← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 66

Sashe 28

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai data nemo shi ta daura sannan ta gaidashi,ya wani amsa ba tare da ya maida hankalinsa gun amsawar ba,ficewa tayi ta daura alwala ta dawo ta dauki jakarta ta koma dakin hajiya babba,a can ta tadda kausar mutuniyar rumana,suka gaisa cikin sabo da juna sannan tace
"Dazun mutuniyar ke mini albishir daurin aurenta next week da ya rayyan"murmushi raihana tayi kamar yadda al'adarta
" eh wlh"
"Wuuu,Allah ya kaimu ya dawo lafiya,dole mu bargaje biki na kece raini wlh" ta fada tana jijjiga hannu irin na wanda zance ya yiwa dadi
"Hmmm,ai aikinku kenan,dama idan bakuyi ba ai ba rumana da kausar bane wasu ne" murmushin raihana ta kuma kawai ta tada salla.

Powder ta sake shafawa bayan ta idar suna hira da kausar lokaci lokaci har biyar tayi,ta yafa mayafinta ta dauki jakarta bayan ta maida glass dinta ta yiwa hajiya qarama sallama.

Daga bakin qofa ta toge tana yiwa hajiya babba sallama zata tafi
"A'ah,shigo mana ina zuwa" inji hajiya babban ta fada tana miqewa,bakin hannun kujerar qofar dakin ta zauna kanta na kallon qasa,ya daga idonsa a hankali yana kallonta tare da kallon yanayin shigarta,komai tayi kyau yake mata,hakanan komai tayi yana qara nuna sanyin ta da sanyin halinta,babu shakka bai ganin aibunsa ko daya kan soyayyarta da ya shiga,bama shiba duk wani namiji mai lafiya da hankali tabbas dole raihana ta dauki hankalinsa,bawai don kyau wayewa ko wani qyale qyale ba,a'a sam,nagartarta kadai ta isheka.

"Ungo wannan raihanatu" inji hajiya tana miqa mata leda,tasan halin hajiyan ba'a maida mata kyauta don haka ta karba hannu biyu tana mata godiya sannan ta miqe a hankali ta fice.

Har ta fara gajiya da tsaiwar saboda qarancin wucewar motoci a titin,daidai lokacin da wata farar matrix tayi parking a gabanta motar rayyan ta fito daga layin,baya ta danja kadan ganin ana sauke glass din motar,magidanci ne wanda a qalla zaya yi shekaru hamsin,sanye da shadda 'yar ciki da babbar riga
"Sannu 'yammata" ya fada yana washe baki,ta kalleshi sannan ta dauke kanta gefe guda a hankali ba tare da ta furta kamai ba,wani takaici ya kamata.

Har ya wuce yanajin zai iya daurewa zuciyarsa sai kuma ya gaza hakan,wani zugi ta dinga yi masa,yayi ribas ya dawo da baya da gudu wanda saura qiris ya bugawa daya motar,a gaggauce ya fito hannunsa riqe da muqullin motar yana karkadashi cike da jin masifa,ya zagaya inda raihana ke tsaye,sai da ya tsaya ya qarewa mutumin kallo sannan ya dubeta
"Wuce muje" ya fada yana duban qwayar idonta,ba tare da ya tsaya saurerenta ba qarasa cikin qasaita ya isa bakin window din motar mutumin,hannayensa duka biyun ya sanya ya dafe window sannan ya duqa saitin fuskarsa din yana dubansa
"Ya kamara kabar gurin nan haka,matar aure kake magana da ita", cikin kidimewa da ganin yadda rayyan din ya dinke girar sama da qasa kamar wani mayunwacin zaki mutumin yace
" af,ai ban sani ba,yi haquri don Allah"ya fada yana tada motar yana tsaye rayyan na kallonsa har ya bace a titin sannan ya juyo inda raihana ke tsaye.

Hannunsa kawai taji cikin nata ya riqe gam yayi gaba tilas ta biyo bayansa tamkar wata doluwa,ya bude gaban motar ya sanyata sannan ya koma mazauninsa ya shiga ya tada motar,tuqi yake a hankali kamar motar bata da lafiya ko shi matuqin,a hankali ya samu gefan titi bayan ya hau titin da bai da cikowar mutane ya faka motar,sai ta daga kai ta kalleshi ga zatonta ko motar ce ta samu matsala,idanunta ta dauke ganin yadda ya juyo baki daya inda take zaune bayan ya cire belt din da ya daura.

Kallonta kawai yake ba tare da ya furta komai ba,kusan minti biyar yana a haka,a hankali ta tsinci kyakkyawan hannunsa mai dauke da zara zaran yatsu saman nata hannun,sai ta dubeshi sannan ta janye hannun nata tana boyeshi cikin mayafinta sakamakon wani shock data ji
"Raihana...." Ya kirata tamkar mai yin rada,wani yarrrr taji cikin jikinta mai hade da wani sanyi da taji ya tsirga tsakiyar zuciyarta
"Kinga asarar da kike son janyo mana ko?,raihana kinqi bani hadin kai da tuni na tabbatar cewa ke da rumana ne ke shirin zama iyali na,me yasa raihana bayan nasan kina sona?,me yasa?"
"SADAUKARWA yaya rayyan,na gaya maka wannan batun yanzu ba,ka taba ganin inda wuta da ruwa suka hadu guri daya?,bazai yiwu ba don haka don Allah don Allah ka barni yaya rayyan ka barni,rumana ta isheka" Tayi masa maganar tana dubansa.

Kansa ya dinga kadawa yana murmushi,bai taba ganin inda mutum ke qin kansa ba sai a gun raihana,hakan na sake dilmiyashi cikin tafkin qaunarta ne kawai,ya tabbatar da cewa ba kowacce mace ce zata samu irin damar data samu ba ta wofantar kadai saboda farincikin watanta,hakan na sake tabbatar masa da nagartarta tare da kwadayin ta zama mallakinsa.

Zare daya daga cikin zoben dake hannunshi yayi wanda ke dauke da tambarin double RR sarqafe da juna,bata ankara ba ya kama hannunta yana kallan dogayen yatsuntsa sannan ya zabi daya daga ciki ya zura mata zoben,bai saki hannun nata ba yace
"Rayyan zai qyaleki kamar yadda kika buqata,amma kada ki zargeshi da rashin neman yardarki duk lokacin da kika tsinci kanki a dakinsa,na riga da na nema,nabar takura raihana amma maganar ban barta ba,bazan kuma barta ba har muddin raina har sai ranar da numfashina ya bar jikin,ko kuma burina ya cika" yana gama fadin hakan ya sakar mata hannu ya gyara zamansa sannan ya tada motar.

A hankali ta maida idonta kan zoban,irin zoben rumana ne sak,banbancin kawai wannan na azurfa ne sabanin wancan da yake na qarfe,zuciyarta tayi rawa,ta yaya zata zauna da zoben a hannunta a gaban idanun rumanan?,ta cire tayi jifa da shi shine muradinta amma sai taji ta kasa hakan,sai taji kamar ana sake manna mata son zama da shi cikin jikinta,a hankali ta sauke hannun nata saman cinyarta tana kallonshi maimakon dazun data daga shi da niyyar fidda zoben.

Ko daya rumana bata bawa kanta wani sukuni ba,shirye shiryen tarbar ranar daurin aurenta kawai take tare da taimakon sisinta raihana,wadda tayi dukkan qoqarinta na danne komai dake cikin ranta tare da hana masa tasiri don farincikin 'yar uwarta qawarta aminiyarta kuma abokiyarta,duk da irin azabar da zuciyarta ke fuskanta,ta kan raya a ranta na wani dan lokaci ne,da zarar anyi komai an gama tanajin zuciyarta dole ta dauki haquri.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:24 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*manzan Allah S.A.W yace"sadaka tana kankare zunubbai,kamar yadda ruwa yake kashe wuta,sallah kuma haske ce"*
______________________

*Babi na ashirin da uku*

_fans gani na dawo,ina godiya ga dukkan jama'ar da suka kirani ko suka turon saqon cigiya ko sukayi cigiyata,na gode qwarai👏🏼_

_ga jama'ar kuma dakemin saqo ta account na watsapp dina suna qorafin naqi kulasu ko nayi blocking nasu, afwan,na sauya number ne saboda wadansu dalilai,ina kuma godiya,jazakumullah_

Duk da daurin aure kawai za'ayi hakan bai hana suyi shiryen shiryen da ba'a rasa ba,kamar sabbin dinkuna da gyaran jiki,komai tare sukeyi kuma iri daya,ko wani abun raihanan ta noqe rumanan bata yarda sai an mata hatta da dan gyaran jikin da akayi mata.

Saura kwana uku biyu daurin auren mutanen nijer suka iso,sun kusa mutum sha biyar maza da mata ciki harda kakar rayyan wato rahinatu wanda shine zuwanta na farko gidan dan nata,nan take yanayin gidan ya fara sauyawa aka shiga hidima da baqi,duk da raihana da rumanan ba kasafai suke samun zama a gidan ba,wani lokaci suna makaranta wani lokaci suna can wajen sabgoginsu.

**************

Ana ya gobe daurin auren suna dawowa daga qoqi ita da rumanan da kausar,sunje an yi musu lalle da kitso,yamma ne liqis don bazai wuce awa daya ayi kiran sallar magari ba ba,a bakin get din gidan dan adaidaita sahu ya ajjiyesu suka biyashi ya wuce.

Motar rayyan ce fake a qofar gidan daga gefe,daga bayanta kuma motar amir ce sai wata motar daban ta wani abokin rayyan din mujahid.

Angon na jingine jikin tashi motar yana amsa waya,sanye yake da qananun kaya,jeans brown da t.shirt fara qal mai gajeran hannu wadda ta fidda murdadden damtsensa da gargasar dake kwance kan qaurin hannunsa,a idonshi suka sauka,idanunsa fes kansu musamman raihanan da ta tafi dashi,saboda yadda gyaran jikin ya amshi chaculet colour din fatarta fiye ma da farar fatar rumana,sun hada ido amma sai ta dauke kai,wani abu ya dinga ji yana tsirga masa,sai yaga ta fita daban cikin su ukun,duk da kallo guda zaka yi mata matuqar kana fa zurfin fahinta da saurin ganiya ka gane jikinta a sanyaye yake,duk da ita din mai sanyi ce amma sanyin nata ya sake qaruwa fiye da yadda take ainihi.

Kai tsaye rumana ta kama hannun kausar wadda tafi kusa da ita tana mata radar ga angonta can,kausar ta qyalqyale da dariya
"Gwara dai ayi a gama kowa ya huta" dariyar itama rumanan tayi ta waiwaya ta dubi raihana dake tsaye a bayansu
"Sisi,gafa mutimin naki can har ya iso" murmushi tayi tare da yin far da fararen qwayar idonta wanda akan idon rayyan tayi,wani siririn murmushi ya saki irin na gefan baki ganin yadda farin yayi mata kyau matuqa,cewa tayi da rumanan
"Eh,tun muna qoqi jikina ya bani,kinsan abinka da zuciya guda"kama baki rumana tayi tana dariya
" oh sisi,dama na fadi,irinku ne idan kuka fara soyayya baku daukarta da sauqi"duka suka sanya dariya.
Chapter 28 · 0% Book details