauki Baby,yace yaron nan ya bani wahala kafin yazo duniya,Naila ta bashi nono ya Sha ta kwantar da shi.

Yayin da Maryam kanwar Annoor ta samu miji bayan ta murmure tayi aure abinta itama,suna ta zumuncinsu da Annoor.
Ihsan tana yin Idda ta samu saurayinta da take so tace tana sonsa bayan ta bashi jari ya kama business babba,ta kashe Masa mugun kudi,ta siya Masa mota bai taba cewa Yana sonta ba sai dai ya nuna shi kawai birge shi take yi,tun tana jira yace Yana sonta har ta gaji ta fada Masa da kanta,kowa ya gansu zai ce masoya ne yanda suke mu'amula,suke waya,yake zuwa gidanta da sauran su,yaci kudinta matuka,Ashe shi Yana kama kasa ya koma wajen Tsohuwar budurwarsa da aka hanashi sabo da baida sana'a Yana komawa aka ce ya turo Kuma ya Kai kudin aure,a ransa yayi tunanin ko ya auri Ihsan din sai yaga tafi karfinsa ita tana da kudi baza ta juyu a wajensa ba kawai ya nemi dai dai shi,sai da Ihsan tace tana sonsa yace ai shi an saka ranarsa da wata,Ihsan ga aji tace ba komai ba damuwa kamar gaske ta nuna bata damu ba, Ashe Kara ta shigar kotu ta kashe Masa kudinta ya yaudare ta zai auri wata.

Sai da suka je kotu sannan ma yaji labari ta taba aure duk lokacin da take kulashi tana da aure,Nan yayiwa Allah godiya da bai aure ta ba, Alkali yaji ma kudin ba roka yayi ba babu manufa kawai ta dinga kashe Masa kudi,Alkali yace ficika bazai biyaki ba tunda ba yarjejeniya kuka yi ba,haka kawai kika bashi kyauta Kuma kin amsa da kanki kyauta kika bashi,Ihsan tace Dan me bazai gane sonsa nake ba shi Dabba ne,Sadeeq me kurkura yace nasan gaibu ne ni da zan gane abinda ke ranki,Alkhali ya dakatar da su yace Allah ya azurta Sadeeq ta hanyarki,ki hakura ki nemi ladan Allah sai Allah ya baki wani na gari,Ihsan tace ni ban yarda ba,Alkali ya Kori Kara yayi rubutu matukar ta takurawa me kurkura sai an yanke mata hukunci,Ihsan ba nasara ta rasa Inda zata sa kanta gashi ta bari an sake ta,gidanta na Kano ta dawo ta kwana tana kuka da dana sani,washe gari da safe ta nufi gidan Haneef.

Gidan ta gani komai ya canja ya Kara haduwa,sababbin motoci ba Wanda ta sani ba,ta danna door bell,ba a Dade ba Khadija ta bude kofar wow,ta zama wata Yar gayu da ita,ta Kara kiba da haske ta zuba kyau cikin kana Nan kaya,Ihsan mamaki ya kamata kamar ba Khadija ba,fuska ta bata tace uban me kike a gidan nan har yanzu,Khadija tace ubanki nake yi,an sake ki me ya kawo ki nan gantalalliya,Khadija ta kalla sosai taga ciki a jikinta bakin ciki ya tokare Ihsan a makoshi,Honey Mero ta shiga kwalawa kira ya fito yana cewa na'am Beb,yaga Ihsan da mamaki yace ke me ya kawo ki ya bata rai,Ihsan tace Baby Dan Allah kayi hakuri,Babyn ubanki dalla fitar min a gida,rungume Haneef zata yi Khadija ta fyalle mata Mari, tace dama haushinki nake ji an sakeki ban sani ba,Haneef yace fitar min a gidana Ihsan,ni kake kora Haneef Ina Yar uwarka yace an Kore ki,karki zubarwa da matata ciki da fadan masifarki,ya fisgi Hannun Ihsan ya bude kofa tare da jefata waje ya kulle kofarsa,Mero harda goge masa hannu kamar ya taba Kashi ta goge masa tace muje.

Haneef ya dakkowa Mero me koya mata karatun Boko tana yi sosai sannan zata zana waec Nan gaba ya sata a makaranta,gashi ya siyawa Jummai gida madaidaici a birni tare da danta Mummir,ya saka Munnir a makaranta sannan ya bude Musu katon shagon cosmetics,Munnir Yana juyawa,Jummai tana siyar da kayan kanti shago guda ya mata a gidan,abinci da komai basu rasa ba,sannan da su za ayi aikin hajji badi harda Mero da shi zasu tafi gaba dayan su.
Mero tace ya kamata naje har gida na gaida Spark da su Mima suga ci gabana,sannan naje prison na nunawa Mummy da tace ban dace da suna Khadija ba sai dai Mero,Ina ji ina Gani ta rada min Mero,sabo da banyi Ilimin Boko ba bamu da kudi mu Yan kauye ne,gashi yau ita ta kare mata ni Kuma Allah ya daga ni,Haneef yace ya kamata kuwa muje gaskiya,Mero tace girki zan mata me dadi na Kai mata prison taci arzikina mutuniyar banza Tsohuwar alakwankwan,Haneef yayi dariya yace kaji za a Kai mata farfesu ma,Mero tace farfesun kaji Maja zan mata.

AsmaBaffa
[3/10, 12:13 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~

91-100

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM

PAGE NAKU NE.
Oufadi
Raliyaisah615

Spark ya kashe kudi na kirki Naila kaya masu tsada kamar me hada lefe haka ya mata su gaba daya ta zabe kayanta wasu duk ta cire kwance da marasa karfi Dake kusa da gidan Abba,da wasu na kauye gaba daya ma duk ta ware musu za a tafi musu da shi,ga gift kala kala tun kafin suna ana ta kawo mata,ko Kamal kayan da ya kawo na jariri ba a magana, saura kwana biyu suna Hidaya,Iman,Mufee,Beauty,Zarah da Aslam duk suka zo sai su Tani daga kauye,Spark ya kama musu Event center suje can suyi taron suna ba a gida ba,har anko su Chika suka yi.
Naila anje gyaran gashi saloon an Sha uban lalle me kyau kamar Amarya,haka su Ikhy ma.
duk sun gama shirya komai abinsu sai 12am ta shugo bedroom din Spark tayi wanka tayi Shirin bacci,yace ki kwashe kayan Nan na jariri da naki sun cike min bed,tace na gaji Allah ta fara kwashewa ya tayata suka Adana ta canja sabon bedsheet ta gyara bed din sannan ya Sha shayin na'a na'a ya kwanta tana gama shafa turaruka masu kamshi na musamman,Spark Yana kallonta sai kace maye,Juyowa tayi taga ita yake kallo,dariya ya bata ta murmusa yace nifa kyawun naki sai mamaki yake Kara bani zo mu kwanta,light ta kashe musu Baby Yana ta baccinsa a bed,Spark ya shigar da ita jikinsa,yace Hallare agaji take nema a taimaka mata ko da mouth ne,Bata Masa musu ba haka ta murje mijinta tass ta jiyar da shi dadi ba tare da anyi wani sex ba ta gamsar da shi.
Washe gari suna ba Wanda yazo gidan Naila a masallaci aka radawa yaro Ahmad,Papa yace kawai a dinga ce Masa Muhammad kar a canja Masa wani suna tunda shi da Ahmad aka sanshi,amma duk da haka iyayin Naila harda cewa tunda ga Spark ai ya kamata ta samu Flash sabo da haka ita Flash tayi masa nickname dinta.
Da safen kaya iri daya suka saka da Spark wata dakakkiyar shadda wata baka,Dake farare ne sai suka zuba kyau ciki,Ahmad ya Sha kayansa Yan kanti wasu farare tas.
Su Rafeeq ne suka zo wai sunzo cin tuwon suna,Spark yace sai dai ku Sha tea,Zarah ce ta fito da jaririn,Arham yace ko dai wannan ni take jira na Kara ta biyu ne itama na Dan ji,Shaheed yace da kuwa Kaci ubanka wannan matar taka,Rafeeq yace ka kyale shi ba iyawa zaiyi ba Kaine ma kayi Masa magana.
Naila ce ta fito da jariri ta Sha takalmi da jaka farare,Spark ya mike yace sai pics,Kamal ya gyara Iphone dinsa ya dinga daukansu romantic pics ga Baby a tsakiya sannan suka yi da sauran suma su Arham,aka dinga pics harda su Goggo da su Zarah.
Chapter 64 · 0% Book details