← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 66

Sashe 65

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallamar daddynsu rayyan ce tasa suka cika da murna,indai suka ga ya sake fitowa a irin wannan lokacin to ranar shi zaya kaisu makaranta da kanshi kenan,duk da yake akwai driver amma wani lokaci shike kaisu don ua binciki yadda karatun kowannensu ke tafiya cikin ajinsa,yaji idan akwai mai wata matsala yayi gaggawar kawo gyara,da daya da ya suka gaidashi mazan na bashi hannu suna musabaha duk da cewa duk asubar duniya shi zai tada su su wuce masallaci tare da mazan,matan kuma suyi tasu cikin gidan,idan ya dawo su gaisa sannan ya sake komawa ya kwanta agun wadda keda girki idan ba fitar wuri zaya yi ba.

Har suka gama gaisuwansu da karadinsu mimi rumana na gefe tana kallonsu,murmushi ya saka ya isa gareta don yasan da alama yau ma an tafka tsiyar da ita
"My little angel waye ya tabamun ke" kafin tace wani abu affan yayi karab yace
"Maamaa ce(haka suke kiran raihana),an zuba mata nata abincin taqi ci ta dinga sawa anty islaha hannu a cikin nata tana jagwalgwala mata,maamaa ta mata magana taqi ji sai ta duketa"
"Ayyah my lil angel,yau kam ni da maamaa ne,amma me yasa idan aka ce ki bari bakiji?,ban hana irin hakan ba?" Ya fada yana zama seriouse
"Ai nikam daga wannan term din idan yara suka gama exam aka shiga sabon aji mimi ta gama zaman gida,makaranta zata fara zuwa,qiriniyarta ya isheni haka nan,sai shegen baki da surutun tsiya"ta fada tana fitowa daga kitchen dauke da lunch boxs din affan da ya manta.

A hankali ya daga kai ya dubeta,duk da cewa cikin kayan barci take maroon colour don sai ta sallamesu take iya wanka sai yaga ba qaramin kyau tayi masa ba har baisan sanda ya kashe mata ido daya ba yana jifanta da wani kallo,da ido ta masa alamun akwai yara fa agun,tuni islaha taga 'yar maganar da ake da ido,dariya ta dan saki saboda yadda zamantakewar gidan nasu ke birgeta,hakan yasa ta miqe ta fara tattara kan qannan nata zuwa wajen mota bayan ta dawo ta gyara inda sukayi breakfast din sannan ya sunkuci mimi tana fadin
" muje lil sis dinmu ki rakamu kinji,daina kuka haka"tuni ta ware dama akwai son yawo.

Yarinyar na qarasa ficewa yayi hanzarin jawota jikinsa,ya rungumeta tsam yana sinsinar wuyanta da jikinta baki daya wanda ke fidda qamshin turaren barcinta
"Wannan kyau haka maamaan yara,meyw sirrin ne?" Murmushi ta saka
"Wani kyau a kayan bacci,ki wanka banyi ba fa hidimar yaranka ta hanani sakat" hannunshi ya dora saman cikinta yana shafawa sannan yace
"Um_um,kodai na sake ajiya ne anan" dariya ta saki tana qwacewa daga jikinsa
"Rufamin asiri don Allah" murmushin ya saki shima ya harde hannunsa yana kafeta da ido
"Meye abun rufin asiri a ciki,i need more,ina so naga gidan nan ya cika da yara fa kinsan ni daya ne gun ummu ko kin manta"
"Yara takwas sun isheka my man don Allah" kai ya kada
"Allah ya sani ina son qari da gaske kuma nake,ki shirya yau da wuya idan ban baki ajiyata ba kamar yadda nake zaton na bawa sisinki,tana can tana zazzabi"
Idanu ta zaro tana dubansa
"Ayyah my man kuma ka barta kwance ita kadai?"
"Bacci takeyi" sai ta saki ajiyar zuciya tana mata addu'ar Allah ya tsaida mata wannan,hannunta ya sake kamowa ya kashe mata ido daya
"Na gaya miki yau ki shirya sosai,ki shirya karbar ajiyata kema,dama naci alwashin kaiku labour room tare keda sisin taki"ya qarasa maganar yana dariya qasa qasa tare da kama siririn hancinta ya dan jashi kadan,qasa tayi da kanta tana murmushi bayan ta dunqule hannunta ta dan daki qirjinsa cikin wasa,hannunsa ya sa ya dafe gun a shagwabe yace
"wayyo" da sauri ta dago tana dubansa bayan ta ware idonta a kansa alamun lafiya?
"So kike ki fasa min zuciyar,bayan ta cika taf da qaunar raiha ita da sisinta,riritata kawai nake don kada ta fashe" sosai maganar tasa ta bata dariya,jin taku ya sanyata janye jikinta da sauri,majid ne ya shigo ya nuna agogon hannunshi yana cewa"daddy zamuyi latti fa yau"
"Ok muje abdul majid" yaron ya juya ya fice rayyan din yabi bayansa yana cewa ta tanada masa abun kari kafin ya dawo,bata iya zama ba sai da taje duba sisinta,saidai ta taras da ita tana bacci,don haka ta dawo tayi aikace aikacenta don basu yarda sun dauki mai aiki ba,ta hadawa rumana source din hanta zalla saboda taji dadin bakinta,sannan tayi wanka ta tsara kwalliya kamar yadda suka saba
.

Ta kowanne bangare ci gaba da qaruwar arziqi ne ke riskarsa,sirrin hakan baya ga addu'ar iyaye ga dimbin jama'a da yake taimakawa iyalinsa sune na biyu,kyakkyawar DANGANTAKAR ZUCI da ta fili,fahimtar juna,goyon baya kwanciyar hankali da nutsuwa da yake samu daga garesu ko da yaushe suma wani sirri ne na qaruwar arziqinsa.

Weekend ne yau,rayyan kan wuni a gida ya sake shida matan nasa,kasancewar yaran kan je weekend lokaci bayan lokaci mabanbantan gurare,misali ga islaha tafi ganewa ta tafi wajen hajiya babba tsohuwa mai ran qarfe can qoqi ita da sagir sune mutanenta,rumana mimi kuwa sarkin rigima mama ce (maman rumana)ke iya mata,don ummu tarkato musu abarsu take ba'a qulla abun arziqi da ita,ummu salma dama ita kyanwar lami ce ba cizo ba yakushi tana gun ummu ita da affan,abdul majid kuwa shi bai da zabi duk inda ta raya masa tafiyarshi yake,gidan sai ya zama isu isu suma su samu su wataya yadda suke so,amma mafi yawanci sunfi yin hakan a weekend din qarshen ko wanne wata,wanda daga nan ran lahadi da yamma zai dibi matan nasa subi kowanne gida su dauko yaran nasu,daga nan kuma su wuce asibiti ko gidan marayu ko gidan nakasassu suyi ziyara,manufar hakan don dasa tausayi da jin qai a zuciyar yaran nasu tun suna qanana,su dinga ganin irin baiwar da su da suke garau Allah ya basu don su kasance ko da yaushe masu godiya a gareshi.

Yauma hakan ce ta kasance,hudu da minti goma suka fito tsaf,rumana da raihana na sanye sa baqar doguwar riga mai azabar kyau da tsada,sau tari shigarsu takan zama iri daya ne musamman idan zasu fita,kowaccensu tayi kyau ta sake cika da kwarjini da kamala ta cikakkiyar mace wadda hankali da nutsuwa ya lullube,tare suka jero har cikin motar raihana na tsokanar rumana wadda ta fara nauyi yanzun,rayyan na zaune cikin motar yana kallosu ta madubi,ranshi fes yana godiya ga madaukakin sarki da kullum yake sake hade masa kan matan nasa.

Kai tsaye gadon qaya suka fara sauka gidansu rumana suka dauki mimi,sannan suka sauka a qoqi suka dauki sagir da ummusalma wadanda
hajiya babba ta cika da su goruba,taura,kurna,magarya da sauran kayan da yaran basu samu,daga can kuma suka tafi gidan ummu wanda ke cikin nasarawa wanda rayyan din bai jima da gina musu shi ba,a can ne suka dan jima kadan saboda sun tarar da abba yana gida,sun sha hira abinsu kam farinciki na cika zuciyar abban na ganin yadda rayuwar yaran nasa gaba daya tayi kyau take tafiya yadda ya kamata,sun sha albarka da addu'o'i,anan ya sanar masa tafiyarau nijer daya tsara dukansu a qarshen sabon wata don zuwa duba dangi,hakan ya yiwa abba dadi sosai yace"kaga ma yayi daidai da nadin da za'a yiwa babanka nasiru shima qarshen sabon watan ne,sannan ya sake dibansu,mota ta cika kenan gida ya dawo full,tuni suka cika motar da karadi da hayaniyarsu kowa na tashi sabgar,rumana ce kusan uwar gayyar ita ke iya ji da kowa,yayin da raihana ke saka musu ido saboda ta fuskanci yaran irin uwarsu rumanan ne 'yan hayaniya ne kada ma takwararta ita da abida suji labari,har gwara islaha da majid.

Ganin cewa sunfi kusa da asibitin nasarawa yasa rayyan din ya yanke shawarar su nufi can kawai suyi ziyara wa marasa lafiya.

Sau uku tana sake kallon gadon zuciyarta na gaya mata bashi bane,ganin isowar fatima gun dauke da baby a kafadarta wadda da alama diyarta ce ita ta sanya zuciyarta wasi wasi,jin an dafa kadarta ya sanyata waiwayowa,fuskarta fadade da fara'a fatiman ke gaida raihana,sai tarasa inda zata sanyata sabida dadi,don har yau suna qaunar raihanan
"Waye baida lafiya?" Raihana ta tambayi fatiman tana amsar babyn dake hannunta,sai ta juya ta kalli mutumin dake yashe saman gado kamar ba halittar bil'adama ba,hawaye ya silmiyo mata tasa hannu ta share
"Kema baki gane ya ammar ba ko anty raihana" duk da ta zaci hakan amma ba qaramin girgizata maganar tayi ba,jikinta yayi matuqar yin sanyi,kafin ta tambaya fatiman tace
"Dabi'ar nan tasa da bai bari ba anty,bayan rabuwarku bai sake dawo mana ba sai da ya fara cuta,kin ganshi har yanzu an rasa gane wace iriyar cuta ke damunsa,iyakacin gwaje gwaje anyi amma a banza kullum abun qara gaba yake,kashi da fitsari duk fita yake tako ina babu banbancin guri,ga wasu tsutsotsi da suke fita masa babu kyan gani jazur da su,duk sanda suka soma fita haka zaita qaraji saboda azabar cizon da suke masa,wani lokaci cikinsa idan ya kumbura kamar an saka masa wani abu,kin ganshi anty raihana sai ido babu um babu um um" ta qarasa maganar hawaye naci gaba da fita,tausayi sosai ya kama zuciyarta,babu shakka ta tausaya masa,suka hada ido idanunsa qur ita yake kallo hawaye na fita daga idanunsa,da alama magana yake son yi mata amma babu baki,zuciyarta ta karye hawaye ya fara fita a idanunta,duk da bata tsinci komai a zamanta da ammar ba amma bai taba cuaguna mata ko cutar da ita ba
"Inna hajjaju" kai fatima ta girgiza
"Hajjaju na nan har yau taqi koda zuwa ta ganshi,ko maganarsa bata so ayi mata,kamar yadda taqi yarda a gayawa kowa bai da lafiya,daga ni sai sa'ida sai anty sa'adah muke dawainiya da ciwonsa" cikin zuciyarta take jin tabbas yana buqatar taimako,taimakon kuwa shine na yadda za'a ja hankalin hajja tazo gareshi,ta yafe masa ta kuma yi masa addu'a ko zai samu sassaucin halin da yake ciki,a haka rumana ta iskesu,suka gaisa da fatiman ta tambayeta mai jiki suka wuce ba tare data fuskanci waye kwance saman gadon ba.
Chapter 65 · 0% Book details