Sashe 63
Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Naila tana shanye shayi da nama kadan ta rage Naman,ta koma kan faten doya da wake taci taci ta koshi ta Sha fruits da ruwa ta Dan huta sannan ta kwanta sai bacci,tun dare sai washe gari da rana ma aka sallame su,Mima a motarta ta wuce da Naila da Goggon gidanta direct,Naila tasan Spark Bai sani ba ta dai yi shuru,sai da yaje gida shi yaga ba nan aka kawota ba,ya nufi gidan Mima Yana cewa ai dalilin dakko Goggo kenan tazo ta zauna da Naila.
Mima tace to ai na sani Malam ka bari dai ta huta ,yace shi wlh a'a,Goggo tace ka bari tayi wanka sosai ta gasa jikinta ayiwa Jaririn sai mu tafi,yace yawwa,Spark tunda ya dauki Jaririn ya Masa addua bai Kuma daukansa ba Yana hannun Yan uwa har so yake a ajiye shi ya dauki abinsa amma daga hannun wannan sai ya fada hannun wannan.
Nurse me jiran Naila ta haihu ta rama Marinta lokacin tashinta yayi amma jira take taki tafiya sai Naila ta haihu,tana can ta kwanta tayi bacci sai da me asibitin yazo ya dinga fada Dan me Bata tafi ba ya Kore ta gida,tace wlh Allah ya hada mu watarana a hanya ai na gane ta.
Naila wanka tayi Goggo ce da kanta tayi mata gashi,Naila har hawaye tayi ta Sha wahala a hannun Goggo da gashin towel,an zuba gishiri a ruwan sabo da kashe wasu kwayoyin cutar,Sai da ta gama Naila tasa shampoo ta wanke gashinta sosai sai kamshi ke tashi,tayi wanka da sabulu ta fito,Mima tayiwa Jariri wanka tas an canja Masa kaya,kayan Naila na asibiti duk da Goggo ta wanke Spark gaba daya ya kwashe ya zuba a washing machine ya sake wanke su,ya zuba na jariri ma ya wanke tas suna kamshi ya tattara a cikin bahon jariri ko kunya,ya saka a mota yazo duk ya kwashe abinda suka zo da shi kaf ya Kai motarsa,Naila ta saka kaya tana daure gashinta da ribbon gashinta yanzu yayi mugun tsayi Dake Jinin gashi ce har ya dawo bayan uwar daadaa da yasha a gidan yari.
Mima wani abincin ta shirya musu suka tafi da shi a mota tace ala raka taki gona ta fadawa Spark yayi dariya yace Ameen,zasu shiga mota Papa yazo ya dawo yazo ya dauki jariri ya Masa addua ya yiwa Naila murna,Spark yace sai fa kazo har gida Papa ban karbi wannan ba,Misam da Rafeeq har gida kaje ganin jariri Nima sai kazo,Papa yayi dariya yace zanzo Inshaallah,na Arham dai in za a haihu har asibiti zanje,dariya suka yi har Arham Dake ya fito shi da Basma zasu tafi,shi yasa Papa yayi zancen ma,Arham yace Allah ya kaimu,ai Bata da ciki wata nawa Amarcina nake Sha kawai ai haka yafi,Papa yace Allah ya bada na gari,yace Ameen yaushe zaka zo muyi hira ne?Papa yace sabo da yana son yayi hira da Spark da Arham,in suka zo ko banza yayi dariya,Rafeeq shi in yaga dama ma yaji yake ya daina zuwa,Misam ma basu Shaku ba,in yazo ma basa hira, Arham yayi dariya yace yau ma dan na gaji ne amma da tuni na zance ka da magana sai na dawo zanzo weekend ai Papa Soja sarkin fara'a,irin wai yasan baya fara'a sosai shine yace sarkin fara'a,Basma tace Papa mun tafi yanzu munyi hankali,Yace to Basma Haka ake so ayi ta hankali,tace to suka tafi, Papa yace a ransa Ina kuka ga wani hankali ai sai dai gaba kuyi hankali tare.
Naila tun a mota ta kira Yan uwa ta fada musu,Mohsin ta fara fadawa,ta fadawa Umma ,ta kira wayar Abba sai da yaji ance ta haihu ya daga wayar Yana murna,tace Abba na haihu,yace Inyee su Naila an girma za a fara koya tarbiyya,Allah ya raya bisa sunna tace Ameen,yace yawwa karki biyewa su Goggo da kauyenci baza a amsa addua ba, kowa yace Allah ya raya kice Ameen, kanki tsaye ki amsa Ameen idan ance kinyi fitsara kice ni na saki kakan yaro ne,Naila tace Nima dai shine na Gani,yace yawwa karki yarda da kauyencin su Goggo,Sannan karki matsawa mijinki da maganar kashe kudi akan kin haihu nasan ku mata in kuka samu waje sai Kun Kai mutum bango ki bari duk abinda ya siya kiyi godiya,Naila tace ai dama Abba ai ba kullum ake kwana a gado ba,Abba da sauri yace a'a Banda ni" Naila kullum a gado nake kwana tun Ina jariri akan gado karami na babata ake dorani" babata Kuma da Mijinta babana kenan suna kan babban gado ni Ina karamin gado,har na girma aka mayar min da gadona dakina gashi har na auri Yar Inna yau shekaru kusan arba'in ban taba fashin kwana akan gado ba,Naila tace gaskiya ne tana murmushi,yace sai bayan suna zamu zo da Yar Inna,su Hidaya dai da su Zarah zasu zo kafin suna,tace to Allah ya kaimu.
Suna komawa gida Naila tace yunwa nake ji da bacci,Spark wanka ya shiga yayi wanka sosai ya fito tare da saka sabuwar jallabiyarsa da Mohsin ya kawo Masa,Naila a dakinta Goggo ta sake yi mata wankan yamma,bata shirya ba sai da taci abinci dare yayi sannan kaya ta sake canjawa ta saka rigar baccinta doguwa me kyau me gajeren hannu Orange color, Goggo tace sai an daure ciki,Naila tasa abin daure ciki na Yan gayu Wanda a kasar waje ma aka siyo mata kala nawa da kyar ake matse ciki da shi na rage girman ciki,sai da ta saka sannan ta shafa turaruka ta Maida rigar Baccin kamar ba ta sa komai ba ciki ya lafe ya dame.
Goggo ma wanka tayi ta fito ta hau Naila da fada yanzu dama da nace ki bashi nono Baki bashi ba? tunda aka haife shi sau daya kika bashi nono sai zam zam kawai aka bashi fa,wannan wacce mugunta ce,boyon nono ya kare yarinya cewar Goggo,Naila ta dauki Jaririn Yana ta cin hannu Yana zare Ido, Goggo tace tsaya na koya miki yanda ake yi,sai da ta koyawa Naila sannan tace to kiyi Bismillah,Naila tayi Bismillah ta juya baya ta fara bashi wai Goggo baza ta kallar mata nono ba,Goggo tace a gaban mu fa kika yi nono har ya girma me zaki boye min shashasha,naga dazu ni nayi miki wanka,Naila tace naji ga Abinci nan Goggo ki ebi abinda kike so,Goggo tace mijin naki fa? Na zuba Masa nasa kina wanka na Kai Masa,Goggo tace Iyye kaji kula da miji,dariya Naila tayi,Naila bayan ya Sha daya ta juya shi yanda Goggo tace ta bashi dayan,Yana Sha Goggo tace ai ya koshi haka,to rike shi a hankali karki hantsila shi zai yi amai,Naila tace Kai wannan yaro haba ace wannan ace waccen,sai da ya huta tace bari na kaiwa Daddyn sa shi ya ganshi,Goggo tace kwaji da shi munafukan banza wlh ki dawo a nan zaki kwana,Naila tace to,ta fice da danta cikin showel ta shiga dakin Spark Yana cin abinci Yana kallo ta shigo
Ya kalleta Yana Jin dadi a ransa yace fada ya kare tace ae mana,kallonta ya sake yi yace wai dama idan an haihu kyau ake yi ne? duk naga in kuka haihu sai mace tayi wani kyau fatarta tana shining,Naila tace ai haka yawanci ake yi sai zuwa arba'in ake dawowa normal,Naila ta juyo fuskar jariri tace ka ganshi fa Kaine babansa Kai ka haifi wannan,Spark yace duniya sabuwa SparkNaila kamanninsa biyu,Naila tace Nima haka nace kamanninsa biyu,sai da ya gama cin abincinsa ya dauke shi,wanne suna za a sa Masa ne? Naila tace oho ka zaba,Spark yace Papa Ahmad in yayi miki a saka idan kina da zabi ki zaba,tace a'a Banda da zabi Kuma ai suna me dadi ne na kololuwa Ahmad fa,Allah ka raya Ahmad bisa sunna,Allah kayi Masa Albarka kasa ya zama mahaddacin Alqur'ani,Allah kasa yayi koyi da fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW),Allah kasa duniya ta amfane shi,muma iyayensa ya amfane mu ya zame mana Alkhairi dukkanmu da Yan uwa da Al'ummar musulmai Baki daya,Allah yasa yayi suna ta hanya me kyau,ya shahara a duniya ta hanya me kyau,ba shaharar Dan Boko Haram ba,Bata Dan kidnapping ba,Bata Dan daba ko wani Dan iska ba,shahara ta hanyar abin Alkhairi,Allah yasa Shahidi ne,Allah ya Masa Albarka,Wannan Dan nawa Ahmad Allah ya sa Masa Albarka,Allah ya bashi lafiya da tsawon rai,Allah ya azurta shi ya raba shi da talauci,Allah yasa Dan Aljanna ne,Allah ya bashi mata ta gari Irina kyakyawa,Spark Yana ta amsawa da Ameen Ameen Yana dariya yanda Naila ta dage take surfa addua ta daga yaro sama tana cewa Allah ga Dana Ahmad,Allah ga Dana Ahmad,ya Rab ya Rab,ya Rab ka amsa addua ta.
Tana gamawa Spark yace well-done uwa ta gari haka ake so wlh uwa ta fara yiwa danta,Shima ya karba yace kawo shi Nima nayi nawa Shima ya tallafe jariri ya Dan daga sama kadan ya fara zubo addua tana amsawa Ameen...Ameen..Ameen sai da suka gama sannan Spark yace yaushe zan dauke shi ne ya tsula min fitsari? Dariya Naila tayi,yace to ai ya kamata ace Danka ya Maka fitsari,Naila tace saurin me kake yi zaiyi ne ai bari a fara barin duwawunsa Yana hutawa ka gani,har Kashi ma zai Maka watarana,yace Ina maraba indai na dana nane,spark da baya daukan yaro amma shi yake neman fitsarin dansa yanzu.
Naila ta dauki Baby tace bari naje sai da safe,sai da safe Ina?wai Ina bed din Baby ne,Goggo tace tare zamu na kwana,yace muje wajen Goggon ni zan mata bayani akan mene haka zamanin da ne wannan.