Sashe 43
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Su biyu ta taras cikin falon wanda bata tsammaci ganinsa ba,rabonta da ganin nasa tun ranar da ya karbi diyarsa,zaune yake ya kwantar da bayansa jikin kujera yana duban falon da qasan idonshi,sai ta rage saurin nata tare da duban agogo,qarfe tara ne na safiyar ranar jum'ar,rabawa tayi gefan ummun tana yin tamkar bata ganshi ba tace
"Gani ummu"
"Kinji 'yar uwarki jiya a asibiti suka kwana tayi bari amma babu wanda suka kira,yanzu haka daga asibitin suke an sallamota ya maidata gida" sai ta narke fuska cikin tausayin sisin nata tace
"Subhanallah,wayyo sisi,Allah ya bata lafiya"
"Ameen,abbanku yace ki shirya kije gidan ko kwana uku ki mata kafin jikin nata yayi qarfi"
"To ummu" ta amsa da sauri tana miqewa zata shige daki ummu ta sake kiranta,tana waiwayowa idanunta suka fada kansa,ta qasan ido yake kallonta idan baka lura ba sai ka zaci a lumshe idanun nasa suke,ta janye idonta tana jinta duk a takure
"Idan da tea din nan hadawa yayanku ya sha kafin ku wuce,ki hado masa da panadol shima kanshi wai ke ciwo,inaga kwanan rashin baccin da sukayi ne,ga rigimar islaha"
"To ummu" ta fada tana juyawa akalarta da sauri zuwa kitchen saboda irin kallon da yake mata.
Ta fito hannunta dauke da qaramin cup na tangaran dauke da tea,a hankali ta qarasa inda yake har yanzu bai sauya zaman shi ba,saidai ummu bata falon
"Gashi" ta fadi tana miqa masa,shiru yayi tamkar bai ji ta ba har ta fara qaguwa,bata jin zata sake masa magana ko zasu shekara hakan tunda ta tabbatar yaji din
"Ajjiye kije ki cire kayan jikinki,kada na kuma ganinki kina yawo da night gown" ya fada cikin wata ginshira,baki ta tabe tana ajjiye cup din a gefansa
"Dama bada su nake yawo ba" ta fada tana juyawa zata bar gurin,hannun rigarta taji an damqo ya janyota har sai da botiran rigar biyu sauka bude kana ta fadi a gefansa,da sauri ta sanya hannunta tana maida maballan,idanunsa duka ya ware a kanta wadanda suka sauya launi yana dubanta
"Wato ke mara kunya ko?,idan aka fada miki sai kin rama,kin girma kenan kema kin taba aure ko?,kin manta sanda kike majina a gaba na?,me kike taqama da shi?" Ita tsoro ma ya bata ganin yadda ya wani juye baki daya,mai ta masa don kawai ta bashi amsa,eh lallai ta yadda da wata a qasa shi yasa rayyan din ke nuna mata wasu halaye,da alama ci mata mutunci yake sonyi ita kuma wallahi ba zata lamunta ba,a yanzu kam ai ita ba yarinya bace aqalla ta mallaki hankalin kanta,tana gama rufe maballan ta zame hannunta a zafafe ta miqe ta wuce ya bita da kallo,sai data shige dakin ya saki ajiyar zuciya ya maida bayansa jikin kujerar kamar yadda yake dazun yana fidda numfashi tare da tsurawa cup din shayin data kawo ido,ji yake kamar a film kamar bashi yayi ba,bai san meke tunzura zuciyarsa haka ba,a hankali ya miqa hannunsa ya dauki tea din ya kai bakinsa ya kurba.
Bakin gadon dakin ta zauna,sai taji qwalla kawai ra subuce mata,me rayyan ke nema daga gareta ne ya soma takura walwalarta haka?,miqewa tayi da zummar zuwa ta samu ummu sai kuma ta koma ta zauna a sanyaye,bata jin zata iya cewa ummu ba zata je ba,ko don darajarta darajar abba da kuma darajar sisinta wanda tasan zataji dadin zuwanta qwarai,hakanan sunfi qarfin komai a gunta,saidai dole ta takawa rayyan birki hakanan tunda ita bata matsa masa ba bata ga dalilin da zai sanya ya tsangwameta ba,a hankali ta miqe ta shirya kayanta da duka a binda tasan zata buqata cikin qaramar jaka sannan ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin baqar doguwar riga tayi rolling da mayafinta.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:51 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*An karbo daga iyad dan himar R.A yace:manzan Allah S A W yace"wanda ya kare mutuncin dan uwansa (musulmi)alhali baya nan,to,Allah zai kare wuta daga fuskarsa a ranar qiyama(bazai shigeta ko ya ganta ba)"*
______________________
*Babi na talatin da uku*
A falo sukayi sallama da ummu ta bata key din motarta saboda a tashi zasu tafi sannan ta fito.
Cikin motar ta tarad da shi,yayi kicin kicin,bata dubeshi ba ta bude gidan baya tayi zamanta,ga zatonta zaice wani abu,sai kuma taji baice komai din ba.
Basu wuce minti goma da fara tafiya ba wayarta tayi tsuwwa,sunan sultan ke yawo kan screen din wayar tata,sai ta saki dan qaramin murmushi tana jinjina yadda sultan din ya faye damuwa da ita,ta daga wayar ta kara a kunnenta tare da sake jingina jikinta da kujerar.
Batasan ya akayi ba sai ji tayi anja wani wawan birki da ya sanyata yowa gaba,wayar dake kennenta ta subuce ta fadi goshinta ya daku seat din dake gabanta,gabanta ke dukan uku uku ta daga kai da sauri ga zatonta hadari sukayi,saidai babu wani abu data gani dake nuna hadari ne,asalima yana zaune daidai kan seat dinsa,hannunsa yasa ya saita mirrow din motar daidai fuskarta,ta nan suka hada ido,kawar da kanta tayi ganin yadda gaba daya fuskarsa ta sauya,wani irin mahaukacin kishi wanda bai san daga ina ya faro ba ke cin zuciyarsa,wayar da take kamar ruwan zafi yake jin ana watsa masa,idanu ya zuba mata ta glass din yana qarewa fuskarta kallo,masifar da ya qudiri aniyar yi sai ya nemeta ya rasa jikinsa yayi sanyi har ta kaishi ga lumshe idanunsa sanda ya tuna wani abu,ya tuna wasu maganganu data taba gaya masa
_Bana son raytan so na soyayya,bana sonka yaya rayyan,kai koda ina sonka rayyan na SADAUKARWA da rumana soyayyar,saboda har abada bazan iya shiga tsakanin rumana da farincikinta ba,qaunar dake tsakanina da ita ta siya mata komai,babu abinda bazan iya SADAUKAR MATA BA CIKI KUWA HAR DA KAI YAYA RAYYAN"_
hanzarin bude idanunsa yayi maganar na masa amsa kuwwa tamkar a lokacin take furta masa su,ko da gasken raihana take bata sonshin?wa take so to?,wa take qauna baya ga shi,baya da hurumin tilasta mata tabbas,amma yana jin wani qarfi da jin cewa yana da hurumin tilastawa zucuyarsa ta qi raihana,ta gujeta kamar yadda ta gujeshi,abinda bai sani ba shine,ita zuciya ba'a mata tilas tayi so ko qi,tana yin su ne a duk sanda taga dama,yana jin wani bala'i a zuciyarsa duk sanda ya tuna ta taba auren waninsa,ta kuma zauna da shi wanda hakan sau da dama yake sanyashi yi mata misbihaving ba tare da ya sani ba,hannunsa ya sanya kawai ya tashi motar sannan yaci gaba da tuqinsa,saidai a wannan karon a kasalance yake, itama maida kanta tayi gefe guda ta saku ajiyar zuciya bayan ta gama hada wayarta data tarwatse qasan motar,tunane tunane fal cikin ranta
.
Ba laifi jikin nata da sauqi,don data isa ma har ta hada tea tana sha saboda yunwar data fara ji,raihanan bata zauna ba sai data gama kimtsa gidan tsaf wanda yayi dadai da gama breakfast dinta,tare suka sauko da rumana dukkansu sunyi wanka,wanda da alama ma shi shirin fita yayi,daki ta koma itama tayi wankan ta barsu nan.
Zamanta a gidan wani irin zama ne data riga ta tsara takunta,matuqar yana gidan zata yi zamanta a daki,tayi waya ko tayi wasu 'yan karance karancenta,rumana nata qorafin me yasa ba zata dinga fitowa ana hira da ita ba,takance kinsan malamar makaranta ce ni dole sai da bita da binciken karatuttuka kada ajefo tambayar da dalibai zasu qureni,tun tana mitar har ta gaji,a kwana uku da tayi cikin gidan tun randa ya kawota bata kuma bari sun hadu ba,ita take komai a gidan bata bari sisin nata tayi komai,har kuwa da hidimar islaha,cikin lokaci qanqani rumanan ta warke sumul wanda hakan ya sanya raihana cewa zata koma,tsalle tayi ta dire tace babu inda zata je wallahi sai ta cika kwana goma cif.
A lokacin rayyan din na kan carfet shi da islaha suna cin abincin dare,bai ko dubesu ba duk da yana jinsu sarai,rumana ta juya ta dubeshi
"Yaya kana jin mu fa,ko baki ba zaka saba don Allah,tunda take ta taba kwana a gidan nan,ni gani nake kamar fa sisi kin rage sona,yanzu yaya ta qarasa kwanakin sai taqi tace tafiya zata yi?"
"Sai me?" Ya fada kansa tsaye bayan ya dubeta
"Da can tare bake kadai ke zama a gidan ba?" Sai suka zuba masa ido gaba dayansu kowa da abinda yake saqawa,bai damu ba yace
"Ki barta,tunda bata son zama da mu muma mun yafe"dira qafa rumana tayi ganin raihana ta juya ta shige dakin da take,bata jin zata sake qara ko minti daya cikin gida
" kai yaya,kai yaya,kai da zaka mana sulhu kuma don Allah sai ka fadi haka"shiru yayi yana ci gaba da cin abincinsa,ta san halin miskilancinsa sarai bazaya amsa ba tunda yaci gaba da abinda yake,saboda haka ta juya da sauri ta bi raihana.