← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 66

Sashe 22

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari ya kama ranar daurin aure ne,qarfe biyu na rana za'a daura saboda dangin angon daga damaturu zasu zo,ankon shadda kafatanin 'yammatan sukayi sea green,ba qaramin kyau 'yammatan kanurin sukayi ba wanda rumana da raihana tuni suka saje cikinsu,babu abinda ke tashi sai yaran kanuri.

Part guda suka ware 'yammatan amarya,suna ciki suna harkokinsu.

Muhsin jikan gidan wanda bazaya wuce shekara goma ba ya shigo yace raihana da rumana suzo inji hajja yakura,rumana kam basa nan an samu qafa,tabi Aishatu wata cousing din raihana gidansu zata debo kayanta na dinner din anjima,don rumanan tace bazata zauna ba gwara taga gari,tafiya mabudin ilimi ce.

Ankon shaddar ne itama a jikinta saidai dinkin buba ne iya gwiwa da zaninta,rigar ta fita ajikinta sosai,ta soke daurin dankwalinta kitson da aka yi mata ya fito,ba wata tazara bace tsakanin part din hajja yakura da nasu ba,sa'an nan sashen babu yawaitar zirga zirga sabida can bayan gidan suke,don haka haka ta fice abinta kai tsaye.

A dan tsakar gidan hajja yakura ma ba mutane sosai,gwaggwanninta ne tayi musu sannu ta wuce.

Sallama tayi sannan ta daga labulen qofar dakin,hajja yakura ce kadai zaune a falon nata,itama sanye take da shadda ruwan lemo wato orange wadda tasha aiki tayi mata kyau sosai,hakanan tsufanta ya buya,tsokanar hajja yakura da tayi niyyar yi ce ta koma ciki sakamakon turaren daya sheqa,babu bata lokaci kuma idanunya suka sauka a kansa,tuni dama nashi idanun na kanta tun sanda ta nufo bangaren jikinsa ya bashi.

Rayyan ne,zaune yake gaban hajja yakuran abinsa tamkar shima daya ne daga cikin jikokinsa duk da kusan haka suka daukeshin,sanye yake da farar shadda qal mai azabar kyau da daukar ido,riga 'yar ciki da wando hadda babbar riga,dukkansu sun sha aiki ash colour,hular kansa safa da agogo kuma duka ash har da sau ciki data gani a bakin qofa ga zatonta wani baqon hajja yakuran tayi na daban,ya zuba kyau wanda fadarsa ma bata baki ne,tamkar wani kyakkyawan balarabe da ya ari kayan hausawa ya sanya,idanunta ta janye tana jin wata fargaba da zullumi na maye gurbin nutsuwa da kwnciyar hankalin da ta dan samu,wani zullo zuciyarta ta fa yi mata,qafafunta sukayi sanyi tamkar an dokesu.

Cike da dakiya ta saki labulen ta qaraso cikin dakin,har yau bai dana kallonta ba,ji yake bazai iya janye idanunsa daga kanta ba,wani irin kyau yaga tayi masa,tsohon tsumin sonta da yake zaton raguwarsa ya fara dawo masa sabo fil ya soma taso masa,komai nata mai sanyi ne kamar yadda halayyarta take,tabbas haka yake
"Gani hajja"
"Gaki kuma......baki ga yayanku bane?" Murmushin yaqe ta saki tare da zama kusa da ita
"Ki bari na zauna mana tsohuwa.....sannu da zuwa yaya rayyan,ya hanya?,an iso lafiya?ya mutanen gidan?"
Ranqwashi hajja yakura ta sakar mata aka tana fadin
"Jimin saunar yarinya?,sai kace 'yar jarida,haka kanawan ke saukar baqi da tambayoyi?" Murmushi ya saki yana duban dan qaramin bakin raihanan da ta sake tsukeshi tare da yamutse fuska alamun taji zafin ranqwashin
"Barta hajja,wata gajiyar takeson taramin da wadannan tarin tambayoyin bayan wadda ke jikina ko?"
"Eh tsabar iya shashanci ne ai" cewar hajja yakura,idanunsa ya lumshe ya budesu,har yau idanunshi na akanta,ita kuma taqi dubansa don so take su raba lafiya ba tare da ya haddasa ma zuciyarta komai ba"komai lafiya lau raihata....."yanayin yadda ya fidda sautin sunan ya sanyata daga kai ta dubeshi,ya kashe mata idonshi daya,tofa abinda take gudu sai da ya faru,tuni ya aikewa zuciya da gangar jikinta wani irin dafi da ya zare mata dukka wata laka ta jikinta tashin farko,qasa tayi da kanta tana jinjina shu'umancin rayyan din,tana jin tamkar da biyu yayi mata irin wannan kallon

Hajja yakura ta mata umarnin ta bashi masauki sannan tazo ta karbar masa abinci,tamkar ta zura da gudu su nemeta su rasa haka taji,tabbas idan batayi wasa ba sai rayyan ya fama mata ciwonta,amma yata iya,bashi yiwuwa ta bijirewa umarnin hajjan tunda bata da wata hujja da zata bata,sai lokacin take data sanin barin rumana tabi aishatu,da tuni ta janyr jikinta ta barta da shi su qarata.

Ta bayan gidan suka kutsa yankin da tasan ba mutane,tana gaba yana binta a baya,hakan ne ya bashi damar qare mata kallo,cikin jikinta ita kanta a tsarge take,tafiya kawai take tana hardewa,jinta take tamkar tare take da dodo
"Kinyi kyau raihata,kinyi kyau sosai,tilas na biyo bayanki saboda 'yan fashi da makami"
"Idan akwai babban dan fashi ai kaine na farko,baka da na biyunsa" ta fada cikin dakiya,da kuma manufar katse duk wata hira da zata hadata da shi,dafin da yake zuba mata da idanunsa kawai sun isheta basai ya qara da kalamansa ba,wata sassanyar dariya ya saki,bata ankara ba yasha gabanta lokaci guda suna daf da bakin falon da zai sauka din,yayi daf da ita,da sauri ta ja baya tana dubansa,idanunshi tsakiyar nata yace
"Idan d'an yankan kai za'a kirani akan sonki raihata a shirye nake da hakan,saboda matsayinki cikin nan....." ya nuna qirjinsa ".....ya wuce duk yadda kike fasaltawa" cikin tata salon dakiyar ta harde hannayensa a qirji tana dubansa,wanda hakan baa qaramin sake tafiya da rayyan din yayi ba,kunne ya zuba don yasanta sarai,magana zata yanko masa cikin sanyi amma mai nauyi
"Yaya rayyan,ba'a so dole fa,ni bani da ra'ayin aurenka.....ina ganin qimarka da mutuncinka a matsayinka na yaya na,don Allah kaci gaba da kare martabarka,kada ka yarda qanwarka ta rainaka" murmushi ya sake kasheta da shi har sai data ambaci sunan Allah
"Son da nake miki da wanda rumana ke miki na tabbatar ya isa ya riqe mana gidan aurenmu,so kada ki damu zamu rayu cikin farinciki da aminci fiye da yadda baki zato kinji?"
"Bana sonka kuma ina nufin abinda na fada din" ta fada a zahirance a hasale,yayin da can qasan zuciyarta take jin rauni da tausayin kanta,shiru yayi yana qare mata kallo,tsahon minti biyu ta kewayeshi ta bude falon ta shiga,bayanta yabi amma sai yaja tunga a bakin qofar falon
"Ga masauki nan" ta fada tana duban wani sashen tare da neman hanyar ficewa daga falon,ta gefansa ta rakuba ta fice din.

Jikinta har rawa yake haka ta dinga neman number din rumanan,don bata jin zata iya sake komawa gun rayyan din,hawaye ne ke layi bisa kuncinta tana sharewa,ita kadai tasan azabar da take ji a qirjinta,kusan sau biyar tana kiran rumana wayar a kashe,saita sauya akalar kiran nata zuwa wayar aisha,najwa ce ta daga a gida kenan ta barta,ta kashe wayar tata ta jingina da bango,kuka tayi nadan lokaci wai ko zataji sauqin abinda takeji cikin zuciyarta,sannan ta ja qafafunta bakin fanfon dake tsakanin shuke shuken bayan gidan wanda shike basu ruwa ta wanke fuskarta,take duk wata 'yar kwalliya dake kan fuskarta tayi nata guri,sai data ratsa dakinsu ta shafa powder sannan ta koma gun hajja yakura ta dauki abincin rayyan din.

Yana zaune saman cushion din falon,ya cire babbar rigar da 'yar ciki da hukar,daga wandon shaddar sai singlet a jikinsa sai kace wanda ke a gidanshi,inji raihana data masa kallo daya ta dauke kai sabida wani nauyin ganinsa haka da taji,
Kafin ta ajjiye tray din dake hannun nata har ya taso ta tallafi qasansa inda hannunta yake,take hannayensu suka hadu,wani shock dukkaninsu suka ji wanda basu taba jin hakan ba tattare da su,karo na farko a rayuwarsu,nata kam ya boyu saidai nashi bai boyuwa ba,kamar ta sakin farantin haka takeji gashi yaqi ya riqeshi sosai tana sakin ba shakka kwanukan zasu tarwatse ne a qafafunsu.

Muryarsa can qasa tamkar mai maye ta yadda yasan ba shakka zai iya illata ta,don yaci burin sai ya tarwatsa duk wani qarfi da take ji ko qin da take iqirari cikin zuciyarta a yau din nan
"Shine kika wanke kwalliyar duk sdon saboda rayyan ya yaba?,saboda nãce kinyi kyau?...." Ya tambayeta yana mata kallon qasan ido
"Dama ba don kai nayi ba...saboda haka baka cancanci ka gani ba" ta fada muryarta na rawa bayan sanyin da tayi,wanda ita kanta batasan da hakan ba,murmushin gefan kumatu yayi yana sake matsowa kusa da ita,badan farantin dake tsakaninsu ba tabbas da hadesu zaiyi guri guda,sassanyan qamshinsa ya dinga bugun hancinta
"Ni rayyan ni kuwa na cancanci ganinta tunda gashi ni din nazo,dayan da kike qaryar shi kika yiwa ina yazo?,shaidar bai damu da ke ba kenan?".

Zuciya a kusa sai wasu sabbin hawayen suka balle mata,bakinta na rawa ta fara fadin
"amir shi ya damu da ni kuwa tunda yana son farinciki na sabanin kai.....ko daama bai damu da ni ba to ni na damu da shi,kuma ni shi nakeso,kai din da kake qwaqwar bana sonka bana sonka na fad......."kasa ci gaba da maganar tayi sakamakon yatsansa manuni da ya sanya yana zagaye tausasan lebunanta da su,wani abu taji yana zagaya jinin jikinta,bugun zuciyarta ya qara gudu.

Cikin rawar jiki ta janye hannayenta da jikinta daga jikin farantin da niyyar barin gun,ba don yayi zafin naman tallafe kwanukan ba tuni duka abincin ciki sun kife a qasa,da sauri sauri ta nufi qofar ficewa daga falon,tuni ya ajjiye kwanukan abinci sannan ya isa bakin qofar falon ya rufeta da faffadan qirjinsa sannan ya zuba ma raihanan idanunshi wadanda ke mata kaifi,don duk wasu alamu da yakeson gani ya samesu tattare da ita,koda bakinta bai furta ba yasan yayi nasara a kanta,duk da haka bai qyaleta ba sai da ya faki idonta ya cafko hannunta,ya sanya tafin hannunshi cikin nata ya rumtse yana kallon qwayar idonta dake digar da hawaye,bacin ransa ya fara tasiri kadan kadan cikin ido da kuma saman fuskarsa,bai iya shiga damuwa ba sam shi yasa baya yadda wani abu ya dameshin,face soyayyar raihanan da tafi qarfin ikonsa
"Kekam bakijin kunyar yin qarya?.....baki jin nauyin budar baki ki cewa dan adam bana sonka?"
Ta lura so yake ya fasa mata zuciya,a hasale ta daga kai
"Eh ai gaskiya na fada."
Kai ya shiga kadawa tana qoqarin qwace hannun nata sai yayi mata riqon tsauri
"Da kyau,kici gaba da fada din,shi kuma rayyan xai baki mamaki,kafin kibar maiduguri idan bakiyi wasa ba zaki koma kano da aurensa a kanki" ya fada yana sakin hannun nata,sannan ya juya ya koma kan kujerar abinsa yaja kwanukan yana budesu.
Chapter 22 · 0% Book details