Sashe 62
Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Naila sai murna ta koma ciki Kuma ta dawo Boss dinta sai kuka sai masifa.
Abba ya kira ta waya ya gaji da complain daga wayar yayi tace hello Abba yace the number does not exist please check the number and dial again,Naila tayi dariya kamar ba gobe Kuma ya fuske ya kashe wayarsa,mamakin Naila Ina Abba ya Iya turancin ma da zai ce haka,Umma ta kira ta Bata labari,Kubra tace Nan yasa Zarah ta dinga koya Masa wai idan number ta daina aiki ya MTN suke cewa,Inda kisan me haddar karatun Qur'ani ya Dade kafin ya iya kullum Kalma Daya ake biya Masa har ya iya Ashe ke yake wa tanadi,kin dame shi da complain,kin San in ya gaji da complain ko zuwa gidan Nan kika yi sai ya buya gwara ma ki daina in kina son zaman lafiya da mahaifinku,Naila tana ta dariya har Spark ya fito a Waka ta bashi Labari,Shima dariya yayi yace an gaji dake to.
Kwana uku da cikar Edd din Naila,yau dai tun safe take Jin yanayi marar dadi ta kasa sukuni Sam,Bata kawo haihuwa bace,sai da ta zauna Zata tashi kenan taji ta kasa,Spark ta shiga kwalawa kira,ya fito da sauri tace na kasa tashi wlh,ya koma ya tattaro kayan haihuwar a Yar jaka me shegen kyau wai su Yan gayu ya sa mata Hijab ta fige ta jefar kanta ba dankwali a haka suka tafi asibiti,yace ko a kira Umman ki da Abba? Naila tace a'a kyale su kar hankalinsu ya tashiiiiiiiii....ta cije baki,Yana driving yace ki dinga salati kinji kina Kiran Sunan Allah, da sunanka zan kira,nace sunanka zan kira? Spark yace yi hakuri,karka sake bani hakuri bana so...sannu to....a haka suka je asibiti,already ya kira Mima,tazo ita da Chika da Ikhy,Naila ana labour room ana fama.
Nurse tazo da iyayi tana cewa ai da sauran lokaci ma akwai gumurzu a gaba,Naila ta yanka mata Mari ta shake ta tana cewa duk wannan azabar da nake Sha kice ba yanzu ba inji ubanki,aka kwaci nurse da kyar,gata yarinya Yar budurwa wata Yar mummuna me dama dama,Nurse dafe da kumatu tace wlh sai na rama Allah ya kaimu ki haihu lafiya,wlh sai na rama,Naila tuni ma bata San tayi ba,Mima tace kiyi hakuri kece yarinya ce baki San ba a zuwa Jikin me nakuda a daga mata hankali ba,nakuda hauka ce Inji nurse ta fice wajen Spark dake waje Yana kaiwa da kawowa,tace Kaine mijinta ko wlh idan matarka ta haihu sai na rama marina da tayi,kawai daga zuwa sai ta shake ni ta mare ni,nakuda hauka ce,wlh tana haihuwa sai na rama,Spark yace wuce ko na Kara miki uku kaga Yar iskar Kwaila in da nasan kece ma zaki je kan matata ki tsaya wlh bazan kawota wannan asibitin ba,so kike a haifo min yata ko Dana kamarki,in macece ki jawo min karbo mata rubutu domin ke sai kafin ki auru sai an karbo miki rubutu,nurse zata yi magana yace kina magana zanyi ball Dake a wajen Nan naga me tsaya miki,kin kalle min Bado Allah ya isa,idonki kadai ya isa yasa Badon ya rage zaki,kar wata nurse wata Yar iska me kambun Ido ta kallar min tsaraicin matata ta cuceni,duk gyaran duniya yaki dawowa dai dai,Nurse dai taji Spark ya fita iskanci Dan tijara ne tayi gaba tana jira Naila ta haihu tazo ta mareta.
Spark dakin ya leka ta window yace Mima karanta mata falaki da Nasi da suratul Iklass kafa uku uku,Mima ta zaci na neman saukin nakuda ne ta fara tana tofa mata a ciki yace ba a nan ba ta Inda zata haihu ta Saman riga ba cewa nayi ki daga mata riga ba,nidai naga ta kaina me yasa ma ba a kira Goggo ba,ace sirika Taga wajen Danta ni ban yarda da wannan tsarin ba,Maman Rafeeq yaje ya dakko tun daga gida ya kawota,gashi asibitin mace daya ce zata shiga wajen marar lafiya,haka yasa Mima ta fito Maman Rafeeq ta shiga,ya sake lekawa yace bakinki kanin kafar ki kar naji kar na gani kin Fadi wani Abu akan palace dina,Maman Rafeeq tace kaima haka kake Ashe irin Arham ne mudai mun shiga uku da jarabar yara.
Sai da ya kira Goggo a waya yace ta taho kawai,Goggo dama Jira take ana kauye an hadawa Naila kayan gyara in ta haihu za a taho Abuja a kula da ita,yace ki zauna yanzu zan sa Azo a taho dake,Shaheed ya biyawa flight Dana Goggo yaje ta Kano yafi kusa sannan ya hau mota drop har kauyen ya dakko Goggo da kayanta suka dawo ta airport suka shiga jirgi Dan lokaci kankani sai gasu a Abuja,Goggo kayanta ta ajiye a gidan Naila sannan Shaheed ya taho da ita asibitin,tana zuwa Spark yace Maman Rafeeq fito wata kusan tafi wata kusan,Kakar ta tazo da kanta ba sako ba,Maman Rafeeq ta tabe baki tace na huta,dama halinku ya isheni,ta fito Goggo suka gaggaisa da su Mima tace Allah ya raba lafiya ta shiga ciki.
Mima suna zaune suna hararar Spark wai ya musu rashin kunya,su Chika suna ta yiwa Naila addua sunyi jugum jugum,Spark sai yanzu yasan ya tambaya yaji haihuwa da wahala,ya Kalli Chika yace wai da wahala ne haka,Chika tace la'ilahaillahu ai mutuwa ce da kanta,Ikhy tace azaba kenan bana marmari yanzu tuni muka yi planning bamu sakewa da wuri Inshaallah,Spark ya sake rudewa ko Sallah ya kasa yi sai da kyar,har dare shuru har yayi Sallar Isha shuru Yana ta addua, Ma'aikatan lafiya suna ta Bada agaji sosai,Naila aka ce tayi Nishi tace karfina ya kare bazan iya ba wlh,Goggo tace in zaki yi kiyi,Naila tace mutuwa zanyi,Spark zama yayi a kujera Dan kafarsa baza ta iya daukansa ba,sai ya fara hawaye tun Yana Yar kwallarsa a boye har ya kasa boyewa,ba sauti sai hawaye,Mima tazo tana lallashinsa tace zata haihu lafiya inshaallah ka daina damuwa duk haka muka yi muma,Spark yace wlh da nasan haka ne da banyi cikin nan ba,gwara ma kar nayi komai to kaddara da rabon za ayi haka,sai da ya basu dariya gaba daya har mutanen wajen da suke jinsu.
Can yaji Naila tana wani irin Nishi tana gurnani kamar zata mutu,sai Kuma yaji kukan jariri ko murna baiyi ba shi dai Yaya Naila,Naila tana haihuwa ta daina gani sai a hankali ta farfado a hankali ta dawo hayyacinta,ta haihu lafiya komai ta gama shi lokaci guda babu wani jiran komai,Namiji ta haifo katon gaske sai yayi kama biyu shi ba Naila ba shi ba Spark ba haka yake,Spark yaji dai Muryar Naila tana cewa Goggo Alhmdllh nuna min shi,Ashe zan iya haihuwa,sai lokacin Spark yaji salama,Dan windon da yake lekawa sun rufe abinsu tuni sabo da ya dame su da leke tun farkon kawota.
Mima suna Murna suka ce Alhmdllh da lafiya ma Inshaallah,Sai da aka yiwa Naila duk abinda ya dace da Allurai da komai suka cire mata Jinin mararta,ga Allura taji karfi a jikinta Goggo ta sa tayi wanka a toilet din,Dake asibitin na manya ne kamar kana gidanka ko Ina kamshi,haka tayi wanka da sabulu me kamshi tace kayan da suka baci a zubar,Goggo tace baki isa ba tana fitowa aka canja mata daki bayan Goggo ta wanke kayan da suka Baci,babu ma abinda ta bata sai iya rigar jikinta,Naila ta shirya kanta tace da kyar nake Shirin Nan iska daukana take sai naji bani da nauyi,Goggo tace ai kin samu me sauki wlh kin haihu lafiya wata ai bata Isa ta iya tashi yanzu ba,Naila tace Chika sai da ta kwana ma sannan ta iya yin wanka.
Jariri Yana nade a cikin showel fari aka sa masa kayansa farare tas da shi Yana ta baccinsa.
Spark ya matsu yaga Nailansa amma Goggo ta hana shiga sai sun shirya.
Naila tunda ta canja kaya ta zura Abaya da wondonta dogo bayan ta shirya kanta ta kwanta bacci na son yin gaba da ita ga wahalar haihuwa,daga haihuwa ai baka isa kaji dai dai ba.
Goggo ce tace ta fito daga wani dakin ta kofar baya ashe aka canja musu room,ta tako da Dan Nisa tace muna Nan fa kuzo kuga jariri da Me jego an haihu lafiya anyi arziki,Spark ne a gaba ya wuce Goggo tace har tayi wanka fa yanzu abinci nake so taci kafin ta huta,Spark yace yanzu za a kawo ai,suna shiga ciki suka hada Ido da Naila Dake kwance,suka sakarwa juna murmushi harda wani signa da Ido wai su sunyi Da,Mima ta karbi jariri tana cewa Masha Allah lallai an samu Karuwa,Naila tace Allah ya nufa,Goggo ta make ta tace ku ko kunyar Dan fari bakya ji a gaban sirika,Maman Rafeeq tace Allah ya raya bisa sunna,Naila tace Goggo nace Ameen?nidai zance Ameen ai addua ce,dariya aka yi Spark yace Allahumma Ameen,Spark ya Kalli Naila duk har ta canja da Gani ta Sha wahala,hannu ya mika mata Yana zaune a gefen bed din ta saka nata ciki,yace sannu kin Sha wahala,Finally dai an haihu na huta da cizo da kuka da masifa,Naila tayi dariya tace kunya ma nake ji yanzu in na tuna,yanzu me kike so? Cikinta ta nuna Masa tace yunwa kamar zanyi me a bani abinci Dan Allah,Arham ne ya shugo tare da Basma da flask wurin kala hudu na abinci daban daban,ga take away Kuma da Spark yace ya taho da shi na fruits da nama me ruwa ruwa, yogurt da sauransu,shayi aka hada mata lafiyayye ta mike zaune Spark Yana Bata a Baki sauran suna ta hirar su,Maman Rafeeq ta Kalli Arham taga ya juya can wai gyara mata adon rigarta yake bayan adon a Saman Boobs dinta suke,rankwashi ta zuba Masa tace Kai dai Allah wadaran halinka,nifa Mima gaba daya yaron nan naki ya kwance min Dan iska fitsararre,Arham yayi dariya yace idan kishi kike yi kawo na gyara miki kema gashi Nan an miki tuta a wajen ai,yaron ya karba Yana Masa addua,Maman Rafeeq tace Allah yasa adduarka tayi Masa aiki badalallen yaro,Mima tayi dariya tace kin da damar min yaro Dan kinje gidansa ya Koro ki sai ki dame shi,Arham yace gani tayi ana soyayyar da ita a zamaninsu babu irinta shine take kishi,Maman Rafeeq tace kaji min yaro ni da mijina yake Dan Sudan mene bai sani ba,har ka fadawa Balarabe kauna.