← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 66

Sashe 10

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Raihana ce tayi suprising dinta ta kwashi hotunan takai aka buda su aka sanya su cikin frame masu kyau,ta kafa mata daya saitin gadonta,ta dora mata daya kuma kusa da bedside lamp dinta,tana ganinsu kuwa ta daka tsalle ta dale raihana tana fadin,
"Wayyo sisi na bani da kamarki"
"Nima ban da kamarkin ai,gudun mawata kenan kan irin son da naga kinawa hoton"
"Kin biyani wallahi,Allah ya biyaki kema"ta fada tana daukar daya hoton dake kan bedside din tana juyashi a hannunta,frame din kawai ma abin kallo ne ballantana yadda hoton ua qawatu a cikinsa
Ta lumshe idonta kana tace "ameen 'yar uwa,fatan kawai Allah ya nuna mana aurenku"tayi maganar tana dariya qasa qasa don tasan ta gama soso mata inda yake mata qaiqayi,tayi kuwa far da ido sannan ta amsa"kai....ameen ya Allah" harda daga hannayenta sama

*************

Duk lokacin da rana ta fito ta fadi sai rumana ta rage ranakun da suka rage rayyan din ya dawo,haka shi din ma daga bangarensa,ya qagu yaga ya dawo qasarsa ta haihuwa,gaba daya zaman england ya gama fice masa aka,ya k'agu ya ganshi cikin familynshi tamkar ce masa akayi ranar ba zata zo ba.

Sosai take shiryawa zuwan nashi,don gaba daya hirarta ta koma ta dawowar yaya rayyyan,duk son hira irin na rumanan daga kun zauna hira mawuyacine ku cinye minti biyar bata sauya akalar hirar taku zuwa ta yaya rayyan ba,dariya sosai raihana ke mata don har canza mata suna tayi, wani zubin takan tsokaneta da lailah majnun,hatta da laces din da taso su sanya wannan sallar ta amso musu takai an dinka musu ita da raihana,don tace shi zasu saka ranar da ya rayyan din zai iso,ragowar kuma idan zasu masa rakiyar gaida family,na raihana dai baya wuce to,babu shakka ita kanta shaida ce na ba qaramar soyayya bace ke gudana cikin jininsu ba.

Hakanan watarab rumana kan zauna tana bayyanawa raihanan kwatankwacin yadda takejin rayyan cikin zuciyarta,don ba zata iya kamantawa ba,wani lokacin raihana ta tayata,wani lokacin tayi dariya,wani lokaci ma tausayi hakan ke bata,tana ganin itakam bata fatan koda zata fara soyayya tayi mata irin wannan kamun,don tana ganin wahala ce zallah cikin irin hakan,zuciya da gangar jiki sam basu da hutu,dariya sau tari rumana keyi
"Raihana kenan,irinku ba shiru shiru din nan,wallahi kunfi kowa rungumar soyayya gadan gadan,gwara mu da bakinmu zamuyi ta fada" murmushi kawai take ta kada kai
"Rumana tawa"
"Raihana tawa" sai su sanya dariya baki daya,don kowa yana ganin cewa yana kan ra'ayinsa,kuma bazai yiwu hakan ya sauya ba
*************

Tsaye suke bakin titi ita da rumana,yammaci ne na ranar jum'a wanda ke dauke da gajimare mai yawa da ya fara canza yanayi zuwa na hadari irin na farkon damina,kasancewar daga kowanne lokaci zuwa yanzu za'a iya samun saukar ruwan sama.

Saloon suka je kamar yadda suka saba,saidai na yau ya banbamta da na ko yaushe,ya zama na musamman din kuwa sanadiyyar kwanaki biyu da suka rage rayyan ya dawo.

Tsaki rumana ta dan ja tana sake kallon titin"mtswee,motar nan ta mana tsiya wlh,da tuni mun jima da mantawa muna gida,for now ya kamata mu yiwa abba complain a kanta ta fara gajiya da mu"dariya maganar rumana ta baiwa raihana,don ta sani sarai wata kalar motar ta hango musu shi yasa ta fara sharhi kan waccar,duk da ita din ma ba wai ta tsufa bane
"To ya za'ayi,qarfen nasara ne da bashi da tabbas" inji rumana.

Tana rufe bakinta motar ta gilmasu qirar sienna light brown, a hankali ta dawo da baya tayi parking gabansu,gilasan motar suka sauka qasa mamallakin motar ya bayyana
"Ranki ya dade hajiya rumana" a hankali ta maida kanta inda akayi maganar,sai ta dan saki fuskarta maimakon dazu da take a daure
"A'ah,farouq dama ana ganinku"
"Gamu kuwa,kune ai ke wuyar gani.....daga ina haka da yammacin nan"
"Wallahi daga wankin kai"
Ya saki murmushi idanunsa na kafe kan fuskar raihana wadda sai ka rantse bata san Allah yayi ruwanshi a gun ba,da ido yayiwa rumana nuni da raihana,dariya taso kubce mata amma ta kanne gami da dafe baki
"To bismillah mana,ku shigo na saukeku a gida" yayi maganar yana bude musu qofofin motar.

Da saurin raihana ta damqe hannun rumana tare da tsaidata,ta san hakan me yake nufi wato ita ba zata shiga ba,qasa qasa tace
"Pls sisi,mota taqi samuwa kuma kinsan akwai abubuwan da zamuyi a gida da yawa da bamu gama ba,gashi hadari ya fara tasowa,kiyi haquri ya rage mana hanya mana" shiru tayi kamar ba zata amsa ba ita kuma tana ta matsa hannunta,ganin yadda mutumin ya zuba mata ido yana son yaji me zai faru tsakaninsu ya sanya kawai ta share ta bita din.

Hira suka dinga yi jefi jefi yana jinsu bata tanka ba,duk da kuwa yadda yaso sanyata cikin hirar sai ta kauce,sosai ua shiga damuwa, don ya dade qaunar ta na wajigashi,koda numberta ya kasa samu don rumana tace ba zata bashi ba sai da yardar 'yar uwar tata.

Cikin mintina qalilan sai gasu a unguwar tasu,ita tafara balle murfin motar ta fice ta shige ciki don a gajiye take sosai,bayan wasu mintina rumana ta biyo bayanta.

Sai bayan sallar magariba suna zaune ta dubeta
"Raihana" ta kira sunanta,dagowa kawai tayi ta dubeta hakan ya nuna tana jinta
"Farouq na neman alfarma na bashi lambar wayarki"
"Dalili da me?" Ta tambayeta kai tsaye
"Saboda yana sonki,so kuma na aure"
Raihana,lokaci yayi da ya kamata ace kin maida hankalinki guri guda kin zabi wanda zaki rayu da shi rayuwa ta har abada wato rayuwar aure,sanin kanki ne cewa a son ran abba a cikin dakunanmu zamu qarasa karatunmu,ke kika gayan yace ya rayyan na dawowa za'a tsaida lokacin bikinmu,to ta yaya kike so nayi aure na barki ke daya?,ke kanki ba zakiji dadi ba,don Allah sis na roqeki ki bude zuciyarki ki saurari masu begenki ko Allah zaisa kiyi katarin dacewa da wanda ya dace da ita,don Allah"ta qarashe cikin sassauta murya.

Murmushi ya subuce mata ganin yadda rumana keta faman lallashinta,ita kanta ta sani cewa ba laifinta bane,hakanan zuciyarta taqi buduwa balle ta karbi kowanne baqo dake karakainan neman shiga cikinta,ba shakka tasan cewa yadda suke qaunar juna ita da rumanan ko 'yan uwansu da suka fito ciki guda basu qaunarsu haka,to ta yaya kuwa zataji dadin zama ita daya idan rumanan ta tafi ta barta
"Yanzu madam me kike so ayi kenan" murmushi ta saki tana sake matsowa kusa da raihana
"Yauwa sisi na,don Allah ki daure ki karbi farouq,koda bai miki ba akwai al'amin tukur ahmad nasan zaki iya tunashi?,yanzu haka mun gama magana da shi na farouq na riga da na bashi number wayarki zaya kiraki....pls and pls sisi kada ki masa miskilancin nan naki" sai ta hade rai,saidai can qasan ranta na wasa ne
"Ok,har ma kin bashi num dina kenan ba tare da izini na ba ko.....kice min rabon num dina kike kawai ga duk mai so" dariya sosai ta baiwa rumana har ta soka qyaqyatawa,kafin tace wani abu ummu ta shigo falon hannunta dauke da leda
"A'ah,tagwayen ummu,da alama ta samu kenan?,ko duk murnar dawowar ya rayyan din ce?" Ta fada tana zama gefan kujera,murmushi rumana tayi yayin da raihana ta dubi ummun fuska a hade"yauwa ummu.....gwara kizo ki rabani da yarinyar nan,ki gaya mata ta daina rabawa mutane numberta"
"Kamar yaya?" Ummu ta tambaya
"Wai kawai bata san mutane ba sai ta dinga basu number dina".

Tuni ummun ta gano inda maganar ta dosa
" banda abun raihana number dai ba wani abu ba,ai lokacinki ne wataran babu mai bada number taki ko kuwa?,nidai fatana kawai ki a kawo min suruki na gari na hadaku nasha bikinku rana daya,ko ba haka ba"su rumana har da sunne kai wai anji kunya,raihana kuwa murmushi kawai tayi.

Ledar hannun nata ta tura musu tana fadin
"Wannan dinkunanku ne na laces da kuka kai a ciki dazu tailor din ya kawo muku,wannan kuma tawa gudun mawar dinkunan dawowar ya rayyan.

Allah sarki ummu,uwa daya da daya,sam basu san ma yaushe ta bada ayi musu dinkin ba,hada baki sukayi wajen yi mata godiya,ta tashi ta basu guri.

Rumana ce ta fara fidda kayan cikin santin yadda dinkunan suka tsaru,atamfofi ne vlisco 'yan ubansu kala uku uku ummun tayi musu,daya dogayen ringuna masu shape din pieces daya aka musu riga da skert,daya kuma riga da zani,duk sai da rumana ta gwada,sun yi mata cif kuwa a jiki tamkar a jikinta aka dinkasu,hakanan sun haskata tare da fidda shape dinta
"Allah ka barmin surukata kuma uwa ta gari"
Dariya ta bawa raihana
"Ameen ni kuma Allah ya barmin uwata ta kaina" ta fada cikin dariyar tana tayata ninke kayan tare da jerasu cikin wardrobe dinsu,don da guda suke amfani,kowa na iya amfani da kayan kowa,ba wani banbanci tsakaninsu

**************

*_monday_*

A qalla ba akasara ba ta shafe sama da awa daya da rabi gaban mudubin tana shafe shafe,goga wancan zana wancan goge wancan,a yau jinta take babu wata halitta da ta kaita farinciki a doron qasa,yau ranar da zatayi tozali da farincikinta rayyan,wanda suka shafe a qalla shekaru kusan tara ba tare da sunga juna ba.

Tun rumana na zaman kallonta har ta gaji ta koma tayi kwanciyarta kan gadonsu,tuni dama ta gama ita nata shirin,kamar yadda halinta yake bata cika sin qyale qyale ba,concealer kawai ta shafa tabi bayanta da hoda wadda ta dace da kalar fatarta,sai mascara data sake tada gazar gazar din gashin idonta,girarta kawai ta gyara don bata amfani da eye brow,kwalli ta zizara da ya sake fidda shape da kyawun idonta,sai dan pink din jambaki data shafawa labunanta,tana sanye ne cikin daya daga cikin laces din da suka tsara sakawa.

Lace ne dan ubansu wanda ko ba'a gaya maka ba kasan ba na qananun kudade bane,orange na aka masa adon baqi da torches na lemin green,abu daya yasa raihana taji ya fita akanta dinkin riga da skert da rumana tasa aka yi mata a maimakon doguwar riga kamar yadda ta zaba.
Chapter 10 · 0% Book details