Sashe 50
Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Basma tana zaune me gidan Arham ya shugo,kunyarsa take ji yanzu ita Kam,Bata so ma su hada ido,kallonta yayi suka hada Ido da sauri ta janye idonta,yace shike nan an daina kallona ma bare muyi Hira,ga chewgum Ina ci zan dawo dan barikinki fa, dariya tayi kadan ta kalle shi tare furta to ci mu gani chewgum din,a gefenta ya zauna ya dawo da Kafafunta Saman cinyarsa Ya fara mata tausa, ana lallaba Basma ga chewgum ana ci tana ganin Dan barikin ta, harda cewa baza ki Dade ba zaki koma school so nake PHD kiyi Inshaallah,Basma taji dadi tace na gode Allah ya Kara budi,Arham ya furta ke zan yiwa godiya da kika bani shashshaka da mai,dariya ta kama Basma tace nidai ba ruwana Allah,motarki tana Nan anjima zan are ta na fita,tace na baka aro ka dauka,tace ai ka bani ma kudin accnt dinka haka kace harda kudin Dake accnt dinka duka,Arham yace kaiii yaushe? Wannan baram baramar ko da wasa bazan yi ta ba,Basma ta saka jaraba tace wlh an Bata sai ya mata transfer ko ta kai kara wajen Mima,Arham yace to in an baki kudin da me za a ciyar dake,ko baki nayi ai baza ki karba ba na sani kina da hankali,Basma tace ni bani da hankali wlh sai ka bani kudina mota dai ka dinga aro amma banda kudi sai ka bani,kin yarda baki da hankalin ke? Basma ta furta ae dama bani dashi ni bana ma fata nayi hankali kawai ka bani kudina da kayi min alkawari,ta fara fushi akan kudinta,Arham tashi yayi yace Banga ta zama ba ya shiga kitchen ya buya sannan ya kira Spark yaji wuya yace ya Banga Aunty Naila bane har yanzu? tayi tazo mana,Kai fa kace kar tazo,Dan Allah tazo,ai zata zo na kaita school zata yi signing wasu takardu jibi zata fara lecture na gaji da masifar Nan ta cikin Naila gwara ta zama Busy,wannan zaman da take a gida tana hutawa taci ta Sha shine yake sata wata tabarar.
Sai da suka dawo ya sauke Naila a gidan Arham ya wuce,tana shiga Basma tace Oyoyo ga Aunty Me darasin aure ,ke fa sai kace dillaliya haka kike, Basma wai wani Aunty me darasin aure.
Basma tace wlh ki fada Masa ya bani kudina da ya min alkawarin ranar first night yace ya bani duka kudinsa na accnt yanzu Kuma wai ya canja,ni nace yayi min alkawari,motarsa ma yace ya bani zai dinga aronta a hannuna amma ita mota nace ya dinga aro ai sai ya bani kudin ko.
Naila tayi dariya tace ke shashasha ce ai wannan wasa ne,dadinki ne yasa ya fada Kinga ya zauce kenan ai sai kiyi murna a kanki ana Sambatu,ko baki yayi ai sai kice ya barshi kawai tunda kin San dalili,Basma tace Ohhh Nan dama dadi ne yasa? Naila tace ae kema in kika fara Jin dadi haka zaki Masa kyautar baki sani ba,ai ni har gidan Abbana nace na bawa Spark,Basma tayi dariya tace tab Inama Abba zai ji kin Masa kyauta da gida,Naila tace ai bazai ji ba ma,Nifa gaskiya da naga Arham yanda ya susuce Allah na zaci aljanun ruwan maliya ne gaba daya a kansa,tunanina Yana da Aljanu masu yawan gaske cewar Basma,Naila tana dariya da wasa da dabara ta dinga Dan ganar da Basma tana koya mata abubuwa.
Abba ne ya fito da tabarma waje kofar gida sabo da irin mugun zafin da ake ya shimfida ya kwanta Yana Shan iska a gindin bishiya yace kaiiiii...Abu marar kyau ma Yana da ranarsa,Zafi ma da ranarsa,ba iya su Mohsin dina bane suke waje,Nima gashi duk tsiya cewa zanyi Ina waje,Mohsin ana can ana labbaika kana kiransa zai ce ai Yana waje Yana kasar waje,duk Wanda suke wata kasar zasu ce Ina waje,Nima gashi duk uban da ya kirani Ina waje Nima, ko ta wannan bangaren ai zafi yayi amfani,Beauty ce ta fito yanzu saura kwana biyar tayi arba'in,ana sa rai da dawowar mijinta shi yasa take ta faman gyara jikinta,Abba yace Ina zaki je Kuma? Kullum sai kin fita wai Ina kike zuwa ne haka? Beauty tace Abba gyaran jiki nake zuwa fa,yace au to jeki a dawo lafiya,tana tafiya Abba yace ana jiran miji kenan Kai yaran zamani karku kashe irin su Jauro da gyaran jiki,Jauro ne kuke birge shi.
Yana haka sai ga wayar Jauro ta shugo,ya daga yace dan halak kaki ambato yanzu nayi gulmarka ni da zuciyata,munci namanka,Jauro yace ai sana'arka ce kana Ina yanzu kana gida? Abba yace a'a bana gida wlh Ina waje na fita waje,Jauro yace ban gane ba kasar ka bari ga number dinka tana shiga,Abba yace Ina waje mana kazo ka ganni Dan Kaine kawai zan fada Maka gaskiya amma Ina waje wlh nima,Jauro yayi dariya ya kashe wayar kawai ya nufo wajen Abba dolo suka Sha hira.
Washe gari Abba da rana ya shiga gidansa cin abinci ya iske Beauty ta hada gumi kamar me ana masifar zafi,yace ke kuwa Beauty sai kace kin fada Swimming pool ko kin fada teku,Beauty tace Abba fanka din ma zafi take hurowa baku da ac bari ya dawo a sa muku AC gaskiya zafin yayi yawa,Abba yace a sa mana har a kitchen sabo da watarana in na shiga taya Yar Inna girki Kinga na huta da hucin gas.
Beauty tace duk za a sa,Abba yace har tabbaci kike bayarwa wato dai ta tabbata kin mallake Mohsin dina Kuma sai abinda kika ce,Beauty tayi murmushi,yace Ina sa rai shi zaiyi mata biyu Ashe mu zuriar mu sai mata daya,Allah yasa Aslam in ya girma shi ya rama min.
Babar Iman tuni ta tare a gidan sahibinta suna cin duniyarsu da tsinke ita da Sudan,amma hankalinsa yaki kwanciya sai bikon Maman Rafeeq yake zuwa yi sabo da ya samu ya gyara kuskurensa,da kyar Papa da dangi suka shiga maganar aka sasanta itama Maman Rafeeq ta koma gidan part din kowa daban, Maman Iman taji dadin Hakan Kuma tana bata girmanta.
Kudin Auren Haidar aka Kai Papa yace a kaiwa Spark,Spark ya kira Papa a waya yace ko haihuwa banyi ba ni gaskiya baza a dora min girma da wuri ba a kaiwa Yan uwanka ka fada musu su Kai can,Naila tace yawwa kana karba shike nan ka tsufa ko Da bamu ajiye ba,furfura ce zata feso Maka da wuri in kana shiga irin wannan sabgar ta manya,Papa Yana jinta ta waya,yace wato matarka ce ta ziga ka ko? Ince kayi Abu kace baza kayi ba,ba ruwanta papa jikanka ne yace kar babansa ya tsufa,Mamansa ya fadawa suka yi communication suka tattauna sannan suka fada min muka yanke shawara,Papa yace ka gama Karyarka ai tunda ba a gabana kuka girma ba ai Kuma sai ta Allah ni,Allah ya shirye ku ya kashe wayar ya kira ya basu address wajen Yan uwansa suka Kai kudi aka yanke rana wata daya tal.
Hidaya kuwa bata da lafiya ta samu ciki sai amai take Shekewa kawai ko me taci amai amai kamar me,tana Amai Iman ma tana nata gasu makwaftan juna sunyi anko sai su hadu suyi ta tattaunawa,Hidaya taje gidan Iman tace ke ashe ciki ne dani,na zaci malaria ce ashe babbar malaria na dauka,ana zuwa asibiti wai ciki,shi kuwa murna yake fa kamar me,ni Gani nayi nayi saurin dauka,Iman tace kin hadu da mugun sauro wlh nima sauron shi ya cijeni,mijina likitane Ina samu tun kafin na fara laulayi ya fada min ashe da gaske yake
inda kisan maye,Hidaya tace har ga Allah bana son cikin nan da wuri haka,Iman tace Ina so ni murna nake wlh,ai ni da shi so muke.
Ihsan tunda ta samu gidanta ta kama me tsada Yan uwanta suka sata gaba basu yarda ba sai dai ta dawo gida tayi Idda a gabansu,ba yanda ta iya haka ta koma Adamawa ta dole ma saurayinta me kurkura Bai sani ba ta fada Masa a waya ta tafi Adamawa,Bai san tana da aure an sake ba ma Sam,suna waya sosai kusan kullum ne sai tura Masa kudi take kamar me.
Mero kuwa ta Sha gyara wajen Jummai,saura Kwana biyu akai Mero gidan mijinta Yan uwan Haneef Maza suka kawo Lefe akwati Sha biyar set uku,an zuba kayan masu tsadar gaske kamar banza,Kauyen sai tururuwa ake ta zuwa kallon kayan Lefen Khadija Maza da mata yara da Yan mata,Jummai ana ta alfahari ana Jin dadi,Jummai ta fashe da kuka tace oh Inama uban Yar nan yana nan yaga duniya,Kai jama'a mutuwa me Yankan kauna Kai rayuwa abar tsoro ce,Sani ya tafi ya barni ni kadai har abada na gama farin ciki tana hawaye ta yagi cinyar kaza tana ci wacce tayi ragowa ta saukar baki,tace bazan sake nishadi ba a duniya,murmushi ko dariya in aka ga nayi a dole nake yinsa ba yanda zanyi ne,Wasu mata suka shigo suna guda suna duba Lefe,Jummai bata San sanda ta washe baki ba tana dariya tare da furta Alhmdllh yarinya ta tayi goshi.