← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 66

Sashe 41

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannayensa soke cikin aljihun short neeker dinsa,kansa a duqe zuciyarsa na harbawa,baisan meye matsayin zuciyarsa a yanzu ba,yawan harbawar da takeyi ne ke damunsa,dalilin da ya sanya yake son kiran mukhtar kenan ya duba shi.

Da sauri mai tsaron qofar ya taso yana tambayarsa
"Yallabai duka su yakubun basa nan,wani abu za'a siyo maka?'hannu ya daga masa
" a'ah barshi sama'ila,katin waya ne zan gangara ma siyo"yana son fita ne da qafafunsa ya dan taka,sama'ilan ya qaraso ya bude masa qofa ya fito.

Daidai qofar gidan motar tayi parking,shi ya sake bude mata qofan wanda fes a idon rayyan,ta gefansu ya wuce yana sakeyin qasa da kansa tamkar bai gansu ba duk da yadda yaji zuciyarsa ta masa nauyi,gabanta ya tsaya yana dubanta
"Tunda bazan samu adress ba, Ataimaka a bani koda phone number ne,pls ranki ya dade,kinga ni ba mazaunin kano bane,zuwa nake na fita duk qarshen sati" tabbas a yanzi ba zata iya hanashin ba,sabida babu wani abu da ya sani a gunta baya ga sunanshi wanda sai da yayi ta magiya,kuma ta lura mahaifinsa ne ke jiransa,a hankali ta karanto masa lambobin yayi serving,ya saki ajiyar zuciya yana mata godiya,yana tsaye har ta shiga gidan sannan ya koma cikin motar yaja suka wuce.

Rayyan na tsaye gun mai credit din motar ta wuce ya bita da wani irin kallo,ya karbi katin tare da yin gaba ba tare da ya tsaya amsar canjinsa ba
"Yallabai canjinka"
"Ka riqe kawai" ya fada yana tafiya ba tare da ya waiwayo ba
"Yallabai suna da yawa fa" wannan karon bai amsa mashi ba ya wuce kawai,murna ta cika mai katin,duk da daman yasan halin rayyan din,don duk ranar daya tashi fidda zaka dukka sai kowa ya daara.

Tsalle rumana tayi ta dale raihanan duka suka zuba saman carfet,hararata tayi tana mata qorafin lattin da tayi na zuwa a makare,ta kare kanta ta hanyar gaya mata abinda ya samu motarta,saiga islaaha wadda dan ihun mamanta ya fiddota,ganin momman nata ya sanyata saukowa da gudu itama daga saman tana kiran sunan momma din,da sauri raihana ta tallafi islahan ta dagata sama ta wurga ta tacafeta suna dariya.

A tsakiya suka sanyata,rumana tace
"Oh,wai nima sai na nemi alfarma ake zuwa min,kamar ni,sisinki rabin jikinki?,ai shikenan"
"Wallahi idan kina fadin haka sai kisa ayi mana dariya,haba sisi ai kinsan dai yadda sisin naki ta zama,babu zama makaranta ma kawai ta isheka" kafin rumanan ta sake cewa komai ya shigo falon,kamar yadda ya fita yanzun ma haka ya shigo,hannayensa soke a aljihunsa yana kallon gabansa,banbancin kawai wannan karon fuskarsa a dinke take tsaf,rumana ta miqe tana cewa
"Na kammala dai yaya kafin ma ka dawo din"
"Da kyau,kinyi qoqari" ya fada yana hayewa saman,saita bishi da kallo ganin sauyawar yanayinsa lokaci guda,sai da ya qulewa ganinta sannan ta maida dubanta ga raihana tana daidaita yanayinta
"Baku gaisa bafa da ya rayyan" murmushi tayi cike da basarwa
"Kai haba,mun hadu fa a qofar gida"
"Ok,bari naje ina zuwa sisi pls minti biyar"murmushi ta kuma yi
" na qara miki goma ma ya zama sha biyar"tana dariya rumanan ta haye saman.

Islaha ta janyo ta dora saman cinyarta ta bude jakarta ta fito mata da chaculets din da ta siya mata ta fara bare mata tana bata tana shanyewa tare da zabga mata surutu tana ta biye mata.

Tana shiga da minti uku yayi sallama fa mukhtar kana ya shiga wanka,yana shiryawa ta dubeshi cikin damuwa
"Yaya amma cewa fa kayi yau muna tare fa"
"Ai mun dadu bamu kadai din bane"
"Amma yaya ai raihana" kiss ya mata saman labbanta wanda ya sanyata yin shiru,ya janye bakinsa yana ci gaba da sanya links din hannun rigarsa
"Kada ki damu,zanje naga dr mukhtar ne" kamar ba zata fada ba sai kuma tace
"Amma yaya na dade ina son gayama qorafina,kwanaki naga magungunanka na tambayeka na meye kaqi gayan,yanzu kuma kana zuwa ganin mukhtar kona tambayeka dalili ba gayan zaka yi ba,me yasa?,me yake damun mijina har haka?" Kai ya girgiza yana sakin murmushi,ya fesa turarensa sannan ya isa inda take ya dagata ya rungumeta sannan ya sanya bakinsa cikin kunnenta
"Bana so ki sanyawa ranki damuwa ko kadan kan cewa wani abu yana damuna,lafiya qalau mijinki yake my angel,pls bana so ki sake tambayata kan wannan batun tunda nasan am fine,mai lafiya ma na shan magani,da wata cuta ce kece ta farko da zata fara sani,but kawai ina ganin mukhtar lokaci zuwa lokaci ne yana min checkup,kuma kinsan hakan yana da kyau"daga haka ya zarme da gaya mata wasu sanyayan kalamai da suka ida kashe mata jiki duk da bata gama gamsuwa ba amma ranta yayi fari qal,ita ta riqe masa wayoyinsa da key din motarsa suka sauko qasa.

Da gudu islaha ta zame daga cinyar raihana ta iso gunsa,ya durqusa gabanta ya mata kiss a goshi,ta daga masa hannu tana masa byebye shima yana mayar mata
" a dawo lafiya"suka fadi kusan a tare,ya juyo yana duban ruman"iya nan rakiyar take yau?"kai ta daga tana murmushi tare da yi masa nuni da raihana.

Kallonta yayi karo na farko saidai baiga fuskarta sosai ba saboda islaha dake tsaye gabanta
"Kya gaida gidan ko?" Ya fada yana ficewa
"Zaiji" itama ta bashi amsa a hagunce kamar yadda ya mata maganar.

Hakanan yake jin wani zafi cikin zuciyarsa,bai sani ba so ne ko kishin ne?,haushin qinsa ne ko kokuwa?,ya kasa banbancewa,kawai dai yasan yana jin wani abu guda biyu cakude a zuciyarsa,saidai daya yafi daya qarfi da nauyi.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽[7/23, 12:42 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*
_____________________

*Daga ma'aqil dan yasar R.A yace:naji manzan Allah S A W yave"babu wani mutum da Allah zai bashi kula da lamarin talakawa,kuma ya mutu ranar da ya mutu alhali yana mai zaluntar talakawansa face Allah ya haramta aljanna a gareshi"*

_bukhari da muslim suka rawaito_
_______________________

*Babi na talatin da biyu*

Sai misalin qarfe tara da wasu mintina na dare ya dawo gidan.

Saman dining suka isa ta ja masa kujera ya zauna sannan ta fara sarving dinsa,ya cira kansa daga danna wayar da yake ya dubeta
"Ina islaha ta shiga ne?,tunda na shigo banji motsinta ba,hala ta gaji da jira na tayi bacci?"sai data tura masa plate din abincin tana shirin zama sannan tace
" daddy ka manta yau weekend ne,kuma wancaj satin bata je gun mammanta ba,dazu ta dauketa suka tafi"
Hade fuska yayi yana dubanta
"Da izinin wa suka tafin?" Sai tayi sakato tana dubanshi
"Amma ina cewa daddy kasan tana zuwa ko?,baya ga haka sati biyu kenan kana hana zuwan nata,me laifi a ciki don taje?,da nan da can duka ba gida bane?,me yasa nake gani ka sauyawa ne daddy?,anya lafiya qalau kake?" Sai ya basar ya ja plate din abincin ya soma ci
"Lau nake,ko dazun ba naje cheakup ba?an gaya miki ni irinki ne lanjare?"sai tayi murmushi kawai tana dubansa,komi yayi burgeta yake.

Shiru ya ratsa tsakani kafin daga bisani ya ajjiye spoon din hannunsa
" bake kikayi girkin dare ba yau"sai ta dage masa gira
"Eh sisi na ce,zazzabi ne ya dawomin dazu sai ta karba tayi kafin su wuce,nasan kuma ba wai rashin dadi yayi ba,don sisi ma ta fini qwarewa"
"Ke kikasan wannan,ni girkin matata kawai na sani" yayi maganar yana ci gaba da cin abincin,dariya ta saki sannan tace
"Wallahi yau yaya na lura rigima kake ji"
"Kuma ke zaki sauketa ba,ya zazzabin,na lura har yau yaqi tafiya baki daya,ko zaki ga likita ne?" Sai ta narke tana dubansa
"Ni kaina ya dameni wlh yaya,da ya tafi sai ya dawo
Idan bai tafi duka ba nan da next week sai naje din"
"Allah ya qara afuwa"
"Ameen" ta amsa masa

*LAHADI*

Kasancewar weekend ne tana gida,hakanan tayi niyyar zuwa duba jikin hajjaju da har yanzu yaqi dadi,gashi batason tarar rana,don haka tun qarfe ta gama hada abun karin kumallo ta dawo daki,tayi wanka ta yiwa islaha,ta musu makeup daidai,bayan ta gayar gashin yari yar ta rabashi gida biyu ta daure kowanne da ribbom,baka rasa dakinta da kayan kwalliyar yara duk saboda yarinyar,wani material ne mai tsada ta fiddo musu wanda ta bata aka yi musu dinki ita da islahan dogayen riguna,iri daya komai da komai,sai suka tashi tamkar uwa da 'ya,ta sanya mata safa da takalmanta ta kamata suka fito don su karya su wuce gidan hajjajun.

Bai wuce mintina da shigowa ba,yana falon suna gaisawa da ummu suka fito,da gudu islahan ta saki hannun raihanan tayi gunsa tana fadin
"Daddy oyoyo"shima cafe 'yar tashi yayi ya azata kan cinya suka soma gaisawa da salon shirmen islahar,sosai kwalliyar yarinyar ta masa kyau ya fidda wayarsa ya mata hoto yace zai nunawa mommy.

" ina kwana"ta fada tana giftashi ba tare data tsaya ba,kamar wanda aka toshe masa baki da tsumma ya amsa a gajarce ganin ummu na gurin
"Ummu me kika dafa yau,ban karya ba na fito"
"Garin yaya?" Ummu ta tambayeshi tana miqewa zata wuce sashen abba don taga ya gama sallar walhar da yake zasuyi magana da rayyan din
"Bata jin dadi ne matar gidan,a kwance na barota"
"Ashshsha,me ya sameta haka?" Ta tambaya tana dakatawa da tafiyar da takeyi
"Zazzabi ne kawai"
"Ai ya wuce kawai rayyan,kuyi qoqarin zuwa asibiti,Allah ya qara lafiya"
"Insha Allah"
"Ka qarasa kan teburin bani na shiga kitchen ba,nasan ba zaka rasa abinda zaka ci ba" tayi maganar tana ci gaba da wucewa.

Sai da ya bata kusan minti goma zaune kana ya miqe ya saba islaha a kafadarsa yana takawa zuwa kan dining din inda raihana ke zaune tana hadawa islaha tea tare da fifitashi yadda zata iya sha,kujera daya yaja ya zauna daga can wani sashen ya janyowa islaha daya ya dorata kai,sai ta zame ta sauko ta nufi gun raihanan,hannu tasa ta dauketa tare da dorata kan cinyarta ta soma bata tea din tare da chips da waina ba tare data daga kai ta dubeshi ba,islaha na mata gwalantonta tana amsa mata.
Chapter 41 · 0% Book details