Sashe 9
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuwa la'asar ta kammala komai,kasancewar biyar zuwa da rabi suke saka ran shigowarsa cikin gidan,tuwon alkama tayi masa miyar kubewa danya wadda ta wadata da zallar tsokar nama da kuma tantak'washi wato k'ashi mai taunuwa ga me buqata,sai lafiyayyen alkubus da tayi miyar taushe,daga bisani da taha zobo wanda ta tafasashi da citta da kanunfari,ya wadatu da lemon tsami,sam bata zuba flavours din nan irin nasu tiyara ba haka ta barshi da original din kayan hadi,sai suger syrup da ta zuba daidai misali yadda bazai cutar ba.
Tun kafin abban yaci su ummu suka fara nasu santin ita da rumana,murmushi kawai ta dinga musu ganin yadda suketa zabga santin ta shige dakinsu don ta watsa ruwa ko zata ji sanyi a jikinta
**********
Qarfe takwas da kusan rabi ne na dare cikin falon abban suke bayan sun kammala cim abincin dare wanda girkin da raihanan tayi ne,suna zaune ita da rumana sanye da kaya iri daya wato material dinkin doguwar riga wadda raihanan ce ta zaba musu style din,daga gefe guda kuwa abba ne da ummu,hira suke abba na bude jakar da ya dawo da ita yana fidda tsaraba
"Abba ka bari sai gobe mana idan ka huta sai ka raba" inji rumana
"Um um rumana,tsaya dai na sallami kowa,don akwai saqonninku da rayyan ya bani,shi din ma bana tunanin zasu wuce wata biyu zasu dawo baki daya har kawu muahhadun,don shima yace ya gaji da zama a can din ga girma na zuwa masa,gwara ya dawo cikin dangi" kamar ta taka rawa don murna amma ta kanne ta dake ganin idanun abba da ummu a gun,duk da haka sai da ta kasa haquri ta qanqame hannayen raihana dake kusa da ita,idanu suka hada kowacce fuskarta dauke da murmushi,ita kanta raihanan ta taya rumanan murna,addu'a take Allah yasa ya hado mata da hotunansa,don rabon da ya turo din an din kwana biyu,kota watsapp ma,gashi tunda ya bar qasar bai sake waiwayota ba.
Jakankuna ne madaidaita guda biyu iri daya ya miqawa raihana daya ya miqawa rumana daya,hannu biyu suka sanya suka amsa suna godiya,ya fidda wata jakar wadda ta dan fi tasu girma ya miqawa ummu yana fadin
"Ga saqon yaronki" cikin alkunya tace"Allah ya amfana"abban ya ajjiye mata a gabanta,ya sake fidda wasu jakankunan ledar wadda daya tafi daya girma,ya miqawa rumana daya,raihana daya yace"saqon yayanku"hannu biyu suka amsa suna sake godiya kana suka miqe suka yiwa su ummun sai da safe,don rumana ta qagu taje ta bude tana meye a ciki.
Har sun kusa ficewa daga falon abban ya sake kiransu suka dawo,wasu litattafai abban ya ciro ya miqawa raihana,daya tarihin masarautar kano ne,dayan kuma tarihin sahabbai ne maza da mata guda dari dari na hausa guda biyu,kana ya fidda doguwar baqar riga ya miqa mata
"Wannan litattafan abbanki dalhatu ne yace na kawo miki yasan ke gwanar karatu ce,rigar kuma tukuicin garar girkin da na diba yau ne" kanta a qasa tasa hannu ta amsa a kunyace tana fadin"na gode abba,Allah ya saka da alkhairi,ya qara girma"
"Ameen ameen,Allah yayi muku albarka"
"Ameen suka amsa" sai ya fidda wani qaramin turare ya miqawa rumana yace gashi itama ladan ganin ido,tana dariya ta karba tana godiya,don ita saqon data samu daga rayyan ma kadai ya isheta,burinta kawai ta isa daki ta bude.
Suna isa ta daka wani wawan tsalle ta dira kan gadonta tana dan ihun murna,tsayawa kawai raihana tayi tana kallonta fuskarta dauke sa murmushi,tabbas ba qanqanin so rumananta kewa ya rayyan ba,tun tafiyarsa daidai da second daya bata taba mancewa da ambatonsa ba,duk da tarin abokanta kuwa amma basuyi isar da suka samu damar shafe koda d'ani daya na soyayyarsa dake cikin zuciyarta ba.
Tsagaitawa tayi tana fidda idanu tana duban raihana
"Sisi,bayan shekaru ya muradina zai dawo,raihana ya rayyan dinmu zai dawo gida,gidanmu zai dawo kamar yadda yake da,sis bazan buda kayan nan yanzu ba,sai na gama shirin yi bacci,so nake su zama abu na qarshe da zan kalla kafin zuwan bacci idanuna"
"Ya kamata..." Cewar raiha tana ci gaba da murmushi
Miqewa tayi har yanzu murmushi yaqi barin fuskarta ta rage kayan jikinta ta daura towel ta shige bandakinsu dake cikin dakin.
Gefan gadonsu rumana ta zauna tana girgiza kai cikin zuciyarta tana fadin
"Rumana....ruma kenan,rumana tawa,rumanan ya rayyan,Allah ya barki da shi" ta qarashe zancan zucin tana janyo jakar da abban ya musu tsaraba ta soma budeta.
Dogayen riguna ne kamar yadda ya riga ya sani kayan da tafi so kenan,ba qaramin burgeta kayan sukayi ba har ta dinga sakin murmushi ita daya,sai mayafai suma masu kyau da takalma,sai turare guda uku irin wanda take amfani da su,maidasu tayi cikin jakar kana ta janyo ledar da ya rayyan ya basu ta zazzage kayan ciki
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
[7/23, 8:40 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*Manzan Allah S A W yace"mutane)masu jinqai da tausayi,ubangiji mai rahama girma da daukaka suma yana jin qansu*
_________________________
*Babi na goma*
Duk kayan dake cikin ledar suka zubo kan katifar,littafin love story ta soma cin karo da shi sabo qar,a bangon littafin wata gajeriyar takarda ce da aka linke ta gida biyu aka maqale ta a jiki.
Murmushi ta saki saboda tuna mata baya da littafin yayi,sanya hannunta tayi ta ciro takardar ta budeta.
Rubutune qanana masu kyau a jiki wanda basu wuce layi bakwai ba
_assalamu alaikum,nasan zuwa yanzu qanwata tayi girman da zata iya karanta wannan littafi,to ga tsarabata nan,asha karatu lafiya_
Ita kadai amma sai taji kunya ta kamata tamkar yana kallonta"ya rayyan,baka da mantuwa"ta fada cikin zuciyarta,ragowar kayan note book me masu kyau farare tas masu zanen furanni da tsuntsaye har cikin shafukan cikin littafin haka suke,kana gani kasan masu tsada ne,guda shida ne da biruka masu kyau da burgewa suma guda shida,murmushi ta sakeyi tana fadi a zuciyarta"baka mance quruciyarmu ba".
Turaren oud guda uku masu qamshi,sai set na sarqa da dan kunne na english gold sirara masu kyau da tsari.
Sosai kayan suka burgeta,tana tsaka da maidasu cikin ledar rumana ta fito
"Ke har kin bude naki tsarabar kenan" ta fada tana qarasowa gefan raihanan
"Eh kam,duba ki gani" ta fada tana tura mata ledar kana ta miqe don shiga itama tayi wankan.
Dariya rumanan ta dinga yi tana tsokanar raihana
"Wato my rayyan bai manta satar novel da kike masa ba ko,da maitar karance karance,hala nima bai mance halaye na na quruciya ba kenan" murmushi kawai raihana keyi tana sauya kayan bacci
"Bai mantawa da nawa attitude din ba ballantana naki,kedai jeki bude musha kallo,hala harda 'yar tsana mai koyar da rawa ya aiko miki" tayi maganar yayin da tayi rub da ciki kan gadon nata tana fuskantar rumana dake gefan nata gadon itama tana saka kayan baccin.
Sai da ta gama komai sannan tayi dare dare tsakiyar gadon,jakar da rayyan ya aiko mata da ita ta fara budewa,wasu plates din cd ne guda biyu suka fara fadowa,ra daga tana dubasu,'yar qaramar dariya ta saka cikin nishadi,dayan album din waqoqi ne wanda ke qunshe da waqa goma dukka masu dauke da kalaman soyayya da tsuma zukata,daya kuma waqoqine kala kala suma duk na soyayyar ne,tana iya tuna wasu daga cikinsu rayyan din kanyi lokaci lokaci kafin barinsa gida,ta sake duba kayan english gold ne irin na raihana sak,banbancinsu kawai nata akwai zobe a ciki wanda akayi zanen RR guda biyu sarqafe da juna,sai turaruka guda biyar,packet uku uku na irin biscuite da chacukets din da yake bata da can lokacin quruciya,tana daga kayan tana nunawa raihana tana tayata dariya"wato tsokana kawai tasa ya rayyan yin aikenan nan da alama"ta fada tana cin dariya.
wata envalope mai fadi ta hago a qasan dan akwatin agogon hannu mai siffar heart,ta miqa hannu da sauri ta bude,takarda ta fara cirowa ta warwareta ta soma karantawa,murmushi kawai ke fita daga fuskarta,da sauri tayi cilli da takardar ta wawuri envalope din ta kuma budeta.
Wasu zuqa zuqan hotuna ne guda biyu ta samu nasarar fiddosu,idanu ta zaro gami da fidda idanu waje kana ta saki wani qaramin ihu da ya sanya raihana miqewa zaune tana tambayarta lafiya,kasa bata amsa tayi sai cewa da take
"Zo ki gani.....zo ki gani sisi,wayyo Allah na" tana fada tana zillo kan gadon ta kasa tsaiwa guri guda.
Da sauri ta sauko daga nata gadon ta qaraso gadon rumanan a dan kidime,a hankali takai idanunta kan abinda rumanan ke nuna mata,hotunan rayyan ne duka guda biyun,yayi masifar kyau cikin hotunan,daya yana sanye da courte baqa da ja,sumar kansa ta kwanta luf,ya sake girma da cikar zati sosai ya zama cikakken saurayi,dayan kuma yadi ne a jikinsa tissue na maza fari qal,an masa dinkin boda,tun daga sama har qafafunsa aka dauki hoton,ya dan karkace kadan yana murmushi,hannayensa saye cikin aljihunsa,
"Sisi na kalli ya rayyan dina don Allah,kalli yadda ya rayyan ya zama.....",
ido itama ta dan fiddo tana fadin"masha Allah,fatabarakallhu ahsanul khaliqin,kinyi dace da ya cancanci a taya ki murna kam sister,congrats"ta fada tana kama hannun rumana
"Alhamdulillah,na gode sis".
Bakin gadonta ta koma ta zauna tana kallon yadda rumana ke ta maimaita kallon hotunan,dariya ta dinga yiwa rumanan har ta dan tsokaneta
" da alamu yau dakin nan babu bacci kenan"dariya rumanan ta saka"haka nake ji a jikina,don yau hira ni da pics din ya rayyan har asuba"
"Allah ya bamu alkhairi to" inji raihana tana dariya kana ta shige cikin bargo
Tun daga ranar hotunan suka zama abubuwan kallo da kuma debe mata kewa,ko waya zasuyi da rayyan din sai ta daukosu ta saka su a gabanta.