Sashe 68
Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Azima kuwa ta Jikin katanga ta fadawa su Scola sakon Mero har yanda tayi kyau da Wanda ta aura,Goje yace mu dai mun shiga uku ko wacce muka Shaku da ita sai ta bar gidan yari ta auri me kudi daga yau baza mu sake kula ko wacce ba duk kuje Yan iska Shegu,'ya'yan mutanen banza ,kana shakuwa da mace sai kaji fit ta fice tayi aurenta,Dan Indo yace abin bakin cikin ma sai kaji Dan prison ne,yanzu dai ji Tantiriya da wannan Dan iskan Spark shege Dan giya,Scola suka sheke da dariya yace Spark dinne Dan giya? Da mene idan ba Dan giya ba Yana magana Yana lumshe Ido kamar zaiyi bacci in ba giya yake Sha ba ubansa Soja yake Sha? Marar neman Albarka,suna ta dariya Scola yace kaji ance ta haihu ma Naila,Dan Indo yace ta haihu? aka ce tsohon zance yace a gidan yari a Nan ya mata ciki,da abinta ta shiga gidansa,daga Dan auren har ta haihu a nan yayi mata ciki karya suke,scola suka dinga dariya da ihu,Dan Indo yace ana kallonta a namiji Ashe shi harka kawai yake Kwasa Allah wadaran Spark kaji, ban taba ganin Dan iskan yaro ba irinsa,suna ta dariya,Malam Jilani Yana zaune yace wallahi Haramun kake aikatawa ranar lahira wlh sai ka Bada shedar abinda ka fada an rubuta,Dan Indo yace Kai rufe mana baki munafukai duk ba da ku aka hada baki ba,Kun fake da karatu,kasan kana fadar gaskiya kazo ka fada mana macece tun farko mana,sai anyi magana ka makale Murya kamar zaka yi amai wai ke Balarabe munga Sudais da Shuriem ma karewa,gashi Nan sauran Yan uwanka malamai sun fita sun barka,su Malam Garzali Kai kana Nan sai ka Kara wata uku sabo da bakin hali,Malam Jilani yace Kai yaushe zaka fita? Kai da aka yanke Maka hukuncin daurin rai da rai,shuru suka yi Dan Indo Yana Jan Kwafa.
Abba da Yar Innar sa suna zaman su lafiya,sana'arsa sai yaga dama ma yake yinta yau rana tana takewa ya gudo gida yayi kwanciyarsa,yaki fita sai Aslam ne ya zauna a shagon ya siyar, Yar Inna tace baza ka fita ba kenan? Yace bazan siyar ba na gaji Wanda ya dogara Dani ma a unguwa ya dogara da aikin banza,in zai kama me sana'ar arziki ya kama ya dinga siyen kayan masarufinsa a can,ni na gaji da auna hatsi nauyin tsiya,sai ka jawo buhu ga nauyi ka zuba a daro,wajen kamfatowar ma ba arziki sai nauyi duk kasusuwana sun fara budewa,sai damatsa nake ajiyewa sai kace Dan dambe,Yar Inna tayi dariya kamar me tace Ina kaga wasu damatsa,in ma kayi damatsa ai haka ake so,ke Yar Inna ki rage budurwar zuciya so kike Naila da Hidaya na auren masu damatsa kema kice irinsa kike so na koma,shi yasa wato naga kin yarda da sana'ar lokaci guda,Yar Inna tace Allah ya kiyaye Kai yanzu ko Gym kake zuwa Ina zaka tara damatsa,Abba ya kwanta ya mimmike yace wayyo Hashimu kwanta ka huta.
Annoor da Iman dinsa suna joint na Shan Ice cream da shawarma,aka kawo musu suna zaune,Baby tana cinyarta ya shiga bawa Iman a Baki tana ci suna hirarsu ta masoya,Ice cream din yake bata tana Sha,sai wani ya fado fuskar yarsu har da rige rigen lashewa a fuskar yarinyar,ya riga Iman lashewa,hannun ta doke tana shagwaba tace ka min wayo Allah dariya yayi yace ni da 'yata kin tsaya kina yanga,wajen kida na tashi harda rawa da hanu Yana bata tana cin shawarma abinsu sharr.
Nabeel tare da Hidaya suna gidan Haidar,Haidar dinma Yana Nan suna ta hira abin su a gidan suka yini.
Su Nabeela ma sun haihu suna zaman su lafiya da mazajen su suna zumuncinsu.
Mero tana Jikin mijinta a bedroom suna hutawa,tace wai Ina Yar uwarka Ihsan ne?yayi murmushi yace tana Nan Kano tana aikinta ta rasa mijin aure har yanzu,ita Kuma auren take so yanzu hankalinta ya dawo jikinta amma ta rasa mijin,taje Adamawa ta dade ta dade ko zata dace amma Ina,ta dawo Kano duk yawan Al'ummar Kano ta rasa mashinshini duk ta rame to karshe dai abokina Yana sonta yanzu zo Kiga murna zai Kara ta biyu da ita,Mero tace maganin marar hankali kenan duniya makaranta,shi yasa in mutum yace shi duniya ya sa a gaba to zai ga duniya,dariya suka yi yace Allah ya kyauta ya raba mu da aikin dana sani ya ja musu Bargo suka shike suka fara soyewa.
Misam ne ya dawo daga Office ya Kalli Chika dinsa ta Sha wanka,daukanta yayi Yana zagawa da ita a parlon,Baby na binsu da kallo Yana dariya,hannaye ta daga tana tsalle har da kuka itama a dauke ta,Chika ya ajiye ya dauki yarsa Yana shilla ta tana dariya,chocolate ya bare ya bata yace Chika ta shirya suje gidan Rafeeq,bayan yaci abinci suka tafi gidan Rafeeq,suna zuwa Rafeeq yace Kai 'Yan anace yau ma an kawo min ziyara kenan ku baza ku dinga bari Ina hutawa ba,Chika dariya tayi tace wlh zamu daina zuwa ma,Ikhy tace kyale shi kawata ni da zaku dinga zuwa kullum ma ai nafi son haka wlh,Arham ne suka zo da Basma da Baby suma,Rafeeq yace Nidai an nace min kowa sai dai ya taho gidana,Arham yayi dariya yace dama biyowa muka yi mene da Kai da za a nace Maka,kaga abar nacewa ya nuna Basma dinsa yace itace me abin bayarwa ba Kai ba,dariya suka yi cike da nishadi,Misam yace sarkin Kwalbewa an Lula duniya sai abinda Hali yayi,Bado yaga ta kansa cewar Rafeeq,cike da nishadi suke hirar su.
Spark kuwa Naila tana samun hutu ya dauke ta suka bar kasar tare da Baby dinsu,suna jirgi suna daukan pics cike da nishadi,Baby Yana ta kiriniya gwanin sha'awa,Naila wata ta Gani a jirgi babbar mace tace Dan Allah dauke mu ta bata wayar matar ta dauke su pics da videos sunyi kyau,Naila tace Kalli yanda muka yi kyau ya Kalli pics din ya mata rada a matse nake Baby uwar Baby matar Baby ta Baby da Babynta Kuma gata Baby itama muna sauka a bani bado,dariya tayi tace Ina Jin wannan kirarin nasan me ake so dai, yayi dariya Yana tuna masifar Naila lokacin tana da ciki ya dinga dariya Yana tuna mata itama dariyar take,tace wlh in na tuna dariya nake yi,Kunnenta ya ciza kadan sannan yace Allah ya barmu tare,tace Ameen Baby Mijin Baby Baban Baby,dariya suka yace Ameen Ameen Allah yasa ko wata na Gani idan zanje zance nayi makuwa nayi batan kai na dawo gida wajenki,Naila ta sheke da dariya tare da furta Ameen.
INA BAWA FANS DINA HAKURI BISA MATSALA DA AKA SAMU A WAJEN POSTING.
WANNAN LITTAFIN NA SAMU MATSALAR TYPING WLH BAN YI SHI CIKIN DADI BA,SABO DA YAZO MIN A BANI DA LAFIYA,GA ZUWA ASIBITI LOKACIN DA AKA SHIGA BOOK2 HAR KUSAN FARKON BOOK3,A BOOK3 KUMA UZURI YA SHIGO MIN DA YAWA BA ZATO WANDA YA JAWO DELAY DA YAWA A LITTAFIN,BAN JI DADIN HAKAN BA SABO DA KOWA YA SABA BANA BOOK HAKA A DADE BA A GAMA BA SANNAN BANA FASHIN POSTING SAI DA DALILI ME KARFI,WANDA A WANNAN BOOK DIN HAR NA GAJI MA DA BADA UZURI,BANA FATA NA SAKE TYPING ME DELAY HAKA,NI KAINA BANA JIN DADI WLH AMMA DUK DA HAKA
ALHMDLLH
INA GODIYA GA ALLAH DA YA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI LAFIYA DA NI DA MASOYA WANNAN LITTAFIN TANTIRIYA A GIDAN YARI.
INA MIKA GODIYA TA GA DUKKAN WANDA SUKA SIYI LITTAFIN NAN MAZA DA MATA,SUKA SA KUDIN SU SUKA SIYA INA MATUKAR GODIYA ALLAH YA BIYA MUKU BUKATUNKU BAKI DAYA,ALLAH YA YANTA KU CIKIN YANTATTUN BAYINSA A WANNAN WATA MAI ALBARKA DA ZAMU SHIGA.
CIKIN SAURI NA KARASA WANNAN LITTAFI KASANCEWAR AZUMI YAZO WATAN IBADA.
WANDA SUKA JAJIRCE DA YI MIN SHARHI KO YAUSHE HAR MUKA GAMA NOVEL DIN NAN WLH BAN SAN MA DA BAKIN DA ZAN GODE MUKU BA MUSAMMAN
BABY AK
AMINA YUSUF BAWALE
HAJJORA INVESTMENT
MURJANATU ABU NA BANGA
DA DAI SAURAN SU INA GODIYA.
SANNAN WANDA SUKA JAJIRCE MA FARKO HAR AKA YI NISA UZURI YA SHUGO MUSU INA GODIYA,DA SAURAN WANDA BASU SHARHI BA KUMA INA KAUNAR KU NA GODE MATUKA.
MASU JIRAN COMPLT KUMA DA KUKE GEFE NA GODE.
ALLAH YASA MUYI IBADA KARBABBIYA.
ALLAH YA BAMU LAFIYA ME DORARRIYA ME AMFANI BAKI DAYAN MU
INA YIWA KOWA FATAN ALKHAIRI MASOYA.
AsmaBaffa