← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 66

Sashe 48

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shirun da taji yayi shike bayyana mata cewa ya kammala,a hankali ta bude idanun nata,ta sanya gefan mayafinta ta goge fuskarta
" na gode qwarai doctor,na tabbata cewa badon kai ba babu yadda za'ayi nasan da zaman wannan BOYAYYEN SIRRIN,na gode"ta qarashe maganar tana miqewa tare da saba islaha a kafadarta.

A hankali take takawa zuciyarta na wani irin harbawa cakude da al'amura daban daban,a hankali ta tura dakin da rayyan din ke kwance har yanzu bacci yake,har ta zura qafarta sai ta cireta ta dawo da baya,sam sai taji ba zata iya zama ba,kai tsaye ta juya ta fice daga asibitin,motar data zo da ita ta bude ta shige sannan ta tayar da ita a hankali suka fice daga asibitin.

Cikin daqiqu suka isa gida,ta kulle ta riqe hannun islaha suka shige ciki,shiru gidan yake kasancewar babu yara,sai lantana kawai a kitchen tana girki,sannu da zuwa ta yiwa rumanan ta tambayeta ina raihana ta gaya mata tana makaranta,ummu fa?,ta sake bata amsa
"Bata dade da shiga daki ba,bacci take"
"Ok,qyale kawai kada ki tasheta" ta fada tana wucewa kai tsaye cikin falon,dakin raihana ta tura don a bude yake,bakin gadon dakin ta qarasa tana zaunar da islaha kai,sai kuwa ta bingire tayi kwanciyarta jinta akan gado,itama gefan gadon tabi ta zauna tana maida numfashi.

A hankali take bin dakin da kallo tana tuna zamanin 'yammatancinsu,abubuwa da yawa suka dinga fado mata,duk da cewa yanayin dakin ya sauya amma har yanzu gadajensu na nan da yanayin tsarin dakin,sai ta miqe a hankali ta isa ma'ajiyar hotunansu,yau tana son gani,tana son tuna wani abu,ta jawo album daya ta koma gefan gadon ta zauna.

Daya bayan daya ta dinga bin hotunan tana dubawa wadanda ba qaramin sake yi mata tasiri sukayi ba,tamkar wani tishi suka yi mata game da wacece raihana a wajenta,tazo tsakiya taci karo da littafin,zata iya tuna sanda taga raihanan na boyon littafin tare da hanata tabawa shekaru kusan uku baya,sai ta zari littafin ta ajjiyr album din ta bude littafin.

Murmushi ta dunga yi a hankali ganin yaffa raihanan ta zauna tana zana quruciyarsu,a hankali ta gangaro kan kalaman,kalaman da suka sanyata ta sake imani ta kuma miqe tsaye hawaye na fita daga idonta,a hankali ta koma ta zauna tare da kifa littafin kan fuskarta
"Dama da gaske doctor mukhtar yake?,ashe da gaske ne?,don me sisi me yasa?,wannan wace iriyar SADAUKARWA ce wannan?wace iriyar ZUCIYA ce haka?,wacce iriyar 'YAR UWA CE wannan?,me yasa kika zalunci kanki raihana,me yasa kika haramtawa kanki farinciki saboda ni?,me yasa kika sa na zama silar azabtuwar zuciyarku da rayuwarku tsawon wadan nan shekarun,tabbas na zama wawiya da na kasa fahimtar abinda sisi na ke so,na zama azzaluma da na zama silar azabtuwar sisi na,wadda burinta ako da yaushe taga taga nawa farincikin,taga cikar burina
.

Da sauri ta jiye littafin ta dauki photo album din ta maida littafin ciki ta miqe ta mayar da album din inda yake ajjiye,garin juyowa taji wani abu ya fado,a hankali ta duqa,zobe ta gani mai dauke da double R,irin nata ne sak,abinda ya rabasu da nata wannan na azurfa ne,ba shakka daga rayyan ta sameshi don da tasanshi a hannunsa daga bisani ta bar ganisa,hakanan bata taba ganinsa a hannun raihanan ba,kai ta girgiza ta maida zoben gurinsa,a fili tace
"Ya isa haka,ya isa,wannan karon fagen na rumana ne" ta fadi tana juyawa wajen da islaha take ta dauketa sannan ta fice daga gidan ba tare da ummu tasan tazo din ba.

*****************

Duk cikinsu babu wanda tace da shi komai.

Kujera ta sanya gaban gadon da yake zaune bayan ta gama bashi tea,idanunta cikin nashi take kallonsa
"Nifa kije ki gayawa mukhtar yazo ya sallameni,babu kwanan asibitin da zanyi maman islaha" murmushi tayi sannan tace
"Dama ai ko bai sallameka ba ka warke yaya rayyan,qila ko bai sallamemu ba mu gudu gida kawai,wannan ciwon daga yau ya qare yazo qarshe" cikin alamar tambaya yake dubanta,sai ta daga masa gira
"Eh,duk cutar da ta samu magani ai kaga waraka ta samu ko?,zaka samu RAIHANA kaga ya zama dole sauqi yazo" ci gaba yayi da dubanta ba tare da yace komai ba,itama kallon nasa take tana so taga reaction dinsa,saidai duk yadda yaji mamakin furucin daga bakinta hakan bai bayyana ga fuskarsa ba,abinda ya sake saka mata yaqinin lallai rayyan din jarumi ne,bata tsammaci dakiyar har haka daga gareshi ba,koda yake ba abun mamaki bane tunda ta fuskanci irin wannan dakiyar har ta tsahon shekara uku ko hudu.

Ganin cewa baida niyyar furta komai baya ga kallonta da yake yasanya cewa
"Eh yaya rayyan,wannan karon zaka samu raihana,zaka mallaketa......"
"Mtswee,wane irin zance kike irin haka ne rumana,bana son shirme da Allah?" Gira ta daga cikin alamun tambaya
"Shirme kamar yaya?,raihana ce silar ciwonka,raihana ce silar rashin sukuninka tsahon shekaru,raihana kake burin mallaka,eh.......hakan ma ba laifi bane,sisi na ta cancanta,ta cancanci hakan,tana da hakaye dabi'u da kyaun da zata samu haka,meye laifi a ciki?"
Wani kallo yake mata jin maganar da take furtawa
"Wa ya gaya miki wannan maganar?" Kai tsaye tace da shi
"Bai zama lallai kaji ba,wannan ba itace damuwarka ba,damuwarka ka samu raihana kuma zaka sameta" shigowar doctor mukhtar shi ya katse musu maida maganar da suke.

Idanun rayyan din qyar kan mukhtar,wani numfashi yaje fiddawa cike da bacin ran da baisan dalilinsa ba,kallon da yaga rayyan din na masa kadai ya sanyashi shan jinin jikinsa
"Da kyau!,baka cika alqawari ba,hakanan kaci amanar da na baka!"tsaf ya gane kan meye yake magana,don haka ya tako a hankali inda suke yana duban rayyan din
" babu wata mafita rayyan sai wannan,zuciyarka ba zata taba daina son raihana ba,hakan na nufin dawwamarka cikin cuta mai barazana ga yankewar rayuwar dan adam,don me zamu zauna mu zuba ido ka halaka bayan akwai mafita?"hannu ya daga masa ba tare da ya dubeshi ba
"Tashi ka fita,kaje ka rubutomin takardar sallamata" ya fada kansa tsaye,yasan rayyan din sarai,miqewa kawai yayi yana murmushi ya kama hanyar ficewa.

Idanunsa ya maida kan rumanan
"Ki bar maganar nan inda take"
"Zan barta matuqar ka tabbatar min bakwa son juna kaida raihana" ido ya dan zubata mata sannan yace
"Naso raihana kuma har yau ina son raihana,saidai na zamuyi aure ba kamar yadda tasha alwashi a baya
.
Da sauri ta tari numfashinsa
"Alwashin da ta sha nice sila,kuma a yanzu nice salar zamowarta matarka in sha Allah"
"Idan kuma nace ni bana so fa?"
"Ko baka so indai ita tana so to dole ka aureta,dole na bata farinciki kamar yadda ta bani"
Murmushi yayi yana kada kai
"To sai mu gani ai,zanga ta yadda zaki ma mijinki auren da ya riga yace baiso ya haqura"
"Zaka gani kuwa"rai ya hade tsaf sannan yace
" kina son bacin ranki kenan ko?"kafada ta daga
"Indai akan wannan ne na shiryawa hakan,na shiryawa duk wani abu daka shirya" ta fadi kanta tsaye,ido ya zuba mata na wasu 'yan sakanni sannan ya jinjina kai.

A hankali ya sauka daga kan gadon,ya nufi kujerar dake ajjiye gefe,ya dauki rigarsa 'yan saman ya zura,ya sanya takalmansa yana duban rumanan,itama sai ta miqe tana gyara rufin mayafinta,baice mata komai ba ya isa inda islaha ke kwance tana bacci ya dauketa ya saba ta akafadarsa,daidai lokacin doctor mukhtar ya shigo riqe da takarda,ya dubi rayyan yana murmushi
"Au da gaske guduwar zaka yi kenan?"
"Eh,banga dalilin ci gaba da zamana bane a nan"dariya mukhtar din yayi cike da tsokana
" eh kam,lallai, a yanzu baka da dalilin zama nima na yarda da hakan,tunda magani na dab da samuwa ko?"harara ya maka masa sannan ya murda qofar yayi ficewarsa,rumana ya miqawa takardar
"Ni da rayyan duk daya ne,basai kunje kun biya komai ba,wannan maganin kawai zaisha na sati biyu,kiyi qoqari madam kiga komai ya tabbata,na tabbatar kema hakan zai qara kwantar miki da hankali,uwa uba ladarki na ga Allah" kai ta gyada tare da fadin
"Insha Allah mukhtar,na gode" sannan tabi bayan rayyan.

_sai kun yimin uziri,muna hidimar biki ne_

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽[7/23, 12:51 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_______________________
*Daga ma'amaru dan abdullahi R.A:daga manzan Allah S A W yace"babu wani mai boye kaya (don yayi tsada shi kuma ya fito da shi ya siyar don ya samu riba)face mai sabon Allah"*

_muslim ne ya rawaito_
_______________________

*Babi na talatin da shida*

Tsaye take bakin titin wanda a qalla ta kusan shafe minti talatin,tun a gida yau motar ta ta mata tsiya hakan ya sanya bata ma fito da ita ba,ganin daliban da zata yiwa karatu biyu zuwa biyar da rabi na yamma ne tana ganin rana tayi sanyi,saidai ga sabanin zatonta har a lokacin akwai sauran dan zafin ranar.

Duka bama wannan ne yafi damunta ba,kusan tun shekaran jiya da abba ya kirata ya mata maganar sun fidda mata miji har sadakinta sun amsa jikinta yake a sanyaye,take yawan jin fargaba,duk da bai gaya mata waye ba ta yankema ranta sultan ne,tunda wancan satin magabantansa suka zo shima kuma asatin tafiya ta sameshi baya qasar.

Tsaki ta yiwa kanta da kanta na ganin baiken damuwar da fargabar da take ji cikin ranta,ta sake maida kanta ga titin ko zata dace,a hankali farar kyakkyawar motar ta wuce ta gabanta wanda hakan ya bata damar ganin wanda ke ciki,ba wani bane rayyan ne,kanta ta dauke tare da jan siririn tsaki haka kawai.

Karo na biyu motar tashi ta sake wucewa ta bangaren da take,wannan karon ya ganta don sun hada idanu,dauke kansa yayi kamar yadda itama tayi masa,wucewarsa babu jimawa ta samu abun hawa.

A qofar gida mai adaidaitan na shirin sauketa taga motar rayyan din fake a qofar gidan,hakan ne ya sanyata cewa mai motar ya juya da ita.
Chapter 48 · 0% Book details