← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 68

Sashe 32

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Chika ce tace ki kyale bawan Allah da abokansa Basma,Arham kallon Basma yayi ta cukule ta turo baki,murmushi yayi yace gyara bakin to yanzu zasu tafi ma,Basma tace ni yanzu nayi course a wajen Siriki na muzurai zan dinga yi,Arham yace Papa? tace ae mana Ina da siriki Soja ace bana muzurai ai nayi asara,Mima ce ta fito da sauri Basma ta koma kujera ta zauna tare da fuskewa,Kawaye suka ce to taso ayi pics Amarya,tana shagwaba ta mike kamar sune Angon a haka aka yi pics,sun dan dade sannan suka tafi.
Mima ce tace Kaci abinci kuwa? Arham yace kika ce baki damu dani ba,tambayarka nayi ni,Basma tace na zuba da zan Kai Masa sai naga suna yin sabon abinci shine na fasa bashi tsohon abinci, yanzu sabon nake jira,Mima tace yayi masu iyawa shike nan da abinci gasu Nan iri iri duk baza a bashi ba sai anyi sabo,haka zai ta zama da yunwa kenan? Basma tace sai da na tambaye shi ai idan Yana da ulcer yace kalau yake shi,shine yasa nace a bari ayi me zafi,dariya Rafeeq yayi yace wani ya shiga uku,Arham ya harare shi da wasa ya wuce ciki,Basma ta mike a ranta tace bari naje na chafe shi,Maman Rafeeq ce tace gidan uban wa zaki je Kuma? Wannan yarinyar idan ba a taka mata birki ba wlh kafin a kaita gidansa tayi ciki,Basma a hankali yanda ba me ji tace ke kin kashe aurenki kinki zama zaki kashe mana namu auren za ace baza muyi biyayya ba,Ikhram tace Kinga Basma jeki ki Kai Masa abincin naga kina mimimi da baki,Basma tace ko minti biyar bazan ba zan dawo,sabo da iyayensa kar su ga bana kula da dansu suce baiyi dace ba Nima ala dole zan Kai,Spark yace Dan Allah jeki kina ta surutu wa ya hanaki ne,ta tafi abinta ta shige kitchen tana zuwa an gama wani girkin ta zuzzuba sai ga Arham ya shugo kitchen din da kansa,tace kaga abincin fa yanzu zan kawo,Arham yace abinka da baka Saba ba ni a barni na eba da kaina,Basma tace wlh bazai yuwu ba kace wani baka Saba ba,yace duk wannan abubuwan wa zai cinye? Basma tace Kaine muje ta tura shi waje muje,Arham yace dole zaki min,ni karki shugo min rayuwa na tabaki kije ki fadawa mutane,Nayi Dan hankali zan iya kin fadawa Papa da Mima amma banyi alkawari ba zan iya canja ra'ayina kana bani haushi zan fada,Arham yace zan saita miki bakin ai wlh,ta dauki abincin suka tafi suna zuwa dakinsa taga Junior a ciki,tace Kai junior ka daina zuwa Nan yanzu kowa yayi zamansa a dakinsa yanzu ba sa'anka bane Arham Kai da Shaheed ku dinga taka tsantsan da shiga dakin nan,Junior yayi dariya yace dama yau dinma tsautsayi ne,to tashi ka tafi naka,yace to ba musu,tace ka samo taka a Mami market dinku ta sojoji tunda Kai dole sai ka zama Soja,Junior ya dauki laptop dinsa ya fice Yana dariya.

Basma ta fara tunanin ta ya zata chafe shi tace gashi Kato ne ashe,tsaki ta ja a ranta,tace ita Naila ta ya take chafe Spark ne ita,Arham Yana kallonta Yana tsince tissue da aka watsar a dakinsa,Basma ta koma kusa da shi ya mike ya juyo zai tafi ta Masa kamar zata dauki yaro karami hannayenta a saitin hammatarsa tayi tayi ta iya ko motsa shi ta kasa,ta fara cika...ci ..cik...cikaaaaaa.....uhmmmm...
ta durkusa a kasa zata daga shi wai ta kafafunsa,tayi nishi ta dage ta kasa,gumi ta hada nan take,Arham Yana kallon ikon Allah yace mene haka? dagowa tayi tace na kasa Cika masakinka zan Maka na dagaka na cafeka shine na kasa,Arham yayi dariya yace kin makara Mima ta Dade da yi min abina tun Ina jariri har aka yaye ni,kawai kace kana min bakin cikin shiga Aljanna baza ka nuna min yanda zanyi ba,Arham yace ai sai an kwanta akeyi,Baki ta tabe tace to yaushe za a kwanta? yace yanzu ma tace to ci abincin Dan wallahi yau sai na kaddamar zan tafi.

Arham ya zauna a gefen bed harda zuba Masa abincin,yace yarinya ta fara cin Sadakin ta ashe dai da alama zaki ci kudinki 200k,wai haka aka biya dama? Arham yace ba a Baki ba? tace ae ni ba a bani ba ko sisi,yace tab tsaya naci abinci wlh baza ta sabu ba a baki abinki so ake auren ya dinga rawa ba a bawa Amarya sadaki ba Ina aure,Basma ta zauna a gefen bed tace lallai ma Kawu Dan Yana kanin ubana shi aka aura ko shi za a yiwa ciki,Arham ya sheke da dariya,yace kura da Shan bugu gardi da kwashe kudi,aje a bi min hakkina kar Kawu ya tafi kauye ba mutunci ne da shi ba,sanda Babana ya mutu ai kasa rike ni yayi,yace bazai iya ba sai yanzu anga na girma an bani sadaki na zai cinye min,sanda Ina yarinya ko fitsari nayi sai ya dinga dukana dole babata ta tafi dani agolanci shine yanzu yaji kudi yayi shuru Yana so ya samfe da su gida aje a siyi Masara a ci tuwo ni Ina nan an yi min ciki yau yawu gobe amai wlh bazan yarda ba.

Arham Yana ta dariya yace wai ke shekarunki nawa ne? tace 17yrs da wuri na gama makarantar secondary sabo da karatun kauye sai a hankali,Arham yace a dawo maganar sadaki fa,tace ai dole na karbo abina Kuma a jikina zan cinye ba wata kadara da zan siya in samu in ta siyan kayan dadi,Arham yace wanne kayan dadi gashi kullum kina ci,tace ni dai a jikina zasu kare kudin,yace uhm uhm Basma dollar tayi tashin gwauron zabi,ba ruwana ni cewar Basma" ta sa hannu ta goge masa gefen bakinsa da dan abinci ya bata, suna zaune ya ci abincinsa ya shiga wanka,Dan kwanciya tayi a gadon tace bari ya fito sai naje na nemi Kawu ya bani sadaki na,kwanciya tayi daga rufe Ido sai bacci,baccin tsiya ne da Basma kamar me cutar bacci.

Yana fitowa ya ga tana bacci ta Kalli sama,Maman Rafeeq kuwa zuwa tayi ta fadawa Mima tace tunda Basma ta tafi Kai abinci taki dawowa wlh tana can Kuma kin San yaran Nan musamman Arham din,Mima ta idar da Sallah tace jeki mana ki Koro ta ko gyaran Jikin ba a yi mata ba,Maman Rafeeq taje dakin Arham ta dinga knocking yaki magana Kuma yaki budewa kamar ba mutum,tace Arham Kai ...shuru yayi Yana Jikin mudubi Yana fesa turare tace baza ka bude kofar ba,magana yayi yace bacci nake na gaji da sallamar baki,Ina Basma ta fito,yace ai ta fita,karya kake ka bude tun kafin ranka ya baci na kira ubanka yazo da kansa,kofar ya bude ta hango Basma kalau tana bacci,tace tashe ta ta fito ke Basma ta shige ciki tare da jijjiga ta,Basma ta mike ta fito,Mama ta taso keyarta gaba.

Ba ayi miki gyaran jiki ba kike wani Kai kanki wajen namiji daga aure,ai Kya bari shi ya nemeki,Basma tace to na bari Allah ya kawo shi tunda bakwa so nayi biyayya shike nan na fadawa Papa kawai,Mama tace sabo da shi ya kawo ki ana miki Abu sai kice zaki fada Masa to dukan mu zaiyi ko me, Basma tana jinsu ana mata surutu ta wuce dakinta.
Tun daga ranar bata Kuma kula Arham ba,Mima tana kallonta ko ance Arham baici abinci ba bata magana,idan yace tazo baza ta je ba,har aka kwashe kwanaki hudu zuwa biyar,Mima da kanta taga zata raina Arham,ba abinda ake sa Basma tayi indai na Arham ne to kuwa baza tayi ba.

Tana zaune a Palo yau duk su Mima suna nan Arham yace Mima ya naga ba a gyara min bedroom dina ba? na manta ma ban sa an gyara ba, ga Basma taje ta gyara,Basma tace to kawai taki tashi tayi zamanta,Mima tace ba Dake nake ba wai me kike yi haka mijinki ne fa amma ba a isa a saki aikinsa kiyi ba.
Basma tace cewa fa kuka yi Ina Kai kaina wajen namiji na daina zuwa,in naje abinci zan Kai sai an biyo sawu na an Koro ni ana min fada Ina dalili ba sai na barshi ba tunda bakwa so,dama ni fada Aunty Naila ta min shi yasa nayi kokarin yin abinda tace Amma tunda kuka ce Ina zubar da ajina shi yasa na daina yi.

Mima tace au Ashe zuciya kika yi kenan? Ae zuciya nayi,duk yanda na Kai ga sonsa bai kai ya ku ba kuka ce bakwa so a kula da shi a barshi yaci gaba da gwaurantakarsa shine nace to na huta,Arham yace banga laifinka ba kinyi dai dai Ina bayanki,Mima ta kalle su tace shike nan Basma yanzu ba ruwan mu ki kula da mijinki,komai kece zaki dinga yi Masa a gidan nan baza a sake bin sawunki ba,Basma tace a ranta sunji wuya sunga zan raina dan su,lallabata Mima tayi tace yanzu kije ki gyara dakin amma karki Dade bana so wani Abu ya faru tun yanzu,tace to ta mike ta tafi,Arham ya Kalli Mima yace na fuskanci a gidan nan da gaske ba a kaunata ni a bani gidana na tafi wlh,Ashe kune kuke hanata yarinya tana so ta bi mijinta sau da kafa,Mima tace je ka fadawa Ubanka ya baka gidan naka idan ka isa.
Chapter 32 · 0% Book details