← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 68

Sashe 29

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baiyi tunanin dakinsa ta shugo ba ya ganta a kwance haka,guntun tsaki yaja sannan ya kalleta yace fitar min a room,kin kulashi tayi,yace ba da ke nake magana ba,idonta ta bude a hankali tace na dawo ai,ka daina turo Yar aiki tana damuna dole sai na dawo kwana a dakinka,ka fada min ni da Kai ba wata Yar aiki ba,ka daina nuna min kana sonta dan wai nayi kishi,yanzu so kake nazo na dawo,ba matsala zan na kwana da Kai ka daina zancen sirrin mu da ita,tsaki Haneef ya ja yace baki da hankali amma naga alama,fitar min a daki,tsawa ya mata ta gaske ba arziki ta mike ta fara tafiya sum sum ta bar dakin yace stupid,ba aikin fari bare na baki iya sex ne aure an fada miki ya ja tsaki,Shirin bacci yayi
Ya Kwanta tare da fara tunanin Khadija,yana tuna abubuwan ta Yana murmushi,Ihsan ce ta dawo ta sake haurawa Saman bed ta kwanta a gefensa,tashi yayi Yana masifa nace bana bukata dole ne,kin Raina min hankali ma,1yr da aurenmu tun farko Ina binki sabo da mu samu mu shirya mu zauna lafiya,ni ke kin sani Umarni nabi ba wai ni nace Ina sonki ba,amma duk da haka na danne na nemeki akan mu zauna lfy nan gaba zamu Iya fara son juna amma ke tunda aka yi aure ba wani Abu na kyautatawa da kika taba yi min.

Prison naje baki taba zuwa ba ko sau daya,daga aikinki sai yawace yawace,sabo da kina da kudinki,wlh shi yasa Maza suke Hana mata aiki,suke karya su idan sun fara samun kudi sabo da wasu irinku mahaukata da baku San me kuke yi ba,kina tunanin son sex zai sa nazo Ina binki kina raina min hankali,sau uku kika taba biya min bukata Shima sabo da a lokacin na hanaki fita ne aiki shi yasa kika yaudare ni da shi,abinda yasa kika ga na saurare ki hakkinki ne yasa Ina tunanin kar Allah yayi fushi dani ,amma naga ke Yar rainin hankali ce,kin makara wlh,na baki dama kinki amfani da ita ni zan zauna Ina binki, da kudi na da komai ki kalle ni ki Kalli jikina Allah ya min baiwa Ina da kyau Alhmdllh,Ina da asali me kyau duk macen da na nema sai na samu .

Baza ki godewa Allah ba Kin same ni bana neman mata,bana caca,bana Shan giya ko wani shaye shaye,ni ba Dan luwadi ba,duk irin wannan Allah ya kare ni bana ko daya,sannan auren zumunci ne amma ban taba wulakantaki ba ban taba fada miki wata magana mummuna ba,amma kin kaini bango wlh wlh bakya gabana yanzu ki sani bana sonki Kuma bazan so ki ba,kin sa min tsanarki a raina,Dan iska ne ni da zan zauna Ina zama da ke haka,dama na gane badan Allah kika aure ni ba akwai wata manufarki.
Ihsan duk ta gama jinsa tace to ya zaka yi Dani ni dai Ina matarka zama daram,bazai wuce kace Yar aiki kake so ba Kuma na gani yanda zaka aure ta indai Ina gidan nan,Murmushi yayi yace idan so nake ko uwata baza ta sani ba za'a daura Kuma haka za a kyale ni,Jikin naki da kike wani ji da shi fin na Khadija yayi? Sannan wani dadi ne da ke? Skin din taki duk a cuccure a manne ya ja tsaki ya kwanta abinsa ya kyale Ihsan a tsaye sororo tana bakin cikin maganar da ya gaya mata,ta dade a tsaye kafin ta juya ta ja Kwafa tace wlh sai na nakasa Khadija naga tsiya sai na Maida ta gurguwa.

Washe gari Khadija da safe tana kitchen tana girkinta,Salamatu tana gyara gidan,Ihsan ta fito da shirinta na tafiya wajen aiki,wankan da ta dauka ko matar da bata da aure baza tayi ba,riga da skert ta Sha na Leshi sun kama ta Sosai Dan mayafinta nata ziriri sharara,taci glass ba karya tayi kyau,Kitchen ta shugo tana uban kamshi,Khadija ta samu ta hankade ta wuce ta dauki Madara tace har abada bazan ci girkinki ba,Khadija tace kanki kika yiwa dama bake nake yiwa ba,ke wlh ki shiga hankalinki cewar Ihsan,Mero ta kalleta tace nufinki uwar gidana wai a haka zaki fita? yanzu ku uwayen gida Kuna haka Ina ga mu Amare,mu da zamuyi koyi a wajen ku sai Kuma kune kuke irin wannan,Haramun ne mace ta bayyana surarta da adonta ga Wanda ba mijinta ba,sannan wani yaji kamshinki ba mijinki ba kina cikin fushin Allah,wannan wlh gaskiya nake fada miki ki daina biyewa duniya kwana nawa akeyi a duniyar,sannan ba Wanda yasan lokacin mutuwarsa Ina jiye miki karki mutu a wannan hali Aunty, ki gyara tun wuri tun kafin a daura auren nan da ni,Ina zuwa kar na riga ki haihuwa Kinga ni yanzu a matse nake na girma da yawa irinmu ake kira da shiga da ragon ka,Ina zuwa zan samu ciki da ragona zan shugo,Ihsan tsaki ta ja tace an fada miki ni haihuwa nake so duk me haihuwa ta haihu ga waje nan,Mero tace to mun gode wlh zan kilo a gado,aikin banza wlh ba namijin da zai wulakantani akan wata da kudina da kyau na Maza matasa suna Nan a gari in dama taki sai a koma hagu,baka samu halak ba sai ka tafi wajen Haram.
Mero tace Allah ya taimake ni Allah yasa bana Jin yaren da kike saukinta ma kenan ban San me kike fada ba,Dan Allah wanne yaren kasar kike? Ihsan ficewa tayi amma sai ta kasa tafiya ta zauna Palo tana jiran Taga Haneef me zasu yi da Khadija.
Sakkowa yake daga step ya Sha shadda fara,kamar a sace shi yayi kyau Yana kamshi,agogonsa me tsada yake gyarawa,Khadija ta fito dauke da flask na ruwan zafi ta ganshi,Ido suka hada ya sakar mata murmushi itama haka" yace wai har kin tashi? Mero tace ba dole ba Oga bai fita na sallame shi ba Ina naga ta bacci,nifa a kan uzurinka idan ban kwana ba bacci ba Allah ya azurtani,idan ba cirrrr yanda naga dare haka zanga rana,Haneef harda shafa gashi yana Jin dadi,Mero tace kayi kyau Sir,yau mata zasu Kalli Allah ya isan Aunty Ihsan da yawa,dariya yayi ya nufi dining,Ihsan ta gama kulewa,to ita taki magana ta tsaya girman Kai.

Mero bayan tayi serving dinsa ya fara ci tana zaune,itama ta zuba nata,Ihsan karfin halin Mero Yana bata mamaki mutum Yana da aure ga matarsa a gefe amma ki zauna Yana cin abinci kuci tare Kuma ga matar a gefe,Ihsan tace laifin Haneef ne da ace bai Bata dama ba ko kallon banza bata Isa ta min ba,wato shi yasa wasu suke kama miji a hannu,idan kina da miji a hannu to ba abinda baza kiyi ba Kuma ki zauna lafiya,shi yasa tunda Mero ta ciri tuta a wajensa shike nan sai abinda taga dama take yi a gidan ba dangin iya ba na baba.
Muryar Khadija taji tace Ogana...ya amsa Yana kora tea,tace jiya kwana nayi Ina mafarkinka,dariya yayi ba shiri,yace me nayi a mafarkin? Khadija tace Ina bacci sai gaka kazo,nace Ina Kwana Hubby na,a mafarki fa nace Hubby na Kuma ka amsa wlh kace na'am Babyna,Haneef yace ni din? Mero tace tun yaushe Kuma,a daren jiya kaga yanda nayi wata hajijiya musamman batun da muka yi a daren jiya cikin mafarki,ai munyi batutuwa,Haneef Yana ta dariya yace Allah yasa banyi komai ba,kayi mana kawai dai ayi shuru da zancen nan ba na ji bane amma anyi batu,Haneef ya zauna Mero tana ta tsare shi da zance yaki tafiya wajen aiki har Ihsan takaici ya sa ta fita abinta.

Tana fita tana so tayi parking wani me kurkura yazo ya daki bayan motarta kadan,parking yayi da niyyar bata hakuri ta fito itama a fusace tana masifa,wanne irin mahaukaci ne kai sai Taga Wanda ta siyawa abinci a resturanta kwana ki,tace Kaine? Yace oh Hajiya kece? Dan Allah kiyi hakuri akasi aka samu wlh,Murmushi tayi tace ba damuwa karka damu Jakarta ta bude tace wai ya sunanka ne? Sadeeq sunana,tace mashaallah ta mika Masa card dinta tace gashi ka neme ni,bani number dinka,ta tambaya tana murmushi,har ga Allah yayi zaton budurwa ce ya Bata number ta shigar ta kirashi yayi saving tata ya wuce abinsa itama ta shiga mota ta Kara gaba.
Khadija kuwa da kyar Haneef ya yaki kansa ya fita daga gidan sabo da yanda yake Jin dadin hirar abin ba a magana.

Sai yamma likis Ihsan ta dawo daga Office dauke da take away dinta baza ta ci abincin Mero ba ta daina ci, Clashing suka yi da Mero zata sakko daga sama itama Ihsan zata sakko,Mero tana gaba Ihsan ta sa hannaye biyu ta hankado Mero daga Saman bene,Mero ta saki Ihu ta gangaro ta fado taji munanan raunuka kuwa.

Salamatu ce ta fito tana salati tayi kan Khadija wacce ke kuka kwance a kasa ranga ranga,tsaki Ihsan ta ja ta wuce dakinta ta saka key ta barsu a wajen tana cewa naga da shegiyar da zaka yi hira Haneef, Salamatu da gudu ta fita ta kira me gadi tace shugo Iro ka taimaka,Iro yace Aradu idan Aunty me mota ce bani zuwa sai dai ta mutu a kawo gawarta,ko sallatarta bazan yi ba bare naje kaita makabarta,Khadija ce ta fado daga bene,Iro yace Subhannallahi ita me ya kaita tunda ba sabawa tayi da hawa bene ba,ta Saba da dakinsu a kauye shiga kamota kamar dakin zomo,daga ka shiga ciki bugul ka fito,tazo nan birni ta saki jiki tace zata biyewa matattakala ai gashi nan,Habiba tace Aunty ce Me mota ta turo ta,Iro yace naji a zuciyata ,Hasashe na ya tabbata dama naji a raina itace sila,ai Khadija ce da shiga sharo ba shanu muje,Iro Yana zuwa ya dauki Mero yace nauyiiiiii....ya ajiyeta yace kut wannan ko mota ta shiga sai ta girgiza.

Ya sake sa hannaye Khadija tana kuka ya dagata ya sake ajiyeta Yana Nishi yace me kike ci haka ke kuwa,ke daga wajen kasar Yumbu aka samar da ke,tabo me nauyi da danko da irin kasar aka samar dake,bazan iya ba ku Nemo wasu mazan,ya sake gwada daukan Mero sai ga Haneef ya shugo yaji kukanta ga Iro ya daga ta,Haneef yaji haushi tun daga nesa yake cewa Kai ajiyeta....sauke ta....Yana hararar Iro ya karaso wajen,in banda kai dan Iska ne Ina ruwanka da ita?
Chapter 29 · 0% Book details