← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 66

Sashe 5

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A rayuwarta yarinyace mai son sanin abinda bata san da shi ba ta fannin ilimi kullum,shi yasa baka rabata da karance karancen litattafan tatsuniyoyi na hausa da turanci,wani lokaci ma rayyan din ke bata wasu nashi na primary dinsa wadanda yasan ya gama da su,hakanan mayyar labarai ce,har abba kan mata tsiya yawancin lokuta idan ta zauna kallon labarai tare da shi,yaga ta nutsu,yakan ce sai kace tsohuwa raihana,dariya kawai takeyi,wani abun ta fahimta wanda turancinta ko larabcinta bai kai ba abban ya fassara mata.

Novel din sa ta hango love story,a hankali ta saci kallon rayyan din,hankalinsa na kan surutun rumana da kuma trolly dinsa da yake ta qoqarin zugewa.

Sake mai da kallonta tayi ga littafin ta gefan ido,sau biyu tana dauka sai ta fara karantawa rayyan din ya ganta,bata mantawa har yanzu idan ta taba kunnenta tana iya tuno jan kunnen da ya mata na kada ya qara ganin littafin a gurinta,duk da kalmomi da sentence din ciki kadai take fahimta bawai labarin ba amma tana kwadayin karantawar,don tana qaruwa da sabbin kalmomi.

A karo na biyu ta sake daga kanta sai taci sa'a ya janye trolly din zai kaita cikin bedroom yana fadin kada rumana ta masa barna cikin kaya yana zuwa,ta amsa da to,amma duk da haka bata fasa daukar wannan ta kalla ta ajjiye ta dauki waccan ta kalla ta ajjiye ba,wanda majority hotunan rayyan dinne na sauka da na candy,sai kuma wadansu daga ciki da ya dauka a nijer da sauran wurare cikin kano.

Hannu ta saka ta zaqulo littafin,cikin zumudi ta soma budewa,bata manta shafin data tsaya ba don haka ta bude ta dora,tun tana daga kai tana kallon bakin qofa ko rayyan zai fito har ta manta ta saki jiki sosai

A hankali taji an zare littafin daga hannunta,kanta ta daga tabi shi da kallo,ya rufe littafin yana ci gaba da zuba masa idanuwansa dake bata tsoro,take kuwa ta tsore idanunta suka fara tara qwalla
"Wato baki ji abinda na gaya miki ba kenan ko?,kema kin fara koyon taurin kai da rashin jin magana kenan,uban me kike karantawa cikin wannan littafin!" Ya tambayeta cikin tsawa,sake tsoratata yayi,take ta gigice,maimakon amsa sai hawaye da ya wanke idon nata har ma da glass din fuskarta,hakan ya sabbaba mata gani dishi dishi,amma ta kasa fidda glasa din.

"Ok,bari jikinki ya gaya miki zaki gayan abinda kike karantawa a ciki" ya fada yana janyo earpiece dinsa dake gefe cikin son tsoratarwa,ai ya tsorata gwanar tsoro,da sauri ta zamo qasan kujerar"kayi haquri ya rayyan,wallahi bazan sake ba"ta fada cikin muryar kuka,take zuciyarsa ta karye don bazai iya tuna sau nawa ya ganta tana kuka ba,kasancewarta ba mai rigima ko rashin ji ba,sai ya bi littafin dake hannun nasa da kallo,ya rasa me yasa take maitar littafin,wannan ne karo na uku da ya amshe littafin a gurinta,ninkeshi yayi kawai ya juya da shi a hannunsa ya sanya cikin qaramar akwatinsa.

Da sauri rumana dake tsaye a bayansu wadda itama tayi shabe shabe da hawayen,glass din fuskar tata ta cire ta goge mata tana fadin"kiyi shiru raihana don Allah"murmushi ta yi mata ta karbi glass din ta maida fuskarta ta janye qafafunta ta lafe jikin kujerar,itama rumanan kusa da itan ta zauna.

A haka rayyan ya tadda su,duk sai yaji shima ba dadi,sai ya saki fuskarsa a hankali ya qaraso inda suke,zama yayi a gabansu ya lanqwashe qafafunsa yana dubansu

*mrs muhammad ce*

📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
[7/23, 8:38 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________

*Daga Abu Hurairah R.A yace:Manzan Allah S A W yace"dukkan al'ummata zasu shiga aljanna,saidai wanda yaqi"sai sahabbai sukace:ya manzan Allah,waye zaiqi?,sai annabi yace"wanda ya bini zai shiga aljanna,wanda ya saba min kuwa wannan shi yaqi"*

_imam bukhari ne ya rawaito_

_________________________

*babi na shida*

"Hala fushi ake da yaya rayyan kenan,shine aka hade masa kai"shiru dukka sukayi,murmushi ya sake yi ya kama hannayensu guda dai dai ya riqe yace"kun sani bana son ku dinga wasa da karatunku,ilimi abune mai muhimmanci,shine yake banbanta tsakanin mutum da dabba,amma ayimin afuwa ko?,kada yaya rayyan ya tafi ana fushi da shi,an yimin afuwan?" Ya fadi yana dubansu,raihana ta fara murmushi ta gyada kai sannan rumanan itama tayi"good"yace kana ya dora"inason inga kun dage sosai kun maida hankali ga karatunku,kun fahimceni"suka gyada kai a tare"ok,yanzu ku yimin alqawarin zakuyi karatu sosai babu wasa koda yaya rayyan baya nan"
"Munyi alqawari ya rayyan" inji raihana
"Eh yaya zamuyi" inji rumana
"Yauwa 'yan qanne na,ni kuma idan na tashi dawowa kowacce zan siya mata tsaraba mai yawa indai naga kun dage din".

Zo kaga murna gurin rumana har da tsalle,hira ya dinga jansu da ita suna tayashi qananun ayyukan da zasu iya,a haka suka ware

_washegari_

cikin motar abba sienna suka shirya yin tafiyar tare da auwal,idan abba ya gaji da tuqi auwal din ya karbeshi,anyi haka ne saboda raihana da rumana wadanda basu da passport,duk da cewa abba yayi alqawarin yi musu saboda gaba.

Raihana rumana da rayyan na can seat din bayan,rayyan ya biyewa surutu da rawar kan rumanan sosai,saboda yana jin kamar suna sallama ne,cikin jikinsa kewarta kawai da wani yanayi maras dadi ke ratsashi,yasan ba zaya samu tamkar qannen nasa ba

Tafiya ce miqaqqiya,tun suna hira su ukun har raihana tayi bacci ta barsu,a hankali itama rumanan baccin ya dauketa suka bar rayyan din shi kadai

*_jamhuriyya nijer_*

Ba qaramin murna da zuwan iyalan yusoufu cikin masarautar akayi ba,don sun dan jima rabon da suzo dukkansu ,kasancewarsa mutum mai taimakon da son jama'ar masarautar tasu hakan ke qara qaunarsa cikin zuciyar iyaye da 'yan uwansa

Sati guda sukayi suna yawo cikin garin diffa da qauyukanta,gidajen 'yan uwa da kakanni,sosai suka sake suka manta ma da tafiyar yayan nasu.

Kwanansu goma kawu muhammadou ya iso,saboda haka yace nan da kwana uku zasu wuce

***********

Qarfe goma sha daya da kwata na safiyar ranar a airphort din tayi musu,motoci biyu sukayi don rakiyar rayyan din,baya ga motar dogarai daya da ta barorin hajiya rahinatu itama guda daya

Jiki a sanyaye suke tafiya yana riqe da hannun rumana da raihana,abbanshi da ummu na biye da su,sai kakarshi rahina da kawunsa alhassan da d'an kawun nasa hamza wanda kusan sa'anni suke,hakanan alhj dalhatu ma ba'a barshi a baya ba,har nijer din yayo tattaki a daren jiya ya biyo jirgi don ganin tafiyar rayyan din,sai da suka qaraso inda babu dama su shiga sannan ya saki hannayensu.

Juyowa yayi yana dubansu,badon dakiya da yayi ba babu abinda zai hanashi fitar da qwalla,gaban ummun ya fara zuwa ta masa addu'a sosai sannan ya wuce gun alhj dalhatu kana ya wuce gun abbansa ya dire gaban kakarsa,duka addu'a ce da nasihohi da suka masa tare da fatan alkhairi.

Ya tako a hankali ya qaraso gaban qannen nasa,kuka sosai rumana take yayin da raihana ke sharar qwalla,tabbas sabo turken wawa ne,hannayensu ya kama sannan yace
"Ba kuka zaku yimin ba addu'a zaku yiwa yayanku,ya kammala karatunsa da sauri cikin nasara ya dawo gurinku kunji ko?" Sautin kukan rumana ya kasa boyuwa sai da ya fito fili,kama hannayenta yayi yana fadin
"Rumana......"katseshi tayi ya hanyar cewa
" yaya,mu kadai kenan zaka bari,mun koma daga ni sai raihana a gida?"
"Yaya rayyan,shikenan yanzu ba wanda zai dinga yi mana karatu ko labari?" Inji raihana.

Duk yadda yaso ya daure sai da yayi qasa da kansa yana jin idanunsa na tara qwalla amma yayi qoqarin maidasu
"Ku yiwa ya rayyan addu'a kamar yadda nace kunji bana so......" Kafadarsa yaji an dafa daidai lokacin da sanarwar neman masu tafiyar ta karade ilahirin filin jirgin,alhj dalhatu ne da suke kira daddy,gefansa kuma kawu muhammadou ne
"Rayyan,wuce ka tafi kada su bata maka lokaci,Allah ya bada sa'a yasa anje a sa'a" tilas ya miqe din kana ya saki hannayensu ya juya.

Gefan rigarsa yaji an riqe,ya waiwayo a hankali yana dubanta,rumana ce fuskarta jiqe da hawaye"yaya rayyan"
"Na'am" ya amsa mata da sauri
"Naji ance idan mutum sukayi aure nasa rabuwa da matarsa?" kusan sai da ta bawa kowa dariya a gun da mamaki,da sauri rayyan din yana murmushi ya gyada mata kai"eh haka ne"
"To me yasa ba zaka auremu ba ka tafi da mu kawai" dariya ta sake basu baki daya ciki kuwa har da raihana,tabbas akwai quruciya mai yawa tattare da rumanan,rashin sanin ma meye auren da muhimmancinsa baki daya ya bayyana tattare da ita.

Saidai lokaci guda baki dayansu hankalinsu ya koma kansi rayyan din lokacin da sukaji yana bata amsa"saidai na aureki ke kadai?,kina so?"murmushi ta saki cike da quruciya tana gyada kai"eh ya rayyan ina sonka"
"Kina sona?"
"Eh"
"Nima ina sonki,zan aureki amma kinsan yaushe?"da sauri ta shiga girgiza kai tana kallonsa"na farko sai kin daina kuka yanzu kita yimin addu'a har na dawo,idan na gama karatu na dawo,na tadda rumana bata wasa da karatu,ta dagewa karatu,ta daina wasa kinga shikenan",hakanan yaji maganar na fita daga can cikin zuciyarsa tamkar a ire iren litattafan da yake karantawa,ya samu kansa da tsare rumanan da ido don yaji me zata ce,dan jim tayi don ta fuskanci baza'a iya auren a yanzu kuma a tafi tare ba,kamar tace a'a sai kuma ta fasa,cikin murmushi tace" na yarda ya rayyan"
"Ok,na faara gani tun yanzu" da sauri ta fara goge hawayen fuskarta tana fadin"a dawo lafiya ya rayyan"kai ya girgiza sannan ya miqe,bai iya juyowa ya sake dubansu ba gudun kada zuciyarsa ta karaya,kawu muhammadou ya kama hannunsa sukayi gaba.

Tun suna hangosu har suka bace musu,yayin da rumana tayi saurin cusa kanta a kafadar raihana tanason boye kukanta wai don kada ta karyawa yaya rayyan din alqawari,da qyar ummu ta lallashesu kana ta kamasu suka nufi gun motocinsu don komawa gida
Chapter 5 · 0% Book details