← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 66

Sashe 56

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ce ta shigo dakin cikin wata gown ta yara baqa,adon baqi akayi mata wanda ya sake qawata yarinyar kamar ka saceta,hannu raihana ta dago mata tana sakar mata murmushi direct yarinyar tayo gunta da tsallenta tana fadin ke nake nema mamma ki bani chaculet,saman cinyarta ta dorata tana fadin
"Zan baki kuwa amma sai kin gayan inda mommynki take" ta dan bata fuska
"Ni bazan rakaki ba bayan koroni tayi wai zatayi wanka" zaro ido raihana tayi
"Wa ya gaya miki ana fushi da momy,babu kyau kice kin daina ko?" Akwai ta da jin magana haka suka horata take ta gyada kai tare da fadin na daina
"Da kyau ahsanti ya ibnati,yanzu zaki rakani inda take?" Kai ta sake daga mata,ta sauketa daga saman cinyar tata ta dauki mayafinta sea grean ta lulluba,umaima coursing dinta dake gefe tana kwalliya ta dubeta cikin tsokana
"Ina kuma zuwa amarya"bata waiwayo ba tace
" ina zuwa"ta kama hannun islaha suka fice.

Sashen rayyan na da wanda ke cikin gidan har yanzu akwai komai a ciki na furniture taga sun durfafa,sai islahan taja tunga ta tsaya tana fadin
"Tana nan,ni mamma ki ban chaculets din zanu gunsu nasrin" murmushi tayi ta saki hannun nata sannan tace
"Kije daki gun anty umaima,wannan me yin kwalliyar,kice ta bude jakata ta baku chaculets" da sauri ta juya na tsalle ta wuce,raihanan ta bita da kallo tana murmushi,tana son yarinyar komai nata irin na sisinta,ta girgiza kai ta nufi sashen.

A hankali ta tura qofar falon wanda ga zatonta babu kowa shi ya sanya bata yi sallama ba,suna tsaye su biyun tana kwance a jikinsa kansa bisa fuskarta,sanye yake da shadda fara qal 'yar ubansu riga 'yar ciki da wando da babbar riga saidai kansa ba hula wanda hakan ya bayyaba hadaddiyar kwantacciyar sumarsa irinta buzaye da tasha gyara,tissue ne riqe a hannunsa yana goge mata fuska da alama hawaye take
"Meye ban gaya miki ba tun ba yanzu ba?"taji yana fadi,gabanta ya fadi har sai data runtse idanu,kuka sisinta take?,da sauri ta qarasa inda suke tsayen ba tare data yi sallama ba don ta mance
"Kinga irinta ko rumana?kinga irinta ko?" Ta fada tana dafa kafadarta muryarta na rawa,da sauri ta daga kanta tana duban raihanan
"Don me yasa zaku cutar da kanki?me yasa rumana kika dage bayan na dade da sadaukar miki,na dade da cireshi daga rayuwata?,bana muradin zama inuwa guda da shi,yanzu me kika yiwa rayuwarki adalci?" Sai ta saki rayyan din ta kama hannuwanta
"Ban fahimci me kike cewa ba me ya faru?"
"Kuka fa sisi na kike,kukan da kowacce mace ke kasa daurewa sai ta yishi kan mijin ta da takeso a irin wannan ranar" kai ta kada tana shirin yin magana rayyan din ya rigata,wanda tun sanda ta furta bata muradin zama da shi ya hasala
"Hey malama ya ishemu soki burutsunki,get out" sai ta daga idanunta tana dubansa
"Baka da bakin magana rayyan,kome ya faru da mu kaine sila,kaine tushe mafari" sai ya zuba mata idonsa da ya dan sauya launi saboda bacin rai,abubuwa da yawa ke sukar zuciyarsa,ya soke hannayansa cikin aljuhunsa yana ci gaba da dubanta kana ya sake taku ya kuma matsowa inda suke
"Kina maida kanki wata tsiya fiye da kima raihana,me zai faru idan rayyan ya rabu da ke?,me kike tsammani ehen?" Kafada ta daga itama cikin bacin rai
"Muradin raihana dama kenan"
"Ok....to...."
Kiran sunansa da rumana tayi da qarfi ya maida hankalinsa kanta,qwalla take fitarwa,sai kawai ta finciki hannun raihana suka shige bedroom din falon ta maida muqulli ta rufe ta samy gefan gadon ta zauna ta kallonta,itama gefanta ta samu kwai ta zauna din.

Aqalla mintina kusan goma kafin rumana ta bude baki ta fara magana cikin masifa
"Mijinki raihana kikewa haka?,kinsan zunubin da kike diba,waye ya gaya miki ma kuka nake?kaina ke ciwo zazzabi ya saukarmin nasha magani na kwanta,ki iya bakinki kisan me zaki gayawa mijinki,haka zaku sani a tsakiya cikin gidan kyna masifa?,to bazai yiwu ba,kuma matuqar kina so na huce kije ki bawa ya rayyan haquri" daga haka ta miqe ta hau shiryawa ba tare data sake tanka mata ba.

Ji take ko haushin me rumanan zata ji ba zata iya bashi haquri ba,saboda haka tayi hayewarta gadon baki daya tayi kwanciyarta tana sauke ajiyar zuciya cikin bacin rai,ya rabata da kowa kowa shi yake bawa gaskiya?sisin tata ma 'yar bayanshi ce,ita mai miji komai tace ba za'a bata masa rai ba,bacin rai kuwa su suka siyeshi,ta fadi ita kadai a zuciyarta tana masifarta.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:51 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*

______________________

______________________
*manzan Allah S A W yace"idan dayanku ya shiga bandaki(zai biya buqatarsa)kada ya fuskanci alqibla kuma kada ya juya mata baya,saidai ya kalli kudu ko arewa*
______________________

*Babi na arba'in*

Tana kwancen babu wanda ya sake tankawa har rumanan ta gama shirinta tsaf sannan ta waiwayo ta dubeta
"Tashi muje" inji rumanan,fuska ta yatsina tare da gyara kwanciyarta,tasan sarai so take su fita ta bawa rayyan din haquri
"Jeki kawai zan fito"ta fahimci me take nufi kai ta gyada kawai ta dauki mayafinta ta rufe mata qofar.

Har yamma tana cikin dakin,sallah kawai take tashi tayi ta koma ta kwanta,ba neman da ba'a yi mata ba amma an rasata,rumanan ma bata gaya musu inda take ba saboda so take ta samu iska sosai,saida lokacin kai amarya yayi sannan ta fadi musu inda take din.

Ta dade cikin bandakin tana kuka har sai da binto yayar mamanta ta fara buga qofar bandakin tana fada cikin barbarci,umaima ke mata dariya tana tuna mata ta mance cewar raihan ba ji take can ba sannan ta sauya harshe.

Cikin awa daya suka gama shiryata cikin shiga ta alfarma,leshi ne dandatsestse mai ainihin tsada riga da zani sannan aka rufe saman da lafiyayyar lafaya,duka hannayanta banguls ne na gold zuwa wuyanta da kunnenta,tsumammen qamshi ke tashi jikinta na musamman,saidai duka wannan kwalliyar hawaye ya nemi bata ta wanda ta kasa tsaidashi,wai yau ita ta auri mijin sisinta,yau ita zata shiga gidan sisinta a matsayin kishiya.

Fada da nasihar data karba mai tsaho ita taja lokaci wajen kaita,sai zuwa bays
An sallar magariba aka fito da ita,kuka take haiqan na zuci da badini,babu batun tayi gardamar fita saboda ta lura bata da wani magoyin baya,ta fuskanci babu mai bin bayanta duka 'yan jam'iyyar rumana da rayyan ne,haka ta dinga binsu tamkar raqumi da akala har zuwa motar da aka tanada don kaita.

Tun la'asar din ta koma gida don shirin tarbar 'yan kawo amarya,kusan komai a sanyaye take yinsa amma hakan ban hanata aiwatar da duk abinda ya kamata ba,bangaren nata akwai wasu daga cikin 'yan uwanta na bangaren mamanta,kausar da meela ma ba'a barsu a baya ba,suna gefe guda suna cika suna batsewa tamkar ma sune rumanan,da biyu suka zauna nan,sunyi ne don son ganin gudun ruwan rumanan a yau,fes ta shirya cikin hadadden code net tayi kyau kamar budurwa saboda kwalliyar yadda ta amsheta
.

Meela da kausar suka dubi juna gami da tabe baki,kausar ta maida kallonta ga rumana wadda ta maida kai wajen danna wayarta
"Allah ya kyauta,kiyashi dai garin jaye jaye yake janyo abinda yafi qarfinsa wallahi"
"Hmmmm,ni wallahi ko qanwata uwa daya uba daya bazan iya yiwa haka ba" cewar meela,a nutse ta dago ta dubesu
"Zuciya ce ai kowa da irin tasa,amma abinda nakeso da ku shine,ke kausar jini na ce bazan iya yanke alaqa da ke ba,abinda zance kawai da ke shine abinda nayi dai kaina na yima wa bake ba,so don Allah ki barni haka kinji,amma ke meela babu wani hadi tsakanina dake,matuqar ba zaki iya saka ido kiyi kallo ba kawai kina iya fita daga rayuwata,zaki iya yanke alaqar dake tsakaninmu" tana gama fadin haka ta miqe ta shige dakin gadonta.

ruf da ciki tayi tana maida numfashi,babu shakka cikin mutane ma akwai shaidanu,so suke qarfi da yaji su dasa mata baqon lamari cikin zuciyarta.

Zaren tunaninta ya yanke lokacin da taji budewar get tare da dannowar motoci cikin kantamemiyar harabar gidan,gabanta ya fadi sai tayi hanzarin kiran sunan Allah sannan ya lalubi mayafinta ta yane kanta ta fito,ita ta kama hannun raihanan har cikin part dinta,part ne da aka masa qawa ta ban mamaki,bedroom uku ya mallaka da falo biyu,daddy dalhatu ya mata kayan gado daya ita da rumana,dangin abbanta suka sake yi musu tare da rumanan dai,sai kuma wanda dangin mamarta suka yi mata,falo daya kuwa abba yusuf ne ya shirya musu ita da rumanan,yayin da rayyan ya shiryawa rumanan daya itana ita kadai.

Hayaniya ta 'yan kawo amarya ta lafa,ya rage saura manya kawai wadanda dangin raihana ne rumanan da kuma dangin ummu,su suka hadasu su biyun suka musu nasiha sosai mai ratsa jiki,baya ga dogon yabo da fatan alkhairi da rumanan ta sha na namijin qoqarin da tayi wajen baiwa 'yar uwarta farinciki
"In sha Allah yadda aka sanmu tun usuli haka za'a ci gaba da ganinmu,da ikon Allah babu shaidan da zaiyi tasiri tsakaninmu" cewar rumana,raihana kam kasa magana tayi sabida wani abu dake tokare da wuyanta,tana jin ta gama quntata rayuwat sisinta,ba zata iya furta komai ba baya ga kuka data ci gaba da yi sosai,irin kukan dake tsuma zuciya wanda ya haddasa tausayinta cikin zuciyar duk wanda ke gun,saboda kowa yasan me take kokawar,amma suna ganin hakan shine gata kuma babban rufib asiri gareta,din babu wanda zaya so ta sake aure makamancin wanda tayi a baya,auren da babu abinda aka tsinta cikinsa face tarin da na sani.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*

______________________
*Daga abu hurairah r.a yace:abul qasim S A W yace"da ace wani mitum zai leqoka(ya leqa maka gida)ba tare da izininka ba,sai ka jefe shi da tsakuwa,sai ka tsiyayar da idonsa,to baka da wani laifi"* bukhari da muslim ne suka rawaito

*a wani lafazin kuma na imam ahmad da nisa'i sukace babu biyan diyya kuma babu qisasi*
_______________________

*Babi na arba'in da daya*
Chapter 56 · 0% Book details