Sashe 19
Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kubra ta dawo baya Beauty ta ja mota suka tafi,Abba yace Allah ya bani kudi na siyawa Yar Inna mota itama ta dinga kaimu unguwa,Beauty tace Kai fa Abba,Ina ni ko Keke bazan iya tukawa ba ai sai nayi hatsari naje na daki trailer bani da wannan kokarin Yar Inna dai Jaruma ita ta tuka,suna hira suka je Abba yace Chinaza ayi mata me kyau har relaxer a sa mata, gashin nan nata a Maida min shi na turawa,Chinaza ita kanta dariya take,Yar Inna tace baza ayi min kitso ba? Yace a'a sai wani Jikon na gaji da shi,aka gyarawa Yar Inna gashi gyara na gaske kamar Amarya za a kaita gidan miji haka aka mata,Abba ya nuna donut a Jikin hoto yace shi za ayiwa Yar Inna,Chinaza tayi mata sosai gashi ya zuba kyau,suna zaune sunfi 1hr ana Abu daya sannan Beauty ta shugo Abba yace ni na gaji Ina jiranku a mota ya shiga mota,aka yiwa Beauty itama nata ana gamawa Abba ya dawo ya biya kudin duka, Beauty tace har zan biya ma,yace a'a an gode miki jeki da abinki,da a baya ne ai bazan biya miki ba ko Yar Innar tayi kadan na biya mata kudin saloon,ki tambayeta kiji taci wahala,ko man gyada bana siya,yanzu kuwa bani da matsala zan mata ko mene.
Beauty tayi murmushi suka tafi.
Suna mota Abba yace yau Yar Inna sai ta Sha Ice cream a garin nan, Kai mu a siyo mata,Beauty ta wuce wajen Ice cream da kayan makulashe,Abba ATM dinsa ya mikawa Yar Inna yace kuje ku siyo, Beauty da Yar Inna suka shiga abinsu suna Hira suka yo siyayyar kayan makulashe sosai kuwa har yara aka siyowa,Beauty ma ta siyo nata duk a cikin kudin Abba suka dawo mota,Yar Inna ta mika Masa ATM card dinsa tace gashi,ya karba kawai yace nasan an min tafka tafka da barnar kudi,Kubra tace to ba kudinmu bane kudinka ai nawa ne,yace uhm haka kuka iya da wayo.
Gida suka koma suka baje kayan makulashe har Abba kowa Yana cin abinda ya Masa,har yara suka dawo suma suka karbi nasu,Beauty har dare tana gidan,Abba yace kinyi girki dai ko? Kinzo nan kin rashe ana ta cin kudina dake ya batun Dana an Masa girki ko? Beauty tace har can naje na Kai Masa abinci Kuma nayi wani ma ya sani,a gidan ne tunani nake yi ko zan sauka lafiya ko Kuma a'a,Abba yace ki sauka daga Ina? da Ina kika hau ? Dariya Beauty tayi tace Abba ko zan haihu nace,yace au lafiya zaki haihu Inshaallah,tace Allah yasa,yace Ameen,yace Naila ta nake wa kwadayin samun cikin nan gata da dangin Miji masu surutun tsiya,bari na kirata naji Yaya,Naila ya kira ta daga suka gaisa yace ya gidan tace Abba lafiya so nake na wani satin zanzo,yace yanzu Naila kina wannan gidan me kyau har marmarin fita unguwa kike? Ai idan da nine ke wlh ba Inda zan fita Ina gida kullum Ina Jin dadina,Naila tace Abba ni na gaji da shi ma makaranta fa zai sani,Abba yace Inye Ashe dai za a gaji Yar Inna a Ilimi,to Allah ya taimaka,yanzu watanki nawa da bari ne? Naila tace wata biyu da Yan kwanaki Abba,yace Kuma ba komai? Tace ba komai Abba banji komai ba ko ciwon Kai bana yi bare na sa rai,Abba yace to na kusa Kuma fara yi miki kuka Naila abin nan yayi yawa sai tausayinki ya sani kuka Kuma,Kuma mijin naki kalau yake? Naila tace kalau yake Abba lafiya lafiya muke komai,Abba da Yar tasa Naila ba kunya,yace to Allah ya kawo Ina ta Miki addua,jiya ma tsohuwarki bacci na hanata sai da muka yi sallar dare sabo da muyi muku addua,Naila tace na gode Abba amma na karaya da haihuwar nan,Abba ko wacce in aka yi aurenta sai ta samu ciki.
Abba yace to ai lamarin Allah ne ba a Masa dole shi yake bayarwa,irin su Jauro Kuma suce me? Gwara ke kinyi bari Jauro ko Jinin Haila bayayi,Naila ta kwashe da dariya,Abba yace Allah da Jauro mace ne ko Jinin Haila bazai yi ba bare ma a sa rai zai haihu.
Naila tayi dariya kamar me har suka gama waya,suna gama waya yace Beauty tashi ki tafi gida kar Dana ya dawo bakya nan,kije ki kular min da Dana,ga surukanki amma bakya kiyi da ita,Beauty tana dariya ta mike ta dauki Jakarta,tace Abba zan Kara cake din nan,Abba yace ajiye Yar Inna ce zata karya da shi da safe,Kubra tace na bar mata,Abba yace gobe ma rana ce Kubra,Beauty dai ta dauki cake tayi Sallama ta tafi,Abba yace kice Ina gaida me gidan.
Spark ne ya dawo ya samu Nailansa tayi shuru tana tunani,a gefenta ya zauna tare da Dora kansa a kirjinta ya kwanta ya furta duk tunanin cikin ne? Nasan bazai wuce tunanin haihuwa ba,wai ni da kika damu kanki Naila na taba miki complain? Ni wlh ban damu da dole sai na haihu ba,idan Allah bai bawa mutum ba kashe kansa zaiyi,wani yaron ma da masifa ne in aka baka shi,Kuma ko Shekara bamu yi ba amma kinbi Kin damu kanki,damuwarki baza ta Baki ba ko ta hanaki,in ma zaki hakura ki karbi kaddara ki hakura,addua ce kawai taki na mene na damuwa,bana son wannan abin da kike yi,da Allah kike fushi ko da wa tunda shine bai baki ba,Naila tace nifa ba tunanin haihuwa nake ba,bana son karya fada min meke damunki to ko takalma kika samo latest a siya miki a huta tunda ke rayuwarki a takalmin sawa zata kare,dariya tayi tace Allah ba wannan bane kawai yau ne naji bana Jin dadi sai na dinga Jin kunci da haushin kowa,Spark yace ko period ne? tace a'a haka kawai sai naji kamar nayi kuka, Spark yace to yi kukan mana tunda gani ba sai na lallashe ki ba,gidan Rafeeq zaka kaini na Dade banje ba naje naga me ciki Ikhram,murmushi yayi yace dazu naji yace yau bazai bude gida ba Kwalbewa zai yini Yana yi na matsa Masa a Office kwana biyu baiyi komai ba
Muje mu hanashi sakewa,dariya Naila tayi tace ku dai wlh kamar abokai,Spark yace Khalid yazo ma da matarsa suna gari yace zai je can muje kawai,tashi tayi suka shiga wanka tare, Spark duk yanda hankalinsa ya tashi a toilet ya so ya kwalbe Naila taki yarda yau,shi tunda ya aureta bai taba nema ta hanashi ba sai yau,sai ta dinga Wayancewa,kyaleta yayi Bai nuna ya damu ba tunda jiki da jini sai ya rabu da ita suka ci kwalliya suka fito zuwa gidan Rafeeq,itace ke driving dinsu suna ta hirar su ta masoya,yace an dai hanani Kwalbewa,Naila tayi murmushi tace sai mun dawo zan baka Bado karka damu,nasan halinka sai ka fara Jin Haushin mutane.
Washe gari Mero ta shirya breakfast,tana tsaye a Palo tana jiran Ihsan ta fito sai ta ganta ta fito daga bedroom a kasa,Haneef ta gani ya sakko daga sama dakinsa,Mero tace a'a lafiya? Haneef yace da aka yi me? tace naga ka fito daga sama dakinka daban,itama ta fito daga kasa dakinta daban fada kuka yi?me ya hada ku kamata yayi ace Kuna Jone ana tashin ku da kyar,ta bude Ido tace Baby kace uhm uhm koma bacci ban gama Jin dumin jikinki ba,amma sai na ganku baram baram,Kai kayi gabas da Kai ita tayi arewa da nata kan,Kai da zanji kace I love you,tace I miss you,ta lumshe ido,kayi mata kallon kauna,ya haka ne bafa mu gane ba mu,Ihsan tace amma ke ban taba ganin Yar shishigi irinki ba,Ina ruwanki to,mata da miji kika sani ko dazu na sakko na shiga wannan dakin.
Mero tace karya ne Aunty tun asuba Ina palon nan Banga motsin kowa ba,Haneef yace kowa dakinsa daban yake kwana Khadija bama hada shimfida,Mero ta bude Baki tace ka kyaleta? Wlh ka Mori sadakinka ko ka Kara aure hauka ake a garin Fir'auna ka taso wlh karka yarda,Haneef ya boye dariyarsa,Ihsan takaicin Khadija ya kamata tace ke na Kore ki daga aiki Yar iska marar mutunci marar tarbiyya Ina ruwanki da aurena,bana shiga harkar mutum amma ke wlh mun sa kafar wando Daya dake,Mero tace Oga ya dakko ni ba ke ba Kuma gyara nayi Allah ya Gani ko a Islamiyya Malam yace in kaga ana ba daidai ba in har kana da hali ka Hana to naga Ina da hali Kuma zan iya shi yasa,Allah ya bamu Ilimi mun nema Kuma mun samu dole mu Fadi gaskiya Mero ta furta kamar gidanta ne,Shi Haneef dadi yaji ta birge shi,dama Ihsan ta dame shi,dining suka zauna,Ihsan ta bude abubuwan sai ta toshe hanci tace wannan wanne irin soye soye ne,Haneef ya kalla yaga shi normal komai ya Masa ya zauna yace serve me,Mero tace ya Maka Kai? Yace yes yayi min,tace an gama ta fara zuba Masa.
AsmaBaffa
[2/20, 2:14 AM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI
BOOK 3
~TAIMAKO~
26-30
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM
PAGE NAKI NE
Chuzahraumar