← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 68

Sashe 37

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Fitowa tayi asibitin tana sharbar kuka da kururuwa azo a taimake ni mijina ya kawo karuwarsa asibiti,Mutane da Yan zaman jinya aka taru aka cika, Ihsan tana musu bayani Yar aiki ya kawo min gida Ashe karuwarsa ce sun dade da sanin juna,bayin Allah ashe a boye dakinta yake kwana,da rana idan na tafi wajen aiki suna tare suna sabon Allah,tun suna yi a boye ya fito da shi fili,Ina zaune Yar aiki da ita yake Hira,da Yar aiki yake kallon film komai Yar aiki karshe har tayata girki yake a kitchen yanzu Bata da lafiya ya taho Yana jinyarta,ba iyayenta ba danginta babu mace shike jinya tare suke kwana ta ya bazan damu ba?

Wata mace ta dafe kirjinta da hannaye tace wannan yayi asara,ai ni tuni na dawo daga safgar Maza,basu da hali tsaf zaiyi abinda yafi haka,wata ma tace amma wannan anyi matsiyaci,wasu kuwa suka ce sai hakuri mazan duk haka suke,Mace daya ce a ciki tace to ke duk kina me? Ya kamata a bincika maybe baya sonki ya aureki,ko Kuma kece bakya abinda ya dace har ya fada wannan safgar Allah dai ya kiyaye,mazan suna ji ba Wanda ya bawa Ihsan gaskiya a Maza sai ma cewa suka yi ke dai ba matar arziki bace ba matar rufin asiri bace,da matar arziki ce baza ki iya yiwa mijinki fallasa da tijara haka ba,mene birgewarki da cinyewa,wannan halin naki yasa yake kula wata,wani yace tab wannan bashi da mata ya Kara aure kawai,idan nine sakinta zanyi cewar wani,Ihsan motarta ta ja ta ware gida ranta fes ta fashe haushinta.

Khadija da Haneef suna Jin abinda Ihsan tace da mutane,Khadija tace karka ji komai duk Wanda yayi Maka kallon banza kayi min kiss a gabansa ko uban waye na yarje Maka,dariya Haneef yayi yace banyi niyyar dariya ba fa Ina bacin rai,oh to ci gaba ke dariya koma ta furta, karka saki Ihsan Dan Allah,Haneef ya Kalli Khadija tare da sa hannunsa cikin nata yace zaki aure ni? mamaki tayi Jin abinda ya fada ba zato,tace Ina Yar aiki kalleni fa Ina ni Ina Kai me kudi, answer me" zaki aure ni? tafin hannaye tasa tare da rufe fuskarta ta furta ae,murna yayi yace na gode,su Hajji da dangina zasu iya hanawa indai ban saki Ihsan ba zasu ce bazan Kara aure ba,zanje da wasu da abokaina a daura mana aure ko basu sani ba indai Mama ta sani shike nan,ita nasan zata amince,Mero taji tayi nasara sai murna take a ranta.

Arham daga kwanciyarsa Haly ta kira Mima a waya ta fada mata, Mima tana dakin Papa tace kaga ka samu Arham da kanka kayi Masa magana wlh tun kafin a Kai yarinya ko ayi mata ma gyaran Jikin yaje ya nace mata,gaskiya in baza ka Masa magana ba a basu gidansu su tafi kawai yafi,ai ba tsari kowa yasan me ake yi,Papa yace Inshaallah wani satin za a kaita ku fara shiryata,ai kafin wani satin ya gama da ita kaje ka yi Masa magana da kanka tunda mu ya Raina mu,Papa yace muje suka fito da Mima dakin Basma Muryar Papa suka ji Yana magana Kai Arham zo Ina nemanka yanzu a part dina,Yana fadar haka ya juya suka tafi,Basma tace kaje za a Maka fada,Arham yace ni Banga amfanin wannan aure ba,na kasa gane kan wannan aure,Basma tace asiri aka yiwa su Papa da su Mima, mahassada sun mana asiri,Arham ya furta naga alama Rafeeq ne yayi min asiri naga yafi kowa bakin ciki Dani sabo da nine sakonsa kar na kamo shi,Basma tace ko Kuma Kawuna ba kana gani Sadakin nan da kyar ya bada su,Arham ya furta ba abinda bazai iya ba sabo da yaga matarsa ta tsufa nononta ya zube yayi yaushi shine yake min bakin ciki,Basma tace Kai wlh da sauranta yarinya fa ya sake aure daga baya sabo da hadama,Papa ne yayi tsawa Arham baka ji ne,Basma itama ba wasa tace gashi nan dama wayarsa ya manta Papa ta furta kamar Soja mace,Arham ya gama saka kayansa ko wandon nasa bai kulle Zip ba kamar zai fado boxers a waje ya fito,Papa kamar ya fashe da kuka sabo da rashin kunyar Arham ta gallabe shi,kallo Daya ya Masa bai sake ba,yace muje marar mutunci,dariya Arham yayi,Papa yace kace baka sonta bata da kyau ban iya zabe ba,Papa subutar baki ce na gane gaskiya,idonka Yana Gani Allah ya saka da Alkhairi Allah yasa a Kara Maka matsayi a wajen aiki,komai yayi perfect,Papa yace kar na sake ganinka a dakin Basma ko tazo dakinka Kun rufe kofa,Kai baza ka bari a kaita ba,Baka sonta fa jikinta kake so wlh in na sake ganinka kaje dakinta ko tazo Kun rufe kofa zaka yi wani Abu sai na Saba Maka,in baka son albarka ka sake zuwa ku rufe kofa ko tazo ku rufe kofa,in kana son albarka Kuma ka kiyaye taba ta,duk wata mu'amula ban hanaka ba amma banda wannan safga,indai kana so in Maka baki dan Allah ka sake azo a fada min,Arham yace har da Baki,ai Allah ne yace Dokar Allah ne wannan,to shike nan kaje ka Kuma tafi ka bani waje,Arham ya juya ya tafi Yana mamaki yace a daura ma aure ace kar kula matar ni na taba Jin haka,shike nan zanyi biyayya.

Komawa yayi wajen Basma ya bar kofar a bude,Basma tace ya barka ne? Arham yace yace yayi min Baki in na sake tabaki sannan kar na rufe kofa in muna tare sai an kaiki gidana,Basma tace har da baki? Arham yace kwarai,tace tab asiri ne,Allah ya karya shi ko waye cewar Arham,yace sabo da bakin ciki a aure ma sai an jefi mutum sai da safe ya juya ya fita,Basma ta rako shi bakin kofa tace Good Night bye ya wuce.

Yana komawa a Palo ya samu Shaheed,yace Mazaje ya aka yi ne? Arham yace uhm Papa ne yayi min baki kar na sake taba Amarya,Shaheed yace illar zama gida Daya da iyaye kenan,Basma tana ganin rayuwa zama da sirikai,Arham yace duk Maman Rafeeq ce take wannan zigar,ka kiyayi matar data kashe aurenta ta dawo,ana tausayinta ashe ita bata Tausayin kanta,Allah ya kawo mata bazawari ko irin Baseeru Kusa ne cewar Shaheed,Junior Yana jinsu yace gaskiya Papa bai kyauta ba a nan ya dace ace ya bari ka dan more,Arham yace kaima dai ka fada ni basu gane nufi na ba ma bazan yi sex da ita ba wannan in ta dinga kuka ai sai kowa ya sani Dan Tabesting a hana mutum wlh duk Wanda naji ya kirani Ango a gidan nan sai na taka Masa birki ni ba Ango bane,Arham ya zauna yana ta surutunsa kamar me.
Bangaren Basma kuwa kwanciya tayi abinta tana tunanin Arham dinta tace mutum Yana son Mijinsa a hanashi sakewa.

Washe gari Misam yazo gidan Mima Yana gidan Rafeeq yazo shima Spark ya shugo suna zaune suna hira da Maman Rafeeq"Arham ne ya fito Yana Jin Haushin kowa Yana Bata rai,Misam yace Ango Ango ka Sha Mai,Arham yace duk Wanda yasan yayi min asiri yaje ya karya abinsa tun kafin ya dawo kansa Yana magana Yana kallon Rafeeq,Papa sun min aure an hanani taba Amarya,sai kulla min tuggu ake yi a gidan Nan Kuma bakin da suke gidan nan ne suke wannan hadin,Maman Rafeeq tace ni kenan? tunda nice bakuwa a gidan nan,Arham yace Nidai ban kama suna ba Baki nace karki fadawa yayarki tazo ta tsine min,Rafeeq yace baka da hankali ka zare Arham,ni dai ba ni nayi Maka aure ba...

Basma ce ta fito sanye cikin doguwar riga fitted tayi kyau sosai,Arham ya bita da kallo Yana cewa Allah ya Kai damo ga harawa ranar kawai ku taho daukan patient zuwa asibiti,Basma ta karaso ta gaida su suka Amsa, Arham dake tsaye ta dan kalle shi ta rike hannunsa ta saki ta wuce, Maman Rafeeq tace nidai bari na tashi daga nan bazan iya Jin wannan Abu ba,Arham yace wlh yanzu na fara batsa a gidan man kowa ya gyara kunnensa ko a bani matata ko aji zancen Hallare da bado,haka kawai ba dama na kebe da iyalina na,Arham yayi Iyali inji Spark Yana dariya,Arham ya bi Basma,Misam yace Dan iskan yaro Hallare ta motsa Kai na tsorata da yaron nan Spark ya gado,Spark yace Kai baka ga iskancinka ba sai ni zaka ce ni ya gado Rafeeq ya gado,Rafeeq yace kwarai ni haka nake lafiya ce,inyi In Kara in sake yi bana gajiya haka nake,ni da naga Ikhram ma ba zaman lafiya,Spark yace tab sai kace Mima ya Kalli kofa yace kar ta jini suna dariya,Misam yace Allah yasa ta jika wlh yanzu Mima ta musulunta fada take yiwa yaranta.
Chapter 37 · 0% Book details