← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 68

Sashe 15

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Spark kuwa tunda yayi waya da Mima ta fada Masa hukuncin da aka yanke duk da ya San zai faru sai da ya shiga damuwa,Yana Office gida ya dawo jikinsa a sanyaye ransa babu dadi,Naila tana Palo tana danna waya ya shugo,ta ganshi wani iri tace wa ya taba min Mijina? Mikewa tayi tsaye ta rungume shi,kankameta yayi kawai taji Spark Yana kuka,Naila bata San an yankewa Mummy hukunci ba,sai da taji tsoro ta janye jikinta da sauri ta rike hannayensa tace lafiya? Me ya faru?
Baby mutuwa aka yi? yace Mummy ta tana gidan yari live in prison,Naila tace oh my God Baby I'm so sorry,Allah yasa wannan hukuncin ya zama silar shigarta Aljanna, Inshaallah baza ta Sha wahala ba ai VIP za a Maida ta ko? Naila ta sa hannaye ta goge masa hawayensa tace ai ba mutuwa tayi ba Baby,kullum in kana so zaka je ka ganta ko? Naila harda hawayen karya wai Dan ta nuna ta damu da damuwarsa, tace gobe ma zamu je ai ko duk abinda take so za a bata.
Rafeeq ne yazo gidan yace Spark kayi rashin Mamanka,tashi yayi ya haura sama kawai kar ma a dame shi zai iya yin kuka a gaban mutane.

Naila tace Kai fa kuka yake baka sani ba,Rafeeq yayi dariya yace Spark da kuka cab,sai kace ta mutu,waye yace tayi kisan Kai,abubuwa ma iri iri duk tayi Kuma yasan hukuncin nan mene abin kuka kawai shagwaba yake miki sabo da kina lallashinsa,naga mota Allah ya sanya Alkhairi,Naila tace Ameen,yace kin fa ishe mu kin kankane mana kayan Dan uwa,Dariya Naila tayi tace Dan bakin ciki sai dai ya mutu,Rafeeq yace zaki ga makirci,Misam ne ya dawo daga kotu yazo direct Shima wajen Spark.

Yace Ina Spark Dan wulakanci sai yaki zuwa,Rafeeq yace kuka yake Yana daki,Misam yace Allah sarkiyiyiyiyi...dole yayi kuka wlh tunda aka tsige shi a nono aka bata,Kai Spark yasha gata a duniya gaba daya Bata bari ya rayu a kasar Nan sosai ba,taje ta tare da shi a kasar waje yayi karatu ta sakar Masa kudi sai da ya zama me kudi ta ko Ina,Kai ku kyale shi yayi kuka Dan Allah.
Ke Naila sai na ganki a nan kije ki kwalbe shi wlh ras zai dawo karya yake,in ya Kara ko kwalla Allah ya bani abinda nake nema cewar Misam.

Naila tace space na bashi naga Yana bukatar a barshi shi kadai,Arham ne yazo yace Kuzo ku taimakeni,sai da ya basu tsoro sun zaci wani Abu ne,yace Papa ya kashe ni wlh ya zabo min wata aladiya Kuma wlh wai sai na aure ta ni ban isa aure ba,a fada Masa ban balaga ba,ya samu waje ya zauna ya zuba tagumi,Rafeeq yace Kai har gata ne da Kai haka sai an zabo Maka mata? Misam yace Kai ba dai wannan Basma ba ta kauye? Na ganta an kawota Papa yace karatu zata yi a Nan,Arham yace ita ce,wannan kucakar,wai na Kai Masa samfur din Naila wai ai yaga itama fara ce yo ni fari nake so Nima ai fari ne,yarinya sododuwa, Rafeeq ya sheke da dariya yace ya batun kudin? Arham yace na gagara ganewa kirjin Maza ne ko na mata,kawai an dakko min mata Maza,Misam yace a'a Arham wlh karya kake wannan yarinyar kace kawai Yar kauye ce zan yarda amma tana da komai me kyau wlh,Arham yace Kai nifa nono inchi inchi ba Wanda ban taba naji ba,ta ya za ace a nan kirjin wata Basma akwai shi,ai Kai Misam ka Saba Bariki kowa me kyau ce a wajenka dole kace haka,Ashar Misam ya dura Masa yace Dan uwarka ba na tuba ba Yar ubanka na taba yanzu.

Ai abin Yana jininka ni dai ku fadawa Papa kawai ya canja min wata,yace bazai canja ba ya riga ya sanar da iyayenta aure ba fashi,dama Kai Dan Iska ne Arham mata kake tabawa kirji? Arham yace duk Yan ajinmu kowacce naji nata,yanzu dai nayi aji class ne dani ba na kowa zan kula ba,amma ni wlh duk Wacce bata da shi bana so,ya zauna ya zuba tagumi,yace ni da nake so a samo min wacce kamar zan hau na zauna a kai sai a dakko min allo,kaje ka fadawa Papa mu ba ruwanmu cewar Rafeeq,Arham yace cewa yayi fa zai sa a kulle ni a guard room dole sai na aure ta ya Ilahi ni ba girma nayi ba,na mene ake gaggawa sai an kaini dakin aure.

Misam ya sheke da dariya yace kar ma a turoka Office dina aiki,ni da an bani jari zan tsaya da kafafu na me zanzo wajenka nayi,ni da Shaheed an bamu jari an kaimu kasuwa an gama mana komai farawa kawai zamuyi,yanzu koya ma mukeyi har motoci zamu dinga siyarwa,to kaje ka fadawa Mima ta rokar ma Papa a canja,Arham yace dariya take ta yi tana murna yanzu yarinyar ma kaunar ta take yi har da yi mata kitso yau fa,nidai Ina zan sa kaina bakina ya ja min.

Har su Rafeeq suka tafi Arham yace shi bazai koma gida ba yayi yaji,Naila tace to ai mu Nan akwai wajen zama Arham abinci Yana kitchen bari naje wajen spark kuka yake,Arham yace kuka Kuma? Sabo da Mummy? tace ae yace Dan Tani su jefar da mukullin gidan yari a teku,zanyi dai dan missing dinta kadan tunda Ina more cinyarta watarana,jeki kina bashi Uhumhum dinsa zaki ji luf wlh karya yake so yake ki bashi hakkinsa cikin sadakinsa,Naila tace Allah ya shirye ka ta haura sama tana dariya,Arham yace ga samfur an Kai sabo da idon Papa yayi shutdown shike nan sai ya dakko Basma daga kauye,kauye fa...

Naila tana shiga ta samu Spark a kwance yayi shuru Yana tunani cikin damuwa,a gefensa ta kwanta ta fara lallaba shi sai gashi ya bige da romance ya daina kunci...

AsmaBaffa
[2/18, 7:33 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~

21-25

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM

Page naki ne
Iya2

Hey lovelies

Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?

Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?

Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?

Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?

Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din

https://wa.link/49vn47

Spark yaji Naila a jikinsa,narkewa yayi Yana shagwaba kamar yaro Dan yaye,duk ya makalkaleta Yana cewa Mummy ta tana can,Naila tana lallaba shi tace kayi hakuri zamu je ko gobe ka ganta normal,zata saba inshaallah,Yau zata yi Kwanan wahala ya furta,Naila ta gaji da korafin Spark yaki yayi shuru,ta hau romancing dinsa tace a ranta bari na gwada maganar su Misam,na tafi ace baka damu da miji ba, daga Dan fara kiss sai ga Spark ya zake,Booby daya aka sa Masa a baki tuni ya manta da wata Mummy a prison kamar Wanda aka Masa Allura ya watsake,Naila tace eyya bama ka Jin karfi a bari later kwanta ka huta kaji,muryarsa taji yace da karfi na zan iya komai ma,dariya tayi tace au da karfinka? Yace sosai .

Mero tana Isa gida sai Ganinta aka yi tsidik a cikin gidansu na bulon siminti ne amma kamar kango haka yake,wani tsohon rubabben gini ne tun ya zaman,dakuna uku ne a gidan sai kitchen din langa langa na karfe sai toilet,Inna ta iske a kitchen tana aikin soya awararta ta yamma,Mero tayi Sallama ta shiga,Jummai ta leko tace ya naji kamar Khadija,Baki ta bude duk taji kunyar yarta ta kasa zuwa su ganta a gidan yari,tace wani satin muke cewa zamu zo Khadija Ashe kina tafe,Munnir da ya fito daga daki yace wlh da kudi Yaya Khadija cewa tayi baza su ba tsada tayi yawa.

Mero tace ai gani na dawo,Jummai ta fito daga kitchen tace ya akayi na ganki Kuma? gudowa kika yi? Mero tabarma ta dakko ta shimfida ta zauna tace a bani abinci naci tukun naci na huta sai naji dadin labari,Ina Abbu? ya fita kasuwa,Jummai kitchen ta koma ta zubawa Mero shinkafa da wake da Mai da yaji ta kawo mata ta kawo mata awara a plate tace Kai Munnir ebo mata ruwa,Khadija ta zauna ta fara cin abinci sai da ta cinye komai tas ta Sha ruwa sannan bakinta ya bude,Abbu ne yayi Sallama ya shugo suka amsa,Baki ya bude ganin Khadija a gida,yace ya aka yi haka ta faru? Farin ciki ya kama shi ya washe baki yace Khadija kece?

Mero tace nice mana da baku zo ba gashi na fito,wai ku haifi 'ya a cikinku amma bakwa sonta haka ake rayuwa,kudi yafi da,Kun San bakwa son yara baza ku iya kula da su ba kuka haifo mu,Allah ya dube ku ya Baku yara biyu kacal amma baza ku iya rike su ba,sabo da son kudi,Abbu Murya a sanyaye yace wallahi tallahi Khadija ba laifi na bane laifin Jummai....Jummai itace mijin ko Kaine Abbu,ka zauna tana gara ka kamar tayar mota" ka karo kishiya mana kayi aure,yo magana ta Allah fa,Jummai baki ta bude tace Khadija ni kike cewa a karo min kishiya? Abbu yace kwantar da hankalinki Jummai bazan ma iya yi miki kishiya ba,Mero tana jinsa takaici ya kamata sosai na halin mahaifin su,Jummai tace tunda halinki zaki dawo da shi na fito na fito da ni akan ke sai kin koya min zaman rayuwa to wallahi ki koma aikatau,ya zama dole aikatau zan kaiki tunda samarin ma ke ba kula su kike ba bare ace za a miki aure to dole ki koma aikin wanke wanke da shara domin ki samo mana kudi,idan ba haka ba wallahi da katifa za a kaiki gidan miji,Khadija tace a kaini da abinda Allah ya hore,Abbu Yana ji Yana gani yayi shuru baya ko magana.
Chapter 15 · 0% Book details