← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 68

Sashe 17

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari sai da yamma likis mota hadaddiya tayi parking a kofar gidan su Khadija,Khadija babu suturar arziki 'Yan tsumman da suke a gida nata ta zabo kala uku masu dama dama,wacce ta dawo da ita daga prison a jikinta shi ta wanke ta goge Leshi yellow and Golden ta saka a jikinta,Mayafi ma tana so ta danyi too match amma ba dama haka ta dauki Hijabinta blue na yadi Dan Madina ta saka abinta ta fito dauke da ledar kayanta,Jummai sai murna take yi tana addua Allah yasa Khadija kije a sa'a Allah yasa wannan yasa shine silar arzikin mu,Allah ya zuba mana sugar a bakinmu Khadija karki bari ya zube bamu lashe ba,Dan Allah kiyi aiki me kyau Banda shiririta,Khadija tace to Inna baki sa min albarka ba,Inna tace Allah ya miki Albarka,Allah ya Bada sa'a,Abbun su Khadija Yana kasuwa tace ki cewa Abbu na tafi,zan fada Masa,Munnir Yana jinsu Yana tabe baki yace mutum yayi sana'arsa a gida bai fi ba amma ka dauki Yarka ka kaita wata uwa duniya baka San Inda take ba Allah ya kiyaye kar a yiwa Yaya Khadija Cikin shege,Harararsa Jummai tayi,har mota ta raka Khadija ta dawo tana ta tsalle tana murna a mota aka zo daukan 'yata,'yata tayi goshi,Munnir tashi yayi ya bar gidan gaba daya.

Khadija kuwa tana mota a baya daga ita sai driver ba Wanda ke kula wani,duk surutun Mero shuru tayi har suka je unguwar Mero sai kallon hadaddun gidaje take yi,suka Isa katafaren gidan Haneef, ta Saba ganin gidaje masu kyau a Abuja shi yasa kalle kallen nata yazo da sauki,gidan Haneef ya hadu karshe ga motocinsa nan iri iri,Driver ne yayi mata iso har Parlo,tana bayansa Yana gaba,a Palo suka samu Ihsan taci shadda sky tana zaune tana Shan fruits,Mero gabanta ya yanke ya Fadi ganin Ihsan Masha Allah da ita son kowa kin Wanda ya rasa,a ranta tace Nima da kyau na ai ba fina tayi ba,ko haske baza ta nuna min ba sai gogewa da hutu kawai,fili Kuma tace Hajiya muna ta sallama Baki amsa ba,babu kyau wlh kaji sallama ka share a Islamiyya an koya mana,tuni Driver ya juya,Ihsan ta Kalli Mero sama da kasa a wulakance tace ke kama kanki,kece Yar aikin da Haneef yace an samo? Mero tace aka samo? Kamar kifi a teku Wanda babu me shi aka dakko dai ko Aunty, Ihsan Ido ta zaro tace Kinga bana son magana ta kwalawa Salamatu kira,Salamatu ta fito tace ga Yar aiki an kawo ki nuna mata komai ki kaita dakinta Dan Allah kuje bana son damuwa.

Salamatu ta ja Khadija bangaren masu aiki ta nuna mata daki da bed da mudubi harda sip dakin me kyau abinta ita kadai,Mero tace ko a gidan miji ka samu wannan ai soyayya sai ba za ayi ba,Salamatu tace ke dai bari Yar uwa kin ga sanda aka kawo ni gidan Nan Inda kisan Yar gudun hijira amma yanzu kalleni kamar takari a saudiyya,Mero tayi dariya tace ai Aunty sai ace ma kece uwar Ihsan din matar me gidan,Salamatu tace ke rabani da wannan ba mutunci ne da ita ba,Mero tace nima Ina da degree din nawa rashin mutuncin,nawa degree din na rashin mutunci dan Cotonou ne ma,Salamatu tace kar a Kore ki baiwar Allah yarinya kibi a sannu kina Yar aiki Ina ke Ina ja da masu gida,Khadija tace zauna ki zuba Ido Aunty Salamatu ni ba ruwana da matarsa Ihsan,shi fa zanwa aiki Kuma ma muna mutunci da shi Yana da kirki,Salamatu tayi murmushi tace ke akan ma'aikatansa bashi da wani sauki aiki kika zo aiki zaki yi Kuma zaki Gani zaki ce na fada miki.

Abinci ta kawowa Khadija tace sunanki Khadija ko? daga gobe zaki fara girkinki a kitchen ni ya Maida ni gyaran gida,Mero tace Allah ya kaimu.
Mero tana nan har dare Bata ga Haneef ya shugo ba,ta fito Palo ta samu Ihsan ta canja sabon wanka da key din mota a hannunta da alama fita zata yi,ko kallon Khadija Bata yi ba ta fice,Mero tace mu ai sai mutum ya bude baki ma yayi magana komai shariyarsa Ina nan dake sai Kinga na fara yiwa mijinki tausa tukun kina Nan,tana zaune a kasa tana maganganunta taji kamshi ya mamaye parlon dagowa tayi a hankali tsorata tayi sosai ganin mutum a gabanta,kirji ta dafe tace wlh na zaci aljani ne,kallonta Haneef yayi tace Ina yini,ya amsa da lfy Alhmdllh,kawai sai Taga ya shareta kamar Bai Santa ba ya zauna a kujera,Mero tace kai, Salamatu ta fadi gaskiya kuwa ba mutunci,wani film aka saka aka fara series ne American film suna ta kallo.

Khadija tace wannan yarinyar bata da wayo,Haneef yace tana kallo an kwace abin magic din an tafi Kalli yanda take tafiya,Mero tace rabu da banza ai jaka ce naga alama,Star dinne ya hadu da yarinyar suka tsurawa juna Ido Mero tace ka dauki remote a hannu za a fara iskanci, da kaga irin wannan kallon sai iskanci a canja tasha in an gama sai mu dawo,Haneef yace a'a ba wani iskanci da za ayi,Baki suka hade waje daya suka fara kiss Mero tace la'ilahhhhhhhhh....murmushi Haneef yayi,Dan Allah ka canja mana tasha kana kallo ya danneta ni dai ba ruwana, La'ilahhhhhhhhh...zai cire mata breziyya,wayyo tonon asiri marakisiyyarta ya cire,Haneef yaki canjawa yace in ana canja tasha ba a gane film,Mero kanta ta Maida bayan kujera ta buya tace in an gama ka fada min.
Ihsan ce ta dawo ta samu Haneef da Khadija suna kallo suna magana,yace tashi ki Gani tsafinta ya dawo,ta dago da kanta tace ya dawo kuwa wlh ana Raina mana hankali gaskiya,Ihsan ta Kalli Haneef ta Kalli Khadija abinda ta tsaya yi kenan tana kallon su ko kulata basu yi ba,yace gashi Nan Bos yazo,Mero tace to ita yarinyar Ina tsafin tayi maganinsa mana,Inama nice....kaiii kuturun Uba ta dirga kansa Kalli wohoho...ya masge ta ariiiii....
Tare suka Kalli season biyu sai gobe Kuma za aci gaba,Mero tace sai da ya dakko dadi,Haneef yace gobe kamar yanzu zasu ci gaba ai,Ihsan bakin ciki yasa ta ja tsaki ta wuce.

Papa ne ya kira Arham ga Mima a gefe Yana ta aikin lallaba Arham akan Basma,yace Dan Allah Arham ka rufa min asiri ka aure ta,mene laifinta kyakyawa da ita komai dai dai wlh ba Wanda bazai so wannan ba,kayi hakuri a hankali zaka so ta,Arham yace ai ni nace a zabo min laifi nane na yarda ai zan aure ta din,Papa yaji dadi yace ko me kake so zan Maka,Arham yace ai kayi min komai Ina karatu ka bamu jari muna sana'a yanzu dai ni a biya min Umrah in ana so aga na kula ta,Papa yace Inshaallah za a biya Maka amma ka Dan kirata kuyi zance ku fahimci juna ita tasan Kai zata aura na mata bayani,Arham yace yanzu a gidan ma sai naje zance?,Mima tace ji min yaro fa ni wlh wannan yaro ko tafiya yayi bazan kirashi ba ko awaya Dan bazan yi kewarsa ba,Arham yace ni din Mima? Ae Kai din idan Shaheed ne ko junior duk zan neme su in basa kusa amma ban da Kai dama ka isheni ni gwara ma ayi ma auren,Arham yace shike nan Mima za a gani ai kince dai ko a waya baza ki kirani ba in bana gari? Tace ae haka nace yace to shike nan.

Papa in naje zancen ma in banda wakar Dan maliyo maliyo me take yi,kana ji dai a gidan nan kullum sai tayi wakar Dan maliyo,ita kadai tafa tafa take yi,tafa tafa tafiyar nan da zamu tare aikinta kenan fa, Papa yace marainiya ce tausayinta nake ji Yar abokina ce a kauye tun muna yara, Allah yayi masa rasuwa tun tana Yar karama,uwarta tayi aure aka tafi da ita agolanci gidan wani,Arham yace au agola ce ma?,shike nan mijin agola ne ni,Papa yace Kai gidanku tashi ka tafi,Arham yace agola kuwa gaskiya ba sa'a,haba shi yasa kirjinta ba komai,Mima ta make shi,Papa yace kyale shi uwarka ma gata Nan haka aka daura mana aure da ita a gidana ta fara,Arham yayi dariya yace Dan dai Kaine papa amma da na Fadi wata magana sai dai da kunya amma da nace sai yayi maganar kamar me kunkuni yanda baza aji me yace ba ya furta Kai ka jawo shi kenan ya fito,ya mike tsam,Papa yace ai baza ku nutsu ba kunyi gado ya zanyi, Mima tace ban gane sunyi gado ba,me kake so kace kenan wajen wa suka gada? Papa yace a bar dai maganar kawai tone tone ba dadi.

Basma kyakyawa ce fara doguwa tana da sura da diri me kyau wulakancin Arham ne kawai sabo da yaga Yar kauye ce bata saka kaya a muhallinsu,Yana fitowa yaci karo da Basma ta fito da gudun tsiya Arham ya kurawa kirjinta Ido yace ba abinda yake motsi kyam haka, Kai ai ya kamata naga suna rawa in akwai amma kyaf kamar nawa tana gudu kyam da su,Allah ya kaimu anjima ai zanje zance wlh sai na taba naji bazan yarda da wannan rufa rufar ba,ko Kuma in tana wanka na Gani da idona baza a kawo min Abu a dukunkune ba,Su Haly ya samu a parlo suna ta Masa dariya haka kawai,suka ce yanzu matarka ta fita da gudu,Spark ya gani a parlon shima a zaune da Naila,Spark yace dama ita ce Basma din? Arham yace oho,Naila tayi dariya tace ai ni Banga laifinta ba wlh kyakyawa da ita haka,ni kyan fuska akace muku Ina so,kyawun kirji da baya ba ruwana da fuskar mace ni zan iya danne fuskar da pillow ma,Spark yayi dariya yace wai yaron nan aure za a Maka,Arham yace ya ranka abinda ka kasa ni zanyi zaka gani 9mnths da Baby boy, Naila tayi dariya tace wato Yan gidan nan baku da Kara wlh akan Allah bai bamu ba, Basma ce ta shugo da gudu kanta a kasa sanye da riga doguwa ta material silk,zata wuce tace sannunku tayi gaba
Arham ne ya rukota harda bata rai irin ba wasa yace ke zauna ki huta da guje gujen nan,ke kafarki bata gajiya ne? Kullum daga Waka sai gudu haka kika ga ana yi a garin nan?
Chapter 17 · 0% Book details