← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 68

Sashe 12

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?

Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din

https://wa.link/49vn47

Jauro ya Kalli Abba Dolo yace bazan biye maka ba,ni ba Kubra bace itace ya zama dole ta dinga biye Maka Banda ni, Abba yace an dora ka a keken bera,ka Sha amarcinka Jauro ni ba wani Abu nace Maka ba,ya maganar zuwan naku Abuja? Jauro yace so nake sai na koma wajen Habiba itama nayi mata kwana biyun ta sai muje kasan mata sai tace sai da kwananta ya zagayo na takalo unguwa,Abba yace ba tace ta baka sati ba,Jauro yace Kai sai na zauna nayi satin? karya take gwada ni tayi,baka San tsiyar mata ba tunda baka taba yin mata biyu ba?

Abba yace to ka koma kace ka fada baza ka iya har sati ba tare da ita ba,itama ka zuga mata karya tunda yanzu dama Kai munafukin mata ne,ban gane munafukin mata ba,Abba yace to Nan kazo kace Maman Annoor ba wata kamarta,can ka koma kace ba kamar Habiba ai ka zama Dan iska kawai a gari,ni bazan iya Kara aure ba sabo da dole na Fadi gaskiya,idan naji Amarya ta kwace ni zan fadawa Yar Inna gaskiya nace ni can yafi dadi,idan Yar Inna ce ta kwace ni sai na fadawa Amarya kaga zaman aure bazai yuwu da haka ba ni Kuma dole sai na fada shi yasa gwara na hakura ,suje da kyawunsu da komai zan karasa da na Kubra.
Jauro yayi dariya yace dama mata biyu ai sai mu gwarazan Maza.

Bayan sati daya Abba da shi za Azo Abuja yace ko Dan yazo yaga gidan auren yarsa ai yazo,Jauro,Annoor,Iman sai Haidar,Jauro duk ya biya kudin jirgi harda Maman Iman Rahma,Abba me 'ya tuni ya fadawa Naila zasu zo da baki,tare da Yar aiki da su Mufee suka shirya girke girke,Spark yau fasa fita yayi,tace baza ka fita bane yau? Yace Ina zanje surukaina zasu zo ai dole na zauna,Naila sai da suka gama komai suka gyara gidan sannan su Mufee suka tafi gida,Naila yanzu har kannen miji ake sawa aiki.

Spark driver ya tura aka dakko su har gida,Abba yau yaga gidan 'yarsa,yace Allah ya Kara zaunar da ku lafiya baza ki fita daga gidan Nan ba Naila, Aljannar duniya, da nasan abin ya Kai haka ai kullum tsaiwar dare zan dinga yi karki fito daga gidan nan,Iman tana kusa da Annoor dinta,ita da Babar tata sai kallon kallo sabo da rashin shakuwa,Suna shiga Sanyi da kamshi ya dake su,Naila ta musu sannu da zuwa suka zauna,Abba yace Naila ki rage cin dadin nan kar kiba ta miki yawa ki jawa kanki ya dinga hango Yan shawalwalai,dariya suka yi,Naila tace Abba ni Ina naga wata kiba a haka,gaisawa suka yi da juna sannan ta haura sama ta kira Spark tace sunzo wai nayi kiba Inji Abba? Spark yace to kina ta cin kudina kin hanani Tara abin duniya ba dole ba,dariya Naila tayi ta jawo hannunsa ya mike suka fita,Jauro yace Ashe masu gidan ana Nan Kai sai kace Amarya,Spark ya iso ya gaisar da su da ladabi ya mikawa Annoor hannu suka gaisa,Iman tana makale a Jikin mijinta tayi shuru.

Abba yace ya Banga kayan ciye ciye bane ni bana so a sani gaba da magana ko lemo babu gwara a ajiye min abinci a tafi a bani waje,Naila ta mike ta dinga jera musu abin ci da Sha,Abba ya Kalli Spark yace Allah ya Baki Naila Lada ashe haka kike Shan wahala a gidan miji Yana kallo bazai tayaki ba,dama samun miji irinmu a zamanin nan ai sai an tona,Uwarki ta fiki dace Naila data sameni,da nine bazan zira mata Ido ta dinga aiki haka ba,Jauro yace ai yanzu babu irinmu a kasar Nan sai dai ko a Larabawa, Su Annoor suna ta dariya,Maman Iman tace ku don Allah baza kuyi shuru ba agaban yaran ku,Jauro yace a'a bama shuru mu bakinmu kalau yake fes kullum ga brush ga aswaki ta ya za muyi shuru,Spark shi dai dariya yake kawai dan abin na su Abba Dolo sai Ido.
Ba ruwansu suka bude abinci sai da suka zaba,Naila tace ko a Kai Dining? Abba yace a'a muna da me ciwon baya Jauro kawo mana abin zama mu a kasa zamu zauna.

Naila taje ta kawo musu suka baje a kasa,Iman ta zubawa Annoor su suna kujera,Abba yace ku a sama zaki ci? Annoor yace ya za ayi ta zauna a kasa Iman a'a,Jauro yace Kai yaro munga Habiba ma yanzu ta hakura zama take,Nan wai Kai gyara kake taya matarka? Kayi ka gama,Haidar tunda aka zo aka gaisa baiyi magana ba sai lokacin yace ni ba me zuba min wato ko naci ko na barshi

Naila har ta yunkura zata mike kiri kiri Spark ya jawo rigarta ana kallo ya fuske yace zauna,Haidar yace Allah sarki ai shike nan ya zuba abinsa,Annoor Yana ta Masa dariya yace wlh Kuma matata baza ta zuba Maka ko ruwa ba,Abba yace shi yasa naki zuwa da Yar Inna suka kwashe da dariya,Haidar yace ni me zance matarka tayi min Abba ai uwata ce,Abba yace ake kaunar mahaukaciya ma bare tsohuwa da hankalinta,har abada baza ka samu irin Yar Inna ba,ga Maman Iman kaji tarihinta dai to bare dattijuwa irin Yar Inna a kanta sai ka wulakanta budurwa,Spark Yana ta dariyar Abba da son Yar Inna.

Sai da suka koshi suka huta sannan mazan suka tafi masallaci Naila ta Kai su Iman bedroom suka yi sallah suka kwanta suna hutawa,Maman Iman bacci tayi Iman ta fito ta samu Naila suna gyara palon da me aiki,ta taya su suka yi wanke wanke suka gyara ko Ina har kitchen,Iman tace Dan Allah Naila kice na kwana a nan gidan kar a tafi dani hotel,Naila tace sabo da me? Iman tace to mijina baida hakuri bazai bari na huta ba na gaji wlh duk ya kashe min kugu,Naila tayi dariya tace zaki Saba ne,ni dai Dan Allah kice zan kwana a nan,Naila tace to shike nan zan gwada,harda bawa Iman Yan tsumi na gyaran jiki ta Sha abinta ta bata wasu ta sa a jaka.

Jauro bayan sun dawo daga sallah yace Maman Haidar ta turo min address din gidan su Haidar,Naila tace ni Ina ganin kamar haidar da wani wlh na rasa gidan waye Kuma,sai naga kamar Yana da kanne kamar babu na rasa Inda nasan me kamar sa,Abba yace ai ga address zamu je har gidan,Spark ya karbi Address din ya duba yace a'a to wannan ai gidan su Rafeeq kanina ne,Jauro yace mutumin fa bai taba haihuwa ba,Ae shine fa sunansa Aliyu Shima sunansu Daya da mijin Mummy amma shi ba a kiransa da Aliyu Sunan garinsu ake fada Masa.

Yace bari na kira Rafeeq muje gidan kawai ,Rafeeq ya kira suna tare da Ikhram dinsa ya gaji da halinta ya kaita asibiti cikinta ma yafi na Chika kwanaki a duniya,Spark ya fada Masa dai a gurguje,yace to ku sameni a gidan ai kuwa mijin Mama Yana gida yau,suka tafi Rafeeq ma ya tafi da Ikhram can,Spark suka tafi gaba daya,suna zuwa Suka shiga har Palo, Maman Rafeeq Hannun bibiyu ta tarbe su,Jauro yace wajen me gidan muka zo,tace ai kuwa Yana Nan ta mike taje ta fada Masa ta dawo tace yanzu zai fito,ta kawo musu ruwa da lemo.

Fitowa yayi cikin shiga ta alfarma Yana tafiya ta manyan masu kudi yanda ya Saba,har ya bude baki zaiyi masifa me ya kawo Maza har palon matarsa baza a jira shi a waje ba sai suka yi Ido biyu da Maman Iman,Baki ya bude mamaki ya kama shi,yace Rahma me zan gani kece? Rahma ta mike tsaye tace nice nan Sudan,Spark yace dama na fada muku da Sudan aka sanshi amma sunansa Aliyu.

Rahma ta dafa Iman tace ga Yarka,Maman Rafeeq da Rafeeq suka zaro ido waje,Jauro yace ga Danka Kuma bakin Dan iska tambadadden dattijo,Abba yace a'a Jauro yaransa suna ji kana zagar musu Uba ba dadi,Haidar yace mene amfaninsa ni wlh a Kara Masa wani,a wajen Aliyu Sudan ya durkushe yayi zaman dirshan a kasa ya Dora hannaye a Kai Yana kuka,yace Rahma ki yafe min na cutar dake son ki ne ya sa na aikata miki haka,har lokacin kina halin ciwon hauka Ina ta bibiyar Inda kike har na ganki a kango na da nake ginawa daga nan zuciyata ta kasa hakuri Dake har naci gaba da amfani dake,dalilin sonki na kasa kula da matata ta aure Ina zaluntarta,farko da na fara bataki Baki samu ciki ba sai dai lokacin da kike halin ciwo na hauka tabbas wlh wannan 'yata ce,Jauro yace Kai rufe mana baki algungumi ko kunya baka ji duk mutanen unguwa sun San kaine ka aikata tunda ana ganinka kana fita da ita,Kai rashin Imaninka yayi yawa mace tana ciwon hauka,Rahma ce tayi magana tace sharrin shedan ne laifin kaka ne data Hana shi ni,ni nasan Yana so na,duk ita ce ta jawo min,Aliyu Sudan yace kwarai kuwa.

Abba yace to shi Kuma Haidar din fa? Jauro yace ai kasan matar da tazo aiki gidanka Yar wanke wanke da shara Binta,kayi mata ciki kuka koreta Kai da matarka,Jauro ya nuna Maman Rafeeq, kece da laifinki wai ku son miji son aure kar asiri ya tonu Kuna kallo mazajenku suna aikata fasadi sai ku Goya musu baya ku kare zancen to yanzu gashi ke ba take yake ba Kuma gashi ya tara yara har biyu ba yaran sunna ba,ke Kuma Allah bai baki naki ba,mutane baza su hakura da jarabawar Allah ba,Kun cuci yara kawai.
Chapter 12 · 0% Book details