Sashe 6
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike da mamaki suke tattauna maganar tsakanin alhj dalhatu da alhj yusuf"ina zaton akwai wani al'amari mai girma tsakanin yaran nan alhaji"
"Ko ba rayyan da rumana ba?" Cewar hajiya rahinatu kakar rayyan din
"Eh sufa hajiya" inji abba yusuf"murmushi alhj dalhatu yayi kana yace"ni kam dama na dade ina suranta wannan tunani cikin raina,ashe bani daya nake ganin hakan ba"murmushi itama hajiya rahinatu ta saki sannan tace"mu din ma gashi da muke nesa da ku yau mun gani,ja'irai harda alqawarin soyayya da aure kamar wasu manyan matasa"dariya hajiyan ta bawa alhj dalhatu da alhj yusuf din baki daya
"Ai hajiya ina zaton wannan alqawari kuwa sai mun tabbatar da shi da izinin Allah,tunda juma'ar da zatayi kyau ai tun daga laraba ake ganeta,da alamu akwai abinda Allah ya dasa cikin zukatansu,qanqantar shekaru yasa basu ganewa mu din ma haka,sai Allah ya bar abun ta fuskar shaquwa,ko ya kake gani dalhatu?"
"Alhamdulillah,ai bani da ta cewa yusuf,da kai da kaya ai duk mallakar wuya ne,ni kaina kana da iko da ni balle rayyan ko rumana,Allah ubangiji ya tabbatar mana da alherinsa,ko ba haka ba hajiya" ita din ma cikin burgewar abota irin tasu take gyada kai cike da gamsuwa"qwarai kuwa,fatanmu idan da alkhairi a al'amarin Allah ya sake hade kansu sosai"
"Ameen hajiya,ina zaton kafin rayyan ya dawo hankali ya gama gamesu,don a yadda kawu ya nunan koda rayyan ya kammala karatun yana da ra'ayin riqeshi zuwa lokacin da zai mallaki abun hannunsa"
"Eh nima haka mukayi maganar da shi,Allah ya zuba masa qaunar rayyan duka cikin jikokin gidan nan,ko da yake dai bashi kadai ba,kusan duka cikin masarautar babu yaron da yayi irin farin jininsa"cewar hajiya rahinatu
" ai hajiya rayyan yarone na gari,dole ka soshi idan ka zauna da shi ko dan qanqanin lokaci ne"cewar alhj dalhatu,daganan suka zarce da zancan rayyan din har zuwa wani lokaci suka kawo gida
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
[7/23, 8:38 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*watpadd:huguma*
_______________________
*An karbo daga abu hurairah R.A yace:Manzan Allah S.A.W yace"mala'iku sunayin salati akan dayanku,matuqar yana zaune a inda yayi sallah bai tashi ba kuma baiyi magana ba,suna cewa:ya Allah ka gafarta masa,ya Allah kaji qansa kayi masa rahama"*
_imam bukhari ne ya rawaito_
________________________
*babi na bakwai*
Kwana uku suka qara a nijer din don qarasa ziyarce ziyarcensu da basu kammala ba suka dawo qasata nijeria gida kanon dabon.
To duk yadda suka tsammaci kewar rayyan abun ya wuce haka,ba rumana ba ba raihana ba,hatta ummu da abba sun shiga sawun kewar rayyan din,sai a lokacin suka qara banbance shaquwar dake tsakanin ahalin gidan.
Wasa wasa sai da rumana tayi sati kwance tana taba zazzabin rashin rayyan din,yayin da raihana ke mara mata baya wajen tayata kwanciya da rashin walwala,a haka ummu ta dinga qoqarin daidaita lamuran gidan ta yadda zasu dawo suci gaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba a baya.
Ba'a samu sauqin lamarin ba sai da rayyan din yayo waya,rumanan taji muryarsa ya kuma sake jadda da mata cewa lallai ta daina damuwa sannan lamuran suka fara daidaita.
Kusan kullum rayyan din yakan kira sau biyu sau uku a rana,safe rana dare,suna gaisawa da kowa,saidai yakan bata lokaci mai yawa tare da rumanan fiye da kowa cikin gidan,sannu a hankali itama sai ta fara koyon waya,abinda da bai dameta ba,dabi'a ce ta raihana,zakayi mamakin yadda ta iya sarrafa waya,ko bai kira ba zata faki idon ummu ta dauki wayar ta kirashi su sha hira yana biyewa shirmenta,saidai ummu ta laluba account din wayarta ta taradda 0.00,indai taga haka to tasan ranar mutanen england sun sha hira kenan.
***********
Sannu a hankali kwanaki suka dinga jujjuyawa suna haifar da nisan al'amura da kuma maida abu ya zama tarihi.
Hakance take kasancewa ga kowanne bawa,tamkar dai iyalan gidan abba yusuf,wanda zuwa yanzu su rumana sun fara sabawa da rashin ganin ya rayyan din nasu,duk da koda yaushe suna tare a waya,indai kaji shiru to babu shakka karatu ne ya sha masa kai.
************
_*Bayan shekara takwas*_
Bakayi kuskure ba ta wani fannin idan ka kirasu da *'yan biyu* ko *tagwaye*,saidai ta sun sha banban ta wasu fuskoki da dama,zaifi kyau a sauqaqe ka kirasu da *AMINAN JUNA*
RAIHANA yarinya matashiya mai kimananin shekara goma sha tara babu watanni,yarinya ce mai sanyi tun daga kan maganganunta halayenta da life style dinta.
Launin fatarta zaka iya kiransa da ruwan qasa wato kalarnan da ake kira da chaculet colour mai kyau da bin jiki,irin launin fatar garinta na haihuwa wato maiduguri,tana da baiwar suma wadda hakan ya bayyana hatta a girarta wadda take a cike kamar yadda gashin idonta yake wanda koda ta saka *MEDICATED GLASS* baya boyuwa,cikar girarta ya sanya suka hade,har wani lokacin rumana kan matsanta mata tace ta bari ta gyara mata,bata da qiba kuma ba ramammiya bace,kamar yadda ba zaka ce da ita doguwa ko gajera ba,medium ce,a murje jikinta yake tana da diri wanda baya iya boyuwa,hancinta mai tsaho ke da tudu ba irin siririn nan ba.
Shigarta a koda yaushe ta doguwar riga ce,walau atamfa ko leshi,shadda ko material,mawuya cine ka sameta da riga da skert,duk da tana da su daidaiku wadanda rumana ke tilastawa a dinka mata,riga da wando kuwa saidai na pakistan.
Komai nata natural ne,bata fiya damuwa da qyale qyale ba,tafi maida hankalinta kan abu mai quality da nagarta,ma'abociyar karance karance da binciken sabbbin abubuwa,wadanda wasunsu sun shafi qasarta da al'ummarta,yayin da waasnsu sukan shafi rayuwar al'umma walau daidaiku ko a jimlace.
Murmushi kusan shine amsarta cikin magana,bata fiya surutu ko doguwar magana ba matuqar ba cikin gida bane cikin wadanda ta saba da su ko familynta ba,a yanzu haka tana shekarar ta ta farko a jami'ar bayero dake kano,inda take karantar law islamic law,
RUMANA matashiyar budurwa wadda shekarunta yake daya da na raihana,tazarar dake tsakaninsu bata wuce satittika ba,yarinya ce mai fara'a,faran faran da saurin sabo da jama'a,yawan surutu da rawar kai da son hira,ma'abociyar son yin sababbin qawaye da abokai,matashiya mai son yin rayuwa mai kyau da burgewa.
Rumana na da hasken fata,duk da cewa ba fara bace qal,amma kai tsaye zaka iya kiranta da farar mace,don ta dan debo launin fatarau ta fulani,tana da zagayayyar fuska mai dauke da dogon hanci,cikakken gashin gira da na ido har ma da sumar kai,idanunta ne basu cika girma kamar na raihana ba dake da manyan idanu,ta zarta raihana tsaho da kadan amma ba lallai la gane hakan ba,bata da qiba kamar yadda take na siririya ba,saidai duk da haka raihana ta fita cikowa.
Dinkunanta basa wuce riga da skert don ko kusa bata son daura zani,don har raihana ta fita daura zannuwa,saita riqe ne zata yiwa raihana kara a yimata doguwar riga ita din ma fitted gown,to anan zakaji kansu,don ita raihana ta tsani fitted gown a rayuwarta,tana son english wears don haka lokaci lokaci tana sanyasu,saidai ba masu fidda tsiraici bane.
Rumana akwai son kwalliya da qale qale,duk wani abun yayi na zamani mai aji ba gama gari ba zaka rasashi a gun rumana ba,haka duk arahar abu indai qyale qyalensa yayi mata to zata siya tayi amfani da shi.
Ma'abociyar ta'ammali da kafafen sadarwa na zamani ce,don zaka sami charting kala kala rumana nayi,kamar facebook,watsapp,snapchart,instagram,palmchart da dai sauransu,hakanan ta bangaren kallan fina finai ba baya bace,kama daga na gida nijeria kudu da arewa dama na qasashen qetare
Indai ka zauna tare da rumana dole ta sanyaka surutu ko bakayi niyya ba,dramer su kenan kullum da raihana,don sam bata yadda ta zama kurmar qarfi da yaji ba,hakan ne ya sanya take da tarin abokai da qawaye ciki da wajen makarantarsu.
Ita din ma b.u.k take zuwa saidai sun banbanta a coarse,ita rumana na karantar mass communication ne.
Sun hadu ta bangaren tarbiyya,tausayi jin qai da qaunar junansu kamar ciki daya suka fito,sai turaruruka da da wasu daga takalma gyalalluka da mayafai iri daya da suke amfani da su,walau a kamfani daya ko kuma masu kaloli iri guda,hakanan wani lokaci ra'ayoyinsu kanzo daya kan wani batu yayin da wani lokaci yakan saba.
************
Ta kusa a qalla mintina goma zaune gefan gadon tana zaman jiranta,yayin da ita kuma take ci gaba da makeup dinta kamar ma babu wanda ke zaman jiranta.
Zaro wayarta tayi ta shiga danne danne cikin zuciyarta tana ayyana ta qara mata minti biyar taga gudun ruwanta,tana shafa jambaki ta mudubin rumana ke kallon raihanan wadda kanta ke duqe bisa screen din wayarta,dariya ta kusa kufce mata,tasan sarai ta gaji da zaman jiran amma ba zata iya bude baki ta mata masifa ba,sau tari hakan suke sai ranar data qureta.
Har ta cinye mintinan rumanan bata kammala ba,sai kawai ta ciro glass dinta tasa tissue ta qara gogeshi ta maidashi kan fuskarta,ta miqe tsaye bayan ta jefa wayarta cikin hand bag ta kulle,mayafinta ta dauka wanda ya dace da kayan jikinta tana yafawa ta dubi rumanan,kamar zata ce wani abu sai kuma ta nufi qofar ficewa a dakin.
Da sauri rumana tabi bayanta ta kamota,dariyar da take boyewa ta kufce mata
"Sorry my blood sis,ai kece wlh kinsan banason wannan kurmantakar taki,ki bude baki kice rumana kiyi sauri amma ba zaki iya ba,kin zauna kin tasani gaba"
"So kike na rufeki da duka?" Ta tambayeta hannayenta goye a qirjinta
"Nop" rumanan ta bata amsa tana komawa ciki don ciro kayan da zata sanya din
"Saif ne ya tsaidani wallahi,shi yasa bana son ya kirani idan ina da abunyi" ta fada tana zaro kayan,daga kai raihana tayi ta dubeta ta cikin glass dinta,sai ta dan bita da kallo,kamar ta tanka sai kuma ta fasa taja bakinta ta tsuke,tana tsaye rumanan ta gama shiryawa a gaggauce,don ko dankwalinta bata samu ta daura ba a hannu ta riqeshi suka fito daga dakin.
A zaune a falo suka tadda ummu suka yi mata sallama,ta basu kayan da zasu kaiwa hajiya babba surukarta,wanda kilishi ne da zuma sai dambun naman kaza,don unguwar qoqi gidan kakannin rumanan suka nufa.