← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 66

Sashe 21

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin yadda dare ya nausa ba bacci babu alamunsa ya sanyata miqewa,tunawa da tayi da ayar nan da Allah yake cewa ((Ku saurara,da ambaton Allah kawai zukata ke samun nutsuwa)),toliet ta shiga a daddafe ta daura alwala,sannan ta fito ta shimfida abun sallah,ba zata iya tsaiwar sallar ba saboda jiri jiri da take ji,sabida haka ta fidda qur'ani cikin ma'ajiyar litattafansu ta soma karatun can qasa yadda ba zata tashi rumana ba,tana yi tana sharar hawaye har sai data ji ta gaji,zuciyarta tayi sanyi sosai sannan ta rufe,ta dade sosai tana addu'a har sai da bacci ya rinjayi idanuwanta sannan ta kwanta

************

Cikin kwanakin duka tayi duk wani qoqari na kawar wa da kanta damuwar da take ciki,ta samu nasara bakin gwargwado,kasancewar shi kansa rayyan din ba ganinshi take ba,tayi qoqarin toshe duk wata kafa da zata hadata da shi,hatta da wayarta kusan ko yaushe a kashe take don kada saqo ko kiransa ya shigo,saidai ko da ta bude din bata samun daya cikin biyun abinda take tunanin,sosai walwalarta ta ragu haka kuma ta dan fada kadan,saidai duka babu wanda ya kawo komai kasancewar cikin jarabawa suke,kuma sun riga sun santa da naci da qwaqwar karatu,bata da wani sukuni idan suka fara jarabawa har sai sun kammala ta fita da kyakkyawan sakamako.

Cikin nasara da taimakon addu'a ta kammala jarabawarta rumana kuma guda daya ta rage musu,har zuwa lokacin bata kuma sanya rayyan cikin idonta ba,ganin zaman hutu kawai zasu fara ya sanyata fara shirin tafiya mai duguri,tunda sati guda ya rage a fara bikin falmata,sannan a gefe guda tana ganin wannan dama ce da zata sake nisanta kanta da rudanin da take ciki,ta sanar da abba tuni ya fara yi mata shirin tafiyar,wanda ya riga daya saba daga shi har daddy dalhatu,har yau ji suje kamar bukhar na raye ne,basu bar yiwa ahalinsa komai ba,duk lokacin da zasu maidugurin basa gajiya da tafiya da hidima mai yawa.

Qauracewar da yayi wa cikin gidan baki daya yayi ta ne don ya samu sassauci itama ya bata damar samun sassauci cikin zuciyarta,bai karaya ba koda na sakan daya,yana jin nasara na biye da shi koba dade ko ba jima,duk da yanakanji zafin kalmar qi data ambata masa,amma ya dauki hakan a matsayin wata barazana ce kawai wadda bata dada shi da qasa ba.

Bazai yiwu su tafi tare da rumana ba saboda jarabawarta guda daya da bata rubuta ba,wadda zata rubuta ta ne ana ya gobe za'a fara bikin,sun yanke cewa ranar data gama zata taho tunda qarfe tara ce zuwa sha daya sun fito,ana ya gobe raihanan zata tafi rumana tayi mata rakiya gidansu gun daddy dalhatu tayi masa sallama,auwalu ne ya kaisu haka suka dawo both din motar dauke da saqonnin da za'a kaiwa umminta fanna,yana qoqarin shigewa cikin gidan raihana ta hangoshi,bayansa kawai ta gano yana sanye da qananun kaya da takalmi rufaffe irin na maza saye a qafarsa,gashin kansa irin na fulanin buzaye ya kwanta har qeyarsa,hannunshi dauke da jakar office da alamu dawowarsa kenan daga office din don taji hucin zafi na fita daga motarsa,ko bata kalle fuskarsa ba tasan yayi kyau don babu suturar da zai sanya bata karbeshi ba,shiru tayi bata nuna ta ganshi ba kamar yadda ta fuskanci rumana bata ganshi ba don batason ta janyo masu shi.

Tana daki tana hada kayan nata jifa jifa tunaninsa na fado mata tana irga yawan kwanakin data dauka rabon data ganshi,wani lokaci ta kwabi kanta wani lokaci taja tsaki har sai da rumana ta dubeta
"Lafiya kike sisi?" Sai ta saki murmushi tana jefar da rigar hannunta
"Lafiya qalau"
"Meke going to?"
"Bana son in tafi ne ni kadai na barki,tafiyar ba zata mun dadi ba" da gaske haka maganar take har cikin zuciyarta,sai rumanan tayi murmushi ta rausayar da kanta
"To ya za'ayi,duk dr buba ne ya janyo mana,da tuni tare zamu tafin,amma kada ki damu,nan da kwana shida kacal zan biyo bayanki" suka saki murmushi tare

**************

Sammakon fita yayi saboda wasu baqi da company din nasu zaiyi,ita din ma qarfe takwas ta gama shirinta tana parlour din abba suna sallama,kudi masu yawa ya miqa mata
"Ga wannan ki kaiwa su fannanan,ki gaishesu da kyau....wannan kuma" ya sake miqa mata wasu
"Ki riqe a hannunki saboda sha'anin biki,duk wani abu da kanuri keyi kada ki yarda a barki a baya kema kiyi ki saje da su kinji?" Ya qarashe maganar cikin barkwanci,abban ba baya bane gun barkwanci da jan iyali a jiki,babu muhallin cewa ba zata karba domin kuwa bataso yaji ta maisheshi baare,ma'ana bata daukeshi matsayin mahaifinta ba,godiya tayi masa mai tarin yawa tana sake jin qaunarsu da ganin girma qima da mutuncinsu cikin idanunta.

haqiqa babu abinda yakai abota da mutanen qwarai dadi,gashi dai abbansu baya doran qasa amma har yau suna cin ribar alaqar da aka ginata domin Allah,har yau suna kula da daukar nauyin iyalansa tamkar yana raye,aboki na gari babu shakka riba ce duniya da lahira,Allah kaci gaba da hadamu da masu sonmu domin Allah,taci gaba da fada cikin ranta ganin irin yadda ciki da booth din motar ke cike da kaya kala kala duka tsarabar daddy dalhatu da abba ne,baya ga kudi masu yawa da suka damqa mata.

Lokacin da auwal ke qoqarin tada motar takai idanunta sashen da yake ajjiye motarsa,wayam bata nan,hakan ke alamta mata mamallakinta ne baya nan,ta rufe idanunta a hankali wani abu mai ciki da rauni na kewaya zuciyar tata,baya kadan ta tuno,wato duk lokacin da zata maiduguri ita kadai ko da rumana ko da ummu ne,shike daukarsu ya kaisu har tasha idan ta kama ta tashar zasu tafi,baya tafiya sai yayita tsokanarsu da zaiyi missing dinsu,har sai motarsu ta daga zaya dawo gida cike da kewa,haka shike komawa daukarsu.

Bayan doguwar tafiya da suka sha cikin ikon Allah suka shigo garin na maiduguri lafiya qalau,kamar ko yaushe gidan kakanninta take sauka,ummin nata ma na can gidan saboda tazo kenan ba zata koma gidan da take aure ba sai bayan an kammala bikin,wannan karon gidan akwai jama'a 'yan uwa ba laifi kasancewar gida ne mai girma da yalwa anan aka yanke za'a gabatar da taron bikin,gida ne part part wani part din ma babu kowa ciki.

Tana parlourn tsohuwa hajja yakura kakarsu wanda yake makeke ne mai dauke da dakuna har biyar,'yan uwa duka na ciki anata murna da ganin juna.

Family ne mai cike da hadin kai da qaunar juna,don haka kusan yawanci 'yammatan familyn wadanda duka kusan age mate din raihana ne shekaru da kuma matakin karatu ma baki daya suna gidan sunata shirye shiryen bikin,suna da wayewa daidai gwargwado don dukansu suna makarantun gaba da secondry baya ga ilimin addinin islama da suke da shi,lallai kowa ya bar gida gida ya barshi,bata bar cikin 'yan uwan nata ba sunata hira anata tsokanarta sabida yadda yaren nasu yaso barin harshenta,don ba komai take iya ganewa ko mayarwa ba,baba gana shi yafi takura mata,abokin wasanta ne abbanshi dan gidan ne.

Dare suka raba bayan sun kebe ita da umminta, sosai takejin wani farinciki na ratsata,duk wani bacin rai da qunci da yayi saura cikin zuciyarta ya dinga qaura daga ranta,lallai uwa ba wasa bace,uwa maba da mama,Allah ka jiqan iyayen wadanda suka rasu namu kuma ka dade su da lafiya da nisan kwana mai amfani,kasa suyi kyakkyawan qarshe,ummin ta dubeta tace
"Wato su abbanki basu gajiya da hidima dai koda yaushe,shekaru kusan goma amma har yau basu mance da Abubakar ba,Allah ya saka musu da alkhairi ya basu ladan abinda suke aikatawa duniya da lahira" murmushi raihana kawai takeyi ta amsa mata da amin.

Kiran rumana ne ya shigo wayarta,sosai suka sha hira take gaya mata ashe bata gayawa ya rayyan zata tafi ba
"Awww,na manta ne sisi"
"Aikam nidai na ruwana,don ya nuna bacin ransa sosai"
Wani zancan daban ta soko mata don kawar da wancan,bata dade da ajjiye wayar rumana ba kiran amir ya shigo,katsewa tayi ta yiwa mamanta sallama ta tafi dakin 'yammatan don sai tafi sakewa a can,sosai amir ke jin dadin yadda yakr ganin sauyi tattare da raihanan,takan sake da shi yanzu ta amsa wayarshi duk da har yanzu bai samu yadda yake burin samu daga gareta din ba.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 8:59 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________

*An karbo daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace"shin wanda yake daga kansa(daga ruku'u ko sujjada)kafin liman ya d'aga nashi,baya jin tsoron Allah ya maida kansa kan jaki(ranar qiyama)"*
___________________

*Babi na sha tara*

Ta sake sosai cikin danginta,ta mance da duk wata qura da ta baro a baya,da ita aka ci gaba da shirye shiryen bikin,inda ta fidda kudi cikin kudin da abba ya bata tayi duk wata siyayya irin ta bikinsu wadda zata sata ta saje da 'yan uwanta itama ta fito a babarbariyar asali.

Kitso aka yi mata mai kyau irin wanda akewa 'yammatan kanuri a al'adance kamar yadda aka yiwa sauran 'yammatan,hakanan aka yi mata jan lallensu mai kyau wanda ya sake qawata fatarta,sai take jinta a kanurinta sosai,musamman idan ta waiga ko ina ta ganta cikin 'yan uwan nata,tabbas gida da dadi yake.

Ranar da rumanan ta taso ta kirata a waya ta sanar mata,da kanta ta shirya zuwa daukarta ita da siyama da najwa wasu cousing dinta da tasu tafi zuwa daya,tun daga tasha suka daukota cikin motar baba gana,gwanin hira sai ya samu abokiyar yi,cike da raha suka iso gidan.

Suna zaune a dakin su biyu rumana na cin abinci tare da huce gajiyar tafiya ta dubi raihana
"Dubeki sisi,wallahi kin koma kanurinki sak" dariya raihana tayi
"Kema jira nake ki huta nan da anjima zan sa a maida ke,don har irin kitso na sai an miki" dariyar itama tayi,tana shirin yin magana wayarta ta fara ringing,murmushi ya wadaci fuskarta kana ta tsame hannunta daga abincin ta jingina da kujera ta daga kiran
"Ranka ya dade,kamar kasan cewa kana raina" inji rumana,ba ko tambaya raihana tasan cewa rayyan ne ta kuma san hirarsu da tsawo,sabida haka ta miqe ta kwashe sauran tarkacen kayan da rumana ta gama amfani da su ta fice a dakin.
Chapter 21 · 0% Book details