← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 68

Sashe 53

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Chika tana Jin labari tace saura ni Allah yasa Nima na haihu lafiya,Misam yace Ameen Ameen,Naila kuwa,tana ji aka bugowa Spark waya Chika ta haihu namiji Kuma yace wow Allah ya raya Rafeeq ya zama Daddy,Naila ta manna kanta a kunnen Spark wai sai ta ji,ya gama wayar sunce a fadawa Naila yace tana ji ma ya kashe wayar,yace yau dai da babu makaranta banji dadi ba gwara kina makaranta gaba daya,Dan iskanci suma masu makarantar sai su ce yau Monday guda ba lecture,Naila tace wato ka tsane ni yanzu ka gaji Dani kora ta kake yi baka son ganina sabo da ka riga ka gama dani,a baya ai baka so ma na bar kusa da Kai" ba komai,yace sorry Ina so aiki zanyi nasan halinki sai ki hanani da rigima shine fa nufi na,Ba wani wa zaka yiwa wayo,cikin ai Kai kayi min ba wani ba shine zaka ce na dame ka,ta juya ta haura sama da Yar gown dinta iya cinya sama ta tsuke kasa a bude peach ta wuce,Spark yace tab yau akwai daru,tashi yayi ya haura sama Shima,ya same ta a kwance tana waya da Abbanta, tace Abba zancen ka ya tabbata namiji ba Dan goyo bane,ban taba sanin Spark haka yake ba bashi da kirki sai yanzu da na samu ciki,tunda na samu ciki ya juya min baya sabo da ya gama dani,Spark Yana jinta bata San ma ya shugo ba,Abba yace indai ba kishiya zai miki ba ai da sauki kiyi hakuri nima uwarki Kubra hakuri nake da ita,yanzu Nima da na Goyata na sauke ta ,jiya ta karta min rashin mutunci ku dama mata ba hankali ne da ku ba,duk haka kuke Baku da tunani baku da hangen nesa bare ku samu hankali,in kin gaji kiyi yaji ki taho gida Ina da daki spare sai kiyi ta kwana da Beauty kafin mijinta ya dawo,ga Abinci kici ki bar shi,Naila tace na dawo gida Kuma Abba? Ni wlh bazan dawo ba me zanzo na zauna nayi,nifa in ba a gidana nake ba kwana Daya ma a wani wajen kamar a kan kaya nake ji na sannan Kai da zaka min nasiha ka bani shawara sai kace na dawo gida,Abba yace na gaji da yi miki nasiha da fada Naila,ke kanki kin San nasihar nan watarana Yar Inna ce take koya min sai nazo na fada,Naila ta kece da dariya Abba ya tonawa kansa asiri dama nasihar ma ba basirar sa bace,Abba nasihar ma sai an koya Maka? Ai kin San ban iya ba,Mohsin ma yasan gaskiya ba iyawa nayi ba,kin San ta ranar ma da za a kaiki gidan miji kwana nawa nayi Ina biya kafin na iya abinda Yar Inna ta koya min? Shine ai kika ga na zage Ina ta fama uwarki ce ta koya min ba yin kaina bane,ai karshen abinda zan iya nace Allah ya tsare a kula shike nan,Naila dariya take kawai,Naila tace Abba baza ka Kara da Yar Idea Dinka ba? Idea me Ina na ganta sai wacce ba a rasa ba,da fa ma ace ba sunana Hashimu Dolo ba to da sai a samu canji amma indai nine to sai dai kuyi hakuri Abbanku bazai iya abin duniya ba,ku godewa Allah da nake iya sana'a ko da akan katifa ne.

Abba yace ban fada miki ba mijinki ya siyo min sabuwar mota me tsadar gaske Baki ganta ba,ga Mohsin tun kafin ya dawo ana ta canja mana gida za muyi gate da wajen ajiye mota,gidan Sale makwafcinmu ya siye shi ya hade da namu aka rushe za ayi katon filin da gate gaba daya gidan za a sake,Naila tace mashaallah an gode to driver zaka dauka? Ina fa na barwa Yar Inna ita halak Malak ta dinga tuka ni duk Inda zanje ta kaini tunda ni dama ba wani fita nake ba,Yar Inna yanzu ta fara koya sai Murza kan mota take yi nace iyyeee uwar Naila taci gaba,Naila tayi dariya tace Abba ko driver baza a dauka ba? Yar Inna ta Isa rabu da ita Jaruma ce,shike nan to a gaishe ta yace zata ji ,Dan Allah ki zauna lafiya da mijinki,ke irin laulayin uwarku kika gado wlh hayyata,cikinku hayyata, ku hana miji sukuni,ki dinga hakuri,wa zaki samu irin mijinki a yanzu,Naila tace ai shine yake jawowa,Spark ya harde hannaye a kirji kawai Yana jinta,tace ai shine ba Dan goyo ba Abba,kune kuke ganin kirkinsa ni yake kunsawa takaici ku ya faranta muku sabo da Kuga kirkinsa,haka yake min abubuwa iri iri ta karkashin kasa shuru nake kawai Abba,Hashimu yace in zaki kwana bazan yarda ba karya kike in da gaske ne ai nace kuyi yaji ki taho mana,a'a Abba ni ka daina cewa na taho gida ai ta wani bangaren Yana da kirki,Kuma ma laifin kadan ne ai,gaskiya ba laifi,Abba yace ayi sai nazo na taso keyar Yata ta dawo gida Ina amfanin zama cikin hakuri da takura,ba sai kazo ba Abba ai Yana kamantawa da kirkinsa,Kuma fa Yana so na kawai dai watarana sai naga Yana min gani gani,zanyi zamana,Abba yace bari na kira shi na kare Masa tanadi,Naila ta furta a'a ba ruwanka Abba ni zan iya da kaina, Abba dariya yayi tun a sannan yasan tsiyar Naila ce karya take ba abinda aka mata dama gwadata ta doayi,sallama ya mata ya kashe wayar,tana Juyowa taga Spark tsorata tayi ta dafe kirji wayyo Allah dan cikina,wlh ka bani tsoro,sai ka dinga min labe kana Jin sirrina haka ake yi a duniya,yace Maza kiyi ta Kai karata iyaye dai tun basa yarda watarana zasu yarda,zaki jawo su tsaneni a banza,suce Ina miki wani Abu,to baka yi din ne? Naga rannan da nace ka siya min ankon wata cewa kayi baza ka siya ba direct ka fada min,na hakura ban ce komai ba banyi zuciya ba na kawo Maka wani agogo nace ka siya min kace to kawai ka Maida ni banza ko zancen ma baka sake yi ba,nayi shuru Nima rannan har gida Matar Yaya Khalil ta kawo wani material da kana Nan kaya tace ka siya kin siya kayi,da Sanda Ina waje ne nayi Imani jikinka na rawa zaka siya,sabo da yanzu nazo na gama yawo kayi min ciki,shine ko yaushe ka kora ni makaranta sabo da baka son ganina nima na daina zuwa makarantar bazan je ba,na fasa karatun tunda badan Allah ka sani ba sabo da ka tsaneni baka son ganina ka kaini school,kullum ban isa inyi fashi ba ka dinga masifa kenan kace Ina Maka asarar kudi haka ko bana Jin dadi sai ka kaini school ta dole to bazan je ba na daina makarantar in zaka Jani ta karfi ka Jani ka kaini,ka isheni ni na gaji duk nabi na tsane ka ma,wani kyanka wani kudinka, wani surarka,wani hallarenka,wani iya Uhum Uhum Dinka wani iya sarrafa uhm uhm Dinka,wani komai naka baya min ya daina min,yawwa ka daina ganin wani kana ja baka ja a wajena baka tafiya aradu,in sanda Ina kauye ne ka min wannan tuni sandata bata sha jininka ba ban fasa Maka Kai da Sanda ta ba,wul wul Ina wulwulata sai dai kaji gaf a goshinka,karka kaini bango ka bari na dawo Tantiriyata a gidan nan wlh baza ta maka kyau ba....tana gama masifarta tace an dai gode Maka ka siyawa Abba Mota again,tanan wajen dai anyi basira Allah ya Kara budi mun gode sosai da sosai.

Spark Yana kishingide Yana kallonta har ta gama yace Uhmmmm....kawai,tace da anyi magana an Fadi gaskiya kace Uhmmm,Uhmmm fa baza ta kaika ko Ina ba,Anbi a damu mutum,da ace ma akwai Inda zan tafi nayi sati biyu na huta ba shike nan ba,fitar ma da na tashi fita nace zanje waje kaza,to Baki da aiki ke sai unguwa Yan..Yan ..yi..yi..ya...chaccha baza kije ba,ke kullum yawo,Dan bado abin alfahari na ba dama na hana nace bazan bayar ba bana so sai an min fyade,kullum fyade ake min a gidan miji,Spark Yana jinta Yana dariya a ransa,kwanaki ma ni me miji wai ni irin zan samu Lada na zauna na sharara Maka wanki nayi guga,yini nayi Ina aiki a kayanka irin zan samu Lada, dake kai ba a ma gwaninta wai kazo ka gani sun fita kuwa ai da kin raba biyu,ke ba iya wanki kika yi ba karki Bata min kaya, maimakon kace wow Baby my life,My Heart Allah ya miki Albarka Allah ya saki a Aljanna shuru kake ji,nace ko Albarka baza ka sa min ba? Wai Allah ya saka miki a baka kiji dadin tauna,na tauna me to shinkafa? a lokacin kyaleka nayi zazzabi nake shi yasa banbi ta kanka ba,,Allah ubangiji ya kawo ranar da masu wanki da guga zasu yi yajin aiki ko Kuma wata matsala ta samu,ka rasa me Maka wanki gashi ka sake kayanka gaba daya tas baka da na sawa muga waye zai wanke Maka ko Singlet,Kuma wlh ko basu yi yajin aiki ba Ina Nan sai na kulla Maka takaici akan wanki zaka ga tsiya,kayan zan samu duk na jika su na barsu a haka,sai ka damu da wanki Ina nan da Kai.
Chapter 53 · 0% Book details