← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 66

Sashe 20

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunanin da ya ziyarceta cikin gajeran lokaci tun kafim takai ga barin falon shi ya sanyata cin birki tare da tsaywa cak,wani murmushi ya qwace mata,a nutse tamkar ba ita ba ta juyo tana duban rayyan wanda itama shi take kallo,ta samu hanyar yakice rayyan cikin ruwan sanyi koda hakan shi zai dawwamar da tata zuciyar cikin kewa da damuwa,bai dauke ido daga kallonta ba kamar yadda itama bata dauke ba,wanda cikin qanqanin lokacin kallon ya sake zama guba a garesu baki daya
"Yaya rayyan"
"Yes" ya amsa yana jin dadin yadda ta ambaci sunan nasa"
"Kace min kana sona,na tabbata ka fada ne ba tare da dogon nazari kan me zaya biyo baya ba"
"Idan haka kike tunani muje a hakan ne,go straight to the point"ta kada idonta cike da farincikin samun mafita gareta mafi sauqi,wadda tasan rayyan baida mafitar daya daga cikin abinda zata gaya masa,tilas kenan ya haqura ya janye qudurinsa....

_shin haqarta zata cimma ruwa kuwa?,muje zuwa.........._

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 8:59 AM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________

*An karbo daga anas dan malik R.A yace:manzan Allah S A W yace"haqiqa ubangiji yana yarda da bawan da zaici wata loma(yaci abinci)ya godewa Allah a akanta(wannan abincin da Allah ya ciyar da shi),sannan ya sha abun sha ya godewa Allah akan sa(abinda Allah ya shayar da shi din)"*

_ruwayar imamu muslim ce_
_______________________

*Babi na sha takwas*

"Yaya rayyan,duk duniya kafi kowa sanin alaqarmu da rumana,ina son sanin yaya zakayi da rumana idan har zaka aureni?,me zaka ce da ummu da abba?,yaya zakayi da amir?,idan kuma mi din bana sonka fa?,me kuma kake son na gayawa duniya?".

Murmushi sosai rayyan din ya dinga yi har ta saki baki tana kallonsa sannan daga bisani ya tsaida idonshi a kanta
" raihana,ke 'yace ta ummu da abba kamar yadda ni da rumana muke 'ya'ya a gunsu,ina mai tabbatarwa yadda suke farin ciki da tarayyata da rumana haka zasuyi yayin tarayyata da ke,kema 'yarsu ce,rainonsu ce,amir kuwa ina tunanin kin manta cewa ni na kawo shi,ni na hadashi da ke,ni na bashi ke,to a yanzun kuma nace na fasa,sabida ni nafi cancanta da ke,hakanan ke kika fi cancanta da ni,baxan cuci kaina ba ina kallo a dauke ko a qwace abu mai qima da daraja daga hannu na ba,hannun karba hannun maidawa,mutanen duniya kuwa magana aikinsu ce,walau kayi mai kyau ko mummuna,babu wanda ke iya musu koda Allah mahaliccinmu yayi abu sai sunyi magana a kai,so ya rage gq kai dan adam kaui kawai abinda ya dace a lokacin da ya dace,ka toshe kunnuwanka daga dukkan wasu qananun maganganu ko gutsiri tsoma ta mutane"yayi shiru yana sake kallonta tate da maida numfashi.

Wannan karon cikin sanyi da nutsuwa yace da ita"Raihana!,nace miki bana son rumana?,ko na gaya miki na fasa auren rumana?,kin mance na gaya miki cewa ni rayyan mijin mace hudu ne,bayan ke da rumana ina da ikon sake auren wasu matan har guda biyu?"ya qarashe maganar cikin sigar tambaya,itama nata idanun na kanshi,wani abu mai kama da kishi taji ya tokare mata wuya,sai taji hawaye nason balle mata,inda tayi namijin qoqarin maida shi,kai ta shiga kadawa,babu shakka rayyan ya wuce duk tunaninta,yayi nisa wanda ya sanya baya ko waiwaye bare yaji kira.

Matsowa ya sakr yi sosai gabanta har tana jiyo hucin qamshin turarensa,ya narkar da idonsa cikin nata tare da yin qasa da zazzaqar muryarsa ya sake kiran sunanta,kiran da ya haddasa tashin duk wata tsiga ta jikinta
"Ina sonki raihata,inajin wani irin so na daban kuma na musamman tattare da ke irin wanda ban taba jin irin nau'insa ba,raihah......ki bani dama don Allah,ki ban damar da zan mallakeku ke da rumana baki daya,in zaunar daku qarqashin inuwata in baku kulawa bisa adalci da amana,ki bani dama in sanar da rumana da kaina.......na tabbatar da cewa yawan qaunar da take miki ba zata bata damar da zata bijirewa zamanku tare ba....raihanah,na tabbatar da cewa shakku kike cikin son da nake miki,saboda kina ganin rumana na fara so?,da rumana nake soyayya?,da ita aka sanya mana rana?,raihanahh,ban yaba zato zan tsinci zuciyata cikin irin soyayyar da take miki a yanzu ba,komai namu raihana iri daya ne,ra'ayinmu,halayenmu da zabinmu duka sunzo daya....me zaihana ki bawa zukatanmu damar da zasu rayu tare?,su morewa dacen da sukayi da juna?".

A hankali ta ware idanunta a kansa wadanda sukayi jazur,wanda ada suke a lumshe,tana dab da gazawa kan yadda yake dafata da kalamansa,ta kusa gaza jurewa ne,tana jin idan ta bashi dama ta hanyar ci gaba da saurarensa zuciyarta ba zata iya daukar nauyin kalamansa ba,zai maidata ne euwa tsundum cikim dan k'ank'anin lokaci,ruwan da bata fatan ya tabata ko kadan,don ta riga ta sani babu ta yadda za'ayi tana cikin hankakinta ta iya hada inuwar aure guda k'ark'ashin jagorancin namiji guda ita da sisinta muddin ranta kuwa.

Kai ta sake kadawa a sanyaye,dab take da sake sakin wani kukan
"Kayi mana adalci yaya rayyan,ka yiwa kanka a dalci"
"Kema ki yiwa kanki adalci raihana,kanki ya kamata ki fara yiwa adalci kafin kowa......" ya fada cikin alamu da suke nuna cewa ya fita daga hanyar lallashi ya fara hasala
"ko kinsan tunda muka fara wannan maganar har yau baki taba bude baki kince BANA SONKA ba rayyan!,zuciya ta BATA SONKA!,don haka bazan iya aurenka ba,magana daya kike RUMANA RUMANA RUMANA dai,ke ba mutum bace ruma ce kawai mutum,ke baki da zuciya a gangar jikinki!,rumana daya ke da zuciya?!"

Idanunta da suja qara girma ta sake warewa a kansa,zuciyarta na wani urin bugu tamkar mai shirin yin tsalle tayo waje,cikin wata iriyar sarqaqaqqiyar murya tace"don me bazan kira rumana ba?,don me bazan kira 'yar uwata ba,'yar uwata mai son farinciki na"
Idonshi cikin nata yace"ok,kin amincewa kanki kina son rayyan?,rumana ce shamakin tsakanin soyayyata da taki?"
So take ta gaya mishi maganar kai tsaye ba tare da shayi ba,ta yadda zata shige shi,amma tasan bata isa ta furta masa ba muddin idanunshi na cikin nata,saboda haka ta janye qwayar idonta sannan tace
"Bana son rayyan so na soyayya,bana sonka yaya rayyan,so nake maka na 'yan uwantaka ba na soyayya ba" sai kuma ta dawo da idon nata kansa
"kai,koda ina sonka rayyan NA SADAUKARWA DA RUMANA SOYAYYYAR......saboda har abada bazan iya shiga tsakanin rumana da farincikinta ba,QAUNAR dake tsakani na da ita ta siya mata komai,babu abinda bazan iya SADAUKAR MATA BA CIKI KUWA HARDA KAI YAYA RAYYAN" ta qarashe maganar hawaye na layi a kan kuncinta,saboda wani irin daci dake tasowa daga qasan zuciyarta har ya zuwa saman harshenta na sadaukar da abinda bata taba son wani abu daban cikin rayuwarta kamarshi ba,abinda ta soshi tun tana mitsitsiyarta,abinda ta soshi tyn batasan darajarsa ba,abinda ta soshi tun batasan wace ita ba,ta soshi a lojacin da take tunanin tsoronsa take,ta soshi kuma a lokacin da take zaton shirme take,ta kuma soshi a lokacin da take zaton 'yar uwarta take tayawa sonshi.

Idanunsa da suka koma launin ja kadai zaka kalla su gaya maka me yake wakana cikin zuciyarsa,da yake namijin duniya ne maimakon taga tsananin bacin ransa sai taga ya jingina da makarin kujerar da yake kai sannan ya lumshe idonsa,siririn murmushi ke fita bisa fuskarsa,shi kadai yasan azabar da yake fuskanta cikin zuciyarsa,so yake yayi cooling kansa da kansa,baison yayi magana cikin halin da yake ciki.

Kimanin mintina biyar sannan ya daga hannunshi murya can qasa yace"tashi ki tafi raihanah,tashi ki tafi"izinin tafiyar takeso ya batan amma batasan me ya hanata tashin ba,maimakon hakan sai ta cure guri guda ta saki wani kuka mai ratsa zuciya,ji take kamar ta fidda zuciyarta tayi wurgi da ita kota huta da jin abinda take ji din,tana ji tamkar zuciyarta bata yi mata adalci ba da ta ci gaba da nacin rayyan din tsawon shekaru,ta kasa mancewa da rayyan"sallamar rumana cikin falon shi ya tsinke wa raihana duk wata jijiya ta jikinta,ganin babu wanda ya amsa mata a cikinsu ya sanyata yin mamaki,rayyan dai na jingine jikin kujera idanunsa a rufe kamar mai bacci,raihana kuma na gefe guda kanta hade da gwiwa,sai ta rasa gurin wa zata nufa,wa kuma zata tambayi meke faruwa a tsakaninsu?,cikin sa'a rayyan din ya bude idonshi,saidai duba daya yayi mata ya maida idanunsa ya rufe,duka bayason ganinsu a gabansa a halin da yake ciki yanzu,yayi tur da soyayya,ashe da gaske babu abibda ke cikinta face takura qunci da raunana zukata?,da gaske dama babu farinciki cikinta?,abinda ya hanashi kula ko son kowacce mace kenan saboda a gaban idanunshi soyayya ta dinga diban karan mahaukaciya da abokan karatunsa,har dariya yake musu yace su suka cusa kansu,ya karkatar da hankalinsa kan idan ya dawo gida yana da matar dake sonsa zai aura wato rumana,ashe dan adam bai gujewa jarrabarsa,baya kuma taba gujewa qaddararsa?.

Ganin haka yasanyata qarasawa gaban raihana tana dafa kanta"me ya sameku sisi"cikun muryar kuka tace
"Kaina rumana...kaina...."
"Dauketa kubar dakin nan,don nima ta goga min ciwon" ya fada still idanunsa suna rufe
"Dama ai kai ka gayyatomu" inji rumana tana taimakawa raihana suka fice daga dakin tana mata sannu da jimamin dawowar ciwon kan tare da gaya mata tabar kukan mana,ta rasa wani raki raihanan ta koyo da take ta yiwa ciwon kai kuka haka.

Tausayinsu ne duka su ukun ya kamata,tabbas dukkansu suna cikin jarrabawa so,shi kam duk yadda kaso guje masa saidai idan bai kama ka ko ya kamaka din ba,idanunta ta rufe bayan ta sha panadol guda biyu da rumana ta bata tana mai bawa kanta qwarin gwiwa,tana ji a ranta cewa ya kamata ta zama jaruma,bai kamata ba taci gaba da kukan da babu mafita ba,bai kamata ta bari damuwa ta ruguza rayuwarta,abu mafi muhimmanci gab suke da fara jarabawa wadda daga ita zasu tafi aji na gaba,idan har taci gaba da dawwamarwa ranta damuwa to babu shakka zata samu faduwa ne,zatayi biyu babu,babu wan babu qanin.

Ganin ta rufe ido ya sanya rumana tafiya gadonta ta kintsa itama ta kwanta ga zatonta bacci ne ya dauke raihanan,abinda bata sani ba shine ko kadan babu alamun bacci tattare da ita,ko marmarin yinsa ma bata yi.
Chapter 20 · 0% Book details