Sashe 13
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A bakin wajen hall din ya ajjiyesu,raihana ta fidda glass dinta ta saka sai ya qarawa kwalliyar tata kyau,rumana ta waiwayo ta dubeshi a shagwabe "haba yaya rayyan,yanzu ba zaka shiga ba" kai ya kada
"Akwai gurin da zani,idan an tashi ki kirani nazo na daukeku"
Kicin kicin tayi da ranta sannan ta dubi agogonta cikin kishi tace
"Ina zakaje a irin wannan lokacin"
"Zance zani" ba rumana ba,hatta raihana dake qoqarin ficewa daga motar sai data dakata,tuni rumana ta fara hada qwalla
"Wanne irin zance kuma yaya rayyan?" Raihana ta tambaya a sanyaye
"Eh sabo nayi?" Ya fada fuskarsa a daure,qasa tayi da kanta tana kadashi "a'ah ba sabo kayi ba" inji raihana,basu ankara ba saiga k'walla kan fuskar rumana
"Subhanallah...rumana daga wasa?" Ai kuwa saita qarasa fashewa da kukan
"Haba ke kuwa wasa fa nake miki....ungo share hawayen" ya fada yana ciro tissue daga gaban motar ya miqa mata,ta amsa ta soma gyara fuskarta yayin da shi kuma ya zuba mata ido yana sakin murmushi qasa qasa,girarsa ya dage yana fadin
"Kinga nayi nasara,wannan kwalliyar da kikayi dama tayi yawa ni kadai ya kamata na gani,yanzu kuwa kinga da na saki kuka na rage farashinta" sai ta soma dan bubbuga qafarta cike da shagwaba,raihana ta rufe bakinta tana yiwa rumanan dariya ta fice daga motar ta tsaya a waje tana jiransu don ta fuskanci abun nasu na masoya ne,ita kadai ta dinga sakin murmushi.
Minti kusan uku saiga rumanan ta fito,shima ya fito daga nashi gun ya dubeta yana cewa
"Idan an tashi ban kammala abinda nakeyi dinba ku wuce qoqi kawai ban yadda ku hau motar kowa ba,zan bi ta can na daukeku"
"An gama ranka ya dade"inji rumana,suka juya suka fara tafiya ya bisu da kallo.
Kiranta taji yayi ta dubi raihana
"sisi minti daya,ko yayi mantuwa ne"kai ta gyada mata ta juya da dan sauri zuwa inda yake tsaye,murmushi ta kuma saki dai,bata taba jin soyayya ta burgeta ba sai yau.
" me yasa aka banbanta muku dinki?"abinda ya fara tambayarta kenan,sai ta dubi rigar jikinta ta dubi ta raihana dake can dan nesa kadan da su,doguwar riga ce a jikin raihanan ita kuma fitted gown
"Kowa choice dinsa ake masa damakuma ma duk daya ne yaya rayyan" kai ya gigiza
"Ba daya bane rumana,kalli shigarki kalli tata" ya fada yana tsareta da ido,sai lokacin ta kula,ko mayafansu duk da iri daya ne amma na raihana ya danfi nata girma,duk a ganinta wannan ba komai bane tunda bata fitar da tsiraici ba,ta mayar da kallonta gurinsa
"Kayi haquri yaya"
Baice komai ba ya juya ya shige motar sannan ya sauke glass din ya dubeta
"Kina iya tafiya,ki kula da kanki..."
"Insha Allah" ta fada ranta ya mata sanyi da bai mata fada ba,tana tsaye tana kallonshi har ya bar gurin sannan ta nufi gun raihana,ra'ayi ne nasu yasha banban,amma tana qoqari sosai wajen canza abubuwan data fuskanci bai dace da ra'ayinsa ba,amma yata iya dabi'arta ce tun asali a sannu take san ran komai zai sauya yadda ya kamata ta yi boyayyar dariya tana jin yadda son rayyan din ke sake ratsata,duk wani tsaruka nashi burgeta yake,bata jin za'a kuma halittar namiji kamarsa a zamaninta.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 8:55 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*Manzan Allah S A W yace "ku guji addu'ar wanda kuka zalunta,domin babu hijabi tsakaninta da Allah(ma'ana kai tsaye take wucewa,take kuma Allah yake amsata)*
______________________
*Babi na goma sha uku*
Suna shirin shiga hall din sukaji ana kiran rumana,
"Rumana dalhatu attahir" suka juya duka ita da raihanan,'yammata ne guda biyu suke nufosu fuskarsu dauke da murmushi,itama murmushin tayi ta nufi inda suke tana kiran sunayensu,kai raihana ta kada cikin zuciyarta tana fadin
"Rumana.....rumana mai jama'a".
Tare suka qaraso gun suka gaisa da raihana suka shige inda ake gabatar da bikin.
Qarfe goma aka tashi na dare,sumayya amaryar ta tsaidasu don haka kusan lokaci guda suka bar gun,motar wani abokin angon usman ce su uku kawai ya debo,rumana raihanan da kuma wata Aisha qawar sumayyan.
Rumanan ce a gaba,gaba daya da na sanin shigarta motar take saboda yadda usman ke janta da hira,tuni jikinta ya gama gaya mata inda ya dosa a matsayinta na wayayya gogaggiyar mace,wadda ta saba hulda da mutane kala kala,duk yadda ta kai ga hade ranta hakan bai damu usman ba qoqarin kafa kanshi kawai yake.
Tafiyar minti talatin suka iso qoqi,dukkansu suka bude murfin motar suka fito har da rumanan,ganin hakan ya sanya usman hanzarin fitowa tare da shan gabanta,gefe raihana ta janye ta samu daya daga cikin dakalin qofar gidan ta zauna tana kallon yadda ake ta dawowa tare da shige da fice cikin gidan,sun gama tsara ba zasu shiga cikin gidan ba zasu tsaya nan waje su jira rayyan saboda gobe suke so su taho gidan kuma ba zasu koma ba sai ranar litinin ko talata an gama biki kenan.
Tana tsaye ne kawai ba tare da tana fuskantar me usman ke fadi ba,Allah Allah take ya bata guri ta wuce,saidai kash abinda take tsoro tuni ya faru.
Motar rayyan ne ce ta shigo layin a hankali bayan ya kunna fitulun motar full light,motoci biyu ne kadai suka rage a gun daga ta usman sai ta anwar wani jikan gidan.
Tsayuwar motar rayyan din daga can baya ya bata cewa mawuyacine idan ba ganinsu yayi da usman din ba,raihana dake latae latsen wayarta batasan meke faruwa ba sai da taga haske ya cika inda suke,kallon sakanni biyar ta yiwa motar ta ahaida motar rayyan ce,da hanzari ta rufe wayar ta nufi inda rumana ke tsaye zuciyarta na tsinkewa tare da addu'ar Allah yasa bai gansu ba,ta matsa gefan rumanan cikin dabara ta rada mata ta tafi gun ya rayyan ita zata ci gaba da tsaiwa da usman zata sallameshi,gyada kai rumanan tayi cikin sarewa tare da addu'ar Allah ya sanya plan din nasu yaci,ko ta kan usman din bata kuma bi ba ta nufi motar rayyan din.
Sai da raihana taga shigarta motar sannan ta maida kanta gun usma
"Kayi haquri don Allah,rumana an yi mata miji,dan uwanta zata aura,yanzu haka shine a can yake jiranmu"sai ya saki murmushi yana dubanta
" tunda an yiwa rumana miji idan banyi kuskure ba naji tana kiranta twin sisternta,me zai hana ki canjeta"wani kallo ta bishi da shi sannan tace
"Nidin ma da nawa mijin,sai anjima" ta juya ta nufi inda motarau ke fake.
Da sallama ta shiga gidan bayan saidai tun kafin ta daidaita zamanta cikin motar gabanta ya buga sakamakon sheshsheqar kukan rumana ta ta cika motar
"Kayi haquri ya rayyan,nima ban san shi ba fa kuma ma bani....." Tuni ta fahimci kan zancan saboda haka da sauri ta katse rumana
"Ya rayyan,guri na fa yazo,ba gunta yazo ba,tsayawa tayi kawai suka gaisa sabo......"
"Ya isa da Allah!" Ya daka mata tsawar data kada hantar cikinta,runtse idonta tayi zuciyarta na harbawa da sauri da sauri,rabon da taji irin wannan tsawar tun kan tafiyarsa england
"Dukkaninku a qalla na baku shekara dai dai kusan bakwai,so ni ba yaro bane,na girmemaku bare kuce zaku dinga wasa da tunani na" ya juyo yana duban raihana,tsoro ya sake kamata,saita hade guri guda ga zatonta mangari zai kawo kata saboda ganin yadda tashi guda fuskarsa ta sauya
"Daga yau ina mai gargadinki kada ki sake bawa rumana kariya kamar yadda kika dinga mata a baya,gargadi ne ba shawara ba,idan kuma kika sake kika karyamin doka,ranki sai yafi na kowa baci" daga haka ya kunna motar yayi ribas ya jata a guje suka fice daga layin suka harba titi.
Shiru ne ya ratsa motar,sai sautin sheshsheqar rumana kawai ke tashi,wanda hakan ya daga hankalin raihana saidai tsoro ya haba qwaqwqwaran motsi,gudun da yake tsalawa da su kawai ya isa ya gaya maka tafasar da zuciyarsa keyi,cikin mintina qalilan suka iso gida,ya sauka ya tura get din gidan kana ya dawo ya shigar da motar.
Rumanan ce ta fara ficewa tana ci gaba da kukanta,ta zura qafarta a waje jiki a sabule tana shirin ficewa ya dakatar da ita
"Amir ya shigo kano dazu mukayi waya da shi,gobe in sha Allah zai qaraso gidan nan don ku gana ke da shi" ya fadi maganar cikin dacin rai
"Allah ya kaimu" kawai tace ta fice daga motar tana son cimma rumana don ta rarrasheta.
Kusan raba dare sukayi zaune raihana na aikin lallashi rumana na aikin kuka da qunan zuciya,hakan ne ya jawo tilas washegari suka haqura da tafiya gidan hajiya babba su kwana suka barwa washegari,sannan kuma ga maganar zuwan amir wanda har ummu ta sani.
Washegari Allah yasa rumana tatashi cikin kuzari da qwarin jiki saboda jin labarin zuwan amir din gurin raihananta,sai kuma kasalar ta koma kan raihana,hakanan takejinta wani banbarakwai wai ita zata tsaya zance da wani,wanin ma da ake fatan ya aureta,kusan duk wani shiri da ya kamata raihanan tayi na zuwan amir din rumana ce ta gabatar da shi,har ummu na tsokanarta
"Irin wannan canzawa haka raihata(da yake haka take kiranta wasu lokutan idan zata jata da wasa)sai kace wadda akace an bada ita amir din ya kawo sadaki?" Murmushi tayi cikin jin kunya tana sunne kai
Rumana ce ta sanyata a gaba kan wallahi yau ko zata mutu ta dawo sai tayi kwalliya,akan me,raihananta mai kyau da aji amma ta dinga boye baiwar da Allah yayi mata,badon taso ba don kada ta bata ran rumanan ta haqura ta zauna ya fara gyara mata fuskar.