← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 66

Sashe 64

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ihun kukan little rumana da raihana taji shi ya sanyata dafe goshinta,suka hada ido da rayyan ya saki dariya tare da kashe mata ido daya,yana riqe da hannun ummu salma daya hannun nasa kuma dauje da qatuwar tedde da ta zaba tace ya riqe mata
"Kaga abinda ka jawo mana ko daddy,sai da sisi ta gaya maka tunda last week ta kawo su ka bari yau muje iya mu da kai,kace sai mun sake kwasosu mun taho baki daya"
"Bakusan albarkacinsu kuka ci ma nace kuzo muje ba?" Harara ta watsa masa mai dauke da soyayya,rayyan akwai son 'ya'ya,bata sani ba ko hakan baya rasa nasaba da kasancewarsa shi daya tilo wajen ummu,inda Allah ya taqaita duk son yaranshi hakan bai sanya ya shagwabasu ko yayi wasa da tarbiyyarsu ba,raihana tace
"Au to ko mu koma gida ne mu barka da su?",kafin yace wani abu sai ha rumana ta zagayo inda suke dauke da takwarar tata,raihana ta dubesu
" uhmmm,Allah ku kuke sake tabara ummu,yanzu don Allah sisi ki ajjiye abdul_majid ki dauki wannan qatuwar?"
"Ba ruwanki,i tamu" cikin salon tsokana rayyan yana kashe mata ido yace
"Like mother like daughter,haka kike sanda kina qarama fa rumana,nasha fama da ke wajen qiriniya,ga wata qaramar 'yar tsallen mun samu nan" sai ji sukayi an tuntsure da dariya,islaha ce ita da Aabida wadda ke bima islaha diyar da raihana ta haifa,sai sagir wanda shine na uku shima yaron raihana ne
"Mommy dama 'yar tsalle ake ce......" Aabida ta fara fadi raihana ta katseta ta hanyar wurga mata harara
"To 'yar jarida zaki fara aikin naki ne?"
"Idan kun kammala ya kamata mu wuce hakanan zamu biya mu duba jikin abba" rayyan ya tunasar da su,hakan ya sanya raihana hada kansu rumana ta sanyasu a gaba suka nufi gurin biyan kudi.

Tana kan layi kafin a zo kanta hankalinta na kan takwararta litle rumana tana bare mata waper taji muryar matar dake gabanta kamar ta santa,biscuite din hannun yaron ne ya fadi bayan sun gama biyan kudi zasu fice ta durqusa ta dauko masa ta miqa masa,tana dagowa suka hada ido,meela ce,baki meelan ta riqe tana duban rumana
"Ashe rai kanga rai hajiya rumana?"
"Kinji maras kirki aini zan fadi haka meela,ko labarin bikinki sai bakin kausar na ji"murmushi tayi rumanan na ankare da ita,akwai alamun sauyi da nutsuwa sosai tattare da meelan,ba meelan data sani ba can shekarun baya
" kin manta an haramtamin zuwa gidanku?"murmushi ta kumayi data tuna abin
"Ai ya riga da ya wuce meela"
"Nima sai daga baya naga gaskiyar mai gidan naki"
Rumana ta kawar da zancan da cewa
"Wannan baby boy din fa?,kar dai naki ne" ta dubi yaron dake hannunta tayi murmushi sannan ta maida dubanta ga rumana
"Ba nawa bane,dan kishiyata ne" idanu rumana ta zaro tana duban meela
"Kishiya kuma meela?,yi miki kishiya akayi?" Dariya meela ta saki sannan tace
"Da labari rumana"
"Bari na biya kudi inzo inji how comes meela da kishiya har da daukar yaronta" tayi maganar suna sakin dariya baki dayansu,qarasawa rumana tayi ta biya duk bill din da yake atm din rayyan din na gurinta sannan ta damqi hannun meela suka fice.

Gefe daya suka samu daura da inda ake ajjiye motoci,meela ta kalli rumana
"Tabbas na yarda idan kana son mutum babu abinda wannan son bazai jagoranceka ka aikata ba,sanda muka hadu da adeel har muka fada cikin soyayya yana da matarsa daya da yaransa biyu,lokacin da yake gaya min hakan tuburewa nayi kan cewa bazani zauna da kowa ba saidai ya saketa,ga zatona son da adeel yake min zai yarda ya saki matarsa,saidai adeel irin mazan nan ne da suka san darajar matarsu ta gida,ya gayan ba zaya iya sakin matarsa ba,saboda babu abinda ta rageshi da shi,hakanan yana sonta kamar yadda yake sona,ganin haka ya sanya nace saidai mu rabu,yace tunda haka na zaba Allah ya hada kowa da rabonsa,na zaci zan iya rabuwa sa deel sai gashi cikin qanqanin lokaci zuciyata ta gaza daukar hakan,tilas na lalubo adeel,ya bayyanan har yanzu yana kan bakansa idan zan iya zama da matarsa da yaransa to,na amince da hakan saboda shawarar da qawata ta bani kan idan na shiga zan iya amfani da son da adeel kemin na gallaza mata yadda naga dama har ta gaji ta fita ta barmin gidan"

"Haka kuwa akayi,bayan shigata na dinga gasata,ita da gidanta amma bata da sukuni,wahala babu irin wadda ban gasa mata ba ita da yaranta a bayan idanun adeel,amma a gaban idonsa sai ka rantse da Allah duk duniya babu wadda ta kaini sonsu,hakan yasa adeel ya saki jiki da ni ya bani amanna,ke in taqaice miki daga qarshe sai da nayi sanadiyyar kamuwar daya daga cikin yaranta da cutar limoniya wanda sai a lokacin adeel ya gane me nake aikatawa cikin gidan,babu bata lokaci ya sallameni,bayan komawata gida na kasa haqura da adeel,nayita bibiya kan ya dawo da ni,yace sam baisan wannan zance ba,qarshe rahama matar tasa abun mamaki ita ta saka baki,abun ya dauren kai matuqa ya sanyayan jiki,don ban taba tsammanin cewa zata ma shiga maganar ba,ke a qarshe da ita na dinga kamun qafa,yace zai dawo da ni amma sai da amincewar rahaman,wallahi rumana na fidda tsammani amma ga mamakina sai tace ta yarda na dawo din,saboda ta yarda har ga Allah nayi nadama bisa ga yadda taga sauyawata,wallahi a lokacin babu wadda ta fado min a rai sai ke da raihana,bayan komawata rumana baki ga yadda zamanmu yake dadi ba,har mancewa nake rahama kishiya ta ce,wannann yaron dake hannu na yanzu yaronta ne wanda ya samu limoniya ta sanadiyyata,na yanke hukuncin karbarsa na kula da shi,rahama kuma ta barminshi halak malak,Allah ya jarabceni da jinkirin rashin samun haihuwa,sai cikin watan da ya wuce Allah ya dubi zuciyata ya bani nawa rabon".

Ajiyar zuciya rumana ta saka kausar ta fado mata a rai wadda itama yanzu ke aure gidan mai mata biyu ita ce cikon ta uku, sannan ta dubi meela
"Kin gani kuma kinji duk abinda nake gaya miki,baka isa ka hana Allah ikonsa ba meela,duk sanda kace sai kasa qarfin qwanjin hana Allah aiwatar da abindabyayi nufi tabbas sai ka fada wahala mai girma,ki godewa Allah da ya soki ya nuna miki hanya ya daidaita rayuwarki tun da wuri,matuqar kace zaka dinga sanya soyuwar zuciyarka gaba da tsarin ubangiji kana cikin wani hali,na tayaki murna meela ina fatan zaki dore"
"Haba rumana,aiko wani naji zai yi irin tawa kasassabar na farkar da shi...." Maganarta ta yanke sakamakon isowar raihana gurin tana dube dube da alama rumanan take nema,bata gane meela ba don haka tana murmushi tace
"Hali zanan dutse,sisi na mai qawaye,yau ke da daddy ne,duk kin wahalar masa da yara sun zagaye shoprite kaf basu ga mommy ba,affan ne yace ya ganki anan" dariya ta saka saboda tuna mata can zamanin 'yammatancinsu da raihana tayi
"To sai ku maida wuqarku,yau meela Allah ya hadani da ita" sai a sannan raihana ta dubi sashen da take,fara'ar fuskarta tadan ragu,don har ga Allah bata aon duk wani mutum da zai zama sikar ruahewar kyakkyawar alaqa fahimta da DANGANTAKAR dake zagayawa tsakanin ahalin nasu ya rabesu,tana tsoro kada meela ta sake dawowa rayuwarsu karo na biyu ta samu nasarar rarraba kawunansu,ga iyali a yanzun sun tara,yaran da suka samu kyakkyawan horo da basa rabewa tsakanin rumana ko raihana,kowacce uwarsu ce.

Ita kanta meela ta karanci raihana,sai ta saki murmushi ta miqawa raihanan hannu,jiki a sanyaye ta bata nata itana sukayi musabaha,meelan ta dora da cewa
"Ki saki jiki raihana,yanzu ni din ba meelan da kika sani bace a baya wadda batasan rayuwa ba,batasan ya rayuwa take ba,zallar quruciya kecin gangar jikinta" sai ta dubi rumana tana neman qarin bayani,kada kai rumana tayi alamar baya tabbacin haka ne,ta yadda da sisinta dari bisa dari hakan ya sanya ta sakarwa meelan murmushi sannan suka gaisa kafin daga bisani sukayi sallama bayan sunyi musayar lambar wayar juna.

Kafin su qarasa inda motarsu ke fake tana jiransu rumana ke bawa raihana labarin meela,kai kawai take kadawa tana sake godema Allah da ya kubutar dasu daga soye soyen zuciyoyinsu
***************

Kamar yadda suka tsara gidansu,wadda bata da girki ita zata kula da yaran baki daya da safe har su wuce makaranta,mai girki kuma kiji da mai gida breakfast dinshi da sauransu,ba ruwanki da hayaniyar yara ki dawainiyarsu naki kawai kula da mai gidan.

Girkin rumana ne zuwa dare ita zata amshi girkin don haka raihana ke dawainiya da yaran da taimakon babbar yayarsu islaha,yara takwas ke garesu,rumana nada uku saboda yawan barin da take samu,islaha sai abdul_majid da suke cewa majid sai ummu salma,raihana nada biyar,abida ce babba,sai sagir,sai mai sunan daddy dalhatu suna ce masa affan,sai abubakar mai sunan babanta suna kiransa musaddiq sai takwara kuma qaramar cikinsu ummu rumana,suna ce mata mimi.

Dukkansu kowa yayi neat cikin unifoarm dinsa,yara ne da ki yaushe baka isa kaga datti jikin unifoarm dinsu ko ka ganshi babu guga ba,hakan ne ya sanya kowannansu shike daukar kyautar wanda yafi kowa tsafta cikin ajinsu,yaran rayyan sunyi fice cikin makarantar saboda baya ga tsafta akwai baiwar qwaqwalwa da Allah ya bawa kowannensu.

Kowa breakfast dinshi yake ci,suna kan dining kowa yasan gun zamansa dama,raihana na tsaye kansu tana kula da kowannensu,haka take musu shi yasa sau tari tare suke cin abinci,saboda ta haka ne take iya gane wanda ke da matsala taci gyaransa,kamar rashin yin bismillah farkon fara cin abinci,ci da hannun hagu,qatuwar loma ko zubar da abinci,rumana(mimi) ce kawai ke rakube kan tata kujerar sabida yanzun raihana ta gama maketa,haka Allah ya yita da tsokanar tsiya,ita bata fara zuwa makaranta ba amma da 'yan makaranta sun tashi itama ta gama nata barcin,tsokani wancan tsokani wannan har sai sun fice sun bar mata gidan.
Chapter 64 · 0% Book details