Sashe 45
Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Qarfe tara na saafiyar ranar yana zaune a falon abban nashi,sakamakon kiransa da yayi jiya yace yana son ganinsa da safe,tunda sukayi wayar hakanan yaji hankalinsa ya gaza kwanciya,sanye yake da voile na maza light green wanda yayi luf ajikinsa ya masa kyau,sumarsa tayi kyau gwanin sha'awa tana ta zuba sheqi kasancewar bai sanya hula ba,jaridar abban ce riqe a hannunsa yake dubawa lokaci lokaci tare da jiran fitowar abban,har ummu ta shigo suka gama gaisawa ta fara jera ma abban kayan kari bai fito ba.
Sanye da dogon hijabi mai hanni ruwan sararin samaniya,fuskarta tayi fayau da 'yar rama kadan da tayi,fitowarta kenan daga wanka tazo daukar kayan karin zata karya don zata shiga makaranta ta qarasa wasu ayyuka na dalibai da bata kammala ba ummu tace ta sake daukar wani flask din ta zuba kunu a kai falon abban,batasan wanda za'a kaiwa ba ta shigo ne kawai hannunta dauke da flask din,cikin jikinsa yaji alamun shigowarta,ya daga kansa ahankali idanunsu suka hadu,ba zai iya tuna kwanaki nawa rabon da ya ganta ba,zai dai iya tuna haduwarsu ta qarshe ita ce ranar da ya maidota gida daga gidanshi,yaso dauke idonsa daga kanta amma sai ya kasa kamar yadda itama taso daukewar ta gaza,can qasan zuciyoyin kowannansu kewar dan uwansa ke taso masa ba tare da sun ankara ko sun yarda da hakan ba,shi ya fara jarumtar dauke kansa wanda hakan ya taimaka mata ta qaraso inda zata ajjiye flask din ta ajjiyr,can qasan maqoshi ta gaidashi ta amsa mata cikin basarwa ta juya ta fice a hankali.
A shirye abban ya fito da alama shirin fita ya gama yi,ya zauna yana janyo tray din da aka shirya kayan karina akansa gabansa yana cewa
"Irin wannan sammako haka rayyan,daka bari ma sai ka taso daga aikinka ai duk daya ne ina gida" murmushi yayi yana shafa sumarsa
"Ai abba gwara dai na fara zuwa din"
"To yayi kyau" inji abban yana qoqarin bude flask din kunun,rayyan yayi hanzarin karba ya bude ya zuba musu a kofi guda biyu yana fadin
"Abba barka da asuba,an tashi lafiya?"
"Yauwa rayyan barka kadai,lafiya qalau ya gidan ya iyalin" "suna nan lafiya abba,suna gaidaka"
"Masha Allah muna amsawa da kyau" ummu ce ta shigo dakin ya abban ua dubeta,
"Jeki abinki fadimatu,yau tare zamu karya da rayyan kada ki damu" murmushi tayi sannan ta amsa ta juya ta fice.
Suna karyawar abban na tambayarsa game da aikin ginin kamfaninsa
"Abba ai baka samu har yau ka shiga ka duba ba"
"Kaidai bari rayyan,sabgogi ne sukayi yawa,amma zan shiga na gani,gida ma can nijer nakeso mu je gabaki daya,an kwana biyu ba'a sada zumunci ba,amma hidima tayi yawa ta hana"
"Gaskiya kam abba,nima ina maganar ya kamata muje din,an kammala ginin kamfani abban,yanzu haka abinda ya rage kawai injinan da za'a zuba,sai ma'aikatan da za'a dauka tunda tuni gwamnati tayi masa rijista dama,suma injinan shekaran jiya nayi cinikinsu ta internet a wani kamfani ,lokaci kawai nake so na samu muje ni da mukhtar mu dubasu mu aunosu a kawosu a kafa"
"Yayi kyau,yayi kyau,Allah ya taimaka yayi muku albarka,sannan yayi muku jagora"
"Ameeen ameen abba" ya amsa yana maijin dadin addu'ar da yayi masa,zancan da suka dinga tattaunawa kenan har suka kammala karin rayyan ya adana kayan a gefe sannan abban ya dubeshi.
"Abinda yasa na kiraka rayya,kan maganar qanwarka ne raihana" sai ya daga kai da sauri ya dubi abban sabida rawa da yaji zuciyarsa tayi
"Ka dade da sanin wace raihana agurinmu,marainiya ce wadda take amana ce a gurinmu,koda baka da wayo sosai amma ma tabbata kasan mahaifin raihana gaba da baya,to duka ba wannan ba,burin kowanne uba shine diyarsa ta samu gidan aure mai nagarta,miji mai nagarta,rayuwa mai nagarta,Allah ya sani fiye da haka na yiwa raihana sha'awa,saidai kuma ba haka Allah ya hukunta ba,kuma abinda duk ya hukunta din shine daidai"
"Gaskiya ne abba" ya fada kansa a qasa cikin zaquwa da jin abunda abba zai furta
"To,a yanzu haka akwai mutum biyu da suka fito suna neman aurenta,akwai wani yaro sultan dan gidan wazirin azare,sai kuma dan uwanta wanda ke can maiduguri wato baba ghana,dan baffanta ne" wata tsawa yaji cikin kunnensa wadda ta toshe jinsa na wasu 'yan mintina,zuciyarsa ta hau tsere,yaji jini na neman haurawa har qwaqwalwarsa,meke shirin sake faruwa?,qaddara ko sakaci?,asara yake shirin sake tafkawa karo na biyu ko kuma me?,abubuwan da ya ringa nanatawa kansa kenan,kusan duk wani bayani na abban baijishi ba sai da ya ambaci sunansa daga qarshe
"Rayyan"
"Na'am abba" ya amsa bakinsa na bari,lebansa na rawa
"Nayi nawa binciken a kansu baki daya babu mai wata matsala,amma gudun sake tafka kuskure karo na biyu ya sanya na baka dama kaima kaje kayimin naka binciken a kansu duka su biyun,tunda ku yaran zamanine kusan kun fimu ido da sanin dabaru,babu wani abu da za'a iya muku alaye a cikinsa,kada ka manta.......RAIHANA MARAINIYA CE KUMA AMANA CE"
"to abba....to abba....in sha Allah" abinda yaji yana nanatawa kenan tare da miqewa kamar wanda aka tsikara,dubansa abban yayi
"A'ah,har tafiya kuma?"
"Eh abba,a huta lafiya"ya fada da hanzari yana ficewa don yanajin zai iya faduwa a duk sanda yaci gaba da tsaiwa gabansa
"To" abban kawai ya fada tare da binsa da kallo ganin sauyawar da yayi lokaci guda,janye idonsa yayi ya miqe yana hada takardunsa da zai fita da su.
Kusan da qyar ya kai kansa a sibitin mukhtar din,wanda cikin sa'a ya sameshi yana nan,kusan tunda mukhatr din ya tallafoshi ya fito da shi daga motar ya fara daina gane abubuwa sosai,duk tambayar da mukhtar din yayi masa babu wadda ya iya amsa masa,ganin tambayoyin basu da amfani ya sanyashi fara bashi taimakon gaggawa,sai daya tabbatar bugun zuciyarsa ya daidaita sannan ya kaishi wani daki na musamman ya jona masa qarin ruwa,ido kawai ya zubawa rayyan din,ashe da gaske akwai irin wannan soyayyar a duniya?,eh gata kuwa yana gani akwai din,amma daidaikun mutane Allah ke jarabta da ita,wani irin so ne da baya badin zuciya ta huta,baya taba baiwa zuciya 'yanci,sone da kakejin idan ka sameshi ka samu komai idan ka rasashi ka rasa komai(kada kuyi tunanin matsanancin so irin wannan cikin littafi ke kawai,a'a a zahirance akwai wadanda Allah ke jarabtarsu da irinsa,saidai a kaso dari kaso uku ne suka gamuwa da irinsa,naga mutane hudu irin hakan).
Tausayin rayyan ne sosai cikin zuciyarsa,tsoronsa daya kada zuciyarsa ta gaza daukar damuwar dake cikinta,tabbas so ba qarya bane,duk yadda kakai ga son fiddashi cikin zuciyarka hakan bai yiwuwa komai dadewar zamani kuwa,har zuwa azahar rayyan na barcin,so yake ya fita ya duba wasu allurai na zai masa idan ya farka a wani pharmacy can hanyar zaria road kuma baya son barinsa shi kadai,dole ya dauki wayar rayyan din ya duba lambar rumana don tazo ta kula da shi kafin anjima ya sallamesu,don sau tari da yayi irin wannan baccin dare yayi ya farka yana iya komawa gida.
Tana zaune islaha na kan cinyarta tana raba mata kanta gida biyu tana matse mata shi da ribbom kiran ya shigo
.
Murmushi tayi tana daga wayar ganin sunan wanda ke kiran ta kara a kunnenta.
Kasaqe tayi jin ba muryarsa bace,hankalinta atashe ta shiga tambayar mukhtar din,ya kwantar mata da hankali kan cewa ba wani abu bane,tazo tadan zauna da shi basai ta sanarwa kowa ba,da hanzarinta ta haura sama ta sauya kayan jikinta ta rufa hijab ta sunkuci islaha suka fito,driver dinsu baya nan a lokacin tilas tayi shahadar quda don na qwarewa tayi can ba wajen tuqi ta tuqa su.
Cikin ikon Allah kuma suka kai lafiya,hawaye ne ya subuce mata tana kallon rayyan tare da girgiza kai,a yau kuma zuciyarta ta qure haqurinta,kawaicinta ya gaza,tana son sanin damuwar mijinta,tana son tasan meke taba ransa,bata kuma shakka mukhtar ya sani,ta waiwaya ta dubeshi idonta na fitar da hawaye
"Mukhtar,na gaji hakanan,na gaji da wannan qumbiya qumbiyar,inason sanin wane hali mijina ke ciki?,inason nasan mene damuwarsa me yake damunsa"
"Calm down rumana,kawai lalura ce......" Dakatar da shi tayi ta hanyar daga masa hannu
"Kada ka gayan haka,kada kacemin babu komai,mukhtar wallahi zan iya hadaka da ubangiji idan baka sanar da ni ba" sai tayi sanyi da muryarta
"Yanzu a matsayina na matar rayyan idan bansan damuwarsa na wa kake so ya sani?,idan ban damu da shi ba wa kake so ya damu da shi?,kafa fa ka manta shine uban 'yata,haba mukhtar,ka taimaka ka gayamin na fita daga kokwanto da rashin kwanciyar hankali,a qalla ko bazan iya bashi lafiya ba ai zan masa addu'a,zan kwantar masa da hankali duk sanda damuwar ta motsa masa" shiru mukhtar din yayi yana auna kalamanta,tabbas gaskiya ta fada,saidai ya ruga da ya yiwa rayyan din alqawari tun ba yanzu ba sirri ne tsakaninsu
"Rumana,ba wai wani abu yasa na qi gaya miki ba,na riga na yiwa rayyan alqawarin rufe maganar can wasu shekarun baya...."
"Indai don wannan ne wallahi Allah na yi maka alqawarin rayyan bazai taba sanin cewa kai ne ka gayamin ba,na maka alqawari kuma tsakani na da Allah" shuru ya sakeyi sannan ya gyada kai ya duqa ya dauki islaha dake ta carkwada masa surutu sannan yace ta biyoshi,yana gaba yana taya islahan surutunta har suka isa office dinsa.
Kujera ya nuna mata yace ta zauna sannan shima ya samu wata ya zauna yana dubanta
"Rumana,ina da yaqinin kina da ko kuma zaki iya bawa rayyan magani idan har da gaske kina sonshi ya kuma warke sumul tamkar babu wani abu da ya taba damunshi"
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:51 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*
*wattpad:huguma*
*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_______________________
*Daga ma'amaru dan abdullahi R.A:daga manzan Allah S A W yace"babu wani mai boye kaya (don yayi tsada shi kuma ya fito da shi ya siyar don ya samu riba)face mai sabon Allah"*
_muslim ne ya rawaito_
_______________________
*Babi na talatin da shida*