Sashe 53
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tukunya ta dauka ta kunna fanfo ta debi ruqa ta dora saman gas,sannan ta dafe kantar tana tunanin meye abu na gaba da zatayi bawai don batasan me zata aiwatar din ba,da sauri ta juyo don isa drowee da suke ajjiye kayan kadin miya taga mece da su kuka ko kubewa,karo sukayi har jikinsu ya hade da juna,da sauri taja baya tana fadin
"A'uzu billahi....."
"Shshshsh....kada ki sake ki qarasa tunda ni ba shaidan bane" yayi saurin katseta,sai ta dubeshi cike da takaici,wato ita ba mutum bace,har yau bata mance ranar da yayi mata ta'awizi,sai ta watsar da shi ta taho da jarumtar ta da niyyar wuceshi ta dauki abinda take da buqata,binta yayi tsaya a bayanta har tana iya jin hucin numfashinsa,ko yaya kuma ya motsa jikinsa na gugar nata,take gabanta ya fadi,jikinta ya fara dan rawa,har taso tayi barin robobin kayan kafin miyar dake jere cikin cupboard din data daura hannunta akai,hannunsa ya miqe da yake ya fita tsaho ya kwaso dukka robobin ya ajjiye mata a gafe cikin sauri ta zame jikinta ta koma gefe guda tana sauke numfashi,cikin dakiya da rashin walwala yace
"Wai ke nan har gaba kike da mijinki,don bazance qiyayya ba saboda wallahi qarya kike kice baki sona" kamar zata tanka masa sai 'yan halin nata suka motsa,bata dubeshi ba ta fara tsintar waken da zata daka cikin miyar kanta duqe,sake matsowa yayi kusa da ita yana shirin dora hannayensa kan kafadarta,da sauru ta janye jikinta kamar wanda ke shirin dana mata wuta
"Kaga malam kada ka soma tabani wallahi" kamar wanda ta zuga sai yayi caraf ya cafki hannunta yana dubanta
"Idan na taba din kuma sai yaya,ko za kici sadakina ne a bulus?"harar ta watsa mas" dadin abun dai ai ba da kudinka ka biya ba ko?"girarsa ya daga
"Au haka kika ce?,taqamarki kenan?"
"Eh haka nace" ta fada cikin tsiwar da bai taba gani ta yima wani ba
"Ok,zaki gani,zaki san cewa ba kasawa rayyan yayi ba,haka naj idan naso ko ban bada sadaki ba ina da qarfin da zan iya tabaki ko?"
"Wannan kuma kayi kadan,tunda ba'yar iska ka samu ba bal....." Bata qarasa ba ya birkitota baki daya cikin zafin nama ya hadeta aqirjinsa,cikin azama ya fara lalubar bakinta lokacin da take yunqurin qwace kanta tana kai masa bugu,sai da ya tabbatar ya hade bakinsu guri daya sannan ya fara aika mata da wasu makamai wadanda tun tana iya kare kanta da qoqarin yin tawaye har abinda yake mata ya fara galaba a kanta,ji tayi ta tureta idanunsa cikin nata wadanda suka sauya launi tare da qanqancewa
"
Tunanin da ya fado masa wanda ya sanya motsuwar kishinsa shi ya sanyashi tureta,ya dubeta idanu a qanqance sun dan canza launi kadan
"Uhmmm,wato na sosa miki inda yake miki qaiqayi ko shine har da yin wani likimo ko?" Ta fuskanci me yake nufi sarai,takaici ya kamata sai kawai ta saki kuka
"Allah sai ya saka min wallahi,kaji haushi dai,ko kunya baka ji ka hada hada 'yan biyu zaka aura" wani mayaudarin murmushi ya saki kana yace
"Ba zaki gane hakan na sai ranar da na hada ku a labour room duka ku biyun" sake qufula tayi
"Allah ya sawwaqe wallahi,aniyarka ta bika"murmushin ya sakeyi
" kema zata biki ne yarinya"ya juya yana shirin fita ya barta da sharar qwalla,har ya kai bakin qofa ya dawo
"Ki dafa duk abinda zaki dafa da ni,don yau madam ba zata yi girki ba na bata hutu tayi kwanciyarta"
"Can ta matse maka,amma wallahi kabar cin girki na" sai ya zuba mata ido yana murmushin qeta
"Tabbas kuwa zakiyi kaffara,girkinki kuma ai yanzu na fara ci,kinga.....kima fa daina wannan fiffiqar,ba don my angel bafa da wannan auran baza'a yishi ba,kiyi a hankali"baqinciki ya mamayeta ta rasa me zata gaya masa ta rama,da hanzari ta bude bakinta
"na tsaneka wallahi rayyan"ya jita sarai amma sai ya kada kai yayi ficewarsa bai waiwayeta ba.
Tana girkin tana hawayen zuci da zahiri,gab da magariba ummu ta dawo,tana jiyosu a falo tayi zamanta kitchen har bayan ta kammala,sai da aka kira sallah taji shiru alamun kowa ya nufi gun yin sallah sannan ta fito tayi dakinta bayan ta shiryawa abba abincin.
Qarfe takwas ta isa falon abban suna tare da rayyan din suna hira,ta soma zuba masa abincin sai yace ta hada musu da rayyan din,suka hada ido ya mata dariyar mugunta
" kinyi rantsuwar banza,koda yake dama kin saba yin rantsuwar banza ai"ya fada qasa qasa yadda abban bazaiji ba sanda ta duqa da niyyar ajjiye kwanukan tuwon,bata tanka masa ba tayi ficewarta,ko falon bata zauna ba ta qule daki ranta na mata daci,da baqinciki ya ciyota kawai saita janyo waya ra kira rumana,babu dadewa ta daga sai kawai ta sanya mata kuka,shiru tayi tana saurarenta,sai da tayi mai isarta sannan tace
"Wallahi sisi baki sona Allah" ko bata tambaya ha tasan kwanan zancan,bai wuce maganar aure ba
"Eh,indai kan wannan ne bana sonki,farin cikinki shine nawa,amma bakison nafison farincikin mijina akan nawa ba?" Wani qarin takaici kenan, aqufule tace
"To shikenan,wallahi Allah ki jawa mijinki kunne idan ba haka ba zan muku rashin mutunci ke da shi" dariya ta kwashe mata da ita sannan tace
"A shirye muke,ai amarya bata laifi" ganin tuburata kawai rumanan ke sonyi ya sanyata kashe wayar ta saki kuka,babu jimawa taji shigowar saqi cikin wayarta
_"kiyita dai damun kanki saboda ni,ki shigo gidan a rame uwar gida ma ta fiki kyan gani"_ wani haushin ya sake turniqeta sai kawai ta kashe wayar ta maida kanta ta kwantar tana ci gaba da tsiyayar da hawaye
****************
Tun bakwai na safe ta tsinkayi rumana cikin gidan wanda batasan dalilin zuwanta ba,tadai ganta taci kwalliya sosai cikin wata shegiyar shadda maroon da tayi mata bala'in kyau,kallo daya zaka mata kasan lallai tana hutawa gidan rayyan.
Tana daki tana jiyo hidimarsu tsakanin falo tsakar gidan da harabar gidan,tuni lantana ta gama break fast har tayi mamakin yadda yau tayishi da wuri,sai kawai ta shiga wanka ta fito ta shafa mai tare da turare ta goga hoda ta zura doguwar rigar atamfa,daki ta cewa lantanan ta kawo mata kayan karin donta fuskanci wani abu suke da ya shafi bikinta,ita juwa ranta soyuwa yake idan taga rumana ta saki jiki ana hidimar da ita,wani lokaci har gorin ta koyi kishi take mata,qyalqyala dariya take tace
"Akan me,bayan na samu saunar kishiya wadda bata iya kula da mijinta ba" da biyu itama take gaya mata haka wai ko hankalinta zaya dawo ga rayyan din,Allahu akhabar(wa yu'usiruna ala anfusihim walau kana bihim kasaasah).
Tana gab da kammala break din rumanan ta shigo hannunta dauke da wata leda ta dubi raihana
"Dama tashi kikayi kika yi kwalliya,don yau zamu karbi lefanki" sai ruwan tea din ya tsaya mata,wata faduwar gaba ta ziyarceta idanunta qir kan rumana dake ajjiye ledar tana bude jakarta tana zarar kudi,sai ta janye idanunta ba tare data ce komai ba,ta tattare duka kayan karin guri guda.
Hijabinta kawai ta dauka da key dinta,babu wanda yaga fitarta tayi ficewarta,sai ta rasa inda zata je,qarshe ta zabi zaman office dinta,nan taje ta bude ta shiga ta qulle tayi kwanciyarta,lokaci lokaci hawaye na zuba a idonta.
Kafin azahar 'yan maiduguri suka zo,ciki harda amma,tunda suka zo take baza idanun ganin raihanan don dama da biyu tazo ba karbar lefe ne ya kawota ba saidai bata ganta ba,ganin haka ya sanya tayi tafiyarta qoqi gun hajiya babba,sanin matsayar hajiya babba kan batun ya sanya har suka gama hirarsu bata ce komai ba,bata koma gida ba sai data tabbatar masu kawo lefen sun watse.
Lefe ne akwati dai dai na alfarma wanda rumana ta zaba ta darje har guda shida rayyan din yayi,yana qorafi yana komai haka yayi su,komai na ciki mai tsada ne babu mai qaramin kudi,sai ganin shi tayi da wasu akwatunan irinsu guda uku maqare da kaya yace nata ne itama,daddy dalhatu ashe tuni ya gaka nashi,akwati shida ragowar shi ya hada suka zama sha biyu,yayin da ya yiwa rumanan itama guda uku ta tashi da shida itama,ba'a rasa tsaigumi tsakaninmu mata,musamman akan batu na kishiya,kishiyar ma irin rumana da raihana,babu abinda ba'a gayawa rumana ba amma ta sanya auduga ta toshe kunnuwanta,tayi namijin qoqari gun ladabtar da zuciyarta,a duk sanda taso yunquro mata da wani abu takan tunasar da kanta wace raihana ne a gunta,hakan shi yayi mata jagora matuqa wajen samun salama cikin birnin zuciyarta.
La'asar amma ta dawo gidan,ko kallon inda kayan suke bata yi ba,raihanan kawai take jira,ba ita ta shigo gidan ba sai da aka soma idar da sallahr magariba a wadansu masallatan,mamaki ya cikata ganin 'yan uwanta na maiduguri,matan qanne da yayyen mamanta harda maman nata ma,saidai rashin sakin fuska da harara da amma ke mata ya sanya jikinta mutuwa.
Tara na dare ne tana dakin raihanan wanda ita daya ce ciki baqi har yanzu suna falo anata kallon lefe da yaqi qarewa,dubanta amma tayi
"Kin bani mamamki raihan,kin bani kunya,yanzu ashe zaki iya auran mijin 'yar uwarki" sai ta daga kai fuskarta cike taf da qwalla tana duban mahaifiyar tata,tabbas tasan babu mai wanketa wajen wasu sai Allah,abinda ta guda kenan tunda fari gashi yazo ya risketa,kai ta kada
"Ba laifina bane wallahi amma,ba laifina bane"
"Najibkuma na sani,amma babu wanda nake gani da laifi sai ke,me kike so duniya ta daukeki?" Ta fada cikin fushi,kasa daurewa raihanan tayi duk yadda taso da hakan,sau ta saki kuka ta sauko qasa kan gwiwarta tare da dora fuskarta kan cinyarta ammin tata,tsakanin da da mahaifi sai Allah,tausayin diyartata sai ya kamata,batason duniya ta zageta ne,tunda tasan mutum kome zakayi baka iya masa,tabbas iyayen yarinyar da kakanminta basu da matsala ko kisqala zarratin,amma cikin danginta fa?,me zasu ce?
"Amma na ki gafarceni,ina roqonki da sunan Allah ki yiwa abba magana su warware maganar nan,irin abinda kike gudarmin amma nima shina gudarwa kaina shekarun baya,sau gashi a yanzu yazo ya riskeni,wallahi amma bani da sha'awar zaman aure da yaya rayyan".
.