Sashe 8
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da taga hudu saura babu motsin rumanan, hakan ya sanya ta miqe tace zata leqa dakin hajiya qarama ta tuna mata qarfe hudu zasu tafi saboda wankin kan da zasu biya,ko da ta shiga hajiya qaraman kawai ta tarar zaune,ta sanar mata ai tun qarfe uku suka fice ita da shukran don haka ta juya ta koma daki,har hudu basu dawo ba don haka tayi kiranta
"Ina kuka shiga ne lokaci na tafiya zamu saloon"
"Bari kawai sis,muna cikin nasarawa,shukra na raka wlh"
"Kika rakata ina?"
"Kedai share kawai,new catch tayi sis sai nazo zaki sha labari" tsaki taja a ranta tana fadin"Allah ya sawwaqe muku"
"Kiyi sauri dai kawai"
"Kada ki damu muna hanya"
Ganin har biyar na neman yi babu rumanan ba dalilinta yasa ta tura mata texs na ta tafi su hadu kawai a can,ranta ba dadi sukayi sallama da hajiya babban don ta tsani tafiya ita kadai inda ta gaya mata zasu hadu da su a can,fada sosai hajiyan ta dinga kan don me zasu zo tare ta fita shegen yawo ta barta ita daya,murmushi kawai tayi "ai ba komai hajiya,tare zamu koma gida", kayan amfani irinsu kuka kubewa karkashi da man shanu hajiyan ta baiwa raihanan tace ta kaiwa fatiman,tace tana gaidata,ita kuma ta dauko atamfa novou ta bata,godiya tayi mata kana ta leqa ta yiwa hajiya qarama sallama,itama fadan ta dinga amma ta gaya mata abinda ta gayawa hajiya babban,ita dinma kyautar humra ta bata 'yar matsakaiciyar kwalba,hannu biyu ta karba ta mata godiya.
A hankali ta dinga takowa cikn nutsuwa kanta a qasa har ta iso bakin titin unguwar ta fara tsimayen adaidaita sahu,bata yi minti biyar da tsaiwar ba farar motar ta giftata,a hankali ta dinga rage gudu har ta gangara gefan titi ta tsaya kana ta fara ribas ta dawo da baya,sam bata ma lura ba don idonta na daya gefan tana duban motocin hayar dake wucewa.
A hankali aka sauke glass din motar mamallakinta ya bayyana,matashin saurayi ne wanda yayi amanna da zamani yake kuma amfana da shi,sanye yake da qananun kaya da hular feecap
" ranki ya dade"taji an ambata,a hankali ta maido kanta gun,ta dubeshi ga zatonta ba da ita ake ba,amma ganin irin kallon da ya tsareta da shi yasa itama ta dubeshi na 'yan sakanni
"Ko zaki iya min alfarmar shigowa na rage miki hanya?" Ya fada yana dubanta fuskarsa dauke da murmushi,gabanta ke dukan uku uku,haka take tun fil'azal,duk lokacin da wani namiji ya tsaidata ko ya furta kalmomin so ko qauna a gareta,ita kanta tasan 'yar qauyece futuk ta wannan janibin,bata iya zance ba balle akai ga soyayya,hasalima bata taba tsayawa da wani d'a namiji ba da sunan so,tsabar rashin sabo da lamarin ke dawainiya da ita,shi yasa rumana ke mata dariya son ranta,kana tace baki da maraba da mutanen daji sis,kamar ba cikin gari aka haifeki kika taso ba
"Ranki ya dade inata magana anqi amsa min" saurayin ya sake fada ganin yayi magana takai sau uku babu guda wadda ta amsa masa,ji take kamar ta tura motar tasa yayi gaba.
Kanta ta sake daukewa zuwa daya bangaren tana addu'ar Allah ya kawo mata mota,duk rumana ce ta janyo mata,cikin sa'a taga tsaiwar adaidaita sahu,shukra ce ta sauko daga ciki kana ta nufo gurin rumanan
"Afuwa sisinmu,munyi laifi afuwa,rumana tace na miki magana ki qarasa ciki ku tafi ta gaya masa inda zai kaiku" bata ko amsa ko daya cikin maganarta ba ta nufi gun adaidaitan tana jin dadin yankewar tsaiwarta da mutumin
Sai da ta shiga adaidaitan sannan ta fuskanci ya fito, yana tsaye shida shukra,wanda da alama tambaya yake mata kan rumanan saboda nuno adaidaitan nasu da yake da yatsa
Ajiyar zuciya ta saki tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da bugawa,idanunta a lumshe kana ta jingina da makaarin kujerar
"Hmmm,sisi na kenan,bisa dukkan alamu dake mutumin can ke son yin magana kika gwada masa halin,wai sai yaushe ni raihana zata bude zuciyarta ga tarin masoyanta?yaushe zaki yarda kisan yadda soyayya take da dadi,koda friendship ne raihana?" Tayi maganar cikin sigar tambaya,bude idanunta tayi kawai tabi rumanan da kallo kana ta dauke kai ta maida kanta titi,kamar bazata tanka ba sai kuma tace"lokacin da hakan ya dace"
"Amma fa kada ki manta ke ba yarinya bace,a qalla dab kike da cika shekara sha tara cif ko?,shine har yanzu lokaci baiyi ba" shiru ne ya ratsa tsakani,a maimakon ta amsa mata ma saita jefo mata tambaya
"Rumana ina kuka je?"
"Gidansu qawata jawahir,naje ganin wasu sabbin samples na lace da mamanta ke kawowa daga dubai,su za'ayi yayi wannan sallar su nakeso mu saka ni dake" ta fada cikin sigar tsokana,don tasan halin raihanan sarai,bata fiya son kayan yayi ko wadanda aka san tsadarsu ba, "daga nan zuwa gidansu sabon saurayin shukhra kuma ba nisa,sai ya leqo suka gaisa shi yasa kika ga mun dade".
Tasan hakanne don ba dabi'ar ruma ce yin qarya ba,hakanan bata iya boye mata komai,amma mamaki suke bata,qawaye da samarinsu bazata iya cewa ga yawansu ba,duka duka yaushe shukran ta hadu da tsohon saurayin ta da har ta sake wani,sai ta zabi tayi shiru don duka babu muhallin magana agurinta ciki batun,wayarta ta ciro wadda take iri daya ce da ta raihanan ta shiga nuna mata hotunan laces din
" sunyi kyau,Allah ya hore ya kuma kaimu lokacin da rai da lafiya"tace mata don kada taga kamar ta gwaleta.
Cikin wani plaza dake titin gyadi gyadi saloon din yake,don haka abakin wakekiyar qofar shigan ya saukesu,suna shigowa rumanan ta sake kacibus da wata qawarta suka tsaya surutu yayin da raihanan taja baya tana jiransu su gama,idan da sabo ta riga ta saba,da wuya su fita su dawo rumanan bata ga wanda ta sani ba,tsaki taja tana neman motar da zata jingina ganin tsaiwarsu tayi yawa,daga kanta tayi tana kallon saloon din da zasu shiga din.
Daafe yake da qarfen daya kare barandar qofar shagon da suke saida botique na maza wanda ke daura da shagon saloon din,ya kafe ta ido tamkar wani wanda yaga wata sabuwar halitta,sosai ta tafi da imaninshi tun tsaiwarta agun,karaf suka hada idanu,tayi gaggawar dauke idonta,don batason kallo ko kadan,daidai da isowar rumana suka jera sukayi soma haurawa saman.
Gyaran qafa aka yi musu da faratansu bayan wankin kai,wannan dabi'arsu ce da suka koya gun ummu,kusan duk qarshen wata tare suke zuwa,wannan karon ne tace ita sai gobe din jibi abba zai dawo daga tafiyar da yayi england ya duba su rayyan da kawu muhammadou,sai raihana da aka yiwa jan lalle iya yatsu,ita kuma rumana ka mata baqi a hannu aka mata gyaran fuska,basu fito daga gurin ba sai da aka kammala sallar magariba gari ya dan fara duhu.
Suna dab da qarasowa inda auwal yayi parking motarsu sukayi kacibus da shi.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼
[7/23, 8:39 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________
*An karbo daga abdullahi dan umar R.A yace:((naga manzan Allah S A W yana irga tasbihi da yatsun hannunshi na dama))*
________________________
*Babi na tara*
Kicin kicin tayi da fuska kana ta janye hannun rumana suka isa bakin motar ba tare da ta barshi ya furta kalma ko guda ba,don ta gama fuskantar abinda yake shirin yi
**************
Tafi mintin talatin zaune gefan gadonta tana duban rumanan wadda ke kwance ruf da ciki tsakiyar gadonta,jinta take tamkar cikin gajimare take yawo tsabar soyayya,ba sai ta tambaya ba tasani cewa da ya rayyan suke waya,indai kaga ta nutsa cikin duniyar masoya irin hakan to babu tambaya tasan ya rayyan ne ya murda kambunsa.
Sosai yadda suke gudanar da soyayyarsu take burgeta,har wani lokacin hakan yakan sata taji itama tana sha'awar yin soyayya,tana sha'awar dandanata taji yaya take,saidai tsoronta takeji,don a karance karancanta tasha cin karo da mutanr daban daban da soyayyar ta yamutsa duniyarsu,duk da tasan wataran dole tayi tunda zatayi aure,saidai hasalima har yau bata ga mutumin da ya cancan ci ta bude masa zuciyarta ba,wadda take jigo ce ga rayuwarta.
Ganin basu da niyyar gama wayar ya sanya ta daukar tata wayar ta kira layin mamanta fanna wadda take kira da ammi,zainabu ce qanwarta ta fara dagawa,sai da suka gaisa sannan ta miqawa maman,hira suka dinga yi da maman nata tana bata labarin abubuwan da suka faru a dangi da wadanda ma ke faruwa,tana jin farinciki sosai tare da kewarsu kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a can,sai da ta qone katin wayar baki daya sannan ta haqura,daidai lokacin da rumana suka kammala wayar da rayyan din.
Ta dan zubawa rumanan ido ganin yadda ta kafe wayar da ido tana kallonta,gyaran murya tayi mata a maimakon magana,a hankali rumanan ta dago tana duban raihana fuskarta qunshe da murmushi wanda yayi sanadiyyar bayyanar dimple dinta
"Mtswee,kin ganni ko sisi,duk sanda mukayi waya da ya rayyan sake dulmiya nake cikin tafkin qaunarshi,baya ga iyaye na a duniya banga abinda nakeso sama da ya rayyan ba"
"Har da ni kenan?" Raihana ta fada bayan ta miqe tana gyara shimfidar gadonta,dariya rumana ta qyalqyale da ita tana fadin"ai kalar qaunar da na miki dabab da wadda nakewa ya rayyan,kema wani sashe ce ta rayuwata raihana,babu abinda bazan iya miki ba"
"Nasan da haka,nima kuma haka kike a gareni,hasalima kin wuce hakan"
"Allah ya bar min ke sisi na" murmushi ta saki tace "ameen" tana komawa saman gadon taci gaba da karanta tarihin garin daura da take
************
Kusan tun safiyar ranar raihana ta hana kanta sakat da girke girken taryan abba,rumana na tayata idan ta gaji ta gudo falo ta sha wayarta ko ta hau charting kana ta koma.
Ba yadda ummu bata yi da ita ta zauna ta huta ba amma taqi sai data kammala,tana qaunar abba tana masa kallo ne na mahaifinta,bata manta alkhairinsa a gareta dama mahaifiyarta,ya daukesu tamkar 'ya'yansa na cikinsa,idan yana hidimta masu sam baya sakawa a tunaninsa bashi ya tsuguna ya haifesu ba,baya gajiya da hidimarsu,babu abinda suka nema suka rasa,don haka itama take qoqari taga tayi duk wani abu da ta lura abban yana so,tana jin hakan shine kadai hanyar da zata iya nuna masa jin dadinta da godiyarta.