← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 68

Sashe 34

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama Khadija ya bude take away din da ya kawo mata da fruits ya sa spoon Yana zaune a gabanta kamar zai shige jikinta ya shiga bata a baki tana ci,Khadija a ranta tace Ihsan ta jawowa kanta mijin ya dawo wajena jinya,Haneef kuwa Yana Bata abincin Yana kare mata kallo,Khadija tace mene ne kake kallo na? sharewa yayi yace ba komai kina da kirki ne na Mori Kawa,tace hmm tana murmushi.
Ihsan kuwa Sadeeq Yana tafiya ta wuce bedroom ta kwanta tana furta what man can do woman can do better wlh,ka kula wata ba kula wani Nima.

Abba ne ya shugo gidan ana gobe sunan Beauty,Naila tazo,Chika,Ikhram,Hidaya,Iman duk suna nan sune a gidan suna zaune a dakin me jego sun cika gidan da hayaniya har tsila Hidaya anyi aure an shige cikin matan aure,Abba tun safe baya nan sai yanzu ya dawo yaji duk sun zo,ya leka dakin,Naila tace Oyoyo Abba,Abba yace sannunku duk kune haka sai kace mutane dubu ne a gidan,dariya suka yi suka gaisa Abba sosai yace to Kuma Allah ya baku naku masu albarka gaba dayan ku,suka ji kunya ya juya ko a jikinsa yayi gaba,Naila ta taso ta biyo shi,suka jero tace Abba tun safe nazo baka Nan,yace Yan barka ne suka takura min,baki ga na rame ba?ai sune suke takura min,abinci bana ci ya tsirga min,Naila tace ai an kusa ana yin suna shike nan,yace ya mijin naki? Naila tace Yana Nan lafiya yace a gaishe ku,ba wata matsala? tace ae,ba zagi,ba duka,ba cin mutunci? ya uwar mijin? Naila tace komai dai dai Abba Abu ya gyaru ba matsala,shike nan haka ake so ai Allah ya Kara zaman lafiya,Abba kaje Umma zata fada Maka wata magana kaje kaji,yace to,ya tafi kuwa Yana zuwa da Yan uwa su Goggo duk sun zo,ya zauna suka gaisa ya wuce dakinsa,Yar Inna ta shiga yace yau na yini ban ganki ba tun da rana nake Jin ciwon Kai amma yanzu har naji kamar na Sha Panadol,kece Panadol din zuciyata Yar Inna shugabar kyakyawan Dattijai,Yar Inna tayi dariya tace au bama shugabar mata kyawawan mata ba ta iya Dattijai ce? Su Naila sun tare wajen,in su Naila suna nan ai baza kizo wajen ba,kin haifi irin Naila Ina ke Ina zuwa wajen,Yaran nan zamani akwai iya zaben mata gasu Nan cikin daki duk babu banza a ciki,wannan tana wane wannan a kyau,Yar Hidayan ma da nake cewa ta gado ni tunda tayi aure ta canja gaba daya ta zabura tayi kyau,gashi nan har yanga take min,Naila ce take haba haba dani,amma ita waya take ma Kuma wlh nasan bazai wuce mijinta ba,shike nan na rasa 'yata"Nabeel ya rabani da ita.

Hidaya ce tayi sallama ta shugo ta durkusa a gaban Abba,yace yanzu na gama gulmar ki kin daina son babanki sai miji,dariya Hidaya tayi tace ni na Isa Abba wlh Ina sonka,yace dadin baki ba,Yar Inna tace tana sonka mana, Hidaya jeki abinki,tana mikewa ta fita, Abba yaje yayi wanka yaci abinci,a daren Annoor yazo ya dauki matarsa,tayi tayi ya barta ta kwana yace wlh bazan iya ba muje gida ko gobe na hanaki zuwa suna" haka ta shiga mota ta bishi ,Hidaya kuwa cewa tayi zata kwana Abba yace wa nake ji tace zata kwana? Naila tace Hidaya ce,yace daga nesa kika zo ga baki ga hanci wlh sai kin tafi,tashi ki koma dakin mijinki da safe Kya dawo,Hidaya tace Abba ya barni fa,sai kin koma Hidaya bari yazo ya dauke ki,Nabeel dama duk gidan ya Masa wani iri bai so ya barta kwana ba amma ta tashi gaba da kuka sai da ya barta.

Abba ne ya kira shi yace kazo ka dauki Hidaya mana Ina nan Ina gidanka da zaka barta ta kwana,Nabeel yaji wani dadi ya dinga godiya,yace Abba Allah ya Kara daukaka,Dan film ne ni ko kuwa wani Cele ne da zaka ce na daukaka,iya Yan unguwa da suka sanni shike nan,haka ma na godewa Allah,Nabeel yayi dariya yace to Alhmdllh Abba.
Hidaya kamar tayi kuka,Naila tana ta mata dariya tace Ina murna zan sarara Abba ya bata komai,Naila tace uhmm su Hidaya yanzu ya wajen yake ne? Hidaya dariya tayi tace ni dai kin San ba Yar iska bace bana irin zancen ku tunda kuka zauna anan banjin kunyi hirar arziki ba.
Haka Nabeel yazo ya dauki Hidaya Yana mata dariya Shima suka tafi gida.

Abba ne ya tambayi Yar Inna me Naila tace ki fada min? Kubra tace wai fa ciki ne da ita wata uku,iya shegen Naila ne ai ba kunya take ji ba in Taga dama Kai zata fara fadawa ma,Abba yace Allah ya raba lafiya,ko wani Hashimu Dolon za a samu,Wlh ko namiji ta Haifa baza a saka sunanka ba shike nan kowa aka Haifa sai kace sunanka,yace na gaji ni kwanciya zanyi,ya kwanta tare da cewa da ke matar kirki ce ai da kin matsa min kasusuwana kin min tausa,tace to Yar Inna ta shiga yiwa Abba tausa,yace kin tuna min babata na taba kurenta Sanda Ina yaro tana yiwa Baffana tausa,Ina zuwa ta Kore ni tafi fura zan dama Masa,Yar Inna tana ta dariya.
yace zan fada miki abin kunyar Baban Jauro kiji

AsmaBaffa
[2/26, 6:14 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~

46-50

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM

PAGE NAKI NE
Amatullah Kamshi

*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*

Yar Inna tace karka fada Dan Allah bawan Allah ya mutu da dadewa,Wa yace yayi sai na fada....Umma ce ta rufewa Abba baki da tafin hannu,yace ko ba yau ba sai watarana na fada,tana sakar Masa Baki yace Jauro da babansa suka nemi budurwa daya suka dinga fada a junansu,Jauro yace da Habiba idan babansa yazo ta fasa Masa Kai da dutse,shi Kuma Baban Jauro ya sa yaran unguwa suka dinga fesawa Jauro Mari....
Shewar su Naila yaji suna hira tayi dadi,Abba yace bazai wuce hirar mazajen su suke yi ba.
Naila ce Spark ya kira ta yace yau ba Kwalbewa,Naila tace Kuma sai Nan da 3days zan dawo,yace ban yafe ba kwana daya na bayar gobe da wuri zanzo na dauke ki da kaina,Naila tace in kayi hakuri da kaina zan dawo,ban yarda ba Baby,kin San Allah ba wai maganar Kwalbewa ba kawai gidan babu dadi ba kowa da ma kin haihu ne sai ki bar min dana ko 'yata muna tare amma ba kowa ni kadai,Naila tana kashe Murya tace Baby,Spark yace Kai Ina Shan Baby Ina morewa wallahi,ga Baby Dan jakar uba Kato,dariya suka dinga yi su Chika sabo da suna Jin wayar me ake yi,tace dama dai kaga ka dade baka siya min komai ba,yace takalmi sabo ya fito kenan,Naila tace ba shi bane fa kamar zata yi kuka,Pleaseeeee....yace uhm Ina jinki,wani turare ne Babynka Kuma yaji kamshin yace Yana so,Spark yace a Ina yaji? Yana ciki ace yaji kamshi Yana so,komai aka tashi ace Baby ne,rannan kika ce yace a baki kudi,ni Gani ubansa idan so yake ya min magana da kansa,ki fada Masa ya sameni ni ubansa muyi magana,Ikhram suna ta dariya a boye an kure Naila,tace ai baza kaji muryarsa ba akwai wani Abu daga uwa sai da suke magana tun Yana ciki babu me Jin maganar sai uwarsa,Spark yace naji wannan karo wata,turare ne na daki Dana jiki,Dana ajiyar kaya,da na toilet etc,duk idan zan siya da dan yawa za a kashe 70k,baya fita kamshin,Spark Yana ji yace shi Dan ya bari a siya Masa ragon suna tukun,yace a yanka Masa ko bashi ne wannan yafi muhimmanci,Ina ATM din Dana baki? Naila tace na siyawa Baby kadara fili na siya Masa,Spark yace Dan Allah da gaske kike ko karya kike? Naila tace da gaske na cinye kudin Nan Amma ba kadara na siya ba,wai nawa ne kwata kwata a ciki,ni bana shanawa a gidan mijina,mene amfanin me kudin,Allah ya hore Maka dole naji dadi wannan kudi baza su dawo ba sisi bazan bayar ba na cinye,murmushi Spark yayi yace idan kin cinye ma ai kanki kika yiwa one Kobo bazan baki ba wlh,gwara na taimaki marasa karfi ke kina ci kina koshi,turare shine matsalarki,kin San ana ta kwana da yunwa wasu yanzu suna Nan suna cewa gari zai waye Ina ma a wuce gobe a tsallake ta a fada jibi sabo da wahala.
Chapter 34 · 0% Book details