Sashe 14
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kyan da raihana tayi kuwa ba qarami bane,saboda rumanan tayi amfani da kayan kwalliyar da suka dace da kalar fatar raihanan
"Gaskiya yau na qaryata da ake cewa wanda bai saba kwalliya ba ranar da yayi baya kyau,kin ganki kuwa my sisi?" Kallon kanta tayi cikin madubin,ita kanta ta yaba sosai da irin kyan da tayi,saidai a son ranta tafiso ta jewa amir din a yadda take,idan zaya sota ya sota da ainihin kyanta bana qyale qyale ba,kamar yadda take ta kuma saba rayuwarta ta ainihin gaskiya da gaskiya ba rayuwar qyale qyale ba,saidai bata furtawa rumanan ba don batason taga kamar ta kushewa qoqarinta da fadi tashin data wuni yau tanayi duk don jin dadinta.
Atamfarta ta dauko sabuwa wadda tare suka kai dinkin ita da raihanan,saidai ita raihanan ba'a gama nata ba ta bata tace ita zata sanya saboda kalar zata dace da fatarta,ba mutuminta bane dinkin riga da skert,kamar ta tunasar da rumanan sai kuma tayi shiru,hijabi ta dauko mai kyau wanda ummu tasa aka dinko musu daga zariya wanda ya dace da atamfar ta zata sanya ba tare data daura dankwalin kayan ba,riqe hijabin rumana tayi
"Haba sisi,duk wannan kwalliyar?" Wannan karon kam dole ta shigar da qorafinta
"Ki barni in sashi don Allah,kinsan dai bana son sanya riga da skert fa,bare wannan duba fa ki gani yadda ya fidda shape dina,pls my sisi kada ki hanani" sai ta sakar mata hijabin kawai.
Qarfe hudu da mintina Amir ya qaraso,bai tadda rayyan ba don baya gida,tun safe suka fice shi da abba,don haka rumana da kanta tayi masa iso suka gaisa,ta shigo da shi cikin zaure na biyu na gidan,ta shimfida masa carfet tare da gabatar masa da kayan motsa bakin da aka tanada saboda shi kafin raihanan ta fito.
Tun daga shigowarta zauren yaji tayi masifar yi masa,saboda kallo daya zaka yi kamata ka karanci yanayin natsuwarta sanyin hali da kamun kanta,ita din ma ba laifi a hakan yayi mata,duk da ba wani sonsa taji cikin zuciyarta ba,amma yanayinsa da dabi'unsa sun mata,amir nada kyau ajin farko,don idan basuyi kunnen doki da yaya rayyan dinsu ba to bazai fishi ba,dogo ne shima fari,yana da kamala a fuska da nutsuwa,sun shafe a qalla a wanni biyu suna tattaunawa,ya mata tambayoyi soaai ta amsa mishi,haka itama ya bata dama ta masa duk tambayar da taga dama,saidai sam bata jinta a sake, kunya da rashin sabo suka hanata tambayarsa komai,sannan daga bisani ne ya soma shirin tafiya.
Leda ce 'yar madaidaiciya ya miqa mata yana fadin"ga wannan babu yawa sai ayi haquri da shi,babban fatana shine Allah yasa na samu muhalli,duk da an gayan baki sauraren kowa,ina fata nine mutum na farko da zaya samu wannan damar"qin amsa tayi hakan yasa yayi rantsuwar bazai koma da kyautar da yayi niyya ba,hannu biyu tasa ta karba kanta a qas tana dada yi masa godiya,ya bita da kallo yana ji tana dade burgeshi tare da shiga zuciyarsa.
Har qofar gida inda ya faka motarsa tayi masa rakiya,saidai kafin ya kai ga shiga ciki motar rayyan ta shigo layin,hakan ya sanyashi fasa tafiya ya fito ya tarbi rayyan din fuskarsa fal annuri,ita kuma raihanan sai ta barsu nan ta koma cikin zauren ta kwashe kayayyakin da sukayi amfani tayi cikin gida
A kitchen ta tadda ummu da rumana na hada abincin dare,rumanan na murmushi ta dubi raihana da alama tana son taji kanun labaran ne,tilas amma tayi shiru ta haqura saboda idon ummu da 'yar kunyar dake tsakaninsu da ita,ummu ce ta tambayeta"har ya tafi ne?"
"A'ah suna tare da yaya rayyan"
"To Allah ya daidaita lamarin"rumana ce ta amsa da "amin".
Basu bar kitchen din ba sai da aka fara kiran sallar magariba zuwa lokacin sun kammala don haka suka fita baki daya donyin sallah.
A hankali ya tura qofar dakin nasu hade da yin sallama,sanye yake da t.shirt maroon da baqin trouser wanda suka haskashi,farinshi da kyansa ya qara fitowa,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa kamar yadda kusan dabi'arsa ce hakan,rumana dake zaune gefan gadon dauke da dan littafi ta dago ta amsa masa,gabanta ya dan fadi,wani kyau taga ya sake mata,sonshi ya sake fisgarta,da sauri ta maida kanta ta sadda tana ci gaba da kallon littafin,shima ya dan bita da kallo,sai ya dauke idonsa ya maida kan raihana dake saman darduma tana zaman tahiya,shiru ne ya ratsa dakin,kowa najin qyashin cewa dan uwansa wani abu,yayin da rumana zuciyarta ke bugawa da sauri sauri sabanin yadda ta saba,ya dan jingina jikin qofar yana harde hannayensa a qirjinsa ganin zaman tahiyar nata ya ja lokaci,idonsa ya sauka kan hotonshi dake saman gadon rumana,sai ya dan saci kallonta,har yanzu idonta na kan littafin,duk da itama satar kallon nasa take,ya sake maida idonsa bangon dakin,hoton raihana da ruma na dinne su biyu,rumana na bayan raihana ta dora fuskarta kan kafadar raihanan suna qyalqyalta dariya,dukkansu suna sanye ne da skert dogo har qasa sai ruga 'yar ciki kai gajeran hannu,sai suka dora wata mai sogon hannu wadda tazo musu har saman gwiwarsu,kansu yasha gyara ba dankwali sai siraran mayafansu dake rataye a kafada,boyayyen murmushi ya saki da ya tuna can wani lokaci baya,sanda aka yi masu gyaran kai ake ajandaf na wane yafi kyau?,sai yaji tambayar ta dawo masa kamar a alokacin rumana ke masa ita,samun kansa yayi da tsurawa gyaran gashin dake hoton ido yana son tantance wanda yafi kyau din,sallamar sallar raihanan ce ta tsinke masa zaran tunaninsa,ya dubeta yana tsaiwa kan qafafunsa sabanin dazu da yake jingine da qofa
"Me ya samu wayarki ne bata shiga?,ki hado mana abinci ki kawo mana dakina ni da amir" ya gaya mata saqon yana mai juyawa yabar dakin ba tare da ya jira ta bashi amsar tambayar da yayi mata ba.
Ta miqe tana ninke abun sallar sai suka hada ido da raihana,qwalla ta gani taf idon rumanan,a sanyaye ta ajjiye abun sallar don tasan inda matsalar take,ta qaraso kusa da rumanan
"Rumana kiyi haquri" kai ta girgiza tana murmushi
"Ko kadan bana ganin laifin ya rayyan yanzu raihana,ni ja jawowa kaina,ya riga yamin shaidar tarin abokai,kinga kuwa ko dawa ya ganni a tsaye koba kulashi nayi ba zan dauka magana muke,zan gyara matsalar da kaina insha Allahu.....ki kai musu abincin nasan yunwa yakeji,ki kuma dawo ki bani labarin amir,nasan ya rayyan ya miki zabi ingantacce" murmushi ta sakar mata kamar yadda itama murmushin ne bisa fuskarta,ta miqe ta maida glasa dinta tafice daga dakin tana jin qaunar 'yar uwarta.
Tana sallama da shi suka fara hada ido,yana zaune kan daya daga cikin kujerun falon rayyan din,ya kafe ta da ido kuwa har taji kunya kamar zata kayar da ita,daidai lokacin rayyan ke fitowa daga cikin dakin sanye da jallabiya da alama wanka yayi amir ya miqe ya karbi tiren hannunta yana fadin
"Sannu gimbiya,Allah ya saka da alheri" murmushi tayi ta juya ta fice ya bita da kallo tamkar ya tsaidata yayita kallonta.
Rayyan ya taboshi yana fadin'"to ai ta fice,sai abar kallon qofar kuma haka ko?"kai ya kada yana dariya
"Allah yarinyar ta tafi da ni rayyan,bansan kana da qanwa kamar haka ba da tuni na dade da yiwa kaina kamu"
"To ai yanzun gashi da lokaci yayi an hadun ko?" Rayyan ya fada yana sauke musu tiren a qasa ya zuba musu abincin cikin plate ya sanya musu cokula,amir ya dauki cokalin amma sai ya kasa cin abincin ya hau sumbatu kan raihanan
"Allah babban yaya don yanzu sunanka ya koma haka ka gama min komai duniya da lahira,kasan raihana irin matan dake masifar tsada ne a wannan zamanin?,irin matan dake wuyar samuwa ga mazaje?" Murmushi rayyan ya saki
"Daga haduwa yau ta yaya akayi kasan haka?" Dariya amir shima ya saki,"haba rayyan,ya kake magana kamar ka manta waye amir isma'il uba?,'yammata nawa na yi maka hasashen halayensu haduwar farko kuma daga qarshe hakanne,ka manta baiwar da Allah yayimin ta wannan fannin,tunaninka kamanninka fa,haka daga maganarka kawai nake gano inda ka dosa,ko ka mance naji wasu daga halayenta tun kafin na iso gareta,wasu kuma na gansu da idona?"shiru rayyan yayi saboda tuna amir din,wanda a da kafin su ganeshi shi da wasu abokansa kallonsa suke kamar mai aljanin gano halayya.
"Yanayin raihanan kawai da kalamanta sun isa su gaya maka wacece ita?,ban taba zaton zanyi katarin samun matar aure irinta ba,sai gashi dare daya Allah yayi min kyauta mafi tsada wato raihana,irin matan da suke zamewa kwanciyar hankali wa mazajensu,gaskiya na gode da wannan kadara mai tsada daka hadani da ita,koda raihana batasona zanyi qoqarin koya mata sona,tunda alhamdulillah ni dinne na farko data fara saurara,kenan kafa kaina agunta bazaya zamemin abu mai wahala ba,don bazanyi saken da zata subucemin ba,ina tunanin da wuya in samu kamarta idan na rasata".
Shidai rayyan cin abincinsa kawai yake yana duban amir din,yana kallon yadda ya susuce kan raihanan cikin qanqanin lokaci
" kaga babab soyayya,ka fara cikamin kunne,kaci abinnci idan zakaci ko kuma na hanaka raihanan baki daya naga ta tsiya"ido ya zaro yana fadin
"Gwara kayimin ai kowanne irin hukunci da kayimin wannan kasassabar" ya saka cokalin da tun dazu yake riqe a hannunsa ya soma cin abincin duk da haka bakinsa ya gaza yin shiru
Daga gunsu rayyan din sai ta samu kanta da nufar dakin ummu,magana takeson tayi da ita wadda zata kawo qarshen komai kowa ya huta.