← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 66

Sashe 51

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da dare tana shiri cikin kayan bacci yayin da shi kuma ya kammala nashi shirin yana tsakiyar gado zaune harde da hannayensa yana dubanta,gefansa take shirin kwanciya ya janyota ta fada jikinsa ya matseta,luf tayi a jikinsa don bata iya bijirewa duk sanda ya sata atarkonsa,cikin dakiya da shan mur yace
"Wai me kike nufi ne?,kina nufin don kin min tayi naqi amsa ahine kika tsiri gaba da ni?"
"Laifi nayi don na aikata hakan?"
"Ok a gurinki ba laifi bane kenan?"
"Eh tace da shi" sai ya shareta ya shiga sha'aninsa don ya fuskanci maganar take so ayita ja.

Da safe yana shirin fita ta dubeshi
"Daddy ina so naje qoqi"ya daga kanshi yana kallonta
" da daddare kuma?"
"Eh" shiru yayi sai da ya kammala abinda yake sannan yace mata
"Ki shirya da yamma kije,bayan sallar isha'i zani gidan sai na daukoki mu taho tare"
"To" tace masa

Qarfe biyar da mintina ta isa gidan,lokacin hajiya babba na zaune suna ta dambe da gyangyadi,bata so bacci ya dauketa ganin la'asar ce
"Oh ke kuma daga ina?" Ta fadi tana gyara dankwalinta da ya karkace yana shirin faduwa,sai data zauna sannan tace
"Kai hajiya,ke dai ko yaushe kamar tsohuwar 'yar jarida,ai ko sannu da zuwa kya fara yimin ko kafin tambayar ta biyo baya"
"Ah ah,to,ai dole na tambayeki,na ganki haka la'asar sakaliya" sai da suka gama 'yan barkwancin nasu sannan suka gaisa,ta miqe ta shiga dakin hajiya qarama don su gaisa,can ta tadda kausar sun baje ita da meela,baki rumanan ta kama tana fadin
"Da kyau,wallahi kuna sha'aninku,wato meel abun ma dan waken zagaye ce?" Tana dariya tace
"Kinsan Allah yanzu nake maganarki,nace mu saka rana zanje na miki wunu,dama nasan dole kimin mita" nan ta zauna cikinsu ta gamu da abokan surutu irinta,sai shida ta fito ta koma gun hajiyan.

"Nifa magana nazo muyi hajiya" ta fada tana zama gabanta"
"Yar nema,dama nasan taki ce ta kawoki" inji hajiyan wadda ke gyarawa islaha da tayi bacci kwanciyarta,lokaci daya fuskarta ta sauya kafin ta fara maganar,wanda ke nuna cewa magana ce muhimmiya,hakan ya sanya hajiyan tattara hankalinta kan rumanan
"Hajiya,kinsa cewa akwai alaqar soyayya ta shekaru tsakanin rayyan da raihana?" Sqi hajiyan ta dan ya mutse fuska
"Kamar yaya?"
"Hajiya,rayyan da raihana suna son junansu tun kafin raihana tayi auren fari,dalilin hakan ne ma ya sanyata yin auren saboda ni".

A hankali ta warwarewa hajiyan dukkan abinda ta sani,da kanta hajiyar ta sanya rumanan tayi mata kiran doctor mukhtar ta waya don ta sake samun tabbaci,shi din ma bai boye komai ba ya yiwa hajiyan bayani.

Miqawa rumanan wayar tayi fuskarta qunshe da murmushi
" alhamdulillahi rabbil Aalamin,Allah ya amsa addu'ata"inji hajiyan,sai ta sake gyara fuskarta tana duban rumana
"Ina fatan kunnuwa na bazasuji wani abu mara dadi ba dangane da ke ba,don na tabbatar ba tarbiyyar mu bace koda kin bayyana hakan" kai ta kada tana duban hajiyan
"Haba hajiya haba,kafin wani ya gayan hakan ni ya kamata na gayawa kaina,kafin na yiwa raihana halacci ita ta fara yimin,rama halacci sai dan halak,ta SADAUKARMIN da farincikinta taje ta auri wani alhalin bata da yaqinin zasu rabu,ta auri wani ta barmin rayyan din na rayu da shi har abada itama ta rayu da wancan har abada,ta SADAUKARMIN da rayyan alhalin tana tsananin sonshi don me ni zan kasa raba rayyan tsakanina da ita duk da son da nake masa?,duk yadda na kai ga kishinsa?,wannan ne kawai halaccin da zan mata,wamnan ne abu na farko da zan fara SADAUKARWA sisi na a rayuwarmu,ta dade tana SADAUKARMIN da abubuwa tun quruciyarmu,duk abinda na nuna inaso tana iya barmin shi ita ta haqura,itace wadda ta zama silar daidaituwar alaqata da rayyan a sanda yazo ya taddani mai tarin abokai da qawaye,sau nawa tana rufan asiri,tana maida laifukan dan aikata zuwa kanta?,hajiya shekara nawa raihana tayi tana jure radadin rashin wani abu kuhimmi da tafi sonsa a rayuwarta wanda na tabbatar ni a karan kaina bazaj iya jureshi ba" kai tavi gaba da kadawa hawaye na fita daga idonta
"Bani da juriya da jarumtar gami da zurfin ciki irin ja raiha amma wannan karon ina fatan na fita dukkan wadan nan abubuwa,ina fata na mata sadaukarwa wadda zata tattara dukkan wata SADAUKARWAR data taba yimin,ina fatan na bata farinciki kamar yadda ta bani,na bata faata nayin ingantacciyar rayuwa" jikin hajiyan a sanyaye take duban jikar tata,tabbas ta riga data sani kishi ba qaramin abu bane,halas ne a gun rayyan ya auresu duka,hakananbsuma suna da haqqin bawa zukatansu abunda suke so,bai kamata ba ba kuma adalci bane su rintse ido suqi kowa sai diyarsu,su take gaskiya da duk wani abu da ya kamata saboda jin dadin tasu 'yar,amma raihana mutum ce,suna jinta cikin jininsu kamar yadda diyarsu take,tana da dukkan wasu halaye managarta wanda sau tari a gunta diyar su take koyo
"Allah yayi miki albarka umma rumana,na godewa Allah da baki zama mai son zuciya ba,duka ita duniyar dama nawa take?,yaran yanzun ne suka dauketa wajen zama,ko yanzu ko anjima ko yau ko gobe dole ka barta,bayan ka barta din kuma babu abinda zai tsaya za'a fasa shi saboda kai,saboda baka nan,Allah ya sani na dade ina yiwa raihana sha'aqr auren rayyan,saboda nasan zaki samu managarciyar abokiyar zama,'ya'yanki zasu sami abokiyar zaman uwa ta gari,hakan mijinku zai samu walwala da kwanciyar hankali" kai rumanan take gyadawa tana share qwallarta sannan ta dubi hajiya.

"Amma hajiya akwai matsala,dalilin da ya sanyani tukararki da maganar kenan"
"Matsala kuma wacce iri ruma,nayi zaton daga gareki ne idan ma za'a samu matsalar"
"Rayyan ne hajiya" bata boye mata dukan yadda sukayi da rayyan din ba ta bayyana mata,kai hajiyan ta girgiza
"Barni da shi,dauki wayarki ki kiramin yusufu da dalhatun dukkansu kice inason ganinsu bayan sallar magariba,yau nake so a gamata" wayarta ta zaro ta kirasu dukkansu suka amsa cewa suna tafe daga kasuwa zasu zarto da yardar Allah,ajjiye wayar tayi tana kallon hajiya
"Amma hajiya ina neman alfarma guda daya" ba tare data jira hajiyan ta amsa ba ta dora
"Idan zai yiwu bana son raihana ta san da maganar nan,a barta arufe har zuwa wani lokaci,wallahi hajiya nasan halinta sarai,tana iya bijirewa zancan,ni na gani na ji kuma ajikina,ta sha alwashi hajiya ta kuma kage kan ra'ayinta tsawon shekaru,to na tabbata a 'yan watannin nan babu abinda zai iya sauyata,hajiya,indai raihana ce tana iya sake auren wani akan ta auri yaya rayyan" kai hajiyan ke gyadawa tana sake nazarin maganar.

Shiru dukkansu sukayi suna jin jina lamarin,zuciyar daddy dalhatu fes hakan ya nuna har kan fuskarsa,yayin da alhj yusuf shima haka tashi zuciyar take amma ya nuna kara bai bayyana ba,yana tausayin yarinyar yana tausayin maraicinta,yana ganin qimar ta yana qaunarta kamar daga cikinsa ta fito saboda nagartar da take gareta
"Alhamdulillah,wallahi hajiya na dade banji wami al'amari da ya faranta min rai kamar wannan ba,kullum da batun yarinyar nake kwana nake tashi,sai na dinga gamin kamar gazawarmu ce ta fito da ita daga dakin mijnta alhalin ruma har yau tana nata dakin,kuma a yanzu babu wanda zamu bawa aurenta mu koma ku kwanta muyi bacci hankalinmu kwance kamar rayyan din,wannan zance ya yimin dafi hajiya qwarai" ya qaraage maganar fuskarsa qunshe da murmushi,hajiyan ta sake maida dubanta ga alhj yusuf
"Yusufu banji kace komai ba" gyaran murya ya danyi
"To hajiya ai ni gani nayi ita rumana kamar bamu kyauta mata ba idan mika ce zamuyi haka" dakatar da shi tayi da sauri
"Au abinda yara suke so zamuyi ko abinda ya dace?,wa yasan da zancan ma acikinmu idan banda tazo da maganar?,muji tsoron Allah mu duba maraicin raihana muyi mata gatan da koda bayan ranmu ba zata taba tizarta ba,za kuma taci gajiyar abinda mukayi din daga kan 'ya'aya har jikokin jikoki" kai yake jinjinawa cike da gamsuwa,kusan shine mutum na farko da zaya so hakan,ba ya fadi bane saboda yana adawa da abun,kawai kara ya nuna da kawaici
"Hakane hajiya,ubangiji Allah yayi musu albarka,ya tabbatar da alkhairi,yasa albarka"
"Ameen ya Allah" sai ta kuma gaya musu alfarmar da ruman ta roqa sannan ta dora
"Ni kaina na amince da abinda ta fada din,din ta rayyan nasan yadda zan biyar da shi,amma ita yarunyar tabbas zata yita jin nauyinku,balle tana tsakaminmu zata dinga gani kamar wami abu ne,barin ma mu mata da ba'a raba mu da gutsiri tsoma,din haka bana son ta sani,koda tasan cewa za'ayi auren nata amma kada ta san cewa rayyan ne wanda zata aura din,kosu maidugurin ku barsu kawai a zuwan wani ne,idan lokaci yayi ko ta kama ko zancan ya fito ta sani" basu da damar musawa,duk abinda hajiyan ta fada ya tabbata,nasu kawai ameen ne.

Alhj dalhatu ne ta fara sanya hannunshi cikin aljihun rigarsa yana fafin
"Barima ki gani kawai hajiya" ya fiddo da 'yan dubu dubu ,duk da cewa ba sababbi bane amma ashirye suke,da alama daga banki ya karbosu zaiyi wata hidimar,a tsakaninsu ya ajjiye
"Ga sadakin dana nan rayyan,naira dubu hamsin ce" murmushin farinciki ya kufcewa hajiyan,tabbas babu shakka wata DANGANTAKAR daga Allah take,musamman idan aka gina ta saboda Allahn
"Ubangiji ya yi muku albarka,kai yusufu dauki sadakin diyarka ka qirga da kanka" shi din ma fuskarsa qunshe da murmushi ya dauki kudin,qasan zuciyarsa cike fal da qaunar bayin Allahn masu tarin karamci da sanin ya kamata,A aljihu ya sanya yana fadin
"Banu haka tsakaninmu hajiya ai babu lissafi tsakani na da dalhatu,Allah ka duba niyyarmu da nufinku ka sanya albarka ka cikin wannan hadi" basu bar gaban hajiyan ba sai da ya kira tasa mahaifiyar rahina ya fede mata komai sannan ya hadata da hajiya babban suka sake magana,itama addu'a tayi sosai tare da sanya albarka mai tarin yawa.
.

A bakin qofa sukayi kacibus da rayyan din wanda ke qoqarin shigowa gidan,cike da girmamawa da ladabi ya tsugunna ya gaidasu sannan ya shige ciki.

Sai da ya leqa ya fara gayar da hajiya qarama,rumana na dakin zaune ita da kausar suna hira,duk da rabin hankalinta ba a nan yake ba,yana dakin hajiya babba,bin bayansa tayi bayan sun gama gaisawa da hajiya qarama ya fice.
Chapter 51 · 0% Book details