← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 66

Sashe 57

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta yiwa 'yan rakiyar raihanan rakiya bangarenta ta wuce don ta sallami baqinta,sai data tabbatar ta sallami kowa sannan ta shiga kintsa bangaren nata kasancewar ba wani baci yayi mai yawa ba don taron kusan duk gidan abba yusuf aka yishi,wanka ta yiwa islaha dake faman gyangyadi ta sauya mata kayan bacci ta kwantar da ita sannan itama ta shiga ta sake nata wankan.

A kasalance take shiryawa gaban madubi wanda hakan ya dauketa mintina masu tsaho bata kammala ba,tana gaban drower rana fidda kayan da zata sanya taji dirin mota,ta ajjiye kayan ta yaye labulenta ta leqa,motar rayyan ce ke shigowa ita kadai,sai ta saki labulen ta koma ta hau shiryawa a gaggauce.

Inda suka fita suka barta bata ko sake motsawa daga gurin ba,bata motsa ba sai da taji shigowar mota gidan,ta miqe sannu a hankali har ta isa ainihin qofar falon ta turata sannan ta murza maqullin data gani jiki ta kulle,bata cire key din na ta barshi a jiki kai tsaye ta wuce daya daga cikin bedroom din da aka fara shigar da ita ta fada saman gadon ta tana ci gaba da matsar hawaye.

Kafin ya kai ga shigowa har ta kammala shiryawa,a falo sukayi kacibus da shi yana shigowa hannayensa dauke da ledoji,yayi kyau abunsa cikin yadin kufta ruwan bula wanda yasha aikin sarauta a jikisa,yadda yake mai kyau haka komai nashi yaje,daddadan qamshi ke tashi a jikinsa,ta dan zuba masa ido sai taga kamar yau din an qara masa kyau,wani abu ya taso mata tayi hanzarin danneshi,murmushi ya sakar mata lokacin da take qoqarin amaar ledojin hannunsa ta zubesu saman table,ya sanya hannunsa ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya,a hankali yace
"I missed you my angel,yauahe rabon da naji duminki,haka kawai kin hana mana zama"boyayyar ajiyar zuciya ta saki sannan tace
"Cikon farinciki nake nema mana ai babu komai din na sarayar mana da wani dan qanqanin lokaci namu" yatsansa ya dora saman lips dinta kana daga bisani ya sauke
"Ina islaha?"
"Tayi bacci,muje kaima kayi wanka don nasan a gajiye kake" ta fada tana miqewa daga jikinsa,babu musu yabi bayanta har cikin dakinta,a nan ta hada masa ruwan wanka,sai wani narke mata yake yaqi yin komai shi daya,ita kuma ta biye masa har ya shirya ta zabi wasu kaya cikin drower dinta ta miqa masa,lallausan yadine mai azabar kyau da ka tsarawa dinki mai kyau,sai ya bita da kallo yana neman qarin bayani
"Su zaka sanya kaje gun amaryarka da su" tsaki ya saki sannan ya wurga mata harara,ya miqe ya zari jallabiya daya cikin irin kayansa da yake bari cikin dakinta ya zura
"Ni bansan ma baki sona ba sai yau rumana"
Murmushin yaqe kawai ta saki,wato baisan wayeshi cikin zuciyarta ba shi ya kaishi gangancin furta haka,yayi maganar ne yana zura slippers a qafarsa zai fice daga dakin,da sauri ta sha gabansa,idanunta cikin nasa
"Kana so ka nuna min cewa ni ba kowa bace kawai gurinka ya rayyan" ta fada ashagwabe idanunta na tara qwalla,hannunta ya riqe don baison kukanta don bata cancanceshi ba
"Shikenan dauko min in saka indai kayane" ita ta dinga ware maaa tana miqa masa yana sakawa har ya kammala,wani kyau taga ya sake mata har ta tsaya kallonsa,yatsansa ya saka saitin idanunta kamar zai tsole mata ido,haka ne ya sanyata sakin murmushi tana fadin
"U r d best husband in d world" sai ta fada jikinsa ya rungumeta tsam,hawayen da taso boyewa suka gaza boyuwa,da sauri ta hau sharewa don kada ya gani jin yana niyyar dagota daga jikinsa.

Idanu ya zuba mata yana kallonta,ta qaqalo murmushi tana cewa
"Muje ya rayyan na raka ka kada sisi ta gaji da jira" tsam ya hade ranshi tare da girgiza kai
"Babu inda zanje kuma kada kice zaki tursasani wallahi" ya saketa ya wuce falon,ya fadi hakan ne don ita din,ya gama karantarta tunda dazun da yashigo.

Kanta ta sake qarfafawa gwiwa ta iskeshi zaune a falo hannunshi dauke da remote yana jujjuya tashoshin tvn,gefansa ta zauna ta fara zuba masa qorafi da mita har sai da ya gaji
"Tunda kin matsa jeki ki kirawota kuzo nan tare"
"Amma ai ba haka akeyi ba kai ya kamata kaje ban......"
"Shshshshs" ya fada yana dora yatsansa saman lebansa
"Idan hakan bai muku ba to ku qyaleni naji da gajiyar dake damu na" ganin yadda ya dinke fuska tsaf ya sanyata miqewa ta nufi sashen raihanan.

Ta dade tana buga qofar saidai ko kotsin mutum bata ji ba balle ta saka ran za'a bude,har ta gaji ta soma da kiran sunanta amma shiru kake ji,tsori yadan shigeta ko wani abu ne ya samu raihanan,da sauri ta juya ta koma bangaren nata ta gaya masa,baki taga ya tabe ya janyota jikinsa ya hau bude ledojin da ya shigo da su masu dauke da gasassun kaji a ciki da fresh milk ya ciro tsokar ya tura mata a baki,sai ta saki baki tana dubansa bayan ta hadiye wadda ta tura matan tace
"Amma ya rayyan bakaji me nace ba,naje inata bugu ba alamar da mutum aciki"
"To me kike son nayi,so kike naje in balle qofar?"
"A'ah,amma a qalla ai tunda kana da muqallanmu kaje ka dauko mu bude muga lafiya"
Shiru yayi mata ba tare daya tanka mata ba yaci gaba da zare tsokar yana bata shima yana ci.

Sai da suka kammala taga yana shirin shigewa bedroom dinta yasa ta dubeshi
"Ina kuma zaka haka?"
"A irin wannan lokacin me ya kamata nayi,bacci ko?"
"Eh zakayi amma ba'a nan dakin ba,ko ka manta daren yau waye kai?"
"Ke kika sani tunda ke kika qulla abunki" ta fuskanci da gaske yake,yau dramer sukeso lallai a tada cikin gidan daga shi har raihanan sabida haka tayi wuf ta shige dakin ta saka maqulli ta zare shi ta jefa saman madubinta kana tadan daga murya tace
"Allah ya bamu alkhairi"
"Dadin abun dai nima ina da nawa dakin ai" taji ya fada,ta maqullin take leqensa yana zaune abinsa saman kujera ya sanya t.v a gaba,tun tana leqensa har bacci ya fara rinjiyarta ta kasa taahi saboda tsabar gajiya.

****************

Gab da asuba rumana ta farka firgigit gabanta na bugawa,sai kuma ta jita kamar a jikin mutum,rayyan ne ke rungume da ita yana baccinsa hankalinsa kwance,babu shakka maqullinsa spare yaje ya dauko ya bude dakin ya shigo bayan tayi bacci,sai ta hau tureshi wanda hakan ya sanyashi farkawa,sai ya sake janyota jikinsa idanunsa lumshe da alama baccin bai isheshi ba cikin muryar bacci yaje rada mata wata magana,laqwas tayi bata sake motsi ba cikin qanqanin lokaci baccin ya sake awan gaba da su saboda gajiyar dake jikinsu.

Ita ta sake rigashi tashi,lokacin shida saura,salati ta saka tana qoqarin sauka daga gadon,idanunta suka sake fadawa kansa,fuskarnan tayi wani kyau,tadan zuba masa ido tana jin qaunarsa na sake ratsata,sai kuma ta tuna abinda sukayi,ya kwaso kwanan raihana ne fa ya kawo mata.
.

Har suka idar da jam'in sallar da sukayi fuskarta na a hade tsaf,taqi koda kallansa,shima yasan ko yayi magana qorafin da zata masa hakan ya sanya bai ce mata komai ba,haka nan itama bata ce mishi uffan ba tunda ya riga da yasan abinda ya aikata din.

Daga nan miqewa tayi ta sake gyara bangaren nata sannan ta zarce kitchen ta shirya breakfast,cikin wasu sabbin warmers ta zuba su sannan ta ware wani daban ta zubawa raihana sannan ta wuce toilet don yin wanka.

Can ta tarad da shi ya hada ruwa cikin bathtub yana kwance ciki,ya daga kai ya kalleta sai ta juya zata fita,ya sanya hannu ya fincikota ta fado cikin ruwan,zatayi magana ya hade bakinsu guri guda ya hanata cewa komai,tare sukayi wankan suka fito,duk wani daure fuskarta sai da ya sanyata dariya har da qyaqyatawa,ya riga da yasan kan kayansa,rayyan ba baya bane wajen sanin kan soyayya,tare suka gama shiryawa har lokacin islaha nata barcinta,ya sake komawa gadon yana dubanta idanunsa a lumshe
"Ba zaka karya bane,sha daya fa ta kusa"
"Bacci bai isheni ba madam, a barni na qara"
"Is ok" ta ce masa ba tare data matsa ba ta fita,don tasan yau me ta qulla musu duka shi da raihanan sai tayi maganinsu.

Kitchen ta shiga ta hada kayan break fast din cikin kwando ta nufi sashen raihanan,bugu biyu kawai tayi aka bude,raihanan ce cikin shigar shadda orange doguwar riga wadda aka yiwa adon stone work da lemon green,kanta yane da siririn mayafi lemon green,duk da ba wata makeup tayi ba kamar rumana ba qaramin kyau tayi ba,murmushi ta sakarwa rumanan duk da itama tana son maida mata martani amma ta dake ta hade rai saboda son nuna mata laifin da tayi,ta rabeta ta wuce,kan daining taje ta ajjiye kayan sannan ta dawo falon
"Yanzun nake shirin zuwa gaida sisi na" harara ta balla mata
"Gaskiya ne,don kinzo gaidani ma ba burgeni zakiyi ba" ta sake hade rai sosai tana dubanta
"Raihana.....ban yi zaton haka daga gareki ba,me kike tunanin kin aikata jiya?,sai kace wata yarinyar qauye ko wadda batayi karatu ba,to idan ma saboda ni kikayi baki burgeni ba wallahi ko kadan" da sauri ta qaraso gaban rumanan tana kama hannunta
"Haba sisi,sisin ki ce fa...." Katseta tayi ta hanyar cewa
"Ba ruwana da wata sisi,farincikin mijina kadai na sani" qwalla ta taru idanun raihanan
"Tun yanzun ya rayyan ya shiga tsakanin qaunarmu kenan?"wani tausayin raihanan ya kama rumanan,ta sani da cew dukkanau suna qaunar juna,kawai dukansu suna hakan ne don qoqarin faranta mata,ita kuma tana jin zatayi duk mai yiwuwa don bawa kowa haqqi da farinciki gwargwadon iyawarta.
Chapter 57 · 0% Book details