← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 66

Sashe 19

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miqewa yayi daga kashingidar da yayi wanda baisan sanda yayi hakan ba
" subhanallah,me ya sameta?"ya fada yana zare ido,itama sai ta narke masa damuwar rashin lafiyar raihanan ta sake tabata,hakan suke dukkansu idan waninsu baida lafiya sun damu da juna,
"Zazzabi yaya,ga ciwon kai,amma zuwa yanzu zazzabin ya sauka sai ciwon kan",sai ya maida idonsa ya lumshe yana jijjiga kai ba tare daya bude ba yace" je kikai kayan hannunkin in shiga in dubata"
"To" tace sannan ta fice daga falon,sai lokacin ya bude idonsa yana binta da kallo,babu wani abu da ya sauya dangane da rumanan a cikin zuciyarsa,yana jinta yadda take dai,tabbas babu ko tantama maganarsa ce ta haifar mata da lalurar,amma baya jin akwai wani abu da zaya sanyashi sauya ra'ayinsa,babu gudu babu ja da baya,da rumanan da raihanan duka halalinshi ne,addini ya bashi damar aurensu baki daya.
Miqewarta kenan daga kan gadon zata shiga toilet tayi fitsari suka shigo,rayyan dinne a gaba rumana na binsa a baya,suna hada ido taji kamar an maidata an zaunar,jikinta gaba daya ya dauki rawa tayi qas da kanta,gaban dresaing mirrow dinsu ya je ya zauna wanda shike facing raihanan,idanunshi fes a kanta yana dubanta,kanta babu dankwali hakan shi ya bawa hargitsatstsen gashinta damar bayyana,sai yaga har rama ma tayi
"Sannu ya jikin?" Murya can qasa tace"da sauqi"
"To Allah ya qara afuwa"
"Ameen" rumana ta karbe zancan
"Don Allah ya rayyan kayi mata magana,yau daya don tana ciwon kai sai kuka take kamar yau ta fara cuta?"sake tsareta yayi da ido cikin nutsuwa yace
" wai haka?...."shiru tayi babu amsa hakan ya bashi damar dorawa
"Take it easy raihana,kada ki qarawa kanki stress kinji,duk abinda Allah ya rubuta bazai taba kankaruwa ba,kuma ba kai kake dorawa kanka abu daga Allah ne,ballanta na abu irin wannan,so kada ki damu ki tsaida kukanki hakan shi zaisa ki warke da wuri,kuma ita rashin lafiya duk qanqantarta kaffara ce ta zunubi,kuka babu abinda zai yaye miki face qaruwar ciwon"
"Atoh,nima haka na gaya mata" inji rumana,tuni raihana ta fahimci inda zancan nasa ya dosa,don haka ta bude baki a hankali tace
"Haka ne,na gode da shawarwarinka,amma wani abun ganganci ke jawo aikatashi,kamar yadda nayi gangancin tsawaita kuka har ya hana ciwon kaina sauka" rumana baki ta bude
"Kada kiyi sabo raihana" dubanta tayi tana jin tausayin kansu baki daya,murmushin yaqe ta sakar mata
"Kada ki damu sisi,nasan me nake fada fa"
Miqewa yayi yana yana daga kafada tare da duban rumana
"Babu gudu babu ja da baya,ba zamu kasa gayawa sisi gaskiya ba ko?" Ya fada yana dageqa rumana gira
"Qwarai kuwa" inji rumanan tana dariya,tuni raihana ta fada toilet abinta bayan tace"na gode"don kada rumana ta fahimci wani abu
"Ki kawo min abincin pls,na ji na yafe hirar yau din"
"Yes sir" ta fada tana sakar masa murmushi shima ya maida mata raddi sannan ya fice,ko babu komai a yau yana jin wani nauyi dada yake jinsa saman zuciyarsa ya ragu daka kaso dari zuwa kaso hamsin,bayajin duk wani abu da zaya biyo baya mai sauqi ne,abu na gaba da zai faru shine yarda,neman yardar raihana,wanda yasan kafin ya samu hakan zai fafata da ita bisa dukkan alamu,shi kuwa sam bazai yadda al'ada ta haramta masa halal da addini ya halasta masa ba.

Sai da ya leqa dakin ummu ya sanar mata ya dawo sannan ya wuce,bai tambayi abba ban don yasan irin wannan lokacin yana makarantar magariba ta manya,shi dinma rashin dawowarsa ne daga gurin aiki akan lokaci ya hana masa zuwan.

Kwana biyu tayi tana jinyar zuciyarta a badini wadda rayyan ya fame mata ciwon dake ciki wanda ada tabo ne yanzun ya koma danye sharkaf,sa'an nan ya cikata da tsoro da firgici,wanda kuma a zahiri jinyar gangar jikinta take na zazzabi da ciwon kai.

Cikon kwana na biyun da daddare bayan sallar isha'i bayan ta kammala bitar test din da take saka ran gobe zata je ta zana,ta zauna tana gyara musu kayan sawarsu ita da rumana,yayin da rumanan ke zaune gefe tana tayata hira,duk da tayi tayi ta hanata amma tace ta barta,tanason gobe ta tashi da qarfinta sosai don ko girkin dare ita tayi makarbiya ta karba tayi musu tunda abincin nasu dama ba wani yawa gareshi ba.

Tun da yayi sallama bakin qofar dakin nasu kafin ya kai ga shigowa gabanta ya buga,rabon data ganshi tun randa ya shigo dubata,aikin bai samun zama kwana biyun sosai,sakamakon shirye shiryen fara aiki da kamfanin da suka daukeshi zaiyi,duk da hakan a rana idan ta samu kadan daga saqonninshi to ta samu guda biyar,wadanda da sun shigo take gogesu cike da fargaba,don kowanne lokaci wayarta na iya zuwa hannun rumana,bugu da qari kuma bata buqatar abinda zai qara ruruta marurun da take jinyarsa take kuma fata da burin ya koma kamar yadda yake da.

Dif tayi har ya shigo dakin hannunshi dauke da littafin sunanu abi dawuud da alama daga makaranta suka dawo,sannu da zuwa rumana tayi masa cike da kulawa ya mayar mata da raddi shima,tilas ta danne zuciyarta itama tayi masa ba tare data dubeshi ba gudun kada rumanan ta darsa wani abun,duk yadda yaso ya kalli qwayar idonta kamar ta sani taqi bashi dama,don babu shakka yayi missing dinta fiye da yadda ya zata,bai kuma fahimci hakan ha sai da ya ganta a yanzu,tana sanye da doguwar riga amma buba wadda aka dinkata daidai jikinta,kanta babu dankwali sai kitsonta qwaya biyu daya bayyana wanda ya zuba kafadar ta ta hagu da dama
"Angel a kawomin abinci"
"Yaya yau bani nayi girki ba,sisi ce,kaga ita ya kamata ka tambaya nima yau na huta" can qasan ransa yaji dadi amma bai nuna hakan ba,saima ya juya ya fita yana cewa"nidai a kawomin abinci yunwa nakeji,banason bata lokaci"
Fuskarta dauke da murmushi tace"don Allah sisi ki amsheni yau mana tunda ke kin gama naki karatun,karatun test nima nakeso nayi,nasan kuma ya rayyan yana iya riqeni"kai ta kada ba tare data dubeta ba
"A'ah,bazan iya ba ban gama warkewa ba nima" rai ta bata sannan tace
"Haba sisi,alfarmar da zakiyimin kawai,ok na gode" ta fada cikin nuna jin haushi,rumana tafi qarfin duk wata alfarma daga gareta don haka tayi maza ta riqe hannunta
"Kaina bisa wuyana,wasa nake miki,yanzu zan cika umarninki 'yar uwa" dariya suka saka baki daya,raihana ta ciri hijabinta mai hannu ta zura ta fice,ta tsaya a tsakar gida ta hada masa abincin cikin basket na kaba da ake hada masa abincinsa ta wuce gefansa zuciyarta na bugun uku uku,a yanzu kam jin rayyan take tamkar wani dodo da bata qaunar haduwar inuwarsu guri guda,don ta tabbatar hakan bazai taba haifar musu da da mai ido ba.

Waya ta sameshi yanayi bisa alamu da mai company din suke magana,ta juya da niyyar ficewa ya dauke wayar daga kunnensa kana ya mata umarnin ta tsaya,kamar ta fice abunta amma sai taga ya zama tilas ta tsaya tunda ko banza rayyan ba sa'anta bane.

Ya kammala wayarshi tsaf ya kasheta ya ajjiye,kafeta yayi da ido yana morewa kallonta kafin daga bisani yace"me kuka dafa?"batace komai ba sai bude masa flask din da tayi,couse couse ne da miyar kayan lambu daya hada da cabbage,carrot,green beans,piece sai hanta a ciki,girkin ya masa kasancewarsa mutum mai son ganyayyaki,hakan yasa baya yarda yaci abinci tsurarsa haka babu ganye a ciki
"Zuba min" ya sake bata umarni,tana zuba abincin yana karantarta,komai a nutse sannan a tsaftace,sake qarfafawa kansa gwiwa yake yaci gaba da yaqin da ya fara tabbas shi ya cancanci ya mallaki raihana ba wani can daga waje ba.

Ta gama zubawa ta miqa masa,ba tare da yace ba taje ta ciro masa lemo da ruwa don duk ta gama da wuri ta fice ta bashi guri,ko bata sani ba tasan kallo yake qare mata,tana shirin miqewa yace "ina zuwa?"
"Daki" ta bashi amsa
"Zauna inaso muyi magana" qam ta tsaya kamar ba zata zauna ba din har sai da ya kuma maimaitawa,tamkar ta fashe da kuka haka ta dinga cikin zuciyarta,shi kuwa hakan dadi yayi masa musamman lokacin da ya fara cin abincin test din ya fara ratsashi
"Yadda kike ta daban haka komai naki yake daban raiha ta" ya fada yana kallonta tare da lullumshe ido kamar mai jin barci,da sauri ta dauke kai saboda wani yanayi da salon maganar tasa da kallon suka haifar mata lokaci guda
"Ya salam!" Ta fada cikin zuciyarta tare da maida kanta gefe guda,wasu hawaye masu dumi suka gangaro mata,abinda take qoqarin dannewa ya taso har yafi qarfinta,ta soma jin tasirinsa kadan kadan wanda hakan ya sanya take jin bazai yiwu taci gaba da zaman ba,miqewa tayi tsaye har yau da ragowar hawayen kan fuskarta
"Zan iya tafiya?"
"Ban baki izini ba" sai da ya cinye abincinsa tas sannan ya dubeta
"Kina da test gobe qarfe tara.....idan kin fito ki jirani ni zan ajjiyeki...."
"Amma tare zamu fita da rumana,duja test din namu lokaci daya ne" ta tari numfashinsa da sauri
"And so what" ya fada hankalinsa a kwance
"Ke da ita din duka matsayinku guda" kai ta shiga girgizawa ranta a bace"ba matsayinmu daya ba,ka daina fada,kuma ni din bazan jira ka ba,zan tafi auwal zai kaini kamar yadda na saba"
Zamansa ya gyara sosai sannan dubeta cikin ido
"Well,hakan zaiyi kyau,kinga kenan zai dace da lokacin da zan sanarwa kowa muradina a kanki,idan kin shirya hakan tun kafin ki gama natsuwa da tayin da nayi miki.....fine kina iya hakan,kinga komai yazo min kenan a sauqi" saura kadan numfashinta ya dauke,ji tayi kamar ma ya fada din ne kowa yaji,sababbin hawaye suka sake silalo mata,wai rayyan wanne irin mutum ne?
"Namiji ne jarumi da baya iya boye abinda ke ransa,mai jumuri da juriyar nema da samun duka abinda ya sanya a gabansa" bata san a fili tayi maganar ba sai da taji wannan amsar,kasa ci gaba da zama tayi ta tabbatar idan taci gaba da zaman zai iya fasa mata wani sashe na zuciyarta,cikin sassarfa ta miqe don ficewa a dakin.
Chapter 19 · 0% Book details