Sashe 60
Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Goggo ma wanka tayi ta fito ta hau Naila da fada yanzu dama da nace ki bashi nono Baki bashi ba? tunda aka haife shi sau daya kika bashi nono sai zam zam kawai aka bashi fa,wannan wacce mugunta ce,boyon nono ya kare yarinya cewar Goggo,Naila ta dauki Jaririn Yana ta cin hannu Yana zare Ido, Goggo tace tsaya na koya miki yanda ake yi,sai da ta koyawa Naila sannan tace to kiyi Bismillah,Naila tayi Bismillah ta juya baya ta fara bashi wai Goggo baza ta kallar mata nono ba,Goggo tace a gaban mu fa kika yi nono har ya girma me zaki boye min shashasha,naga dazu ni nayi miki wanka,Naila tace naji ga Abinci nan Goggo ki ebi abinda kike so,Goggo tace mijin naki fa? Na zuba Masa nasa kina wanka na Kai Masa,Goggo tace Iyye kaji kula da miji,dariya Naila tayi,Naila bayan ya Sha daya ta juya shi yanda Goggo tace ta bashi dayan,Yana Sha Goggo tace ai ya koshi haka,to rike shi a hankali karki hantsila shi zaiyi amai,Naila tace Kai wannan yaro haba ace wannan ace waccen,sai da ya huta tace bari na kaiwa Daddyn sa shi ya ganshi,Goggo tace kwaji da shi munafukan banza wlh ki dawo a nan zaki kwana,Naila tace to,ta fice da danta cikin showel ta shiga dakin Spark Yana cin abinci Yana kallo ta shigo
Ya kalleta Yana Jin dadi a ransa yace fada ya kare tace ae mana,kallonta ya sake yi yace wai dama idan an haihu kyau ake yi ne? duk naga in kuka haihu sai mace tayi wani kyau fatarta tana shining,Naila tace ai haka yawanci ake yi sai zuwa arba'in ake dawowa normal,Naila ta juyo fuskar jariri tace ka ganshi fa Kaine babansa Kai ka haifi wannan,Spark yace duniya sabuwa SparkNaila kamanninsa biyu,Naila tace Nima haka nace kamanninsa biyu,sai da ya gama cin abincinsa ya dauke shi,wanne suna za a sa Masa ne? Naila tace oho ka zaba,Spark yace Papa Ahmad in yayi miki a saka idan kina da zabi ki zaba,tace a'a Banda da zabi Kuma ai suna me dadi ne na kololuwa Ahmad fa,Allah ka raya Ahmad bisa sunna,Allah kayi Masa Albarka kasa ya zama mahaddacin Alqur'ani,Allah kasa yayi koyi da fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW),Allah kasa duniya ta amfane shi,muma iyayensa ya amfane mu ya zame mana Alkhairi dukkanmu da Yan uwa da Al'ummar musulmai Baki daya,Allah yasa yayi suna ta hanya me kyau,ya shahara a duniya ta hanya me kyau,ba shaharar Dan Boko Haram ba,Bata Dan kidnapping ba,Bata Dan daba ko wani Dan iska ba,shahara ta hanyar abin Alkhairi,Allah yasa Shahidi ne,Allah ya Masa Albarka,Wannan Dan nawa Ahmad Allah ya sa Masa Albarka,Allah ya bashi lafiya da tsawon rai,Allah ya azurta shi ya raba shi da talauci,Allah yasa Dan Aljanna ne,Allah ya bashi mata ta gari Irina kyakyawa,Spark Yana ta amsawa da Ameen Ameen Yana dariya yanda Naila ta dage take surfa addua ta daga yaro sama tana cewa Allah ga Dana Ahmad,Allah ga Dana Ahmad,ya Rab ya Rab,ya Rab ka amsa addua ta.
Tana gamawa Spark yace well-done uwa ta gari haka ake so wlh uwa ta fara yiwa danta,Shima ya karba yace kawo shi Nima nayi nawa Shima ya tallafe jariri ya Dan daga sama kadan ya fara zubo addua tana amsawa Ameen...Ameen..Ameen sai da suka gama sannan Spark yace yaushe zan dauke shi ne ya tsula min fitsari? Dariya Naila tayi,yace to ai ya kamata ace Danka ya Maka fitsari,Naila tace saurin me kake yi zaiyi ne ai bari a fara barin duwawunsa Yana hutawa ka gani,har Kashi ma zai Maka watarana,yace Ina maraba indai na dana nane,spark da baya daukan yaro amma shi yake neman fitsarin dansa yanzu.
Naila ta dauki Baby tace bari naje sai da safe,sai da safe Ina?wai Ina bed din Baby ne,Goggo tace tare zamu na kwana,yace muje wajen Goggon ni zan mata bayani akan mene haka zamanin da ne wannan.
Spark tashi yayi suka tafi da Naila yayi yayi akan Goggo ta fahimta amma Goggo taki yarda,fita yayi Dan yaji haushi,Naila tace Kinga yaji haushi in haka ne mene amfanin yace bazan zauna a wajen Mima ba,wlh ba wani Abu zai min ba,kin sani kema ba halin yin komai,sabo da haka yasa aka taho dake,kullum muna tare dake da jaririn ace bazan kwana a can ba,Goggo tace wlh bari na kira uwarki na fada mata tunda baki da kunya tafiya zanyi,Naila ta kwanta a gadon ta ajiye Baby a gefenta,Spark shi kadai ya kwana ya hakura Kuma da safe ma bai ce komai ba bai nuna fushi ba ko a fuska har wasa suka yi da Goggo,washe gari haka Goggo tayi komai na gidan ta gyara ko Ina ta kula da Naila da Baby,girki me aiki tayi,haka Naila ta sake kwana da Baby da Goggo har kwana uku,kwana na ukun ta kira Abba a boye ta fada Masa,Abba yace kyaleta bari na kira ta,Abba ya kira Goggo ta daga waya,yace wanne dalilin zaki je ki Hana su sakewa daga ganin sarkin fawa sai Miya tayi zaki,birni ba haka ake yi ba yanzu,ki kyale yarinya,Goggo tace so take ayi mata wani cikin da wuri,ayi mata mana ke Ina ruwanki a jikinki yake,ana ta murna a kira Goggo sai kizo ki watsawa mijinta kasa a Ido ki kyaleta,iya aikinki kiyi Dan Allah.
Goggo tace shike nan tunda ku birni Kun lalace babu kunya taje ta kwana,idan yaro Yana kuka ai tayi sintiri a hanya zuwa dakina, yace ba komai tayi sintirin ya kashe wayarsa.
Naila tana shugowa Goggo tace munafuka har da fadawa ubanki kije kiyi ta kwana ai mayyar miji,dariya Naila tayi tace naji.
Yau da dare bayan Yan barka sun tafi tayi wankanta ta saka riga da wando blue na bacci ta Sha kyau ta dauki Danta ta yiwa Goggo sai da safe,ta shiga bedroom din Spark,baiyi tunanin kwana zata yi ba,yace Goggo ta ishe ni da nasan haka ne bazan kawo ta ba wlh,Naila ta fara hada gadon Baby a gefen nasu hadadden bed fari tas da shi,Spark yace ta yarda ne ki kwana? Naila tace tun yaushe na fadawa Abba ya kira ta a waya kuwa yace ba ruwanta da mu,Spark yaji dadi yace yawwa tsohuwa ta ishe ni haba,Naila tayi dariya ya dauki Baby,yace yaron nan ya bani wahala kafin yazo duniya,Naila ta bashi nono ya Sha ta kwantar da shi.
Yayin da Maryam kanwar Annoor ta samu miji bayan ta murmure tayi aure abinta itama,suna ta zumuncinsu da Annoor.
Ihsan tana yin Idda ta samu saurayinta da take so tace tana sonsa bayan ta bashi jari ya kama business babba,ta kashe Masa mugun kudi,ta siya Masa mota bai taba cewa Yana sonta ba sai dai ya nuna shi kawai birge shi take yi,tun tana jira yace Yana sonta har ta gaji ta fada Masa da kanta,kowa ya gansu zai ce masoya ne yanda suke mu'amula,suke waya,yake zuwa gidanta da sauran su,yaci kudinta matuka,Ashe shi Yana kama kasa ya koma wajen Tsohuwar budurwarsa da aka hanashi sabo da baida sana'a Yana komawa aka ce ya turo Kuma ya Kai kudin aure,a ransa tayi tunanin ko ya auri Ihsan din sai yaga tafi karfinsa ita tana da kudi baza ta juyu a wajensa ba kawai ya nemi dai dai shi,sai da Ihsan tace tana sonsa yace ai shi an saka ranarsa da wata,Ihsan ga aji tace ba komai ba damuwa kamar gaske ta nuna bata damu ba, Ashe Kara ta shigar kotu ta kashe Masa kudinta ya yaudare ta zai auri wata.
Sai da suka je kotu sannan ma yaji labari ta taba aure duk lokacin da take kulashi tana da aure,Nan yayiwa Allah godiya da bai aure ta ba, Alkali yaji ma kudin ba roka yayi ba babu manufa kawai ta dinga kashe Masa kudi,Alkali yace ficika bazai biyaki ba tunda yarjejeniya kuka yi ba,haka kawai kika bashi kyauta Kuma kin amsa,Ihsan tace Dan me bazai gane sonsa nake ba shi Dabba ne,Sadeeq me kurkura yace nasan gaibu ne ni da zan gane,Alkhali ya dakatar da su yace Allah ya azurta Sadeeq ta hanyarki,ki hakura ki nemi ladan Allah sai Allah ya baki wani na gari,Ihsan tace ni ban yarda ba,Alkali ya Kori Kara yayi rubutu matukar ta takurawa me kurkura sai an yanke mata hukunci,Ihsan ba nasara ta rasa Inda zata sa kanta gashi ta bari an sake ta,gidanta na Kano ta dawo ta kwana tana kuka da Dana sani,washe gari da safe ta nufi gidan Haneef.
Gidan ta gani komai ya canja ya Kara haduwa,sababbin motoci ba Wanda ta sani ba,ta danna door bell,ba a Dade ba Khadija ta bude kofar wow,ta zama wata Yar gayu da ita,ta Kara kiba da haske ta zuba kyau cikin kana Nan kaya,Ihsan mamaki ya kamata kamar ba Khadija ba,fuska ta bata tace uban me kike a gidan nan har yanzu,Khadija tace ubanki nake yi,an sake ki me ya kawo ki nan gantalalliya,Khadija ta kalla sosai taga ciki a jikinta bakin ciki ya tokare Ihsan a makoshi,Honey Mero ta shiga kwalawa kira ya fito yana cewa na'am Beb,yaga Ihsan da mamaki yace ke me ya kawo ki ya bata rai,Ihsan tace Baby Dan Allah kayi hakuri,Babyn ubanki dalla fitar min a gida,rungume Haneef zata yi Khadija ta fyalle mata Mari, tace dama haushinki nake ji an sakeki ban sani ba,Haneef yace fitar min a gidana Ihsan,ni kake kora Haneef Ina Yar uwarka yace an Kore ki,karki zubarwa da matata ciki da fada,ya fisgi Hannun Ihsan ya bude kofa tare da jefata waje ya kulle kofarsa,Mero ta harda goge masa hannu hannu kamar ya taba Kashi ta goge masa tace muje.