Sashe 60
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba daya ya rasa ta inda zai fara lallashinta,da baki zai lallasheta ko da me?,kallonta yake yana shafa kanta duk da ta kifa fuskarta taqi dubansa,azabar da takeji ne kawai ya isheta,ga wani haushin rayyan din da tsoronsa daya rufeta,ji take kamar ta tashi ta fella da gudu,gani take kamar zai sake mata wani abun ne,da zata iya gaya masa daya barta kada ya sake rabar jikinta,
.
Ajiyar zuciya ta dinga saukewa,ya sake dubanta wata qaunarta na sake ratsashi,tausayinta na irin shigar zafin da yaso yi mata ya kamashi,babu shakka Allah ya masa baiwa da managartan mata har biyu,wanda babu abinda zaya ce masa sai godiya,babbar baiwa ce da ba kowa ke samun irin hakan ba,ya kasa jurewa har sai daya ranqwafa cikin sanyi ya sumbaci goshinta,duk da barci ya soma fusgarta amma ta jiyoshi,taci gaba da sakin ajiyar zuciya har baccin yayi awon gaba da ita.
Tunda ta koma bangarenta ta sake gyarawa islaha jikinta ta kaita bedroom dinta ta kwantar sai ta miqe ta zauna
"Mommy mu koma gun momma" sun riga da sunyi barci kema ki kwanta kiyi"sai ya maqe kafada cikin shagwaba
"Mommy" yatsanta ta dora kan lebanta tare da zaro mata idanu
"Banason shirme,c'mn ki kwanta nace miki" tilas ta koma ta kwanta tana sonyin kuka.
Dauke idonta tayi daga kan yarinyar bayan taga ta kwanta,wayarta ta dauka ta kamo suratul baqara ta dan rage volume ta ajjiye kan bedside drower ta kana ta miqe ta shige toilet ta daura alwala,ta jima saman abun sallar tana bin sautin karatun wata nutsuwa na saukar mata,ta tabbatar tayi abinda ya dace kuma tana da yaqinin Allah bazai barta taji wani radadi ko dana sani ba,kayi abinda ya dace da sai Allah ya tsaya maka,ko sanda ta kwanta kan gadon bata fasa bin karatun ba,sautin na ratsata nutsuwa na saukar mata,sannu a hankali bacci ya sureta ba tare data sani ba cike da nutsuwa.
Har ya gama shirin fita masallaci bata sani ba,sai lokacin ya tuna aqulle suke,laluba ma'ajiyar maqullan gidan yayi yayi sa'a ya samu guda daya da shi yayi amfani ya fice.
A hankali ta bude idanunta da suka daddaure,ta juya idanunta ta qarewa dakin kallo,bata ga alamun yana ciki ba,miqewa tayi ta lallaba ta sauka daga gadon ta fice daga bangaren baki daya.
.
Sau uku yana gwada spare key don bude bangaren nata amma yaqi buduwa,alama ce ta cewa ta bar wani key din kenan jikin qofar,tausayinta ke ratsashi,yaso ace ta bashi damar lallashi,ko ba'a gaya masa ba jikinsa ya bashi tana can tana kuka ne.
Qarfe goma ya shiga sashen ta,a gaban dining ya sameta tana shirya abinci,tayi kwalliya kuma kyau cikin dinkin material riga da zani,ta daga kai suka hada ido,sai tayi saurin kau da kai jin gabanta na faduwa,ya isa inda take din ya janyota ta fada jikinsa ya matseta gam,ta saukar da ajiyar zuciya tana gaidashi tare da sake shigewa jikinsa,ya amsa sannan yayi kissing lips dinta yana qorafi
"Ko ki leqo ki dubani bayan ke din mai laifi ce ko?" Ya fada yana dan mintsilarta a kafada,ta saki dariya cikin son basar da maganar,don tasan qorafin kullesun da tayi jiya zaiyi
"Yanzun nake shirin kiranka dama,na gama shiryawa zan wuce"
"Zuwa ina" ya fada bayan ya dagota yana duban fuskarta
"Qoqi mana,ka manta yau za'a karbi lefan alawiyya(qanwarta)" kai ya gyada yana shafa sumarsa
"Ok...ok,haka ne fa,amma da dai kin haqura angel ina da....." Da sauri ya katseshi ta hanyar bubbuga qafanta a qasa
"Haba dear,da kanta fa ina cewa ta gaya maka tun ran daurin aurenku,kuma kaga nice babbar yaya ya kamata ace ina gurin"
"To Allah ya kiyaye hanya,qarfe nawa zaki dawo" tadan yi far da ido alamun tunani sannan tace
"Ko bayan magariba ne pls dear.....ko kazo ma kawai mu dawo tare?" Ta fada cikin sigar tsokana tana kanne masa ido daya,murmushi kawai yayi tare da jan kumatunta,qimarta da yake qara gani a yanzun tafi gaban haka,ba kowacce mace bace zata iya yin abinda tayin,wani girma tare da qauna ta musamman ta sake samu daga gareshi,ita ta zama silar dawowar farinciki cikin rayuwarsa,ta zama silar mallakar abu mai daraja da tsada a duniyarsa
"Duk yadda my angel tace" juyi tayi jikinsa tace
"Thnaks abban islaha" sannan ta miqe tana daukar mayafi da jakarta dake saman kujera tana cewa
"Ga breakfast dinku nan na sallameku,ka gaida sisi kace na dauke mata basai taje ba" shiru yayi ba tare da yace komai ba,sai hannu da yasa ya amshi jakar hannunta da zummar yi mata rakiya
"Ina kuma islahan?"
"Wai,ai tun safe safina(daya qanwar tata)tazo ta dauketa zata rakata karbo kayan snacks na baqi,daga nan kuma naji shiru nasan qoqin suka wuce", driver ne ya jata suka fice daga gidan sannan ya juya ciki.
Sake komawa yayi karo na hudu don sake gwadawa,cikin sa'a ya samu ta bude,ya tura ya saka kansa ciki,shiru bangaran haka nan bata falon,ya sake shiga yana kallon dakunan baccin dake jere har zuciyarsa tafi karkata ga guda daya wanda ke saitinsa kai tsaye ya nufi ciki.
Tana zaune takure kan abun sallah,tunda tayi wanka tayi sallah take zaune a gun,tsabar kukan da take ya sanya mata wani shegen ciwon kai,duk yadda taso taji haushin rayyan kuma zuciyarta taqi aminta,ta kasa jin haushin nasa yadda duk taso cusawa zuciyarta,tsayawa yayi yana kallonta hannayensa harde a qirjinsa kafin ya taka sannu a hankali zuwa gabanta,zaman dirshan yayi har gwiwarsa na taba tata wanda hakan ya sanyata dago kai tana duban wanda ke gabanta
.
Yatsunsa ya sanya ya soma share mata hawayen dake malala kan fuskarta,sai ta sanya hannunta ta riqe hannun nasa gami da kau da fuskarta,cikin rawar murya tace
"Tunda Allah yasa ka samu cikar burinka ka sallameni rayyan,ka fidda ni daga inuwarka" zame hannun nasa yayi ya kama dukka hannayenta ya sanya cikin nashi
"Bana son wannan zancan raiha bana sonshi,kina qona zuciyarta kina cutar da ita,kinfi kowa sanin ba don haka nake sonki ba,ba wannan soyayyar nake miki ba,me yasa kike neman sauyawa daga raihanan da na sani,so silent,innocent girl,mai good characters?,kina sanya zuciyata tana aikata abinda bai kamata ba,kinga jiya kin jawo na kusa cutar da ke,inda wani mummunan abu ya faru da ke kina zaton zan iya yafewa kaina?,ina sonki ina kishinki,so please nd pls na roqeki ki tsaida duk wani abu da kike tunani,wadda kike son farantawa ba ta haka takeso ki faranta mata ba,nine mai faranta mata ke kuma ki faranta min"
"Amma dai kasan cewa bai kamata......"
"Na gaji na gaji da jin kalmar bai kamata ba,bamu kyauta ba,bai dace ba and so on" ya fada a dan tsawace,sai ta saki sabon kuka,janyota yayi jikinsa yana dan bubbuga bayanta cike da tausasawa tare da sauke ajiyar zuciya,saita tsinci kanta da ci gaba da kwanciya cikin jikin nasa tana fidda hawaye.
Tsawon mintina ta diba tana yi ba tare da ya hanata ba kana daga bisani da yaga bata niyyar tsagaitawa ya dagota yana dubanta
"Is ok bana son sake jin sautin kuka,kinyi sallah?" Kai ta gyada masa
"Wanka fa?" Kamar tayi banza da shi sai kuma ta sake daga masa kai,miqewa yayi ba tare da yace komai ba ya shiga toilet dinta ya hada ruwa mai zafi sannan ya dawo ya sameta inda take zaune
"Oya muje ki sake wanka ki gasa jikinki" dagowa tayi tana dubansa baki sake duk da bata iya ganinsa tar saboda hawaye da ya cika idanunta babu glass kuma a fuskarta,yana nufin shi zaya yi mata wanka ma?,ganin tayi shiru ya sanya ya sake maimaita maganarsa,sai ta sauke idonta qasa tana tura baki hawaye na sake sintiri kan fuskarta
"Kai baka jin kunyar sisi na?"
"Kada ki sake min maganar wani idan muna tare idan ba haka ba ranki zaya baci,get up!" Ya fada cikin daga murya,tsoro ya kamata ganin yadda ya tsare gabas da yamma ya kafeta da wani kallo da ya yiwa nata idanun kaifi wanda ya sanyata ba shiri ta miqe tsaye,wani sashe na zuciyarsa cike fal da tausayinta,amma ya fuskanci idan ba hakan ya biyo mata ba bazai yiwu ta saitu yadda yakeso ba,Allah ne ya soshi ya tuna cewa raihanan gwanar tsoro ce,bata son tsawa ko fada ko kadan.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:51 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_______________________
*Daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace"mafi yawancin abinda yake shigar da mutum aljanna sune:tsoron Allah da kyakkyawar dabi'a"*
_______________________
*Babi na arba'in da hudu*
Gefan gado ta samu ta zauna ba tare data ce komai ba ko ta yi wani abu ba,yayin da shi kuma yaci gaba da kallon abarsa yana jin wani abu na ratsa dukkan jikinsa,ya fuskanci zamansa zaya hanata sakewa tayi shirin kwanciya hakan ya sanya ya dauki littafinsa a hannu ya fice daga dakin,ganin ficewarsa ya sanyata sakin ajiyar zuciya tare da miqewa cikin sanda ta tura qofar dakin ta sanya mata key ta zareshi ta dorashi saman mirrow sannan ta shige toilet.
Sai data gama komai ta sanya kayan bacci doguwar riga mai gajeran hannu,ta shafe jikinta da humra sannan ta haye gadonta bayan ta kashe wutar dakin.
Tana gab da kammala addu'o'in baccinta taji ana qoqarin bude qofar,ta saki dan siririn murmushi don tasan ta riga ta rufe saboda haka bata damu ba ta gama addu'arta ta shafa,tana shirin jan bargo ta rufa ya turo qofar dakin,gabanta ya fadi sai ta kasa komawa ta kwanta,ya kunna wutar dakin idanunsu suka hadu,wani kallo yake jifanta da shi mai cakude da murmushi kan fuskarsa,a hankali ya tako zuwa gefan gadon ya haye kana ya zauna tsakiyarsa,yana mata kallon qasa qasa yace
"Wai anya kuwa ke din ba amaryar qauye bace?,har da wani rufewa miji qofa uhmmmm raiha?" Ya qarashe maganar da tambaya tare da sanya hannunshi yana qoqarin janyota jikinsa.