← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 66

Sashe 27

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dauki wayar rumanan da takardar ta sanya mata gefan kanta ta yadda tana tashi su zata fara gani sannan ta rataya jakarta ta fito.

Babu motsin kowa kamar yadda ta zata,don haka hankali kwance ta fito daga gidan,layin nasu tsit yake kasancewar bai da yawan mutane koda da rana ne ma balle da sassafe irin haka.

Ta bayan layin nasu tabi,tana tafe a hankali iskar safiya na kadata kamar yadda tunaninta ke ci gaba da kaduwa,zuciyarta nason ta fara zafi kamar yadda take mata amma ta daddage ta hanata,daga nesa kadan da ita ta hango shi yana tafe yana sassarfa sanye da kayan motsa jiki green and white,bata tabbatar da shi bane har sai da yazo gaf da ita,dauke idonta tayi a hankali tayi gaba,shi din ma baice komai ba yayi gaban,saidai kuzarin jikinsa da ya sake raguwa,ya hangi abubuwa masu tarin yawa cikin idonta da ma fuskarta baki daya,saidai yaya zaya yi?,duk yadda yaso ta bashi daka ta qiya,a yanzun da ya ganta ya tabbatar akwai damuwa mai yawa cikin zuciyarta kamar yadda take cikin zuciyarsa,duka su biyun ta gwammaci su zauna cikin damuwa da takurar zuciyoyinsu,ta gwammace ran mutum daya ya faranta na mutum biyu kuma ya shiga qunci akan wani dalili mara tushe bare makama,sam baya jin hakan adalci ne take shirin yi musu.

Ba wasu mutane cikin makarantar sai jefi jefi wanda basufi ka qirgesu da yatsun hannunka ba,kai tsaye ta wuce hall din da zasu dauki lacture din yau,kusan itace mutum ta farko data shiga gurin,babu kowa sai jerun kujeru reras da suke cike da hall din,can baya ta tafi ta zabi daya daga cikin kujerun ta zauna akai sannan ta dora kanta a gurbin da ake dora littafi,kamar ta fiddo zuciyarta waje ta huta da abinda takeji,kukan ma yaqi zuwa ballantana ta samu salama kan abinda takeji.

Qarfe tara da rabi wayarta ta shiga ruri,share kiran tayi saboda tana zaton ko amir ne,kiran da akaci gaba da yi ya sanyata sanya hannu ta ciro wayar ba tare da ta duba mai kiran ba ta kara wayar a kunnenta
"Wayyo sisi,kin tafi kin barni da kayan murnata ni kadai dawa zanyi sharing farincikin da nakeji cikin zuciyata"muryar rumana ta doki dodon kunnenta,lumshe idonta tayi tana ci gaba da jiyo karadin rumanan
" sisi bansan da me zan saka miki ba a rayuwa,duk wani abu na farinciki ke kike fara sanar da ni a rayuwa"
"Farincikinki shine nawa sisi" qwalla suka tararwa rumanan
"Allah ya bani abinda zan saka miki da shi sisi na"
"Kada ki damu,duk abinda raiha tayiwa rumana tamkar ta yiwa ita kanta raiha dinne"cikin karyayyar murya rumana tace
" duk da haka sisi farinciki na bai cika ba,Allah ya sani nayi farinci qwarai da gaske da Allah ya bani damar mallakar miji daya da daya irin yaya rayyan,amma sisi banason ace anyi bikina ba tare da ke ba,bana so na tafi na barki ke kadai"dariyar qarfin hali raihana tayi
"Kada ki damu rumana,komai lokaci gareshi,hakanan kowa da irin tasa QADDARAR,idan Allah ya kawo nawa lokacin babu tsumi babu dabara ai"
"Hakane sisi na,amma zan tanada miki wani abun mamaki kafin ki dawo tukuicin albishir din da na gani"
Murmushi ta danyi
"Ina maraba da hakan"
"Ok saikin dawo"

Tunda ta ajjiye wayar ta sake maida kanta yadda yake a dazun,tun tanajin shigowar mutane da dai dai da dai dai har hall din ya soma cika daga bisani malamin ya iso.

Zata iya cewa bata fuskanci komai ba cikin darasin yau,ta dai tsinci kawai abinda ta tsinta shima din tana daga kwance,yadda ta zama farkon zuwa haka ta zama qarshen tashi wajen qarfe biyu saura na rana,ta miqe da qyar tana jin yadda qirjinta yayi nauyi,da qyar takai kanta bakin titi ta samu a daidaita sahu ta hau,bata sha'awar zuwa gida don tasan rumana na can na jiranta,kuma tasan bazataji dadi ba idan ta ganta cikin yanayin da take ciki,kewar danginta ya kamata,duk yadda takai ga 'yan uwa a garin kano bata da ko daya,bata tabajin hakan cikin jikinta ba sai yau,saboda haka tace kawai mai motar ya kaita qoqi gidan hajiya babba kakar rumana.

Cikin 'yan mintuna suka iso,gidan shiru babu kowa kasancewar babu yara a gidan kamar yadda muka sani,saidai fes yake kamar ko da yaushe,hajiya qarama na bakin fanfo tana daura alwala suka gaisa,ta fara zolyarta ina amare?,kuma yau naga zahra banga wata ba ina kika baro 'yan biyun naki?"murmushi tayi tace
"Daga makaranta na biyo ai hajiya ba daka gida nake ba"
"Ayyah,koda naji",jakarta ta cire itama ta daura alwalar kawai sannan ta wuce dakin hajiya babba.

Kan abun salla ta sameta saidai ta idar lazumi take,fuskarta fal fara'a tace
" a'ah,raihanatu kece kike tafe?"murmushi tayi
"Wallahi hajiya daga makaranta nake ina yini"
"A'ah,fara yin sallarki naga kamar alwala kika daura" ta fada tana tura mata wata daddumar dake kusa da ita ta shimfida.

Kafin ta idar din har baaba ramma ta kawo mata abinci cikin kula guda biyu,bayan ta idar suka gaisa
"Ina kika baro ruma.....oh wai ruma da aure akwai kallo" inji hajiya babban tana dariya tare da tabe baki,dariya hajiyan ta bawa raihana har ta dan dara
"Tana gida hajiya"
"To Allah ya sanya alkhairi,jiya baban nata yake sanarmin ai da ya shigo gaidamu da daddare,Allah ya nuna mana naku,Allah ya kawo muku na gari kuma" inji hajiya babban,har zuciyarta tan son raihana,jininsu ya hadu sosai,murmushin jin kunya kawai tayi ba tare da ta amsa ba
"Nikam so nayi ma wallahi ace rayyanun ya hadaku baki daya keda 'yar uwarki,kinga shikenan an huta,tuwona maina,kowa yasan kowa babu wani sauran fargaba" wani mummunan faduwa gabanta yayi,ta qwalalo ido kamar wadda aka hurawa yaji ba tare data san tayi hakan ba,sai qwalla ta cika mata ido saboda sosa mata ciwonta da hajiyan tayi ba tare da ta sani ba
"Haba hajiya,Allah ya sawwaqe na auri mijin 'yar uwata" maganar ta fito ba tare data shirya ba.

sakin baki hajiyan tayi tana dubanta,abinka da gwanar salati sai kuwa ta debo shi"la'ilaha illallahu muhammadarrasulullahi,oh ni 'yar nan,yo meye?,haramun ne ko kuwa",sai kuwa hawayen ya gangaro kan kuncinta
"Don Allah hajiya kiyi shiru maganar ma babu dadin ji,indai zan auri mijin rumana zan iya auren mijin zainab kenan" kama haba hajiyan tayi,ganin lamarin ya girmeta
"Tabdijan,ashe kema wawiya ce ban sani ba?nace haramun ne?" Kai ta girgiza cikin zaquwa a bar maganar
"A'ah hajiya,amma ai ana barin halas don kunya ko?" Haushi ya kama hajiyan,a hasala tace
"A wanne hadisin ko kuma a wanne qur'anin?" Shiru tayi ta rasa wacce amsa zata bata ma,sai yau ta taba yarda da zancan rumana da tace mata hajiyan muguwar rigimammiya ce
"Mu to ba haka muke ba,ke da rumana ganinku muke kamar mahaifa daya kuka kwanta,kuma wallahi kinji na rantse miki da rayyan yace yana so da sai an hada masa ku duka,akwai abinda yafi haka kwanciyar hankali ne,yaranmu munsan hannun wanda suke,wanda koda mun mutu munsan ba zasu wulaqanta ba".

Da sauri ta kuma kallin hajiyan zuciyarta na kadawa,godiya ta dinga yiwa Allah da bai matsi bakin rayyan ya gayawa kowa ba,da sauri ta saki murmushin yaqe don son kawar da maganar tace
" hajiya kwantar da hankalinki,ina ma da miji ni,lokaci kawai nake jira don mu sake fuskantar juna,bari na kira miki shi ma ku gaisa"hannunta na rawa ta fito da wayarya ta fara neman lambar amir
"Oho dai,bazamu shaideshi ba kamar namun ba ko?" Daidai lokacin da kiran ya shiga,cikin zumudin ganin rana ta farko raihana ta kirashi da kanta ya daga
"Kashe na kiraki" amir din ya fada,ba'a wuce sakan biyar ba ya kira din kuwa,bayan sun gaisa ta miqawa hajiya wayar suka fara gaisawa.

Wasa wasa saiga hajiya hira ta miqa ita da amir harda kwasar dariyarta,raihana na kallon ikon Allah,sai kawai ta janyo kular abincin ta bude ta zuba ta soma ci kadan kadan tana kallon yadda suke hira kamar sun dade da sanin juna,sai da taci rabin abincin sannan sukayi sallama hajiyan ta miqa mata wayarta.

"A haka dai yaron akwai hankali da shiga rai" hajiyan ta fada,murmushi raihana tayi ko banza ta toshe wata kafar da take qoqarin balle mata ta zame mata babbar barazana,don ta riga ta san matuqar hajiya babba ta fara tada wannan maganar to babu wanda zai musa mata tsakanin abba da daddy dalhatu,hannu hajiyan tasa suka ci gaba da cin abincin tare,tuwon dawa ne miyar kuka da yasha man shanu
"Da Allah zai kawo rayyanu nasan ba qaramin jin dadim tuwon nan zaiyi ba" inji hajiya babba,itama raihana abinda take qissimawa cikin ranta kenan,saboda ta sanshi gwanin son abincin gargajiya ne kamar ita,a nan suke fada da rumana.

Ba qaramin jin dadin zuwanta gidan tayi na,sunyi hira sosai da hajiyan,ta dinga bata labarukan yadda rayuwa take a ashekarun baya da yanayin yadda ake aure a lokacin,har ta dinga jin sha'awar irin auren gargajiya babu dorawa kai nauyi ko a'ala masu yawa,sannan ta dinga jin cewa zata iya auren amir koda bata sonshi,saboda yadda hajiyam ke bata labari ita kanta batasan waye mijinta ba wato marigayi tahir babansu daddy dalhatu sai da aka kaita dakinta,kuma gashi mutuwa ce ta rabasu wato auren mutu ka raba kenan,sai wajen qarfe uku ta haye kujerar hajiyan,ba dadeqa bacci ya dauketa anan saboda bashin baccin da ta dauka daren jiya.

Cikin baccinta ta dinga ji kamar muryarsa,a hankali ta dinga bude idonta,shi dinne yana zaune gaban hajiya babba suna ta hira abinsu,yana sanye da shadda baqa dinkin tazarce da wando kansa babu hula,fadin kyawun da tayi masa ma bata bakine,ta haska fatarsa sosai,ta dauke idonta tana qoqarin tashi zaune,shima yana ankare da ita tunda ya shigo falon yayi arba da ita,rigar jikinta ta fidda shape dinta sosai,hakan dankwalin kanta yayi nashi gu sabida bacci,wani kyau yaga ta qara yi masa har ya tsaya ya morewa kallonta na sa'o'i kafin fitowar hajiyan
"Yauwa dama yanzu nake shirin tashinki kiyi salla hudu garda rabi" inji hajiya babban
"Eh na tashi" ta fada tana neman dankwalinta jikin hanzari ganin yadda yake qare mata kallo da ya qarasa kashe mata jiki da daure jijiyoyin jikinta.
Chapter 27 · 0% Book details