Sashe 4
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tuni jikinta yayi laqwas ta fara tara hawaye don tasan tsiyar da ta aikata,cikin shafi shida babu wanda tayi shafi guda full,wani shafi layi takwas tayi,wani biyar wani hudu kai wani ma layi biyu,dukan rubutun idan aka hada bai wuce shafuka biyu ba.
Kallonta kawai yayi hawayen da ta tara ya fara gangarowa,tasan halinsa sarai kan karatu bashi da wasa,tsawar da ya daka mata sai da ta raihana curewa guri guda kasancewarta mai tsoro da rashin son hayaniya,ummu kuwa dagowa tayi don ta tabbatar wani cikinsu ya aikata ba daidai ba,yayin da uwar gayyar ta qarasa barkewa da kukan
"U r very stupid!,tun ban kai ga bugunki ba ma kin soma min kuka,rumana don kinga ina miki wasa shine kike nema ki raina ni?" Kai ta shiga girgizawa yayin da ummu ta shiga tambayar ba'asin abinda ya faru.
Littafin kawai ya nuna mata ya koma ya zauna ya tsatstsare rumanan da ido,girgiza kai ummu tayi tana boye murmushin fuskarta,don ita dai ba zata shiga tsakanin rayyan da rumana ba,don babu mai shiga fadansu,ko ka shiga ma qarshe kai zasu bari da cizon yatsa.
"Yanzu dai babban yaya ayi haquri,a qara mata lokaci ta gama yanzu ta baka,ke kuma rumana ki maida kai ki gama,idan ba haka ba ko zai hukuntaki bazan tare miki ba"girgiza kai tayi ta amshi littafin ta duqufa yin aiki baji ba gani,saidai har yanzu qwalla take,hakanan lokaci lokaci takan dago ta dubi fuskar rayyan din da ya hakimce a gabanta fuska a dinke ya bude littafinsa yana ci gaba da dubawa,saidai lokaci lokaci suna hada ido ya manna mata harara,abinda ke sake sanyata kukan kenan,don ta tsani ganin fuskar yaya rayyan din a haka.
Daga gefe guda shi dinma baijin dadin kukan da mutuniyar tasa take,amma dole yayi mata hakan,wasanta yayi yawa,har ya zarce son wasa rawa da waqa ya koma kan wasa da karatu.
Cikin lokaci qanqani sai gashi har ta kammala,ko dama can rumanan ba wai daqiqiya bace,kawai irin yaran nan ne da wasa ya musu yawa,gata da son tsalle tsalle,ta matsa gabansa ta miqa masa littafin cikin raunin murya tana fadin" yaya na gama"hannu daya yasa ya amsa ya duba yaga yayi kyau sannan ya miqa mata yana duban raihana
"Iya su kenan assigment dinku na yau?" Tana kwashe pencil dinta da sharpner ta amsa da "eh"
Sallamar abba ce ta ja hankalinsu bakin qofar falon,dukkansu suka miqe suna masa sannu da zuwa.
Ido ya shiga rarrabawa ganin baiga rumana ta sheqo a guje yadda ta saba ba,can ya hangota a baya tana share hawaye,murmushi yayi,da gani ba tambaya ita da mutuminta rayyan ne,don babu wanda fushinsa ke sata kuka a gidan irin rayyan,raihana ba gwanar fada bace baka jin kansu,ummu kuwa duka 'yan lelenta ne basa laifi bata musu laifi.
Shi dinma bai shiga fadan ba don kada gobe da safe a wareshi,ice cream kawai kawai ya bata mutuminta da yake siyo mata ya miqawa raihana chaculets don tafi sonsu ita kuma,sai dan jan kunnen rayyan din da yayi.
Bangarensa suka wuce shi da ummun yaje yayi wanka kana ya pdawo dauke da wani file ya dorashi saman kujera suka wuce cin abincin dare.
Ta kasa sakewa taci abincin yadda ya kamata,sai kallon rayyan din take taga ko ya huce?,saidai har yau fuskarsa a daure take,duk da shima baijin dadi amma baiso su qyaleta ta sangarce da qin karatu da haka suka kammala cin abincin wanda sai da ummu tayi da gaske rumanan taci abincin sosai.
Abba ne ya tsaida rayyan ganin yana niyyar wucewa sashensa,ya dauki file din yana fitowa da wasu takardu kana yace
"Allah yayi fatima tafiyar rayyan dai ta tabbata,kawu muhammadou dai ya dagewa tafiyarnan,yanzu haka passport dinsa da komai ya kammala,har makarantar da zai fara zuwa ma sun bashi admission".
Hakanan rayyan din ya ji zuciyarsa na bugawa,sam bayason barin gidansu iyayensa qannensa qasarsa ma duka,baya jin shaquwar dake tsakaninsu zata barshi koda ya tafin ma ya iya zama a can din,maganar ummu ce ta katse zaren tunanin da ya fara" Allah sarki kawu muhammadou sarkin zumunci,baya gajiya ya riqe uba yanzu zai riqe dansa,Allah ya saka masa da alheri"
"Ameen ameen......rayyan banji kace komai ba" da sauri ya qaqalo murmushi,saboda ko kadan baya son yayi abinda zai saba da ra'ayin mahaifan nasa
"Abba Allah ya sakawa kawu da alkhairi"
"Ameen,wadannan.....foarm ne na banki nakeso ka cike nan da gobe,account nakeso na bude maka,bazan bar kawu yayita dawainiya shi kadai ba bayan tawa da yasha,inaso lokaci lokaci na dinga tura maka wani abun ka dinga amfani da shi" hannu biyu yasa ya amsa yana godiya
"Amma alhj shekara sha bakwai zasu bude masa account?" Inji ummu,dariya abba yayi
"To ai ko su ba zasu ce rayyan shekararsa sha bakwai ba,wannan sarqin tsawon"
Dariya sukayi ita da abban.
yana shirin zai miqe abban ya kuma dakatar da shi
"Ka soma shiri tun yanzu,saboda ina zaton next week zaka wuce nijer,zaka musu sati uku a can,a can kawun zai taddaka daga can zaku wuce,saboda haka passport dinka na nijer ne yana hannun kawu,amma na sa an maka na negeria ma tunda itama qasarka ce ta haihuwa" godiya ya sake yiwa abban.
"Abba.....ina yaya rayyan din zai tafi ya barmu?" Rumana ta fada muryarta na rawa,sai lokacin abban ya tuna cakwakiyar da aka tafka da akayi maganar gaban rumana,cikin sigar lallashi yace da ita"london ne rumana,makaranta zaici gaba da zuwa"
Cikin shirin barkewa da kuka tace"abba me yasa bazai ci gaba anan ba?".
Rayyan yasan sarai idan aka ja maganar yanzu zata barke musu da kuka don haka yayi dabara ta hanyar sakin fuskarsa
"Ba dadewa zan ba,amma indai kikai kuka to idan na tafi bazan dawo ba" kafada ta maqale tana fadin"um,um"
"Ok to maza aje akwanta gobe da school ko?"
"Ya rayyan,biskit" sai lokacin ya tuna da biskit din da yake bata,dubansu yayi yace su biyoshi su karba,
"Ke raihana ba zaki ce komai ba?" Inji abba yana dubanta sanda suka miqe zasu bi rayyan,murmushi kawai tayi tace"abba ai kai kace karatu yana da kyau,yana kuma da dadi,kuma naga yaya makaranta zaije ko?"
"Hakane raihana,Allah yayi muku albarka"
"Ameen abba" ta fada tana bin bayansu rumana da tuni suka fice, yayi"raihana kenan,Allah ya jiqan mahaifinki,dabi'unta su suke tunamin bukar da fanna,Allah ya gafarta masa"
"Ameen ya Allah,ameen abba"
"Ita kau sarkin rigima rumana bansan ya zaku kaya da ita ba,na fuskanci ba mai iya controlling dinta sai rayyan"murmushi ummu itama ta saki" wallahi kuwa abba,ai na rasa wannan shaquwa irin tasu",murmushi abban yayi yana saqa wani abu cikin ranshi"wannan da sun gama mallakar hankulansu sai ace ko son juna suke"ummu ta kama baki"ni zan gaya maka haka abba ni da nake wuni da su,yadda kasan hassan da usaina"
"To Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi cikin rayuwarmu baki daya"
"Ameen abba"
************
Cikin kwanakin rayyan ya shiga hada kayanshi,duk da cewa duk abinda yake jikinsa a sanyaye yake,wasu lokutan idan rumana taso rigimar tata sai tasa kukan bazai tafi ya barta ba,hakanan shima sai yaji tafiyar bai sonta,baya son yin nisa da su,amma babu yadda ya iya kam tunda bai iya musu ko canzawa iyayenshi magana ba.
Yadda abba yaso ya tafi nijer a sati na gaba hakan bai yiwu ba,don rigima sosai rumana keyi kan tafiyar,kukan yau daban na gobe daban,sai duka gidan ya zama wani irin shiru,saboda abinda ya taba rumana ya taba raihana hakanan ya taba uban tafiyar rayyan,idan rumana bata ci ba raihana ma ba zata ci ba saboda girman shaquwar dake tsakaninsu,to shima rayyan din ba ci zaiyi ba.
Tilas abba ya qara sati biyu,zuwa lokacin su raihana sun gama jarabawa a makarantar islamiyya da boko ma baki daya,sai su tarkata baki daya su tafi nijer din duka su yiwa rayyan din rakiya
***********
_Bayan mako biyu_
Yau ya kama kama gobe ne tafiyar tasu,dukkaninsu rumanan da raihanan babu wadda bata murnar tafiya nijer din,don wannan shine zuwansu na farko
Saloon sukaje da qunshi raihana rumana da ummu,su aka fara yiwa don haka suka qosa a tafi gida,kada ma rumana taji labari,don gani take kamar idan ta koma gidan zata tadda rayyan din ya tafi,don haka ummu ta sa auwal ya maidasu gida daga baya ya dawo ya dauketa.
Sam sun auwal ya mance basu karbi muqullin parlourn daga hannun ummu ba, wanda shi zai sadaka da sassan gidan baki daya,sa'a daya sukaci yaga gefan rayyan din a bude don haka suka nufi can zasu jira ummun.
Kace kace suka tadda shi cikin aikin hada sauran kayansa wadanda zai bari a gida yana killacesu,sauran wadanda zai tafi da su kuma yana hadasu guri daya
Da gudunta rumana ta qarasa gurinsa wanda hakan ya hanashi jin sallamar raihana,dan kwalinta ta zame tana nuna masa gyaran gashinta"wow,amma fa kinyi kyau angel"dan zumburo baki rumanan tayi"amma yaya ummu tace na raihana yafi kyau.....don Allah yaya a kalli nata...ai nawa yafi kyau ko?"ta fada cikin sigar tambaya,dariya ya saki yace"to ai ni ban ga natan ba duk da nasan na my angel yafi kyau"da sauri ta qarasa gefan kujera inda raihanan ke zaune ta ruqo hannunta,wai a dole sai rayyan din ya gani ya kuma zabi natan,waiwayawa yayi yana kallonsu cikin dariyar rigima irin ta rumana,zame hannunta raihana tayi tana girgiza mata kai alamun ba zata ba,ganin haka ya sanya rumana ta zame mayafin kan raihanan tana dariya,cikin daga murya tace"yaya rayyan ka gani....yi sauri ka kalla".
Ya dubi abinda take nuna masa din,duk da gashin raihana baikai na rumana tsaho ba amma yafi nata cika,irin cukus dinnan ne kuma yana tafe da tsahonsa,baqi ne sidik fiye da na rumana mai yauqi rashin cika da ga kuma tsaho,itama natan yayi kyau kamar na black american,an dameshi da ribbom yanata sheqi,murmushi yayi yayin da ta saki kan raihanan bayan ta tabbatar ya gani din ta nufoshi"ba nawa yafi yin kyau ba yaya"
"Sosaima kuwa" ya bata amsa yana murmushi,itakam raihana na gefe sai ta fidda glass dinta ta saka tana bin tulin takardun da littatafan rayyan dake gefanta da kallo.