← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 66

Sashe 26

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon ginin take tana murmushi babu shakka ya tsaru kam,ko ba'a gaya mata ba tasan tsarin rayyan dinne,mutum ne mai tsari doka da qa'ida,a hankali tabi wani dogon guri sai gata ta bulle baya,tsugunne suke duka su biyun yana riqe da singalalin hannunta
"Na kawo ki ne nan don ki sake tabbatarwa kanki rayyan bazai yaudareki ba,don ki sake tabbatarwa rayyan baya magana biyu,ki kuma sake nutsuwa da cewa ni din bazan guje miki ba,riqe alqawari sai dan halak rayyan kuwa dan halak ne,wannan shine ginin da nakeyi akwai part dinki a ciki inda zaki zauna,wanda nake saka ran kafin dawowata akammala ginashi"ya qarasa maganar murmushi mai sanyi da kyau kwance bisa kyakkyawar fuskarshi,ita din ma martanin murmushin ta maida masa,a hankali ta samu ta janye jikinta,sannu sannu ta jingina da ginin da take tsaye kusa da shi,wasu hawaye da batasan na meye ba suka bi kuncinta,iyakar saninta burinta shine rayyan ya janye mata,ya janye matan ya kuma ja baya da ita,maimakon ta samu farinciki da nutsuwa kamar yadda take hasashe sai kuma taga akasin hakan,koda yaushe kewarsa take,koda yaushe sake jin wani bala'i take cikin zuciyarta,wani rashin sukuni ne ke sunno kai cikin rayuwarta,tana tsoron kada dai a ce zuciyarta ce ta soma qoqarim bijire mata,zuciyarta ce ta gaza da ci gaba da boye dubun nan abubuwan dake bunne cikinta.

Cikin saurin ta tsaya sosai da qafafunta tare da goge hawayen idanunta bayan ta cire glasa dinta ta gogeshi shima,da sauri ta dora hannunta saitin zuciyarta tamkar mai magana da wani tace
"Baki da ikon bujire min alhalin ina da iko a kanki,na dade da haramta miki abinda kake hanqoron a kansa,na kuma yiwa kaina alqawari"
Ta sauke hannun nata a sanyaye ta maida glass dinta.

Tana shirin juyawa ta fice a gun,idanu suka hada da shi yana tsaye ya jingina kafadarsa jikin bango hannunsa da qafafunsa harde cikin 'yan uwansu,duk sai taji wani iri,babu ko shakka yaji me take fadi
"Muna iya tafiya?" Yace da ita,bata amsa masaba face gaba da tayi.

***************

Shigowarsu kenan daga makaranta shi da abban,rayyan din na qoqarin wucewa sashensa abban ya dakatar da shi
"A,rayyan idan ka gama abinda kake ka sameni cikin gida,akwai maganar da nakeso mu tattauna"
"To abba" ya fada ya wuce ciki.

Hadisan hannunsa ya ajjiye sannan ya shiga toilet ya watsa ruwa,bayan ya fito ya sauya kaya yayi shafa'i da wutiri,har ya daga waya zai kira rumana ta kawo masa abinci sai kuma ya fasa,wunin yau duka hakanan yaji baya jin yunwa.

Su uku ne cikin falon abban,shi abba sai kuma ummu,yana zaune ne daga gefansa yana jira abban ya kammala wayar da yake yi,minti biyar ya dada sannan sukayi sallama da wanda yake wayar ya ajjiye
"Rayyan" abban nashi ya kirashi
"Na'am abba" alhj yusuf ya gyara zamansa yana dubanshi
"Kwanaki nawa ya rage maka ka tafi uk"
"Eh abba,saura sati biyu"
"To masha Allah,mun gama magana da alhj dalhatu duk da ahi yace aji ta bakinka tukun,amma mun gama magana da mahaifiyarka gata nan,tsawon watannin da zaka diba a can din ya haura kwanakin aurenka,hakan ya sanya ruma ta shiga damuwa ko ba haka bane?" Kai ya gyada
"Haka ne abba"
"To abinda muka ga yafi dacewa kawai shine a daura aurenku hankalin kowa ya kwanta,idan yaso duk wata bidi'a da zata biyo baya kuma idan Allah ya kaimu ka dawo daga tafiyar koma mene ne ya rage naku sai kuyi,zuwa lokacin gininka ya kammala,sannan raihana ma in sha Allah kafin lokacin muna saka ran ta samu miji,sai a hada duka ayi a gama,don bai kamata mu takura ta ta fidda miji ba,tausayin maraicinta nake"

Maganganun biyu masu nauyi duka suka yi masa dirar mikiya lokaci guda
"Abba.....na gode Allah ya saka da alkhairi,duk abinda kuka yanke yayi daidai abba,a tayamu da addu'a....amma abba...." Sai kuma yayi dan shiru
"Amma me?"
"Raihana ai ta samu miji abba"

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 8:59 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*Daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace"kada mace ta aurar da mace,kuma kada mace ta aurar da kanta*
_______________________

*Babi na ashirin da biyu*

Murmushi abba yayi sannan yace"eh na sani ai rayyan,ko ba amir ba?,yazo ya sameni har mun gaisa ma,abinda yasa bakaji nayi saurin zartarwa ba na basu lokaci ne su fahimci juna sosai,yadda raihanan da kanta zata zo ta gabatar min da maganar,bana son tursasata,nafiso tayi zabi a hankali don ta dace da na gari,tunda naga duka duka watansu nawa da haduwa baici sun gama sabawa da juna ba,musamman ita raihanan da bata saba hulda da kowa ba".

Qasa yayi da kansa yana jin wani abu mara dadi,baiso abba yayi masa yankan hanzari ba,bazai iya maida maganar abban baya ba da yace masa "abba nine mijin da raihana tayi"
"Gaskiya ne alhaji,yaron kuma na fuskanci yana da hankali,don har ni yake kira wani lokaci muna gaisawa" cewar ummu,wani kishi ya kamashi jin suna yabon amir,hakan ya sanyashi miqewa yana fadin
"Abba zan wuce"
"To rayyan,Allah yayi muku albarka,Allah ya albarkaci aurenku ya sanya nutsuwa da kwanciyar hankali a cikinsa,inaga sai ka fara shirin daurin auren ko,don nan da sati biyu za'a dara,satin gaba kuma sai ka wuce course dinka"
"To abba,na barku lafiya" ya fada yana juyawa ummu ta bishi itama da addu'a farinciki fal zuciyar su na ganin aurem dansu da 'yarsu rumana.

Zazzafan huci ya fesar sannan ya fada saman kujerar,hannayensa biyu ya sanya yana yamutsa gashin kansa,gaba daya kansa ya dauki caji,babu tantama yayi farinciki da aurensa da rumana,saidai abinda ya kassara rabim farincikin nasa rashin samun cikakkiyar matsaya dangane da mallakar raihana,babban abinda ya masa burki kan sanar da DANGANTAKAR ZUCIN da sukeyi shida raihana rashin samun hadin kanta,ya bata dama ne ta gamsu da kanta ta amince zata aureshi,ya tabbatar da ya samu hakan daga gareta da tuni an dade da wuce gun,yanzun haka zaya zuba ido ya rasata kenan?,kansa ya shiga girgizawa shi kadai yana fadin"bazai yiwu ba"bayajin zai iya barwa raihana wani,ba zai taba yarda al'ada ta cuceshi ba,bazai yarda al'ada ta haramta masa abinda addininsa ya halatta masa ba wanda ko a gun Allah baiyi laifi ba idan ya auri raihana,irin macen da annabi ya kwadaitar da mu mu aureta,kan me zai yarda wata banzar al'ada ta haramta masa halas,abu guda ne zai yarda ya haramta masa raihana yasa hannu bibbiyu ya karba ba tare da haufi ba shine ADDINI.

Baisan tsawon lokacin da ya kwashe haka ba sai daga ido yayi yaga qarfe sha biyu saura na dare,ko abincin bai samu yaci ba,duk tunaninsa ya tafi kan yadda zaya bullowa lamarin,daga qarshe bedroom dinsa ya shige ya sakarwa kansa ruwa a shower kusan mintina ashirin sannan ya samu sauqin abinda yake ji,sallah raka'a biyu yayi ya rufe da wutiri,addu'a yayi sosai kan neman zabin Allah ya hada da istihara,kafin ya bar saman abun sallar sai yaji duk wani fargaba da damuwa tasa ta yaye,nutsuwa da kwanciyar hankali na ratsashi tamkar ya samu rumana da raihana baki daya.

Sai da ya nutsu saman gadonsa bayan ya rage hasken dakin sannan ya fidda wayarsa ya shiga gun rubuta saqo ya lalubi lambar rumana ya fara rubuta mata gajeran saqo kamar haka
_haqiqa babu wani bawa da ya isa ya hana abinda Allah ya qaddara afkuwarsa faruwa,ina farincikin sanar miki da yardar Allah ni rayyan yusuf zan zama miji gareki rumana sati biyu masu zuwa,goodnight and sweet dreams my angel_

Daidai lokacin wayar na hannun raihana tana duba wasu litattafai cikin dacument din rumanan,ko kadan ji tayi bata jin bacci hakan ya sanyata bayan ta gama abinda zatayi ta karbi wayar,da shigowar saqon tayi zaton kamfanin waya ne,murmushi tayi tana cewa mutanen sisi na"don tasan halin rumanan ta tsani saqon da kamfanin waya ke nacin aikowa,musamman idan ta ciro wayar da karsashinta tana zaton ko rayyan ne ya turo saqon taga sune,yanzun nan zakaji qorafinta.

Idanunta ta lumshe bayan ta gama karanta saqon,wani sashe na zuciyarta na taya rumana samun cikar burinta,tana tayata murnar mallakar rayyam,yayin da wani bangaren na zuciyarta ya samu rauni,hawayen da batasan manufar zubarsu ba suka fara kwaranya mata,sai ta ajjiye wayar a gafanta ta kwanta gefan damanta,kuka ya subuce mata har sautinsa na shirin fitowa,hakan ne ya sanya ta toshe bakinta da blanket dinta,kuka ta dinga yi sosai irin kukan dake sosa zukata,irin kukan dake bayyana rashi da kewa,kukan bankwana da farinciki,kuka ne dake karya zuciyar duk wanda yasan halin da zukata suka tsinci kansu,tun tana yin kukan da dan sauti har ya zaman sautin bai fita,a hankali idanunta suka kumbura lebunanta da fuskarta,fuskar ta dinga mata wani radadi da fitar huci,kanta ya dinga sarawa tana daga kwancan amma jiri ke dibarta.

Qarfe biyu harda rabi amma idanunta tangaran tamkar an yaye mata wami hijabi,biyu da arba'in ta miqe daga kan gadon nasu ta shige toilet ta daura alwala ta dawo kan gadonta wani sanyi ka ratsata,guri guda ta cure,da hannunta ta dinga tasbihi ga ubangiji,don ita kanta ta gaji da radadin da zuciyarta ke mata sauqi kuma take nema,sai kusan uku da arba'in bacci ya saceta.

Bata farka ba sai da taji rumana na bubbuga filonta tana fadin
"Sisi yau kece da makara kuma,ki tashi kiyi salla har wasu masallatan sun fara idarwa" bata yarda ta tashin ba saboda idanunta sai data tabbatar rumana ta tayar da sallah sannan ta miqe,jikinta a mace murus tamkar wadda aka lakadawa duka,hakanan zuciyata wani iri takejinta kamar wadda ake shirin jefawa kurkuku.

Ko kafin ta idar da tata sallar rumana ta koma bacci,don haka tayi hanzarin shigewa toilet tayi wanka.

Qarfe bakwai da rabi ta gama shirinta tsaf cikin doguwar riga ta lace wadda tayi mata kyau,saidai yadda fuskarta ta jirkita ya rage fitar kyawun nata baki daya,ta sake kallin fuskarta a madubi har yanzu a tashe take,shi yasa ta shirya ficewa daga gidan da wurwuri,don batason wani yaga fuskarta har ya nemi ba'asin abinda ya haddasa mata faruwar hakan,duk da bata da lacture sai qarfe goma zuwa sha biyu na rana.

Paper ta fidda 'yar qarama tayi gajeran rubutu akanta
_da kin tashi wayarki nakeso ki fara dauka ki duba inbox dinki,ni na wuce schl sisi_
Chapter 26 · 0% Book details