Sashe 33
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Qasa tayi da kanta don ba zata iya jurewa kallon qwayar idonta da yake ba
"Qarya kike raihana......qarya ne da kike iqirarin kinfi kowacce halitta dake doron qasa qaunata,dalili kuwa banga hakan ba,banga alama ba raihana,banga alama ba" ya fada cikin zafi,kallo daya zaka yi masa ya gaya maka zuciyarsa tafasa take,sai ta sake sadda kanta kawai ganin yadda lokaci guda idanunsa suka kada suka koma launin ja,tabbas da zai yiwu da kuma akwai dama data ciro masa zuciyarsa ya ganewa idanunsa,saidai bata da buqatar hakan,tafiso ya tafi a yadda yace yazun,su tafi a bata qaunar tasa
"Raihana" ya kirata cike da zafi,bata dubeshi ba shima bai damu ba yaci gaba
"Na baki dukkan wata dama data dace,shiru da nayi da maganarmu nayi ne don na baki dama da 'yanvin da kike da su,na baki damar gamsuwa da kanki cewa zaki aureni ni rayyan,na baki dama wadda koda munje gaba da maganar bamu da banbamcin ra'ayi,amma na fuskanci baki da adalci,hakan yasa kika kasa yi mana adalci ni da ke,to ina so na sanar dake...... wannan ce damarki ta qarshe,wallahi,wallahi,wallahi,kinji na rantse miki....,ni rayyan matuqar na dawo daga england baki tsaida shawarar da zata zama adalci tsakaninmu baki daya ba....ko da yardarki ko babu zan sanar da magabata,kuma sai na aureki ko ta halin qaqa,qarshen qiyayya ki kashe rayyan a daren da kika zama matarshi,fine,wannan ya rage naki" ya fadi yana miqewa ya gyara t.shirt din jikinsa sannan ya sanya kai zai fice,cike da qarfin hali tace
"Hmmm,sai mu gani ai,yadda ba'a yi muku auren dole ba wallahi nima babu mai yimin" har ya daga labulen zai fice sai ya sakeshi kana ya waiwayo,murmushi ya saki sannan yace
"Zaki gani kuwa,ki jira lokaci shike da amsa" ya fada kana ya fice abinsa.
*mra muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:28 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*Daga abu hurairah R.A yace manzan Allah S A W yace"idan aka kirayi dayanku zuwa walima to ya amsa,idan ya kasance mai azumi to yayi addu'a,idan kuma baya azumi to yaci(daga abincin walimar)"*
_______________________
*Babi na ashirin da biyar*
Za'a iya cewa tarihi ne ya maimaita kansa,kamar wancan karon tafiyarsa england na farko cikin filin jirgin saman malam aminu kano,saidai wannan karon akwai banbance babance masu tarin yawa.
Tsaye take gefe gudu harde da hannayenta,kanta na kallon wani sashen daban,sai ka rantse da Allah batasan me rayyan da rumana keyi ba,duk da tayi qoqarin janye zuciyarta daga lamarinsu amma kunnuwanta na iya jin komai.
Kwance take saman qirjinsa tana zubar hawaye,yayin da shi kuma hannunshi daya ke gadon bayanta yana shafawa alamun rarrashi,idanunshi kafe kan raihana da taqi yarda ko sau daya su hada idanu,yana jin duk cikinsu babu wadda ke jin abinda yakeji cikin zuciyarsa,dauriya da dakiya kawai yake gwadawa irin ta maza.
Da qyar ya samu ta tsagaita kukan sannan ya rabata da jikinsa,ya dubeta
"Sai ku kira sisinki muyi sallama ko?" murmushi ta sakat mishi sannan ta qarasa inda raihana take,hannunta ta riqe wanda ya sanya raihanan juyowa ta dubeta,fuskarta cike da damuwa yanayin idanunta a birkice
"Lafiya sisi?" Rumana ta tambayeta,murmushin yaqe ta saka a hankali sannan ta girgiza kai
"Babu komai sisi na,me kika gani,kawai banjin dadin jikina ne"
"Cuta kike a tsaitsaye raihana,kuma kinqi yarda da maganata,har yanzun kin kasa yarda da qaddarar rashin amir,tabbas babu abinda yafi rabuwa da masoyi zafi,koni yanzu ni kadai nasan me nakeji tafiyar da ya rayyan zaiyi na wata shida,bare ke da kukayi rabuwa rabuwa ta har abada,kiyi haquri Allah zai maida miki mafiyinsa insha Allah" kai kawai ta iya jinjinawa,babu shakka baka taba sanin muhimmancin abu sai lokacin da ka rasashi,a yanzun take sake jin rashin amir din sosai,take kuma sake jin maraici cikin jikinta gaba da baya.
Ta rasa abbanta,ta rasa amir sannan gashi finally ta rasa rayyan,tabbas jarrabawa ce sosai cikin rayuwarta da Allah ke rabata da wadanda take da buqatar zama da su,tana fata kuma zata cinyeta.
Mintina biyar ya rage a fara nemansu don haka ya dube raihana a gaggauce sannan yace
"Haka ake sallama da mutum,kin koma gefe guda kin tsaya" cike da dakewa da basarwa gefe guda kuma saika tsammaci wasa ne tace masa
"Ina laifina ma da na rakoku?"
"Madalla,zan miki tuni dai,kada ki mance da maganarmu,ki jirayi dawowata"
"Wacce magana ce ni aka wareni ba'a gayan ba,wariyar launin fata za'a nunan?" Rumana ta fada a shagwabe,gaban raihana ya buga,ta saki ajiyar zuciya sanda ta jiyo rayyan na fadin
"Me kike ci na baka na zuba,ki bari na dawo mana,ni da kaina zan gaya miki" murmushi ta saki kana tace
"Allah ya dawo min da kai lafiya to"
"Amin my angel" ya fada yana kissing dinta a goshi.
Share qwalla tayi tana daga mishi hannu ya juyo ya dubesu baki daya kafin ya qarasa bacewa ganinsu
***************
To xamu iya cewa ya tafi yabar kowaccensu da zazzafar soyayyarsa cikin zuciyarsa,yayin da shima yake can yana dakon nasa,sau tari takan ga kewar rayyan da rumana keyi nafila ce akan tata,dalili kuwa shine ita tana iya fada,tana iya bayyanawa hakanan tana da 'yancin nunawa,itakam bata da wannan da 'yancin sam.
Ta sha ganin kiransa amma sai ta share taqi dagawa,wanda idan yaga hakan sai ya cillo mata saqon karta kwana ma sms tunda ita ba charting take ba,
..
Kalaman soyayya ne danqare a cikinsa da kuma sake jadda da mata qudirinsa na babu gudu babu ja da baya ta jirayi zuwansa,duk sanda ta karanta hakan qirjinta kan tsananta bugawa,duk da cewa bata taba mancewa da maganar tasa ba,kullum wayewar gari da ita take kwana da ita take tashi,addu'a sosai kawai ta tsananta tare da neman mafita wajen ubangiji,don ta lura rayyan ya shallake tunaninta.
*************
Kwanci tashi babu wuya wajen Allah,hakanan yau da gobe bata bar komai ba,sai gashi rayyan ka dosar wata na hudu da tafiyarsa,watanni buyi kacal suka rage masa ya dawo.
Cikin satin da ake ciki jikin hajiya babba ya motsa,har takai ta ga kwanciya a sibiti,randa aka kwantar da itan suna makaranta,ummi tayi musu waya ta gaya musu idan sun tashi daga lactures da wuri suyi abinci su kawo asibitin tana can su taddata.
Qarfe biyar saura suka isa asibitin suka fara bin kwatancan dakin da suke,suna shiga barandar da zata sadaka da kebantattun dakunan rumana tayi kacibus da qawarta,suka gaisa da raihana,ba zata juri tsaiwa ba don haka tayi gaba taba duba lambobin dakunan.
Daki na uku ta murda qofar ta tura tare da yin sallama,mutum uku ne cikin dakin banda marar lafiyar dake kwance ta hudu,biyun mace da namiji saman carfet dake shimfide a dakin suna hira kadan kadan,yayin da dayan wanda ya da alamu ya girme musu yake zaune kan kujera hannunshu dauke da waya yana danne danne wanda shigowarta ya sanyashi daga idonsa.
Ganin ba dakinsu bane ya sanyata cewa"sannunku ya musu jiki"wadanda ke saman carfet din ne suka amsa mata da cewa da sauqi
"To Allah ya qara afuwa"
"Ameen ya Allah" suka sake amsa mata har na kan kujerar
"Hala dakin gaban nan ne daki na uku ko?" Wannan karon macen ce ta amsa mata da eh shine
"To na gode" ta fada da hanzarinta ta fice kana ta rufe masu qofar saboda zuba mata ido da na kan kujera yayi kamar wani sabon maye.
Sun samu jikin hajiyan da sauqi ba laifi alhmdlh,raihana na gefanta hajiyan na mata hira kadan kadan tana amsa mata.
Basu tashi tafiya ba sai wajen takwas na dare,sun tsaya jiran halima qanwar daddy dalhatu da zata kwana da hajiya gashi bata zo ba,uncle salis ne ya kirata ta shaida masa cikin nuwaira yarinyarta ke ciwo wlh shi ya sanya tayi jinkiri amma gata nan zuwa,daddy dalhatu yace tayi zamanta ta kula da ita Allah ya bata lafiya.
Ganin ana shirin zuwa dauko hauwa'u dayan qanwar tasa ya sanya raihana tace a barta ita zata kwana,daddyn ya dubeta yace
"Kiyi yaya kuma raihanatu da makarantar idan banda abinki?"
"Ai daddy gobe da jibi duk bani da lacture bazan ma shiga makarantar ba"
"To shikenan yayi kyau,Allah yayi miki albarka"
"Ameen daddy", ya juya ya dubi rumana
" to kefa?"sai ta dan ya mutsa fuska
"Zuwa zan dinga ina komawa..." Ko kafin ta qarashe ma hajiyan ta tareta cikin muryar marasa lafiya
"Banso ma ki zauna,raihan ta isheni"
"Dama nima ba zaman zanyi ba,a hana mutum wayar dare" ta fada ciki ciki tana ficewa a dakin
"Za kici qaniyarki" inji maman rumanan ta fada din ita taji me tace.
Bayan tafiyarsu hirarsu suka ci gaba da yi da hajiyan,sai data gaji ta kwantar da ita ta gyara mata rufar sannan ta fita don siyo musu ruwa da basu da shi ta sanya cikin fridge din dakin.
Saura kadan suyi gware,ya danja da baya tare da cire eye piece din kunnensa yana qare mata kallo ya furta
"Am sorry,ban kula ba" kai kawai ta kada ta kewayeshi ta wuce ya bita da ido
Da safe ummu ce ta fara aiko da breakfast,auwalu ta aiko gashi yayi wuri basu fara bari ana shiga bangaren nasu dakunan ba,don haka yayi kiranta ta fito don ta karba,kamar jiya da shekaran jiya,yauma yana tsaye bakin qofar nasu dakin,ya bita da kallo kamar yadda ta fuskanci kusan ko al'adarshi ce haka oho masa,dauke kai itama tayi kamar kullum din tayi gaba abinta.
Ta fara dauko kwandan farko don ba zata iya dauka duka ba,data dawo ba taddashi bakin qofar ba ta shige dakinsu ta ajjiye sannan ta sake fitowa,yana tsaye bakin qofar dakin hannunshi riqe da daya kwandon,murmushi ya sakar mata sannan yace
"Ina kwana,don naga bakison kula kowa,ko dakinmu baki sake shiga kin gaida mamarmu ba"yayi maganar yana miqa mata kwandan,amsa tayi kawai tare da ce masa
"na gode" ta juya ta koma ciki.
Ta gama bawa hajiyan tea kenan aka turo qofar,idan bata manta fuskarba budurwar da ta gani ce shekaran jiya a maqotan dakinsu.