Sashe 39
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana direta tayi gun abba da gudu ta daleshi,ya qarasa gaban iyayen nasa fuskaraa qunshe da murmushi,suma murmushin suke cike da qaunar dan nasu da jikanyarsu suna sauraran shirmen surutunta,cikin girmamawa ya gaidasu suka amsa tare da tambayar rumana
"Tana tafe ma,na barta gida tana qarasa wani ayyuka ne,data kammala din nan zata zo"
"Masha Allah,hala sunyi waya da 'yar uwarta raihana ne" sai ya kada kai
"A'a,gaskiya abba ban sani ba ko sunyi"
"Ok,na dauka ta sanar da ita mutuwar auren nata ne" abban ya fada yana barewa islaha ayaba wadda yaci ya rage yana miqa mata.
Cikin rashin fahimta ya dago ya dubi abban,jin yayi shiru baice komai ba ya sanya ummu tayi zaton baiji abinda abban yace ba don haka ta dora bayani
"Jiya bayan isha'i sai gata da mummunan labari,kuma da kansa yake fadin babu abinda tayi masa sai shima da ya zalunceta" shiru ya sakeyi kana daga bisani yace
"Allah ya kyauta ya rufa asiri ban sani ba kam banda yanzu"sai yayi saurin sako zancan kamfaninsa da ake ta aikinsa a yanzu,ganin hirar tasu ta kasuwanci ce yasa ummu miqewa,islaha sarkin son yawo tayi saurin tashi daga gun abban tayo gunta,dungure mata kai ummu tayi
" kaji ni da ja'irar yarinya,tun dazu ai qina kikayi sai yanzu da kika ga na tashi,to nikam bazan dauki kishiya ba,muje ki taka fa qafafunki"qememe taqi kuwa dole ummun ta dagata,dariya su abban suka yi musu don sun saba da ganin dramer dinsu.
Toilet ta shiga tayi wanka sannan ta fito ta saka wata doguwar
Riga da ummun ta bata,kitchen ta shiga ta dauki abincin nata sannan ta koma dakin ummun,ba laifi ta samu kam taci albarkacin maganganun da abba yayi mata,ba qaramin kwantar mata da hankali suka yi ba,tabbas babu shakka ba qaramin dace tayi da uba ba nagari,nagartaccen uba irin abba yusuf din.
Ummu na gama wankewa islaha jikinta data bata da yoghourt a bakin fanfo rumana tayi sallama ta shigo,kallo daya zaka mata ka gane tana cikin kwanciyar hankali da dacen gidan aure
"Sannu,sai yanzu?"
"Wallahi ummu,sauri nake tayi nazo na gaidaku don gidan sisi na ma zan wuce?"
"Au to daina saurin itama tana ciki,tama dakina" ummu ta fada tana daukar islaha tare da rigarta data dauraye mata
"Wayyo,ai bata gayan yau zata zo ba itama,kinga da tuni munyi sabani kenan" ta fada tana shigewa ciki da gudu gudu sauri sauri.
Kallo daya tayi mata jikinta ya bata ba lafiya sisin nata take mata ba,ita din ma hada idon da sukayi sai ya haifar mata da rauni,duk yadda taso danne damuwarta ta gaza hakan har suka kai ga zubowa,jakarta ta saki wadda take mahadi da lace din jikinta ta qaraso inda raihanan take,hannuwanta ta kama itama muryarta na rawa tana tambayarta meke faruwa,kuka tayi sosai bisa kafadar sisin nata,a hankali ta dinga ware mata zare da abawa don ranar wanka ba'a boyon cibi.
Tashin hankali rumanan ta shiga ba kadan ba,idanunta sun rufe bala'i take zabgawa kamar yanzu abun yake faruwa,ta zagi ammar ta zagi maisara ta zago anty saudat,tama rasa da wanda zatayi,miqewa tayi tace gidan hajjajun zata,qarshe raihanan ce ta koma ban baki,da qyar ta zauna sai ta saki kuka tana jin ciwon rayuwar da raihananta tayi,sai ya zama babu mai rarrashin wani tsakaninsu har sai da ummu ta shigo ta musu fada ta dora da
"Ke kuma da zakiyi lallashi sai kika zauna kuka hada kai baki daya kuka zama daya,banso kada na qara ganin hawayen daya daga cikinku,abinda ya faru ya riga ya faru,Allah ya sanya haka ne yafi alkhairi" ta fice,kira ya shigo wayar rumanan,ta janyo wayarta a kasalance ta daga
"Hello yaya" ta fada tana jan majina,shiru yayi daga can bangaren yana saurarenta
"Kuka kikayi ko?'rayyan din ya tambayeta,sai zuciyarta ta sake karyewa,muryarta ta soma rawa
" is ok,ya isa,shi yasa dama na kiraki na ja miki kunne,ashe ma nayi latti ko?,to bana son koke koke kin gane?"kai ta daga tamkar tana gabansa
"Insha Allah yaya"
"Ok,take care"
"To yaya" daga haka suka ajjiye wayar baki dayansu
Cikin dakunan dake falon dakin rumanan ta zage suka gyarashi tsaf yadda raihanan zata ji dadin zamanta,babu abinda babu cikin dakin komai ya zama neat.
Har dare rumanan na gidan bata tafi ba,sosai wunin da sukayi ya debe mata kewa ya sake sakata sakewa tare da hana mata damuwa,musamman islaha daketa shirmenta da wasanni raihanan na biye mata,farincikin yarinyar ya ninku,wuni tayi ajikin raihanan taqi kowa.
bayan sallar magariba rayyan ya iso gidan don tafiya da su,kicin cikin rumanan tayi tana fadi qasa qasa don ummu taji
"Sisi kadai zamu bari a gida,kawai mu tafi da ita don Allah" sarai yaji abinda take fadi din amma sai yayi banza ya share,ummun ma bata ji ba sai da ta tako musu zuwa qofar waje,a lokacin rayyan tuni har yayi gaba da islaha,daman ita raihana ma bata ma fito daga daki ba
"Ummu,don Allah mu tafi da raihana,kinga nan gida babu kowa,inaga sai tafi sakewa a can gurinmu" kai ummun ta kada
"Haba dai rumana,daga mutuwar auren jiya kawai sai yau ta fice,abbanku bazaya bari ba,kuma nima ina da buqatar diyata kusa da ni,baya ga haka ma idda zata fara ai kin sani" a shagwabe tace
"Ummu sisi na fa ba zaman iddan da zatayi,bai dora mata idda ba" wani iri ummu taji zancan,sai tasa ido tana duban rumanan jin zancan banbarakwai,sai kuma lokacin rumanan taji nauyin zancan da ta fada,a kunyace tayi gaba ta shige motar da rayyan ke ciki yana ta faman doko mata horn.
A sanyaye ummun ta juya ta koma cikin gidan,kai tsaye dakin raihana ta nufa,akan abun sallah ta taddata tana lazumi saboda tana fashin sallah ne babu damar yin sallah,shigowar ummun ya sanyata yunqurin tashi sai tayi saurin dakatar da ita
"Yi zamanki,magana dama nazo muyi"
"Tom" ta fada tana komawa ta xauna
"Da gaske ne ammar bai dora miki idda ba?" Sunkuyar da kanta tayi qasa saboda yadda maganar tayi mata ba zata,kunya ce ke dawainiya da ita,ummun ta fuskanci hakan don haka tace da ita
"Daga kanki muyi magana raihana kada ki cuci kanki kiyi zaman iddar da bai wajaba a kanki ba,ni mamarki ce da bai cancanci ki boyen komai ba" da qyar ta iya bude bakinta bayan wasu daqiqu tace
"Eh,bai dora min ba"shiru kawai ummu tayi tana tunanin wanne irin zama ne haka raihanan tayi?,wacce iriyar cutarwa akayi mata tsawon zamansu?,wanne irin haquri da zurfin ciki take da shi
" ikon Allah"shine kawai abinda ummun ke iya fada tana jijjiga kai kana daga bisani ta miqe ta fice,ajiyar zuciya raihan ta saki,tasan babu wanda yayi wannan katobarar sai rumana.
Da fari zancan da ya je kunnen amminta na mutuwar auren fada ta dinga har da shirinta na zuwa ta tarad da raihanan har kano,sai da abba ya zauna ya fayyace mata abinda suka sani sannan jikinta kuma yayi laqwas bata sake cewa komai ba face Allah ya zaba abinda yafi alkhairi.
*****************
Cikin sati guda ta samu kwanciyar hankali,wanda bata taba tsammamin zai yiwu ta sameta haka da sauri ba,ranar da ta cika kwana bakwai ranar ta koma baki aikinta,yadda ta zaci abubuwa sai suka dinga zuwa mata da sauqi wanda hakan ya sake kwantar mata da hankali,babu abinda ta nema ta rasa.
Dawowarta kenan daga makaranta,wanka kawai tayi taci abinci tana falo tana hutawa ita da mai aikin ummu lantana suna taba hira taji sallama,babu ko shakka muryar fatima take ji,tsaye ta miqe tana amsa sallamar tare da cewa a qaraso ciki,fatiman ce a gaba sai anty saudat da anty sabira,ta qarasa a hankali tana musu sannu da zuwa tare da amshe babyn anty sauda dake hannun fatima wanda bata samu ganinsa ba sai yau,ta musu masauki cikin falon,ta saka lantana ta kawo musu lemo da ruwa,sai meatpie data yi musu jiya da dambun naman kaza.
Dukkansu babu wadda ta iya cin komai,daga gaisuwa ma shiru ne ya ratsa falon,kallo daya zaka yiwa fuskarsu ka karanci alhini qarara saidai babu abinda tace,da taga shirun yaqi katsewa ne ta sake cewa karo na biyu
"Yaya hajjaju take fatim?"
"Uhmmm,tunda abin nan ya faru hajjaju jikinta yaqi dadi raihana,kwana shidan nan da kikaji shiru duka hankalinmu a tashe yake hajjaju na kwance a asibiti sai jiya aka sallamomu,don Allah raihana kiyi haquri ki yafe mana,sanda ammar ya sanar da hajiya washegari ya sakeki ina gida na zarto daga asibiti da nakai musaddiq allura,ni na fara zaginki ina cewa gwara da ya rabu da juya,hajiya namin magana amma idona ya rufe haka,fatima na gefe tana kuka bata ce komai ba sai da ammar din ya fita bayan hajiya ta masa umarnin ya dawo dake ya bata haquri kan bazai iya dawo dake ba ni kuma ina sake zugashi cewa dai dai ya yimin,sai da ya fita ne fatima take gayawa mana komai,a nan ciwon hajiya ya tashi,ammar ya cucemu ya bata mana zuri'a,yanzu haka bamusan ma ina yake ba....." Ta qarashe maganar tana sakin kuka fatima da sabira na sharar qwalla,sabira ce ta bude baki tana fadin
"Don Allah kiyi haquri raihana,haqiqa babu shakka an cutar da ke,kuma ke din 'yar halak ce da kika gaza fallasawa dan uwan mu asiri,tabbas bashi kadai kika rufawa asiri ba har da mu kanmu kin rufa mana kuma kin mana gata,Allah ubangiji ya miki sakayya da alkhairi,ya hadaki da dukkan wani alkhairin rayuwa".