Sashe 38
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Randa ta iso washegari raihana ta yiwa gida tsinke cikin motarta,a falo ta samu rumanan na zaune,gaba daya ta zama wata 'yar lukuta,dariya raihana ta dinga mata tana tsokanarta
"Yar tsalle haka kika koma?" Itama rumanan tayata dariyan ta dinga yi har sukayi suka gama sannan suka hau hiran yaushe gamo.
Sunci abinci sun ture kwanukan gefe lantana mai aikin da rayyan yasa aka samawa ummu zata zo ta kwashe,kallon raihana sosai rumanan keyi har sai data gaza shiru
"Amma sisi kina lafiya?" cikin yanayi na rashin fahimta tace
"Kamar yaya kenan?"
" Kin sauya ne sisi,duk da fatarki ta nuna kina cikin hutu da jin dadi amma yanayinki ya qaryata hakan"sai ta saki murmushi harda 'yar dariya cikin basarwa
"Da a watannin baya kika zo ba zaki fadi haka ba,ko kin manta ban fi sati uku da gama jarabawa ba,kin kuma san yanayin karatun namu ba sauqi,bani da kwanciyar hankali fa har sai dana kammala ta" jinjina kai rumanan tayi tana murmushi
"Au kuma fa hakane,amma naji dadi da nayi zaton ko da matsala ne"
"A'ah,babu wata damuwa kamar yadda nake miki fata kema babu" murmushi ta kuma yi sannan ta dafa hannun raihanan
"Duk inda ake neman miji na qwarai sisi na yaya rayyan ya kai,namiji ne wanda ya amsa sunansa ta kowanne fanni" ta kanne mata ido"idan nace miki ta kowanne fanni hakan nake nufi"sai suka saka dariya don ta fuskanci inda zancan nata ya dosa,ta katse dariyar ta dora
"Matsalata daya ce idan ma akwaita,wani lokaci sai naga yaya rayyan din cikin damuwa,idan zanyi tambayar duniya yakan ce min babu komai,wani lokaci yace ba damuwa bace mai amfani da zai sanar dani,sai ya wuni ya kwana haka,sai daga baya kuma don kansa ya koma normal" shiru raihanan tayi zuciyarta na son fara wuce qa'idar gudunta.
A hankali ta sauke numfashi sannan tace
"Bai kamata ya barki cikin damuwa haka ba,amma ina ganin tunda damuwar tasa ya riga ya sanar dake ba wata muhimmiya ko mai amfani bace ki haqura da saninta,tunda bai tauye wani abu daya na rayuwarku ba ko?"
"Haka ne,kawai bana son ganinsa cikin damuwar ne" ta danyi murmushi
"To ya za'ayi,babu dan adam da zai rayu baida damuwa totally,bare ma maza wani lokaci wani abun nasu basa bari ka sani wani haka attitude dinsa yake,kici gaba da addu'a da godiya ma Allah"
"Haka ne sisi,to Allah ya bamu dacewa"
"Amin ya Allah" daga haka suka dora wata hirar
Bata bar gidan na sai wajen takwas na dare,tamkar kada ta tafi,tamkar su zauna da sisinta kamar yadda suke a da,saidai babu dama haka ta baro gidan cikin kewa.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:41 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*An karbo daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace"wanda ya riqi kare wanda ba karen kiwo ba(wanda zai dinga raka dabbobi kiwo),ko karen faruta ba kona gadin yabanya,za'a dinga cirar lada daya kullum cikin aikinsa"*
_bukhari da muslim ne suka rawaito_
*_(qalubale gareku masu kiwon karnuka cikin gidajensu haka kawai saboda ado ko qawa ko burgewa,bugu da qari mala'ikun rahama basa shiga gidan da yake da shi,yaya kake zato idan kazo mutuwa mala'ikun rahama suzo daukar ranka?)_*
________________________
*Babi na talatin*
_na samu mantuwa wajen sanya number din page a baya,ashirin da takwas ne da ashirin da tara,ga babi na talatin nan in sha Allah_
Kamar yadda kowa ya sani duk duniya babu macen da za'a ce an saka taji farinciki koda ita ta buqata balle ita da bata shiryawa hakan ba haka kuma bata tsammaci haka ba,kasa miqa hannu tayi ta karbi takardar illa baki da ta bude ta bishi da kallo,babu abinda ke dada masa nauyi irin qwayar idonta,ji yake ta dora masa wani nauyi mai yawa,wani kwarjini yake jin ta masa fiye da yadda yake kallonta a baya.
A hankali ya qarasa gabanta ya sanya hannu cikin aljihunsa ya zaro bandir din kudi 'yan dubu dubu guda uku ya hada da takardar ya ajjiye a gefanta ba tare da ya iya kallonta ba sannan yace
"Kiyi haquri raihana,ki yafe min,idan kinso tafiya yanzu na kira driver dinki yana waje zai kaiki har gida,Allah ubangiji ya saka miki da mafificin alkhairi,ya haska rayuwarki,ya miki sauyi mafi alkhairi" yana gama maganar yayi gaba da hanzari yana ficewa daga falon.
Tafi sama da minti ashirin zaune tamkar mutum mutumi,ta rasa me zata tuna?,wanne abu ya kamata ta aiwatar?,miqewa kawai tayi tsam ta shiga dakin gado ta dauki wayarta,ko hijabin jikinta bata damu da sauyawa ba ta zura silifas dinta tayo waje.
Driver din kuwa na tsaye jikin motar tata,yana hangota ya bude mata qofa,dama yasan da fitowar tata amma saidai baisan dalili ba,ta shiga ya rufe sannan ya tada motar suka fice.
Sai da motar ta saitu kan kwalta sannan taji wasu hawaye masu dumi sun fara bin kuncinta,mutuwar aure ba abu bane mai dadi sam ga diya mace,kanta ta kifa saman cinyoyinta ta dinga risgar kuka ba tare da sanin driver ba.
Ta daga kai tana duban gidan nasu lokacin da suka iso,fargaba da tsoro suka cikata,me zata ce da ummu da abba?,wanne irin daci zasu ji idan suka ganta agidan da sunan wadda aurenta ya mutu,babu yadda zata yi haka ta sanyo qafafunta waje ta fito kamar mai ciwon qafa,drivern ya miqa mata muqullin motar yana fadin
"Hajiya ga muqullin" kai ta kada
"Ka koma da ita gida kawai"
"Hajiya mai gida ai yace idan na kawoki lallai lallai na damqa miki muqullin" bata da buqatar doguwar magana saboda haka ta miqa hannu kawai ta karbi muqullin tare da yin gaba.
Ummu na zaune cikin falon ita da mai aikinta,suna hada ido da ummun wasu sabbin qwalla suka zubo mata
"Subhanallahi,lafiya raihana,daga ina haka ke da wa?" ummun ta fadi tana miqewa tare da taro raihanan,tuni ta fada jikin ummu ta ida sakin kukan da take ta riqewa,kama kafadunta ummun tayi sannan ta shige da ita bedroom dinta wanda a yanzu ya koma saman benan da rayyan ya dora musu.
Kusan minti ashirin suna zaune gefan gadon suna fuskantar junansu,kallonta kawai ummu keyi tun dazu take risgar kuka,ta qyaleta ne tayi iya son ranta ko wataqila hakan zaisa ta samu sauqin radadin da takeji a zuciyarta har ta samu damar yi mata bayani,da qyar tayi controlling kanta ta miqawa ummu takardar hannunta
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda ummun ke maimaitawa,sai ta daga takardar tana sake karantawa amma wannan karon a bayyan
"Ni ammar ammar mu'azzam na saki matata raihana abubakar saki biyu ba tare da ta yimin laifin komai ba,hasalima nine mai laifin kuma nina zalunceta,ina mata fatar samun miji na gari tamkar ita".
Numfasawa ummun tayi bayan ta kai zuciyarta neaa da qyar
"Baki cancanci kiyi kuka ba raihana,tunda Allah ya sanya bake kika zalunceshi ba,shi din da ya zaluncekin ya jira sakamako,Allah ai baua barci yana madakata yana jiranmu,bari abban naku ya shigo" haka ummu ta dinga kwantar mata da hankali,ganin har goma ta kusa abban bai shigo ba yasa ummu ta sanyata tayi wanka nan cikin dakinta,ta kuma bata kayan barci ta saka sannan ta tusa ta a gaba da abinci tace sai taci.
Kallonta take cike da rausayi,sai a sannan ta lura da ramar da raihanan tayi,tun asali zurfin ciki ne da raihana na masifa tun suna yara,kusan tun kafin ta dawo hannunta tasha jin yadda umminta kan rufeta da fada kam shegen zurfin cikinta,don a haka a yanzu ta rage kaso tamanin cikin dari,sanadiyyar ma da ya sanya cutar idonta tayi tsananin da ya kaita da sanya glasa kenan har yanzu qin faden abinda ke damunta da wuri
"Duk wanda ya kalleki raihana ko ammar bai fada ba yasan yana zaluntarki" cewar ummun cikin zuciyarta,bayan ta gama ta sanyata ta kwanta,tace kuma kada ta soma sanya wani abu cikin ranta,bacci takeso tayi sosai.
Rashin dawowar abban da wuri ya sanya bata tada masa maganar ba ta barwa washegari,cikin daren kasa bacci tayi,amma batayi kwanan zaunem banza ba,sallah tayi mai yawa har sai data dinga jin gajiya sosai cikin jikinta
*****************
"Haqiqa naji dadi qwarai da ya zamanto bake kika zalunci ammar ba,saboda girma da nauyin haqqi irin na aure,wanda duk wanda ya kuskura ya zalunci dan uwansa tofa yawanci tun a duniya Allah yake sakayya,haqqin aure na da saurin bibiyar mutum tun a duniya kafin aje ga lahira,na bincika kuma na tabbatar da cewa baki da laifi ko guda daga bakinsa,to alhamdulillah,inaso ki saka a ranki cewa haka Allah ya tsara miki,mutum bai isa ya gujewa qaddararsa ba,bana so ki sawa ranki damuwa,ki nufi ubangiji da dukka buqatunki,na tabbatar da cewa in sha Allahu ba zaki taba wofinta ba,Allah ya miki albarka" cewar abba yusuf kenan yana duban raihana dake durqushe gabansa kanta na duban qasa cikin hawaye
"Ameen abba,in sha Allah zanyi amfani da nasiharka,na gode Abba Allah ya qara girma"
"Ameen" ya amsa mata
"Tashi kije abinki kinji" ya sake mata magana,ta miqe a sanyaye ummu ta kalleta cike da tausayi
"Idan kinyi wanka break fast dinki na kitchen"
"To" ta amsa tana ficewa daga bangaren abban.
A bakin qofa sukayi kacibus da shi wanda sauran kadan suci karo lokacin da take share qwallar idonta
"A'uzu billahi minash shaidanir rajim" ya furta,da sauri ta daga kai ta kalleshi,wannan ne karon farko da ta sanyashi a idanunta tun bayan da suka dawo nijeria gaba daya,sanye yake da yadin maza tissue fari qal,wanda aka yiwa dinkin dogon wando da riga iya gwiwa mai gajeran hannu,yayi kyau ya sake haske,jikinsa babu abinda ke fiddawa sai daddadan qamshinsa sumarsa ta sake kyau da yawa sai walqiya take alamar hutu da jin dadi,yana dauke da islaha a kafadarsa wadda take kallon bayansa tana ta zuba masa surutu,daga nesa sai kayi tsammanin bacci take bisa kafadar tasa.
Wani haushi ya quleta,ita yakewa ta'awizi kome?,sai kawai ta kewayesu ta shige ciki.