← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 66

Sashe 62

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anan ya narke mata,sai data masa duk wani abu da rumana ta sabar masa,kama daga wanka tayashi shiryawa har ma da qarin zaba masa kayan da zaya saka din,ganin an kusa kiran isha'i ya dubeta fuskarsa fes da walwala
"Ki jirani naje sallah na dawo sai mu wuce gun sisinki muci dinner ko?" Ya rada mata a kunnenta,ta dan janye jikinta saboda yadda salin maganar tasa ta sanya tsigar jikinta tashi tana dubansa
"To" kawai tace masa,ya dauki carbinsa mai dannawa ya maqalawa yatsansa ya fice.

Tana idar da tata sallar ta wuce wajen rumanan,don bata son ya iskota bare ya matsanta mata kan dole sai sun jera sun tafi tare don tana kunyar hakan.

Hira ya tarad da suna yi,ya jefa mata harara ya gayada kai tare sa daga hannusa ya mata alamar zan kamaki ne,sai ta kawar da kai gami da basarwa cikin zuciyarta tana sake tuna tsiyar da zata qulla,don ko bai fada ba idanushi da kallon da yake mata ya gama gaya mata fitinar da ya tanada.

Kamar yadda suka aaba cike sa raha da barkwanci suka ci abincinsu,ita tafara zamewa da zummar tana zuwa ta barau falon suna kallon wani film a tashar mama africa,tana shiga falonta ta mayar da key ta rufe ta bar key din a jiki ta yadda ba wani key da za'a saka a sake bude qofan,ta fada saman kujerarta bayan ta kunna kayan kallonta taci gaba da kallin film din da ta barsu suna kallo saboda ya mata kyau,a nan barci ya kwasheta ba tare data sani ba.

Cikin barcinta ta soma jinta cikin wata duniya,a fari taso ta tsorata amma qamahin mayen turaren baccinsa ya gaya mata waye,cikin fargaba da tsoron rayyan din ta sakar masa kuka sosai wanda shi ya taka masa birki,murmushi ya saki mai hade da 'yar dariya sannan ya lakace mata hanci
"Raiha raguwar kawai" ya fada yana janta cikin jikinsa ya matseta gam yana sauke numfashi,luf tayi a jikinsa tana jin dadin yanayin tare da rage farashun kukan nata ahankali kadan kadan har wani dddadan bacci wanda ya sakata sake qudundunewa jikin rayyan din yazo ya saceta bata sani ba,shi kuwa sake rungumeta yayi yana sakin murmushi din ya tabbata da idanuwanta biyu ba zata riqeshi hakan ba.

***************

Randa ta cika kwana hudu ta gama lissafinta na cewa ta fita girki tunda kwanan zawarawa zatayi kwana uku kenan,ta kammala sallar magariba kenan ta fito falo tana jiran isha'i,sanye take da dogin wando pink colour sai rigar itama pink 'yar cikin mai gajeran hannu iyakarta saman cikinta wadda daga gabanta aka yiwa don furanni ash mai qyalli,ta saman kuma ash ce mai tsawo har gwiwarta,gabanta gaba daya abude yake hakanan tana da dogayen hannuwa pink colour,ba qaramin kyau kayan suka mata ba,hade rai tayi data ganshi yana fitowa daga kitchen dauke sa kofin qarau wanda ya cikashi da fresh milk da zuma,itakam tsoronsa yanzu take ji,tsoro ma take kada gaba yafi qarfinta,cikin sauri tace da shi
"Ka manta yau girkin sisi na ce" sai ya qaraso kusa da ita tamkar zai fada jikinta ya kashe mata ido daya hadi da daga mata girarsa yace
"Raihata ba bazawara bace ko kin manta?,hakanan siain tata ma ta san da hakan,ta kuma san kwanaki bakwai sisinta zatayi,amma....." Ya dan dakata kadan yana lalubar qwayar idanunta sannan ya dora
"Bansan ya akayi haka ta kasance ba duk da rayyan dan gatan Allah ne,sisinki tasan ke wace ya akayi sweet rayyan bai sani ba?,ummmm" ya qaraahe maganar yana kama qugunta tare da mannata ajikinsa ya kuma hade fuskarsu guri guda har hancinsu na gogar na juna,gama daya ya gama kashe mata jiki,ba zata iya wata magana ba,rawa jikinta ya soma har ya fuskanci haka,sai ya saki dariya ya dago fuskarta yana kallonta idanunta ta runtsesu gam
"Shikenan,adana amsar tambayarki,zuwa anjima kya gaya min,ungo qarasa shanye wannan,saboda anjima ko......" Ya qarashe gaya mata maganar cikin kunnenta wanda hakan ya sanyata saurin bude idanunta da sukayi narai narai kamar zata faahe da kuka tana kallonsa,murmushi ya saki ya kai mata cup din bakinta tare da fara zuba mata madarar yana cewa
"Ba wannan raihar nake son gani ba,jarumar raiha nakeso,wadda zata karbi mijinta duk yadda yake,banason ganin karaya gunki tun yanzu ubmm,saboda rayyan mayen raihana ne kin manta tun a baya,so kiyi haquri da shi hakanan" bata ce komai ba ta bude baki ta kurbe sauran madarar,tasa harshenta tana lashe lebanta,ya sa mata ido yana kallonta sai shima ya sanya harahen nasa yana tayata lashewar wanda sauran kadan hakan ya zubar da su a qasa rayyan din yaui jarumtar tararsu,suka hada ido sai duka dariya ta kubce musu lokaci guda,ta cusa kanta a qirjinsa tana boye fuskarta sabida wata iriyar muguwar kunya da ta kamata.

*************

Kwanaki bakwai rayyan din yayi mata kamar yadda addini ya tanada,cikin kwanakin rayyan din ya sake mata wani mugun tasiri cikin rayuwarta,ya sake yiwa zuciyarta wata babbar illa a sonshi,yayi nasarar tone duk wami sirri da tayi niyyar boyewa dangane da irin tsntsar so da qauna da take masa,a kullum kwanan duniya bata gajiya da yiwa rumana addu'a data tsamo rayuwarta daga halaka,sai yanzu take sake gasgatawa rayuwarta ba zata taba zama dai dai ba ba tare da rayyan ba,wani sone ashe boye can qasan birnin zuciyarta mai tarin yawa wanda tsantsar QAUNA ABOTA SON SADAUKARWA DA DANGANTAKA suka taka muhimmiyar rawa wajen boyeshi,tabbas babu shakka alkhairi danqo ne baya faduwa qasa banza,idan da tabi son ranta abaya qila da zuwa yanzu dukkansu basu samu wannan farincikin ba,duk wanda yayi alkhairi zaiga alkhairi a can gaba,walau a nesa cikin rayuwarsa ko a kusa.

Randa ya koma dakin sisin nata ita da kanta ta musu sai da safe,data dawo bangarenta taji kewarsa nason kamata sai tayi shirin kwanciya kawai,ta kunna karatun qur'ani abinta,haqiqa maganar Allah gaskiya ce da yace DA AMBATON LLAH KADAI ZUKATA KE SAMUN NUTSUWA,mafi akasarin mutane dakan tsinci zuciyarau cikin wani hali na qunci ko quntata sun saki Allah ne ko hanyar Allahn,tilawa tayi mai yawa kafin bacci ya sureta,cikin aminci farinciki da nutsuwa tayi cikakken bacci mai cike da kwanciyar hankali.

Qarfe tara ta kammala yi musu break fast wanda tun jiya ta cewa rumanan ba ita ba shiga kitchen da safe gobe itama amarya take,wanda ta musu ma na kwana bakwai Allah ya bada lada,zuwa goma na safe ta kammala komai ciki harda wanka da kwalliyar data cakare cikin wata shadda ja wadda aka yiwa adon stone work baqi,abinka da chaculet colour sai tayi masifar haskata,bata je ganin ko sun taahi ba don kada ta takurasu,sai ta kunna kallo ta kama tashar arewa arewa 24 tana kallon maimaicin shirin haske matan arewa
.

Tare suka shigo hannyensu sarqafe da juna
"Sannu da hutawa amaryarmu raiha" rumana ta fada da yanayin salon da rayyan kan kirata da shi,dariya ta saki tana juya ido sannan tace
"A ga wace amaryar dai tsakanin ni da ke" dariya sukayi baki daya,raihanan ta dora da cewa
"An tashi lpy sisi"
"Lafiya qalau,ya kwanan kadaici"
"Ban yishi ba" ta fada tana miqewa tare da gyara daurin dankwalinta sannan tace
"Muje mu karya har lokaci na shirin qwacewa,ko yau mijin naki ba fita zaya yi ba?" Ta qarashe cikin salon tsokana,rayyan dake harde da hannayensa yana faman kallon adonta tun dazun yace
"Me ruwanki da ni?,tunda ko arziqin gaisuwa ban samu ba" itakam wani kunya da nauyi ne ya hanata ce masa komai,rumana tayi gaba taba cewa
"Me zaya hana,bari na fara hada masa tea ya dan sha iska"sai ta danyi murmushi sannan ta qaraso gabansa ta rage tsawo tace
" barka da warhaka yallabai,Allah ya taimakeka"lumshe ido yayi,kirarin ya masa dadi,sai ya dan janyo ta jikinsa yana cewa
"Wannan irin gaisuwa haka raihata,kada fa ki rudani" ta janye jikinta da sauri tana duban sashen da rumana ke tsaye can wajen dining area tana hada masa tea tare da amsa kiran da ya shigo wayarta,sai tayi fari da idanunta tare da harde hannayenta itama tana dubansa,murmushi yayi sannan yace
"Na rasa gane wanda yafi wani iya ado tsakanin ke sa sisinki,any way ina son aci gaba da wannan kwalliyar,tana burgeni"
"An gama yallabai" ta fada tana dariya ganin yadda ya wani langabe yana sake bin kwalliyar tata da kallo har sai da ta tunkuda qeyarsa cikin salon wasa ta dan daga murya tace da rumana
"Zo ki dauki mijinki don Allah hakanan"
"Ko baki fada ba" inji rumana tana dariya itama.

Da yammaci tana qoqarin shiga kitchen raihanan ta fado cikin kitchen din,ta shirya tsaf cikin atamfa riga da zani simple,kanta lullube da mayafi hannunta saqale da jaka,dubanta rumana tayi bayan ta dora tukunya saman gas
"Hala fita zakiyi"
"Eh,amma zuwa magariba zan dawo in sha Allah"
Tayi mata Allah ya tsare sannan ta fita.

Batasan ma islaha taje daukowa ba sai da suka zo cin abincin dare,ta shigo riqe da hannunta,yarinyar tayi kyau cikin shigar riga da wando
"Eh lallai,abun ma 'yar wariyar launin fata ce ko?,hala daddy da hadin bakinka ma" gira ya daga mata yace
"Yes......haka kawai ki bar mana gida shiru bayan muma muna da buqatarta" murmushi kawai tayi daga bisani suka soma cim abincin wanda islaha duk ta buwayi kowa da karadi raihana na biyewa takwarartata.
.
****************

Ranar daya ga watan daya itace ranar da ta kama rayyan zaya bude katafaren kamfaninsa wanda a qalla ya kwashe kusan shekaru shida yana gina shi.

Tamkar 'yan biyu haka suka fito a ranar,komai nasu iri daya ne,hatta da jaka takalmi zuwa sarqa da dan kunne,ranar ba qaramin burge mutane sukayi ba,sai wajen la'asar suka dawo gida,wanda nan ma sun dan taho da mutane saboda washegari rayyan ya shirya musu gagarumar walima da za'a gabatar a cikin gidan,qannan rumana ne sai kausar da meela,wannan karon kam raihana ma ta samu baqi qannanta su zainab tun daga maiduguri kasancewar lokacin yayi daidai da hutun makaranta da aka nawa dalibai,amma ta barsu da qyar zasuyi kwanaki uku.

Tun dazun meelan ke bin rumana da kallo ganin yadda mu'amala ke gudana tsakaninta da da raihana tamkar wasu 'yan biyu,kishi takeji sosai cikin ranta tare da ganin baike da rashin wayo na rumanan,tana jin idan itace kam qila da ta dade da mutuwa bayan faruwar auren rayyan da raihana.
Chapter 62 · 0% Book details