← Book details Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 66

Sashe 63

Dangantakar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bata samu sararin tarar rumana da maganar ba sai data dauki warmers daga kitchen ta bawa zainab qanwar raihana data aiko a bata warmers ta sake musu girki saboda baqi,a balcony ta cimma rumanan tana shirin shiga falon,sai ta dubi meelan ganinta a gaggauce
"Ah,ba dai har tafiya ba?" Kai ta girgiza gami da tabe baki
"Ba tafiya zanyi ba,wani abu na gani da zuciyata ta gaza jureshi" sai rumanan ta dan sauya fuska tare da cewa
"Kamar me fa?"
Dan shiru tayi tana kallon rumana kafin daga bisani tace
"Wallahi har yau mamaki kike bani rumana,wai kishiya kikewa hakan?,kin manta kishiya ko ta'yar tsana ce sunanta kishiya?,wallahi Allah kinji ja rantse miki,tsaf na lura da take taken raihanan nan,shi yasa sam bata kwanta min ba naji na tsaneta,idan bakiyi da gaske ba kin maida hankalinki ba sai ta zamemiki qarfen qafa,wake wani son kishiya ko amince mata banda ke?,to wallahi ki sauya taku,qauna ce tasa nake gaya miki gaskiya,don bazan ga abinda zai cutar da ke ba na kasa gaya......."
"Dakata don Allah jamila" rumana ta fada cikin fushi
"Wannan itace qaunar da kike min din?,qaunar da zata saki bani gurguwar shawara wadda banu komai cikinta sai wahala?,shin kin manta tun kafin ki sanni raihana ta sanni?,kin manta tun kafin ki fara qaunata raihana ta fara qaunata?,bari kiji,ko bansan raihana ba ayadda halayyarta take bazan iya cutar da ita ba,sau nawa ma jamila ina gaya miki ki fidda idonki kan zamantakewata da 'yar uwata?,kinsan me raihana ta yimin a rayuwa?,kinsan cewa da raihana muguwa ce da tuntuni ta jima da tarwatsa rayuwata cikin ruwan sanyi ba tare da na san cewa ita ta aikata hakan ba?,bakisan cewa da raihana taso kanta ba da tuni bani a kan bigiren da nake kai yanzu?,kin qureni jamila.....kin qureni,abu daya nakesom sanar miki,daga yau babu ke babu rumana,sai hali yazo daya ake abota ko,to ta wannan fannin halayyarmu tasha banban sabida haka qarshen qawancenmu yazo".

Cikin jin haushi meela ta dubi rumana
" au,don ina gaya miki gaskiya?,to shikenan,basai kin koreni ba,daga yau ba zaki qara ganin fuskata ba,kuma duk abinda ya sameki nan gaba kiyi kuka da kanki tunda baki daukar shawara...."
"Babu abinda zaya samesu sai alkhairi,kuma ko baki fadi haka ba bazan sake barin wata cikin mata na taga wannan fuskar taki ba,ballantana ta saurari mugunyar shawara daga wannan masharrancin bakin naki ba,wannan ta zama rana ta qarshe da zaki sake biyowa koda ta layin gidan nan ne,idan kuma kinqi ji bakya qi gani ba" suka ji muryar rayyan cikin kaushi zafi da bacin rai yana fada,gaban meela ya fadi jikinta ya dauki qarma,ba shiri ta rabasu ta wuce qafa na rawa da gaggawa ta fice daga gidan.

Sai da yaga ficewarta sannan ya qara taku ya iso inda rumana ke tsaye,ya dubeta qimarta na dada qaruwa cikin ransa,dattakonta na sake ninkuwq haka nan qimar iyayenta na sake hauhawa a idanunshi,sai kawai ua janyota jikinsa ya rungumeta,cikin taushin murya yace da ita
"Allah yayi miki albarka,ya baki aljanna,ba shakka da za'a samu uwayen gidan irinki da gidan aure ya zauna lafiya,don Allah ruma ta kada ki yarda da zugar qawaye ko misqala zarratin,yawancinsu basu da burin da ya wuce suga sun haifar da tashin hankali a gidajen auren qawayensu,pls rumana kimin alqawari....." Sai ta dago tare da dora yatsanta saman lebansa
"Kada ka roqeni daddy,nasan kaina,nasan wace raihana hakanan nasan waye kai,ka manta cewa dukanmu mu ukun AMINAN JUNA NE?,DANGANTAKAR ZUCINMU kuma Allah ne ya ginata ba mutum ba?DANGANTAKA CE tun quruciya,duk katangar da ubangiji ne ya ginata kuwa ba wanda ya isa ya rusata,na godewa Allah da ya sa ka zamanto adalin miji a tsakaninmu,soyayya bata rufe maka ido ka wancakalar da haqqin wata daya a kan 'yar uwarta ba,na kuma sake godewa Allah da ya sanya na samu sisi na fiye ma da yadda nayi zato,wannan kawai ya isheni"
"Allah ya albarkaceku,ya muku sakayya da aljannatul firdaus" ya fada yana sake matseta cikin jikinsa tare da bata kiss a goshi.

Yadan rabata da jikinsa yana dubanta
"Baqi sun hanani sakat my angel,yunwa nakeji a bani abinci naci na koma cikinsu"
Hannunshi ta kama tana cewa
"Muje na rakaka gun sisi na kaci acan,dutynta ne,kuma na tabbata ta tanada maka kalar abincin da kake so" yana biye da ita yace
"Iyeee,wato ke ba zaki iya da ni ba,matan nan fa na fahimci ma ball kawai kuke da ni,kowacce so take ta nunan 'yar uwarta ta fita,haka jiya raiha ta yimin saura kadan na zaneta da tsintsiyar kwakwa" ya qarashe maganar nayan wani cin magani kamar gaske,harara ta watsa masa sanda suka isa bakin qofar falon raihan
"Kai kama fara dukanmin sis?,wlh da mun maka yaji dukanmu ka zauna kai daya" wata dariya ce ta kamashi har sai da ya qyaqyata har da 'yar qwallarsa,saiga raihanan ta fito tayi kuwa biji biji da alama tasha girki
"Yauwa gashinan sisi ki bashi abinci yaci" kai itama ta langwabe
"Haba sisi babu 'yar kara ma,maimakon ki karbeni ni da na fito daga kitchen yanzu dubi jikina fa?" Sai rayyan ya dubesu yana bata rai
"You see,yanzu na gama fadi qwallo kawai kuke da ni,idan abincin ma baza'a bani ba basai na haqura ba"da sauri suka kama kunnuwansu raihana tace
" tuba muke yallabai mun mun isa"ya wani dake shi bai yarda ba fushi ya rabe raihanan yana wucewa ciki tare da fadin
"Dadin abun ai zan iya sake kawo wata,idan kuna abinku na tafi wajenta nasan ita ai tana maraba da ni"
"Kambu,wallahi ya rayyan mafarki kake,mu kadai aka haifa maka na gaya ma gaskiya"
"Barshi sisi" inji raihana tana hararan bayansa kana ta juya ta bishi.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[7/23, 12:54 PM] El-hajj💥: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
*NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*

*wattpad:huguma*

*©haske writers asso💡*
*(home of expert and perfect writers)*

_____________________
*Daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace"Allah madaukakin sarki yana cewa,ni ina tare da bawa na matuqar ya ambaceni,kuma labbansa suka motsa saboda ambatona"*

_imam bukhari ne ya rawaito_
_______________________

*Babi na arba'in da bakwai*

Zama ne suke mai cike da aminci ban sha'awa gami da qayatarwa,kowacce na iya nata bakin qoqarin wajen ganin ta kyautatawa 'yar uwarta,ta boye damuwarta,ta kaucewa abinda zai taba ran 'yar uwarta,hakanan kowaccensu na qoqari matuqa wajen ganin ta kyautatawa yayan nasu kuma mijinsu rayyan,wanda ko da yaushe cikin yabawa matan nashi yake,ko da yaushe cikin godiya ga Allah da kuma godiya ga iyayensa yake,wani lokaci idan suka shagwabashi da yawa yakanji tamkar babu yashi duk cikin fadin duniya.

Sau tari wadanda basu sansu sukan qaryatasu idan aka gaya musu cewa abokan zaman juna ne,kamar wani lokaci da rumana ta sake bari,taji jiki sosai raihana ke jinyarta,wata mata dake kusa da dakinsu take nuna sha'awar yadda raihanan ta damu da lalurar rumanan,tana yaba yadda take kula da ita,tace da alama 'yar uwar nan taki ita kafai ke gareki ko,qirji ta dafe gami da qwalalo idanu sanda raihana ke gaya mata yadda suke
"Amma gaskiya da alama yarinya quruciya ke dibanki,waye ya gaya miki ana yiwa kishiya hakan?,kinsan ma me kishiya ke nufi kuwa,tun wuri ki rufawa kanki asiri ki janye rawar qafar da kike akan wata aba wai kishiya,ba amana tsakaninku har abada" wani banzan kallo raihanan ta yi mata,baqincikin da ya tokareta ya hanata cewa matar komai,bugu da qari kuma dama can ba mai surutu bace sabida haka sai ta tashi kawai ta barwa matar gurin,bata sake yarda sun hada inuwa ba har suka baro asibitin.

****************

Yau da gobe ta Allah ce,a hankali rayuwa ta dinga tafiya musu yadda ya kamata,dama hakan take,ita rayuwa duk yadda ka dauketa haka take zuwa maka,idan ka debota da zafi bakinka ne,idan a sanyaye ka daukota ka hutama ranka,sannu a hankali rayyan ya rabata cire mata sha'awar zuwa aiki,ga 'yar kanzaginsa a gefe rumana,babu haufi ta tattara aikin ta ajjiye shi gefe,ta tattara hankalinta kacokam kan kula da mijinta gami da tattalinsa,wanda zuwa lokacin ta tabbatarwa kanta cewa rayyan din saboda shi aka halicci zuciyarta,shine rayuwarta,taso ta zalunci kanta da zuciyarta ma baki daya da taso fifita DANGANTAKAR ZUCI akan ta FILI DA GANGAR JIKI.

_*8:30 pm ado bayero mall zoo road*_

A hankali kowane daya cikin iyalin mai cike da ban sha'awa ke zagayawa cikin makeken kantin yana zabar abinda yake so,wadanda sukayi qanqanta cikinsu suna tare da yayyensu da suka fisu hankali,duk da suna yin hakan lokaci lokaci amma na yau din na musamman ne,saboda maamaa(raihana)zata kwashesu ne da zarar sun samu hutun qarshen zangon karatunsu sai maiduguri wanda dama lokaci bayan lokaci tana tafiya da su suyi hutu na mako daya ko biyu haka suke,wannan kuma yazo daidai da bikin zainab qanwarta.
Chapter 63 · 0% Book details