← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 66

Sashe 29

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yammata ya kuka tsaya daga nan,ku qaraso mana" sukaji muryar amir yana fadi,idanunsa kan raihanan,murmushi rumana tayi sannan suka fara takowa a hankali zuwa inda suke
"Kaidai kawai kace mu sake matsowa ko ka samu damar ganin sahibarka sosai" tamkar ta soki rayyan da mashi a qirjinsa haka yaji,take 'yqr fara'a da farincikin da ya samu sukayi qaura,wani kishi ya kamashi,ji yake tamkar yace da su su wuce cikin gida babu halin haka saboda haka sai ya daure fuska kawai
"To laifi nayi,na tabbata kema angonki na da muradin ganinki ko ba haka ba?" Ya qarashe zancan da sigar tambaya sannan ya waiwaya yana duban rayyan,sam tunda yazo ya fuskanci rayyan din ya sauya,amma bai kawo komai ba cikin ransa ganin kusan haka yanayinsa dama yake,sai ya ta'allaqa hakan da cewa qila akwai wani abu daban dake dumunsa.

Kafada rayyan din ya daga hadi da yarfar da hannu "a'ah,wannan ai zancanku ne bana shiga ba" ya fada yana sake duban wayarsa dake tsuwwa da alamu wani kiran ne ya sake shigowa wayar tasa,ya daga wayar ya kara a kunnensa kana ya matsa dan nesa da su,saidai duk da haka yana hango duk abinda ke faruwa.

Mintina tsakani ya sake dawowa yana dubansu amir da mujahid
"Ko na wuce ne ni kadai,su mansur sun qaraso don na fuskanci ku kun samu wani aikin ko?"
"A haba,ai ana tare muje kawai mu sama musu masaukin kada su qosa da jira" inji amir da yake miqawa raihana wayarta dake hannunshi tare da fadin
"Princess zamu je mu dawo,a tanada min abu mai dadi" so take ta maida masa amsa ta irin salon da yayi mata maganar ko don rayyan da yasa musu ido amma sai bakinta yayi nauyi ta kasa illa cewa "to" da tayi tana qoqarin bin bayansu rumana.

Har sun kusa shigewa get din gidan rayyan din yayi kiran rumanan ta koma da baya,kusan minti goma basusan me yake gaya mata ba,hakanan raihanan taji ranta ya dan sosu musamman data jiyo rumanan na qyalqyaltar dariya,sai tayi hanzarin kwabar kanta da zuciyarta,mujahid ne ya dan daga murya yace da rayyan
"Kai man,kaifa muke jira ka ishemu da qorafi kuma kai ka tsaya tsinkar fure"
"Ku tafi mana,ai ba makaho bane mi bare na nemi dan jagora" rayyan din ya fada yana sallamar rumana ya juya gunsu mujahid din yayin da ita kuma ta koma wajensu raihanan.

Ajiyar zuciya ta saki lokacin da suke takawa zuwa cikin gidan,ta lumshe ido kana tace
"Na godewa Allah da ya mallakamin burin raina yaya rayyan,askiya babu abinda yafi soyayya dadi"
"Idan kayi dace da masoyi ba" inji kausar,idanu rumana ta bude tana duban kausar
"Ai duk duniya banajin akwai wanda yayi sa'ar masoyi kamata ko ba haka ba sisi?"ta waiwaya daya barin nata tana jefa tambayar ga raihana,wadda tayi shiru tanajin yadda bugun zuciyarta ke tafiya a hagunce,kokawa take da zuciyarta na kada ta yarda tace zata ji kishin 'yar uwarta,murmushi tayi cike da nuna jarumta da dakiya
" qwarai kuwa sisi na,qyale kausar kawai"
"Ni din ma tsokanarta nake,kowa ya riga da ya sani ai sa'a kam kin yita,saidai Allah ya sanyamu a danshinku"
"Amin wallahi kausar ina muku sha'awar haka" inji rumana.

Jefi jefi suka dinga wuce baqi suna gaisaqa da wadanda sukazo ranar,a kitchen suka tadda ummu tana hada kan kwanukan abincin dare da tuni aka kammala jiran lokacin cinsa kawai ake,sai raihana taji tausayinta,tunda satin ya shigo ita kanta bata samu hutu ba,gashi su ba zama suke sosai ba ballantana su kama mata aikin
"Sannu ummu,sannu da aiki" raihana ta fada cikin qauna tana shigewa cikin kitchen din tare da karbar babban ludayin hannunta da take kwashe shinkafa cikim cooler taci gaba da zubawa
"A'ah raihana,aisai ki bata jikinki,ku da aka yiwa gyaran jiki?'dariya ta danyi
"Lah,sai kace nice rumanan,ai ita kadaice ba'aso ta bata jikinta" murmushi ummun tayi tana kallonta cike da qauna
"Kema Allah ya bada na gari ya nuna mana lokaci dai" kasa amsawa tayi illa murmushi kawai da tayi,daidai lokacin da rumana da kausar suka qaraso don ta barsu bakin fanfo suna magana da wata maqociyar su wadda zata musu friedrice din walimar da zasuyi gobe bayan gama daurin aure saboda gwanace tayi bala'in iyawa.

Sannun suma suka yi mata,raihana ta kammala zubawar ta sauke tukunyar ta tarata bakin fanfo,ummu ta sake matsowa
"Kinga barshi hakanan,ai an kammala komai,kuje ciki umminki fanna ta iso dazun da azahar" wani tsalle rumana tayi tayi waje cike da murnar jin ummin tazo,shiru raihana tayi,take taji jikinta yayi sanyi,farincikin zuwan mahaifiyar tata ya lullubeta har ta rasa me zata yi?sai kawau tace "to" ta wanke hannayenta ta fice a kitchen din
A bedroom dinta ummu ta sauketa kasancewar babu kowa ciki,hajiyan nijer dakinta daban ita da 'yan tafiyarta tace ba zata zauna dakin surukarta ba,rumana an baje anata kwasar hira da labarin maiduguri,tana ta tambayar mutanen da ta saba da su da wadanda ta sani ummin kuwa ta biye mata sunata hirarsu kausar na tayasu.

Gefen ummin nata ta samu ta zauna,fuskarta qunshe da murmushi tace"sannu da zuwa ummi"
"Yauwa raiha" ta fada tare sa sake maida kanta gasu rumana,sai ta waiwaya gun qannenta zainab da amira dake ta faman murnar ganin yayar tasu,ta yafitosu suka dawo kusa da ita nan suka fara hira tana tambayarsu wasu al'amura,musamman kan karatunsu,alhmdlh komai yana tafiya fiye da yadda take zato,don mutumin da ummin nata ke aure yanzun mutum ne mai wadata ga matuqar sauqin kai,ya rasa matarsa ne ta fari wadda ta rasu data haifa masa samari har uku.

Basu qara minti goma ba rumanan ta miqe tace bari suje su fara shirin yin sallah magariba ta gabato suka fice,zamewa tayi daga tsakiyar su zainab din ta dawo gefan ummin sosai,a hankali ta dora kafadarta saman ta ummin nata
Haqiqa uwa daban take,wani karyewa taji zuciyarta tayi sai kawai ta saka kuka,zainan da amira sai suka saki baki suna kallonta
"Me haka kuma raihana?,meye akayi miki na kuka da girmanki?" Inji ummin ta tambayeta,kasa amsa mata tayi don kota bude bakin bata da abinda zata gaya mata,ganin bata amsa mata din ba ya sanya ta qyaleta ba tare data sake ce mata komai hakanan bata hanata yin kukan ba,don tana jiyo qamshin damuwa mai yawa cikin kukan nata,amma ko damuwarce bata son tambayarta bare ta bata hanyar kawo mata qarar wani idan ya bata mata,tayi tsit tana sauraren sautin kukanta har sai data more da kanta,a hankali taji zuciyarta na yin sanyi,quncin daya tare mata a qirji ya sassauta,ta bude bakinta muryarta can qasa tace
"Kukan murna nake ummi,murnar ganinki,yaushe rabonki ummi da kano?" Murmushi kawai tayi sannan tace
"Raihana,har yau akwai wautar 'ya'yan fari tattare da ke,ke da zakiyi farinciki sai kuma ki buge da kuka?,Allah ya shirya".

Dole ta dauki dangana ta dorama zuciyarta don ta bawa ummin da sauran qannen nata jin dadin ziyartarsu da sukayi,tare sukaci abincin dare rumana nata mata tsiya yau ta gujeta ko?,murmushi kawai tayi mata
*************

Qarfe tara ne na safe amma gidan cike yake da 'yammata qawaye da 'yan uwan rumana,abinka da mai yawan qawaye da mutane kala daban daban.

Tana daga kan gadonta tana kallo da saurarar duka abinda ke faruwa cikin dakin dake cike da 'yammata,har yanzu kayan bacci ne jikinta ta kasa tashi balle ta tabuka komai,tsananin faduwar gaba take ji da wata iriyar kasala.

Rumana wadda ta kusa shafe awa daya gaban madubi ana mata makeup ta juyo ta dubeta
"Sisi wai ba zaki tashi hakanan ki shirya ba?,baki gani gidan sai sake cika yake,kuma akwai abubuwa fa da ke zakiyi su" murmushi ta danyi sannan tace
"Afuwa sisi,yanzun zan tashi in sha all
Cikin minti goma sha biyar ta fito daga wanka,shadda ce iri daya suka dinka ita da rumanan maroon colour da aka yiwa aikin stone work daga sama har qasa da milk da maroon din stones,banbancin kawai raihana doguwar riga ce rumana riga da skert ne,miqewa tayi daga kan kujerar bayan an kammala yi mata kwalliyar tana duban raihana
"Bismillah ni an gama min" langwabar da kai raiha tayi tana shirin yin qorafi,sarai rumanan ta gane me take son fadi saboda haka tayi saurin rigata ta hanyar dora yatsanta kan lips dinta tace
"Shshshsh just obey before complain,yau rana ce ta musamman,saboda haka dole ki zauna amiki makeup malamarsu,oya bismillah" hakanan ta zauna saman kujeran yayin da sauran 'yammatan suka sa dariya suna tsokanar raihana kan rashin son makeup,itakam murmushi kawai ta bisu da shi da batason cewa komai,kafin mai kwalliyar ta fara saidata roqeta lite make up zata mata don Allah.

Cikin minti arba'in saiga raihanan fes,tayi wani kyau na daban,kai kace itama amaryar ce musamman lokacin da aka yi mata daurin dankwalinta yabi kanta ya zauna gwanin sha'awa
"Wow,wow sisi na,gaskiya ke ta dabance shi yasa bakison amiki make up wallahi,sai duka na raina kyan mu" cewar rumana tana qarewa raihanan kallo
"Nima haka zance kika riga ni" inji umaima cousing din rumana,masha Allah haka kowa ke fadi,camera umaiman ta fidda ta fara musu hotuna su biyun,sai suka tashi tamkar wasu tagwaye masu mabanbantan kamanni.

Shigowar ummi dakinne ya katse musu hotunan da sukeyi,ita kanta sai data tanka kyan da sukayi,sosai yaran nata suka burgeta,sai ta tsinci kanta cikin zuciyarta tana mai addu'ar Allah ya fiddawa raihanan itama miji na gari nan kusa
"Kizo ki karba muku abincinku kafin anjima ki kasa fita don tsakar gidan namu ya fara cika" inji ummu tana duban raihana
"To ummi" inji raihanan tana yafa milk din mayafinta daya dace da kayan tabi bayan ummun.

Aikam dai tsakar gidan nasu masha Allah,don har duburcewa taso tayi ganin yadda ido yayo kanta,hakan kuwa baya rasa nasaba da saninta da sukayi ba gwanar qyale qyale bace sai yau gashi bisa fuskarta,da kuma yadda shigar tayi musu kyau,kusa da hajiya babba ta tsaya kanta qasa tana murmushi jin yadda hajiyan keta tsokanarta wai yau 'yar tsalle ta koya mata rawar kan kwalliya.
Chapter 29 · 0% Book details