← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 66

Sashe 37

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baisan ta qaraso ba sai daya ji sallamarta,sanye take da kayan bacci baqaqe wadanda suka haska farar fatarta,abinda ya tsaidata kenan wanka tayi tayi shirin kwanciya,murmushi ua sakar mata yana jin tausayinta har cikin ransa,tana ta dawainiya da shi tana bashi kulawa,yana ji a ransa zuwa yanzu yaci ace shima yayi wani abu,ya kamat ace ya kawar da duk wani rauni dake cikin zuciyaraa wanda shike janyo masa jin raunin a gangar jikinsa.

Miqa mata hannu yayi fuskarsa qunshe da murmushi
Ba tare da bata lokaci ba ta sanya nata hannun cikin nashi itama,ya janyota ta fada jikinsa,luf tayi tana jin wani dadi na shigarta,don yau kusan shine karo na farko data samu irin wannan tarbar
"Amaryata,naga alama rashin lafiyata ta takuraki ko,ya kamat mudan matsa daga inda muke nasan sai kinfi sakewa" murmushi tayi sannan ta dage masa gira
"Ok,good,inaga zamu koma england" zaro ido tayi tana cewa
"Da gaske yaya"
"Na taba miki qaryane" ruqunqumeshi tayi tana dariya tare da girgiza kai cike da farinciki
"Wayyo yaya na gode na gode"
"Amma fa zamu dan jima" ta dubeshi tace
"Kamar kwanaki nawa?" Shiru ya danyi sannan ya saki ajiyar zuciya
"Eh to.....idan so samu ne idan mukaje gaskiya ba nan kusa zamu dawo ba,inaso na hada masters dina ne a can,kinga kuwa atleast zamu yi shekara biyu ko uku" ashagwabe ta dubeshi
"Kuma nawa karatun fa yaya,shekara daya fa ta rage mana mu kammala"cikin tsokana ya daga mata girarsa daya
" ni da karatun wanne yafi muhimmanci"dariya ta saki sannan tace
"Fada ma ai bata baki ne,amma dai nima yaya da zaka sama min wata makarantar a can basai na dinga zuwa ba?" Shiru ya danyi sannan yace
"Bari mu gani" sosai ya cukuikuyeshi tana ta murna.

**************

Cikin sati biyu rak ya kammala musu komai na tafiya,yanajin cewa shine mafita qwalli daya da ta ragewa sauran rayuwarsa na samun sabuwar rayuwa da farinciki mai dorewa,hakanan hanya guda daya da zata sashi mantawa da duk wata qura data taso taso birne rayuwarsa.

Da kansa ya dauketa ya kaita gidan raihana don suyi sallama,saidai shi bai shiga ba yace zai dawo ya dauketa.

Wayyo Allah,kada kaso kaga irin farincikin da sukeyi ma ganin juna,mutanen da bacci ma baya rabasu sai gashi aure yasa sun kwashi kusan watanni biyu rabon da suga juna,wuni sukayi hira ko abinci basu bi ta kaiba,sai fatima ce ta agaza ta dafa musu,yadda raihanan ta canza haka rumanana,saidai rumanan ta fita canzawa sosai,don har wani qiba ta fara yi.

Sosai raihana tayi murna da jin tafiyar tasu,tana fata wannan shine ragowar murfin rufewar case dinsu rufewa ta har abada,addu'a ta musu sosai tare da fatan samun kykkyawar rayuwa mai dadi.

Yamma lis rayyan ya dawo daukarta don zai kaita gidansu can na suyi sallama,sai data shiga ta gaida hajjaju sannan raihanan ta rakota,sun gaisa tamkar kowanne dan uwa da dan uwansa,don ko kallo cikakke babu wanda ya yiwa dan uwansa,tana daga musu hannu har suka fice.

Sashen hajjaju ta koma don kota koma sashen nata bata da wani abunyi,har ya zame mata jiki rashin dawowar ammar din akan kari,ta taddasu fatima a kitchen nata kici kicin kwaba alkubus ta rasa yadda zata sarrafa,hajiya na gefe tana sille mata,raihana tayi murmushi ta karbi bowl din ta fara kwabawar
"Hajiya Allah dai ya ceceni baquwar anty ta tafi gashi ta fansheni,don Allah kada ki cewa su nasir bani na kwaba ba yau na shiga tara a gidan nan,zan tsaya dai naga yau yadda take kwabawar yake tashi yayi kyau"
"Dadai ya fiye miki" inji hajiyan ta fice ta bar musu kitchen din.

Basu bar kitchen din ba sai da suka gama kwabin suka dora sannan suka dawo falo,raihana ta bawa fatiman kanta tace ta kitse mata ki guda shida ne don ya dameta,bayan sun kammala girkin fatiman tace basai tayi nata ba,ta dauko flask din ammar ta diba musu ta kai mata har sashen nasu.

Haka suke zamansu mai dadi ita da surukan nata babu sawa babu fitarwa,wani lokaci ka tana iya cewa tafi jin dadin zama da su fiye da ammar din,wanda tsakaninta da shi umarni ne da hani,ba mugunta ko cutarwa dai tsakaninsu,ci sha sutura da tufafi kudin kashewa saidai ta baiwa wani,hakanan ya siya mata mota ya ajjiye mata driver kasancewarta ba maison tuqi ba,hakanan duk abinda takeso ko takeson zuwa waya kawai zata masa ya barta,saidai baisan damuwarta ko matsalarta ba,sau tari da hajjaju data dauka kamar uwa ko fatima data sanwa matsayin rumana take shawara,da safe yake fitarsa bai shigowa sai tara ko goma,da yayi wanka ya ci abinci sai bacci sai kuma wata safiyar.

Kullum ta Allah sai tayi waya da sisinta,amma ko sau daya bata taba cewa da ita wani abu ba,ganin yadda ta samu kwanciyaf hankali kada ta daga mata hankali ko ta sata wani tunani ja daban,duk da itama bata ajema ranta wani abu can ba,kawai ta barshi ne kan cewa harkar kasuwancinsa ne suka sha masa kai suka fi qarfinsa

***************

Sannu a hankali rayuwa ke miqewa tana tafiya tare da juyawa da bawa yadda Allah yaso.

Shekara guda kenan da aurensu inda take lissafin zama cikakkiyar lauya nan da 'yan watanni masu zuwa,zuwa lokacin ta fara dora ayar tambaya a kan zamanta da ammar,koda wasa bai taba marmarin rabarta da niyyar sauke haqqin aure ba,bawai damuwarta ce hakan ba,amma ta riga data sani babu wani aure da aka taba ginashi ya tafi a haka,nauyi da kunya irin ta 'ya mace ta hanata tunkararsa ko sau daya da maganar,ta maida hankalinta kan al'amuranta wanda duk ciki kowanne yake tafiya mata daidai cikin taimakon Allah.

Bata fara damuwa ba sai da ta lura da yadda su fatiman ke maitar ganin 'ya'yan yayan nasu,haka yake ga hajjaju ma don ita bata taba nunawa ba ma,amma ga mai hankali ya isa ya gane,duk da ba wani canji suka nuna mata ba amma tana jin damuwa cikin ranta,damuwarta bata dadu ba sai da ciki ya bayyana jikin rumana,tayi farinciki tayi murna tayi dariya duka ita kadai,ji take tamkar itace zata haihun,don dan sisinta nata ne,a lokacin ne taci damarar tunkarar ammar da maganar
**************

Sanye take da kayan bacci ruwan madara,riga ce doguwa wadda ta zarta gwiwarta mai hannun best sai 'yar samanta mai digon hannu mai wuyan v shape,tsawonsu daya da ta ciki da ta wajen,kayan sun mata kyau sosai,jikinta nata qamshin turaren maidoguri,kusan duk dare shigarta kenan,amma bata taba ganin ammar ya kalla sau uku ba,duk da hakan bata fasa ba don tana ganin tana yin abinda ya dace ne.

Kamar ko yaushe ta taras da da shi a falo ya kammala cin abincinsa suna waya da maisara wanda duk dare bayan ya dawo sai ya kirashi,tana gefansa har ya kammala,ya dubeta yana gyara zamansa
"Ya akayi ne gimbiya" murmushi tayi kawai ta kauda kai"kamar gaske ta fada cikin zuciyarta"
"Naga alama bakin nan naki akwai magana" ya sake yin maganar yana danne danne a wayarsa,gyara zama ta sakeyi sannan ta dubeshi
"Haka ne,amma dai labari nazo in baka"
"Uhmmm,gaya min Allah ya sa alkhairi ne"
"Shine ma" ta fada ataqaice sannan ta dora
"Kasan sisi na ciki gareta wajen watanni biyar baya?" Ido ya zaro yana dubanta
"Haba don Allah" cikin qarfin gwiwa ta kada kai
"Wallahi Allah" sai ya sake maida kansa ga wayarsa
"Kai amma fa na musu murna"
"Bama ita kadai ba,yawanci sa'annin bikinmu wasu sun haihu,wasu sun kusa...." Sai ta dan tsagaita tana jan numfashi ko zata ga wani canji tattare da shi,babu abinda yace illa
"Amma sunyi qoqari" maganar taji wani bawai,amma sai ta dora din da abinda takeson cewa
"Nace ammar baka sha'awansu don Allah,baka sha'awan kaima ace ga yau ga danka na cikinka" dubanta yayi kana ya sake dauke kansa still dai bisa wayarsa
"Hmmmm,ina so man"
"Amma banga ka dauki hanya ba ai,tunda dai ammar 'ya'yan nan ba a kasuwa ake zuwa a siyosu ba,ba kuma a ruwa ake sha ba,baka taba kama hannun matarka da wani manufa ba,to ta ina kake so mu samu zuri'a?" Shiru yayi ba tare da yace komai ba yana danne danne a wayarsa,har tayi zaton bazaice komai ba sannan ya ajjiye wayar gefansa ya kalleta
"Amma dai raihana babu abinda kika nema kika rasa cikin gidan nan ko?,me zai hana mubar wannan maganar" kai ta shiga kadawa
"Wannan kadai ba shine aure ba,idan shine aure da sai nayi zamana a gidanmu ba tare da na dora maka nauyin ciyar da ni ba" sai ya harde hannayansa guri guda yana kallonta
"Yanzu kenan sha'awa ke damunki" sai tambayar ma taso bata dariya
"Ko kusa,amma ammar babu wanda zaiyi aure baiso ganin jininsa ba,burin duk wanda yayi aure shine ya samu zuriya,ko bayan haka laifi nayi don naji wani feelings a matsayina na wadda ke da miji kuma shekarunta suka kai?" Tayi masa tambayar kanta tsaye tana zuba masa idanuwa,sai ya kasa ci gaba da kallonta saboda kwarjinin da idanunta suka mata,yayi shiru yana nazari sannan daga bisani yace
"Nasan kinyi haquri kuma kinyi kawaici,amma ki dada,ban da lafiya ne kuma ina kan neman magani" sai duka jikinta yayi sanyi,tausayinsa ya kamata,idanunta suka cika da hawaye,cikin rauni tace
"Ayyah kayi haquri ammar,ban sani ba,me yasa baka gayan ba tuntuni,da ka gayan da bazan ma tambayeka ba,Allah ya baka lafiya yasa kaffara ne a gareka"
"Ameen,na gode" ya fada yana miqewa tare da cewa zaije ya kwanta ya wuce ciki.

Ta dade zaune a gun jikinta a sanyaye,tausayinsa ta dinga ji sosai,ta dinga nadamar ma yi masa maganar data yi,sai daga bisani itama ta miqe ta bishi.
.

Cikin lokutan kanta ya dauki zafi sosai semester tazo qarshe,karatu take tuquru saboda ta samu ta fidda sakamako mai kyau,sau tari a gajiye take dawowa gida,gurin hajjaju ma wani lokaci suke karbar abinci da su fatima keyi.

Cikin nasara ta kammala jarrabawar sai kuma sauran tsarabe tsarabe da kan biyo baya.

****************

Cikinta na shiga wata na tara rayyan ya dawo da ita gida don ta haihu a nan bisa umarnin ummu,saidai shi bai samu zuwa ba sai zata koma zaizo su tafi tare.
Chapter 37 · 0% Book details